Showing 228001 words to 231000 words out of 332344 words

Chapter 77 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

30871

kasa gane abinda take so ta ce. Ya ce, "Jidda meye na kukan? Ki faWa min meye a cikin na ki?." Ta kalle shi ta goge idanunta ta ce, "Ka tambayi Didi." Bai yi ?asa a guiwa ba ya kira Didi kai tsaye ya saka a speaker, tana Wauka ko gaisawa basu yi ba ya ce, "Meye a cikin Jidda? Ta saka ni a gaba tana kuka, wanne ciwon ne a ciki?."

Didi ta yi dariya ta ce, "ita bata faWa maka ba?."
"Inda ta faWa ai bazan kira ki ba."
"ciki ne da ita Omar." Omar ya wara ido ya ce, "bana son wannan wasan da ki ke min Didi."
"Ba wasa bane Omar da gaske ne, in zaka tuna lokacin da na ce maka na rakata asibiti ai cikin aka tabbatar mana dashi, ta ce kar na faWa maka ne shiyasa na yi shiru."

Cikin ruWewa ya ce, "Wai da gaske ki ke?."
"Wallahi da gaske nake Omar, kaima ka kusa zama uba." ?it ya kashe wayar ya cilla ta kan kujera ya zubawa Nayla ido yana kallonta ya rasa wanne irin farin ciki zai yi. Nayla ta goge idanunta ta ce, "Likita ya ce duk abinda nake yi shine yake sakawa. Rouhi ina kewarka nima, amma ban san ina barin ka ba sai bayan na yi."

Shi ba ta wannan yake ba a lokacin, ya mi?e tsaye ya ri?e hannunta ta mi?e itama ya kalli cikinta ya kalle ta ya ce, "yanzu da gaske kawai Wana a nan Jidda?" Ya faWa yana Wora hannunsa akan cikinta. Nayla ta Waga kai alamun eh ya jawo ta jikinsa ya rungume ta yana cewa, "Alhamdu lillah, Allah na gode maka, ashe nima zan ga wannan rana Jidda?. Kina da ciki fa, cikina ne a jikinki, zaki haifi yaro ko yarinya. Jidda na kasa sarrafa farin cikin da nake ciki, na kasa ri?e kaina..." ya faWa cikin ruWewa yana shafa bayanta.

?agota ya yi daga jikinsa ya Waga rigarta yana kallon cikin ya kalle ta ya ce, "yanzu a nan akwai Wana?." Sai ta yi dariya ta ce, "Da gaske akwai." Ya sumbaci cikin nata ya Wago yana ?are masa kallo kamar bai kallon wani abu, ya zube guiwarsa a ?asa ya sake yin kissing cikin tare da tsotsar fatar jikinta cikin tsananin farin ciki. Mi?ewa ya yi ya kalle ta ya rasa abinda zai ce mata. Kisses yake yi mata a ko ina, fuskarta wuyanta da duk inda ya yi masa. Ta lura ya kasa magana a ruWe yake, ya ri?e hannunta amma ya rasa abin faWa.

"Jidda kin karSi ajiyata shine ban sani ba? Jidda meyasa baki faWa min ba?."
"nima ban sani ba, sai lokacin da mu ka je asibiti da Didi akace na sati huWu ne."
"Ya Salam! Jidda yanzu ya kai sati biyar kenan ko shida? Jidda Wana yana cikin ki har wannan kwanaki ban sani ba, Meyasa baki faWa min ba?."

Nayla ta ce, "ina so na baka mamaki, kuma ina so naga farin cikin da zaka yi, in kana can bazan gani ba." Sake mayar da ita jikinsa ya yi cikin tsananin farin ciki yana cewa, "Na gode Jidda, na gode da ki ka karSi ajiyata Jidda. Na rasa me zance miki, na rasa me zan ce da zan nuna miki ina cikin farin ciki Jidda...." Lumshe ido Nayla tayi cikin jin daWi, kafin ta ji ya ce, "Yanzu me ke so?" Ya faWa yana Wago ta daga jikinsa yana kallon ta fuskarsa ta kasa Soye abinda yake zuciyarsa.

Ita Nayla tausayi ma ya bata, duk da kewar ta da yake ciki amma farin cikin samun ciki ya kore ta, ta san yana cike da kewarta da kwaWayin kasancewa sa ita, amma maganar ciki ya kore wancam batu. A sanyaye ta ce, "Babu komai Rouhi." Ya girgiza kai ya ce, "A'a ki faWa min, ki faWa min meye ki ke so Jidda zan kawo miki. Ki faWa min don Allah, kar ki ce babu komai, ki faWa ina jiranki." Nayla ta ce, "So nake ka yi ha?uri, ka daina fushi dani."

Ya zaunar da ita ya tsuguna gabanta ya ce, "ki daina faWa ni bana fushi dake, in ma ina yi na daina duk abinda ya faru ai Wana ne silar faruwar shi. Shine yake wahalar min dake ni kuma na kasa fahimta, ki yi ha?uri kin ji? Ki bawa Wana ha?uri shima." Nayla ta shafa fuskarsa ta ce, "Ka nutsu Rouhi, cikin Wanka ne fa, ka nutsu don Allah, duk ka koma wani iri."

"Kyautar Wa fa Allah ya bani, ciki ne dake Jidda, dole na fita a nutsuwata." Nayla ta ce, "ka dai nutsu ka ji." Ya zuba mata ido kawai yana kallonta yana jin sabuwar soyayyarta na shiga zuciyarsa. Ya ri?e hannunta ya ce, "na rasa me zan ce miki, amma ina so ki san na gode, na gode, na tabbatar da ?aunarki a gare ni mai yawa ce ba kaWan ba. Tunda har ki ka iya Waukar cikin Wana ban san wacce irin soyayya ki ke yi min ba. Na gode Ashiq, ina sonki, ina ?aunarki."

Murmushi ta yi ta ri?e hannunsa duka biyun ta ce,"nima na gode da ka zaSe ni ka mayar dani uwa a wajan Wan da zamu haifa." Murmushi yayi ya sake Waga rigarta yana shafa cikinta ya ce, "ni yanzu me ki ke so ki ci? Akwai abinda ki ke so?." Nayla ta ce, "bana son komai, so nake ka zauna a tare dani na yi bacci a jikinka." Da hanzari ya dawo kusa da ita ya zauna ya kwantar da ita a jikinsa ya ce, "Koda maciji zai sare ni bazan motsa ba sai kin tashi, ki ji bacci na adadin awannin da ki ke so, ni mai gadin ki ne" ya faWa yana sake kwantar da ita a jikinsa.

Nayla murmushi take yi, duk yadda take hasashen yanayin da zai kasance abin ya wuce haka, ya kasa ce mata komai jikinsa har rawa yake yi saboda murnar tana da ciki, lallai ta yarda da maganarsa da ya ce yana son yara dan yanzu ta tabbatar da hakan.

Tun daga ranar Omar ya amsa sunan mai gadin Nayla, babu abinda yake barinta tayi shi yake yi mata da kansa, baya so ya ga ta motsa saboda kar wani abun ya samu cikin ta gabaWaya hankalinsa na kan cikin duk ya rikice. ?angaren harkokinsa komai yana tafiya yadda ya kamata, an fara aiki an kuma tura da takalma China, an kuma samu kyakykyawan feedback akan hakan.

? ?? Kamar ko yaushe suna zaune a falo yana matsa mata ?afa kamar wacce cikin ya tsufa ya ce, "kina ji." Ta kalle shi dan ta san labari ne ta ce, "ina ji."

"Wani mail na samu tun farkon dawowa ta, sai ban mayar da hankali a kai ba saboda ban Wauka na gaske bane. Sai Wazu aka kira ni aka tabbatar min da na gaske ne, shi mutumin ma na ganshi ido da ido kuma na tabbatar da gaske Win shine."

Nayla ta ce, "meye kenan?." Ya kalle ta ya ce, "Saboda nasarar da na samu, kuma ni ne na farko a Africa da China suka fara aiki dashi shugaban ?asa ne yake son ganina, an bani appointment gobe monday in sha Allah zan je." Nayla da hanzari ta ce, "da gaske.?"
"Da gaske nake." Nayla ta buWe ido sosai ta ce, "Rouhi president fa...." Ya Waga mata kai alamun eh, ta ce, "Rouhiii wannan ai abin farin ciki ne, ni wallahi na rasa ma me zan ce."

"Kar ki yi farin ciki da ya yawa kar ya shafi abinda yake cikin ki, ki yi kaWan." Ta harare shi ta ce, "yanzu ba ta ni ka ke yi ba ko?."
"Ni na isa." Nayla tayi dariya ganin yana murmushi shima ta ce, "Rouhi zan bika Abujan." Ya kalle ta ya ce, "Da kina tunanin a nan zan bar kii? Ina zan iya zuwa na bar rai biyu a gida? Tare da ke zamu tafi." Tayi murmushi ta ce, "Yauwa Rouhina." Murmushi ya yi ya ce, "da safe zamu tafi, tashi mu je ki kwanta." Bata musa ba ta tashi suka kwanta kamar ko yaushe babu komai a tsakaninsu sai dai baccin.

Ranar ji tayi a zuciyarta ko me zai faru sai dai ya faru amma ta gaji da ganin mijinta a wani hali, cikin ikon Allah kuma bata ji abinda take ji ba sai ma kuka da take yiwa mijinta ganin yadda ya rikice mata jikinsa yana rawa sosai. Ya bata tausayi ta kuma san ya yi ?o?ari ri?e kansa sosai, shi kuma sai daga baya ya fahimci abinda ya faru duk hankalinsa ya tashi kar wani abun ya samu babynsa. Naylan ce ta dinga kwantar masa da hankali tana cewa babu abinda zai faru sannan ya nutsu ya jawo ta jikinsa suka yi bacci. Kamar yadda ya ce washe gari da safe suka wuce zuwa Abuja.
KRB3P086
Nana haleema.

? ?? A hotel suka sauka Nayla a gajiye take kamar wacce tayi tafiya zuwa wata ?asa, ana yin sallar azahar ta yi bacci bai tashe ta ba ya shirya ya fita dan lokacin da aka bashi saura awa Waya. Har inda yake aka zo da mota za a tafi dashi, Omar sai a lokacin ya ji tsoro a zuciyarsa kar a sace shi. Addu'a ya dinga yi a zuciyarsa abin mamaki sai ga su a villa road. Da aka shiga villa ya ga yadda ake tafiya zuwa ciki a nan ya tabbatar da gaske shine a fadar shigaban ?asa ba ?arya ba ce.

?? Shugaban ?asa ya girmama shi sosai, sun gaisa, sun zauna sun tattauna an yi musu hotona kafin a ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????Wauko shi a dawo dashi har inda aka Wauke shi. Omar ya kasa Soye farin cikin da yake zuciyarsa, sai furta alhamdulillah kawai yake yi dan Allah ya yi masa abinda bai yi zato ba.

A haka ya dawo hotel Win da suka sauka, yana buWe Wakin Nayla ta mi?e tsaye ta kalle shi shima ita yake kallo da murmushi ta ce, "Daga yin bacci sai ka gudu?." Ta danna wayar ta haska masa hoton da ake ta posting ta ce, "sai hoton ka na gani."

Takowa ya yi a hankali ta ?araso inda take ta shiga jikinsa ta rungume shi ta lumshe ido ta ce, "Meyasa baka tashe ni da zaka tafi ba?."
"Ba a tashin mai ciki in tana bacci."
"In ji waye?."
"In ji Hajja, akwai wani lokaci da na ji ta ce haka." Murmushi ta yi ta kalle shi tana kallon fuskarsa ta ce, "So i just want to know the gist, what's been happening in the villa?."

Kiss ya to mata a goshi ya ce, "I didn't understand what you said, can you explain what you mean in Hausa?." Hararar wasa ta yi masa ta ce, "I will never continue take this kind of? disrespect from you. You know how to speak English." Murmushi ya yi ya ri?e fuskarta ya ce, "Yeah, but small small." Dariya ta yi ya ja hannunta suka zauna ta ce, "faWa min, ina ta so na ji me ya faru ka sanar dani."

Shi kallon fuskarta ma kaWai farin ciki yake bashi, balle in ya tuna tana da ciki sai ya ji kamar Allah ya gama yi masa komai a duniya. Kallon ta ga ya yi yawa ta ce, "Rouhii i'm waiting." ?an buWe ido ya yi ya ce, "ya kira ni ne dan ya saka bani ?arfin guiwa, kuma kin san mene....? ya yi mamaki da ya ganni, ya yi tunanin zai ga babban mutum irin wanda ya girma sosai sai ya ganni a yadda nake. Ya ji daWi sosai, babban abinda ya burge shi ma yadda na kasance mutum na farko africa da ya samu wannan dama..." ya yi shiru bai ?arasa ba yana kallon ta.

Ta girgiza hannunsa ta ce, "ka cigaba mana." Ya ce, "Ya yi murna sosai, Wan Africa, Wan nigeria, musulmi, Bahaushe kuma Wan kano. Abin ya yi masa daWi sosai, especially da ya tambayi qualification Wina na ce masa I haven't done even the secondary school, he was so excited and surprised about that. Mr president ya ce duk abinda nake so ko nake bu?atar wani abun the door is open for me, zan iya tambayarsa duk abinda nake so a kuma duk lokacin da nake so. Ya girmama ni sosai Ashiq, ko iya haWuwa dashi da nayi babbar girmamawa ce a gare ni, amma yadda ya yi min Win ne zaki yi mamaki sosai."

Nayla ta yi murmushi ta ri?e hannunsa ta ce, "i'm so proud of you, bani kaWai ba gabaWaya nigeria suna alfahari da kai, yau social media a kan ka ake magana. Rouhii abin alfahari ne a gare ni, abin farin ciki ne a gare ni sosai, kana ganin shugaban ?asa ma yana alfahari dakai."

"Nima ina alfahari da samunki, kin san me ne?." Ta girgiza kai ya Wauki wayarsa yana dube-dube ya nuna mata ya ce, "?an mata suna damun mijinki da dms." Nayla ta kalla ta kalle shi kafin ta karSi wayar, bata buWe ko wanne ba duk tayi deleting ta yi blocking ta kalle shi ta ce, "Wannan shine abinda bana so, shiyasa yau sam ban shiga comments section ba dan zai iya sakawa zuciyata ta buga."

Bai ce komai ba ta kalle shi ta ce, "Ko dai zaka yi deleting handles Winka? Ya aka yi ma suka san handle Win ka da suke tag Winka in sun yi posting?. Gaskiya ka faWa musu a daina tag Win account Winka." Murmushi ya yi ya ce, "To."
"Dariya ma na baka ko?."
"A'a, burge ni ki ke yi, in kina kishina ina jin daWi sosai." Bata ce komai ba ya ce, "Ki manta kawai, this means nothing to me" ya faWa yana fara shafa cikinta kamar yadda ya saba.

Ta kalle shi ta ce, "Didi ta sani?." Ya Waga kai ya ce, "Ta kira ni, tana ta kuka." Murmushi Nayla ta yi ta ce, "Dole ta yi kuka, itace mutum ta farko da zata fi ?aunar cigaban ka a rayuwa." Murmushi ya yi sosai yana kallon cikinta yana tuna wacece Didi a gare shi, ya ce, "Hajiya Didi, ina so ta yi dariya da farin ciki sosai a rayuwarta." Nayla ta ce, "ta cancanci hakan. Yaushe zamu koma?."

Ya kalle ta ya ce, "Sai gobe in sha Allah."
"Allah ya kaimu."
"Amin." Hira suka cigaba da yi akan abinda ya same su cikin farin ciki da jin daWi.

? ?? " " " " " " " "

? ? ?? Narma tun bayan da ta ga Omar a airport ya nuna ba shi bane gabaWaya bata cikin hankalinta, ta koma wata iri har da kwanciya zazzaSi duk ta ruWe. Mum suna zaune ita da Dad da Najwa harda ?awarta Safna a Wakin ta tana zaune bata tea tana sha.

Dad ya kalli Safna ya ce, "Safta da gaske Omar ne?." Safna ta ce, "i'm not sure Dad, because the way he looks....his dress, his face and everything is different from that thug. But ta dage shine, ni ban san me zan ce ba." Dad ya yi ajiyar zuciya kafin ya yi magana Najwa ta ce, "Dad kalli nan" ta faWa tana nuna masa wayarta.

Kallon wayar ya yi yana kallon Omar da Mr president sun yi shaking hand, ga yanayi na farin ciki a kan fuskarsa. Zooming fuskar Omar ya yi yana kallo kamar tiger kuma kamar ba shi ba, Najwa ta ce, "shine wanda take magana a kai." Dad ya mi?awa Safna wayar ya ce, "wannan ne wanda ku ka gani a airport?." Safna ta ce, "yes Dad shine."

Narma ta ce, "Dad can I see?." Bai musa ba ya nuna mata ta yi wata ajiyar zuciya ta ce, "Wallahi he's my Faruk, Dad ka kalla da kyau zaka gani." Mum ta karSi wayar tana kalla ta kalli Dad ta ce, "How come that useless man has been taking picture with president? You have to think about this. Maybe me kama dashi ne amma ba shi ba." Narma ta ce, "Mum, Dad, wallahi shine, Ni na san shi ai ko? To wallahi shine, if not ku saka a bincika muku zaku tabbatar."

Dad shima dai yana ganin fuskar Tiger akan fuskar wannan Omar Win, ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Don't worry my dear, i will find it for myself."
"Dad if you find him and you are sure that shine, can you allow me to marry him?." Dad ya kalle ta kamar yadda take kallon sa ya ce, "Let me find it first."
"Dad ka amsa min..."

Dad ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Yes, zan bar ki aure shi." Dariyar farin ciki ta yi ta ce, "Thank you my? Dad." Mum fita tayi daga Wakin saboda haka Dad ya bi bayanta, ya same ta a Waki ta kalle shi ta ce, "meyasa ka ce mata haka? Do you mean you will let her to stay with him..useless man?." Dad ya ce, "Calm down, na san abinda nake yi fa, but I have been seen the face of Tiger in this picture."
"Okay kaima ka yarda shine?."
"I'm not saying that, but ina da bu?atar na nemo abinda yake faruwa."

Mum ta ce, "okay... just imagine as he's, zaka yarda ta aure shi?." Dad ya ce, "why not? Shine fa mutum na farko da ya yi signing contract da ?asar China, kin san nawa ake samu in aka haWa kai da ?asar waje kuwa?. Kina ganin yanzu ya je ya ga Mr president, waye zai ?i irin wannan ya zama inlaw Winsa?."

Mum ta ce, "Dalilin da ya saka nace ba shi bane ba ai, ina ya ga ilimin da zai zama haka?." Dad ya ce, "shiyasa na zama so confuse nima, ina ya ga ilimi da zai zama haka a rayuwarsa?." Mum ta ce, "ya dai kamata ka yi tunani" tana faWa ta fita ta bashi waje. Ya sake kallon hoton Omar yana sake ?are masa kallo, tabbas kamar Tiger Win da ya sani a baya kamar kuma ba shi ba.

? ? ?? " " " " " " "

Dawowa su daga Abuja abubuwa suka cigaba ya da gudana a tare da Omar da masana'antarsa, mutane daga ko ina zuwa suke


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login