Showing 300001 words to 303000 words out of 332344 words

Chapter 101 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14401

ni mai ri?e mata Marmerh ce, balle kuma jininta nake aure. KarSar Marmerh da ka yi shine daidai, tunda mahaifinta ya amince ina maraba da zuwan ta. Allah ya bani ikon kula da ita, Allah ya bani ikon yi mata tarbiyyar da Didi zata yi alfahari da ita a ranar lahira."

Ya ?an?ame hannunta yana girgiza kai tare da cize baki ya ce, "Amin Jidda, na gode, na gode Jidda. Na gode da soyayyar da kike yiwa Didi da zuciyarki da gangar jikinki, Allah ya saka miki da alkhairi."

Murmushi ta yi ta ce, "Amin ya rabbi. Ka daina gode min don Allah, Marmerh ?ata ce, Didi kuma Yayata ce. Ina ?aunar Didi har zuciyata, ina ganin girmanta, ina jinta kamar jinina. Bani da mai bani shawara sai ita, ko Sata min rai ka yi ita nake kira ina kuka na faWawa, ta bani ha?uri ta kuma bani shawarar yadda zan yi, bata taSa kallona a matsayin matar ?aninta ba, ko yaushe kallon ?anwarta take yi min. YaMar nayi babban rashi a rayuwata, ba kai kaWai ka rasa Didi ba har dani."

Ya yi murmushi ya ce,  daman ta ce min sai ta riga ni mutuwa, daman ta ce min tana so ta bar duniya kafin na rigata, saboda tana so ta barwa Marmerh ni a duniya. Huhhh..ashe haka Allah ya tsara, zata bar duniya ta bar Marmerh a hannuna.

Nayla ta bishi da kallon tausayi, gabaWaya ya canja mata kamar ba shi ba, yayi sanyi da rauni kamar an canja masa halayya, ko a kamanni ya canja gabaWaya. Sanyi da raunin da Didi take fatan gani a tare dashi sai da ta bar duniya ya bayyana.

Nayla ta ce, "Daman ba ta ce maka ka daina faWa akan cikin jikina ba, har ta ce maka ka yi addu'ar Allah ya ingnata cikin ba?. Har ta ce baka da tabbacin zai zauna ko?. Huhhh YaMar cikin fa ya zube, amma wallahi..." dakatar da ita ya yi ya ce, "Kar ki rantse, koda zubar dashi ki ka yi da kanki na yafe miki balle kema baki san ya fita ba. Tashin hankalin da kika shiga har cikin jikinki ya fita ya tabbatar min ba ?aramin matsayi Didi take dashi a wajanki ba."

Ta ce, "bayan kun fita daga Wakin asibiti ku ka bar mu ka san me ta ce?." Ya girgiza kai a sanyaye, ta ce, "Ta ce in na haifi mace a saka sunan Hajja, in namiji a saka sunan Abiy. Sai nayi dariya ban Wauka wasiyya take bar min ba" ta faWa murya na rawa sosai ta kuma cewa, "na ce mata in ?an biyu ne fa, ta ce in duka mata ne a saka sunana dana Hajja, in kuma ne maza ne a saka sunan Abiy da sunanka" ta faWa tana kallon idanunsa.

Nayla ta ce, "ina ta dariya a lokacin ban Wauka wasiyya ba ce, ta kalle ni ta ce kana sona sosai, nima na ce ai nima ina sonka. Ta yi dariya bayan ta yi salati ta kalle ni ta ce itama tana sonka ba ni kaWai ke sonka....." Nayla ta faWa tana kwantar da kanta a ?irjinsa tana kuka. Ido ya lumshe yana shafa bayanta. Nayla ta ce, "ashe ruwan da na bata ruwan ?arshe ne, ta ce min kamar bata sha komai ba ashe na ?arshe ta sha a duniya."

Bayan ta yake shafawa a hankali ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Mun yi babban rashi, Allah ya gafarta mata, Allah ya lulluSeta da rahamarsa. Tabbas Allah baya barin wani dan wani ya ji daWi, da ace hakan na furuwa da Allah ya bar min Didi a duniya ko dan maraicina. Duk da wahalar da ta sha dani sai Allah ya karSi rayuwarta ya bar ni a duniya, sai da ta zama silar shiryuwar halayema sannan ta tafi ta bar ni. ?ar halak kenan!.

Nayla ta amsa da amin, tana jingine a jikinsa har lokacin kafin ta Wago ta kalle shi ta ga ita yake kallo. Kallon ?afarsa da hannunsa ta yi, sai ta mi?e ta ?arasa wajan drawer ta Wauko nail cutter ta dawo ta zauna kusa dashi, gyara masa farce take yi tana yi tana hawaye. Sai da ta gama ta fita zuwa falo wajan Umma.
P118

Ranar Omar da Marmerh ya kwana a kusa dashi, hannunsa yana jikin ta cikin kewar mahaifiyarta. ?aunar Marmerh yake ji fiye da komai a duniya, ji yake a baya ba sonta yake yi ba, sai yanzu yake yi mata asalin so.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin alhinin rashin Didi, Omar bai dawo daidai ba, yana ?o?arin karSar ?addara ne amma wani lokacin yana gazawa. Haka zai zauna a Waki yayi kuka son ransa sannan ya daure ya cigaba da harkokinsa. Ya rame, ko baccin kirki baya samu balle abinci, kullum cikin tunani da kallon hoton Didi yake. Sai da aka sake yi masa hoton ?irjinsa saboda nauyin da yake yi masa aka sake bashi magani.

? ? Kamar yadda burin Didi na ?arshe ya kasance Omar ya cika mata shi, gidan danginsu na uwa da uba babu inda bai je ba. Baba Adamu da Kawu Sulaiman godiya ya dinga yi musu akan gida da kayan Wakin bikin Didi. Farin ciki suka dinga yi ganin Omar a gidajensu kamar ba shi ba. Ya sake yana girmama kowa, babu Waurarriyar fuska balle tsawa ko masifa.

Tun daga lokacin ya zama Wan dangi, wannan ya kira shi wannan ya kira shi. Girmamasu yake yi kamar yadda Didi take yi, kuma ya basu matsayin iyayena zuciyarsa. ?an uwansa wanda basu san shi ba yanzu duk sun san shi, cousins maza da mata duk sun karSi number Omar ana gaisawa.

? ? Omar ya zama mai sanyi, duk wannan hargagin nasa da faWa babu, magana ma sai ta zama dole yake yi balle har ka ga Sacin ransa. Kamar yadda Didi take yawan tambayar abinda zai saka shi yayi rauni amsar ta bata bayyana ba sai bayan babu ranta, ashe rashinta shine raunin Omar. Ko yaushe Marmerh tana kusa dashi, hatta bacci a kusa dashi take yi. Yadda yake nuna ?aunar Marmerh ?arara baya nunawa Musliha, baya iya Soye ?aunarta da kewar mahaifiyarta da yake ji a zuciyarsa.

Tsohon gidansu na kusa da gidan Hajja ya saka aka rushe gabaWaya, aka siyi gidajen da suke kusa da gidan aka tayar da ginin babbar islamiyya wacce za a dinga karatu da komai kyauta. ?angaren ha?a ruwa, siyan abubuwa da za a iya yiwa mamaci gata dasu Omar ya yiwa Didi babu adadi, fatansa Allah ya kai ladan kabarinta. Duk wannan hidimar kafin Didi tayi kwana arba'in ya yi su, har lokacin bai ji a ransa ya yi mata abinda zai wadaceta a kabarinta ba.

Ranar da ta kwana hamsin da biyu a kabari, suna zaune da Nayla da Marmerh da Musliha kamar ko yaushe. Omar ya yi shiru ya jingina da kujera yana kallon sa, Musliha tana kwance a ?irjinsa, Nayla tana zaune a gefensa ita da Marmerh da take ta game a waya. Nayla ta bishi da kallo, sai su kwashe awa Waya a haka indai ba ita tayi magana ba bazai ce komai ba, ya takure rayuwarsa sosai, ya koma zaman kaWaici ba ko yaushe yake yin magana ba. Gani yake kamar farin ciki da walwalarsa ta tafi, gani yake tunda ya rasa Didi murmushi ya ?are a rayuwarsa.

Kowa ya san shi aka yiwa mutuwa, duk wanda zai yi kewar Didi a bayansa yake, shiyasa ya koma kamar ruwa ko yaushe ciki bin ?asa yake yana kwanciya. Shiyasa dangi da ????? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?an uwa suka dage da yi masa addu'a, dan lamarin nasa sai an haWa da ro?on Allah. A ranar ne ya sakko daga sama ya zauna a falo, amma kullum yana sama, saman ma a cikin Wakinsa.

A sanyaye ta ce, "YaMar." Ya sauke kai ?asa ya kalle ta bai amsa ba, ta langwaSar da kai ta ce, "tun Wazu nake magana baka ji." Ya gyara zaman Musliha a jikinsa ya kalle ta ya ce, "Ban ji ki ba."
"Ta ya zaka ji ni kana tunani?." Ya sauke numfashi bai ce komai ba. Nayla ta ce, "Ka cigaba da ha?uri, kar tunani ya jawo maka ciwo. Kaga likita ya ce dole ka cire damuwa, jininka ya?i dawowa normal, sannan ga ciwon kan da ka ke fama dashi. Nauyin da ka ke ji a ?irjinka shima ance damuwa ce, in baka yi ?o?arin kawar da ita ba zata jawo ciwo babba" ta ?arasa faWa a sanyaye tana kallon sa.

Ya kalle ta suka haWa ido ya ce, "Kin taSa rasa wanda ki ke so Jidda?." Nayla ta kalli idanunsa ta ce, "Na rasa mahaifiyata, na rasa Didi." Yayi murmushi ya ce, "Mahaifiyarki daman baki rayu da ita ba, kai tsaye zan iya cewa baki santa ba. Baza ki Worar da zafin rashin wanda ka ke so a kanta ba. Duk da mahaifiya ce, ko baka tashi ka santa ba rashinta yana taSa zuciya. Nima ban san tawa mahaifiyar ba, amma ina jin zafin rashinta a kusa dani." Nayla ta bishi da kallo ganin yana Wan murmushi ya ce, "Na san kina son Didi, kina ?aunarta sosai, zaki ji zafi da ciwon rashinta a zuciyarki. Amma baza ki Worar da Wacin mutuwa akan Didi ba, zaki Worar da zafinta ne a lokacin da kika rasa makusantanki Ya faWa tana lumshe ido tare da jan numfashi, ya sauke numfashi ya buWe ido ya kalle ta ya ce, "zaki WanWana zafin rashin wanda ka ke ?auna ne in aka wayi gari na mutu na barki, daga lokacin zaki tabbatar da ba ?aramar juriyar rasa Didi nake yi ba. Juriyar da nayi baza ki iya irinta ba, ko rabin jurewar da nake yi baza ki iya ba Jidda!. Yanzu duk abinda zan faWa miki baza ki fahimta ba, kina kallona a matsayin wanda ya kasa karSar ?addara kawai, ba ke kaWai ba, kusan kowa a haka yake kallona. Na yi miki uzuri, baki san Wacin mutuwa ba!.

Nayla ta sauke numfashi ta sunkuyar da kai, ta mayar da hawayen da suke ?o?arin sakko mata, dan yanzu ya zama mai raguwar zuciya, ko ya tayi hawaye a gabansa sai ya tayata, baya iya ri?e kansa ko kaWan, indai ya tuna da Didi sai ya zubar da hawaye. Saboda haka ko da taji kukan rashin Didi bata yi a kusa dashi, zata ta tashi ta kulle kanta a banWaki tayi kuka ta wanke fuska ta fito. Yana bu?atar kulawa saboda har lokacin jininsa bai sauka yadda ake so ba, ga nauyin da ?irjinsa yake masa, ga ciwon kai da yake fama dashi kullum.

Sai da ta mayar da hawayen ta Wago ta ce, "Haka jarabawar Allah take, akwai zafi da ciwo da raWaWi. Sai dai mu yi fatan Allah ya bamu ikon cinye ta ba tare da kuskure ba." Ya lumshe ido ya ce, "Amin Jidda. Akwai ciwo, akwai raWaWi kam sosai. Shiyasa bana fatan ki riga ni barin duniya, in sha Allah ni zan tafi na bar ki." Nayla ta yi shiru bata ce komai ba dan muryar ta tayi rauni sosai, ta ja numfashi ta jingina da kujera tana shafa kan Marmerh da take ta game cikin nishaWi.

Omar ya sake sauke numfashi ya kalle ta ya ce, "Jidda." Ta kalle shi ba tare da ta amsa ba ya ce, "na manta ban faWa miki ba, gobe zamu tafi umrah in sha Allah, zan je na yiwa iyayena da Didi addu'a." Nayla ta girgiza kai ta ce, "Allah ya nuna mana goben lafiya."

"Amin ya rabbi. Kin san meye?." Ta girgiza kai alamun a'a, ya gyara zama ya ce, "tun Wazu nake so na faWa miki sai na manta. Na yi mafarki da Didi cikin kyakykyawan yanayi, tana faWa min duk addu'ar da nake mata tana zuwa inda take" ya faWa yana kallonta da murmushi.?

Nayla ta ce, "ikon Allah, nima nayi mafarki da ita YaMar. Wai a mafarkin kana ta tafiya baka yi mata magana, sai take cemin kalle shi sai fushi yake yi akan yana gaishe ni bana amsawa, kuma fa Nayla ina amsawa ji ne baya yi, amma yanzu na faWa miki ki faWa masa ina amsawa. Bana haddace mafarki in nayi, kafin na tashi daga bacci na manta. Amma wannan har hango shi nake yi a idona."

Lokaci Waya fuskarsa ta washe zuwa annuri da farin ciki, ya gyara zama cikin farin ciin da ta jima bata gani a kan fuskarsa ba ta ce, "Da gaske?." Ta yi murmushi ganin shima murmushin yake yi ta ce, "Wallahi da gaske nake." Ya ri?o hannunta ta matso kusa dashi ya ce, "na jima ban ji labarin da ya yi min daWi kamar wannan ba, kin ga hakan yana nufin addu'ar da nake yi mata tana zuwa gareta ko?." Ta Waga kai alamun eh, ya yi mata pecking Winta a goshi ya ce, "Naji daWi sosai Jidda."

Murmushi ta yi yana kallon sa, ya ce, "Kin san ne nake kuWuri a raina?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "Su Umma nake so na kai umrah, da Umma da Mama da Anty Aisha. Ya ki ka gani? A haWasu dasu Kawu?."

Nayla da murmushin jin daWi ta ce, "YaMar indai akwai dama a haWa dasu kawai, ladan da za a samu wanda zai je har kabarin iyayenmu da Didi." Ya girgiza kai cikin gamsuwa ya ce, "in sha Allah zan yi hakan. Har su Bashir nake so su je, da nayi niyar mu tafi da Bashir to in bana nan shine akan komai, ya fisu ilimi da wayewa, yana kuma saurin Waukar abu in aka koya masa shiyasa nake iya bar masa komai. In muka dawo sai yaje, in ya dawo sai biyun su je su ma. ?an amanata ne, tun muna marasa jin magana muke tare har yanzu."

Nayla da take ta murmushin jin daWi ganin ya kawar da damuwar kamar ba shi ba ta ce, "Allah ya cigaba da buWa maka a rayuwarka, baza ka taSa yin baya ba saboda kyautatawa na ?asan ka da ka ke yi. Rashin Didi ya saka ka manta komai da ya wuce, gashi kana ?udirin alkhairin da ladansa zai je har inda take ya same ta."

Murmushi ya sake yi yana ri?e da hannunta har lokacin. Ya ce, "Haka ne Jidda. Tabbas da ace Didi tana da rai da babu dalilin da zai saka na kalle su..." sai ya girgiza bai ?arasa maganar ba ya canja wata ya ce,? "sai mijin Didi, ina so na shigo dashi cikin harkar kasuwancina, duk da yana aikinsa amma ina so na shigo dashi mu cigaba da yin komai tare, ya ki ka gani?." Nayla ta ce, "shawara ce mai kyau, amma ka tuntuSe shi ka ji." Ya girgiza kai alamun zai yi hakan.

? ?? Sallama aka yi tare da shigowa falon, suka amsa a tare suna kallon wacce ta shigo. Narma ce ita da Safna, sanye da hijjabi har ?asa. Ta tako cikin nutsuwa zuwa cikin falon suka zauna tana kallon su tana murmushi. Narma ta ce, "Ina yini." Nayla ta amsa da fara'a tana kallon ta. Narma ta kalli Omar da tunda ya amsa sallamar ya Wauke kai ta ce, "Ina yini Omar, ya aka ji da ha?urin Didi?."

Omar ya ce, "Alhamdu lillah."
"Allah ya gafarta mata, Allah yasa ta huta."
"Amin ya rabbi. Na gode" ya furta a sanyaye ba tare da ya kalle ta ba .

Narma ta ce, "Na so nazo tun lokacin, bana Nigeria kuma ba lafiya ce dani ba, sai da na samu sau?i sannan nazo." Jin yayi shiru bai bata amsa ba sai Nayla ta ce, "Babu komai, Allah ya ?ara miki lafiya, Mun gode da zuwan ki." Narma ta yi murmushi ta ce, "Amin, na gode. Didi Yaya ce a gare mu gabaWaya, ta yi min nasihar da ta shiga zuciyata lokaci guda, kuma nayi amfani da ita naga riba mai yawa a rayuwata. Allah ya haskaka kabarinta."

A tare suka amsa da amin kafin Nayla ta ce, "bara a kawo muku ruwa." Narma ta ce, "A'a mun gode, akan hanya muke zamu koma Abuja yanzu" ta faWa tana mi?ewa tsaye. Ta kalli Omar da ba ita yake kallo ba ta ce, "za a yi aurena cikin kwanakin nan, muna son design na product Win ku zamu bayar as souvenirs." Omar ya girgiza kai ya kalle ta ya ce, "Allah ya kaimu, ya sanya alkhairi." Ta amsa da amin ta yi musu sallama suka tafi.

Narma tana fita Nayla tayi ajiyar zuciya mai tsaho, Omar ya kalle ta suka haWa ido sai ya Waga gira sama, murmushi ta yi dan ta lura a hankali ya fara dawowa Omar Winsa, addu'ar da ake yi akansa ta fara ratsa shi.

Shima murmushin ya yi bai ce komai ba, ya kalli Marmerh da take gefe kamar babu ita a falon tana game a wayarsa. Yayi murmushi yana kallon ta ya ce, "Marmerh kamar bata nan, tana ta game kamar babba." Nayla ta kalli Marmerh, ta kalle shi ta ce, "ba kai ka koya mata ba?." Ya kalli Musliha da take jikinsa a kwance ya ce, "ita kam Didina babu ruwanta, ta kwanta a jikin ?aninta Omar shine kawai abinda take so" ya faWa yana yi mata pecking Winta a goshinta.

Nayla tayi murmushi kawai bata ce komai ba, ya dawo da kallonsa gareta ganin tayi wani iri kamar ba ita ba. Ya san tunda aka yi rasuwar nan ya canja mata, ya watsar da lamarinta, ba ko yaushe yake damuwa da lamarinta ba. Baya nuna mata soyayya da kulawar da take bu?ata daga gare shi, bashi da lokacin komai sai na tunanin Yayarsa da zubar da hawayen rashinta. Ya san tana bu?atar lokacinsa sosai, ta yi ha?uri da juriyar halin da yake nuna mata, sanann ta taya shi jimamin rashin da ya yi, bata taSa nuna masa gazawa a kan hakan ba. Ya ji rauni da tausayinta ya mamaye masa zuciya, sai yayi nufin kawar mata da damuwa, cikin murya mai daWi ya ce, "yaushe za a yi Yayata ?anne ne Madam?."

Nayla ta Wan wara ido tana Wan murmushi ta ce, "nima ban sani ba." Ya shafa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login