Showing 171001 words to 174000 words out of 332344 words

Chapter 58 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

30894

wahala?."

Abiy ya ce, "ke Win!. Duk laifin mahaifiyarta ne ya shafeta, mahifiyarta ta baki wahala saboda kin zo a bayan ta kina haihuwa ita bata haihu ba, kin manta kafin ta samu cikin Nayla ta ro?eki afuwa kuma ki kace kin yafe mata ku ka daidaita zaman ku. Ta Wauki Ahmad da Jawad kamar yaranta, a lokacin da aka tabbatar kina da cikin Jidda ta sadaukar da lokacinta da komai wajan kula dake, ashe itama da cikin Nayla a jikinta ba a sani ba. Kin rigata haihuwa da sati biyu ta haihu, ku ka cigaba da kula da yaran a tare har Nayla ta kai shekara shida a duniya. Lokacin da mahaifiyarta Nayla take ciwon ajali me ta ce miki? Amanar Nayla ta bar miki a hannunki saboda ta yarda dake zaki kula da ita ko babu ranta. Ashe ke kin????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
karSi amanar kula da ita ne saboda ta girma ki zuga ni na aurar da ita ga wanda bai dace ba, mu kaita inda zata sha wahalar rayuwa kamar yadda ki ka WanWana kaWan a hannun mahaifiyarta kafin komai ya wuce. Ashe a fatar baki ki ka yafe mata, ashe? baki yafe mata har zuciya ba ko Zeenatu!?."

Mama kuka take yi domin ta san Abiy ya gama ganota, sai ta ji kunyar da bata taSa ji ba a duniya, kunyar ta mamaye mata zuciyarta da gangar jikinta, idanunta sun yi mata nauyi saboda tsananin kunyar da take ji, guiwarta ta sage ji take kamar ta zube a wajan saboda kunya. Musamman da ta Wago ido ta ga Jawad, Ahmad, Jalila da Jidda a tsaye a bayan Abiy da alama duk sun ji abinda aka ce.

Abiy ya girgiza kai cikin takaici ya ce, "Meye ribar ki in Nayla ta sha wahala a gidan mijinta? Wacce riba zaki zamu?. Kin manta kina da Jidda, kina da Jalila? Su ba mata ba ne..? Meyasa bakya tunanin abinda ki ke ?o?arin yiwa marainiyar da aka bar miki amana za a iya yi musu suma?. Kin manta su ma mata ne zasu iya faWawa irin gidan da ki ke so Nayla ta faWa? Ko dan kina ganin Jidda ta yi aure ta samu mai kuWi bazata wahala ba? Ba ki san sakayya na iya canja komai ba ko Zeenatu?. Ba ki san alhaki kwikwiyo ba ne? Ba ki san duk ?an?antar ha??i sai Allah ya fitarwa da wanda aka zalunta ba?. Kin san masifar da take cikin cutar da maraya? Kin tashin hankali da sakayyar da take cikin cutar da wanda bai yi maka komai ba?. Zeenatu kin san illar cin amanar wanda ya yarda da kai?."

Mama bata ce komai ba kanta yana ?asa cikin kunyar ?a?anta da shi kansa Abiy Win. Bata taSa jin kunya wani ba kamar yadda take jin kunyar Abiy da yaranta. Abiy ya kuma cewa, "Yanzu kun je gidan Nayla kin faWi magana mara daWi, kin zagi mijinta, kin faWi magana wacce bai kamata a ji ta a bakin ki ba matsayinki na uwa a gareta. Yanzu da ya biyewa zuciya ya rama abinda kika faWa masa da bai cuce ki ba?...." Ya ?ara faWa yana binta da kallo ganin ta kasa ko motsin kirki.

Abiy ya girgiza kai ya ce, "yaron da yake amsa sunan siriki a gare ki ya buWe baki ya faWa miki magana mara daWi a gaban ?arki ai ya gama cutar da ke. ?arki Jalila har faWa miki ta ke yi, tana cewa Mama hakan bai kamata ba amma sai ki ka mare ta saboda bakya a faWa son gaskiya, idanunki ya rufe burinki kawai Nayla ta sha wahala. Kin je kin ga ba wahala take sha ba hankalinki ya tashi ba haka ki ke son gani ba."

Abiya ya sauke numfashi ya ce, "Wallahil azim kin bani mamaki matu?a, na Wauka in ki ka ga maciji zai sari Nayla zaki shiga ki kare ta ya sare ki a madadinta, ashe ke ce macijin da ki ke kai mata rasa. Kin zuga ni an yi auren nan ba tare da laifin Nayla ba, na gano hakan nayi miki shiru saboda ke uwace a gare ta har gobe, kin yi mata abinda ko wacce ta haife ta bata yi mata ba shiyasa na ?yaleki. Na san ke kika saka aka turo min text Win da ya tunzura ni har na kai ga aura mata Omar, na san ke kika shirya komai, kallon ki kawai nake yi. Duk abinda ki ka yi bai ishe ki ba, sai da ki ka Wauki ?afa har gidanta ki ka je dan kawai ki tarwatsa mata farin cikin da ke ciki, Hakan a gare ki daidai ne ko?."

Abiy ya kalli Mama inda take kallo tana kuka,? ya juya ya ga yaranta ne gabaWaya a tsaye jikinsu ya yi sanyi. Abiy ya nuna su ya ce, "ko kun san itace ta saka na aurar da Nayla ga Omar?" Ya faWa yana Wauko wayarsa ya shiga whatsapp ya mi?awa Ahmad ya ce, "karanta wannan."?? Ba musu ya karSa jiki a sanyaye ya fara karanta abinda yake rubuce.

_Assalamu alaika Abiyna. Na san lokacin da message Win nan zai same ka na jima da zuwa Kano, kayi ha?uri Abiy ban tafi dan Sata maka rai ba, na tafi ne saboda na samarwa kaina kwanciyar hankali da nutsuwar zuciyata. Abiy Ina son Omar, Ina so nayi rayuwa dashi, babu namijin da nake ji zan iya rayuwar aure dashi sai shi kawai. Hakan ba laifina bane Allah ne ya Wora min ban kuma isa na cire da kaina ba. Abiy zan iya rasa raina in kace bazan auri Omaar ba, zan kuma iya rabuwa da kowa dan nayi rayuwa dashi Abiy. Na tafi wajan dangin Ummana, na san su baza su ?iyi min abinda nake so ba, duk da Omaar ya kasance ba irin wanda ake so bane amma na tabbatar zasu san yadda zasu yi wajan samar min da farin ciki. Na san su zasu bani farin cikin da ka kasa bani Abiy, dan wallahi in ba a aura min shi ba sai na shiga duniya!. Da wannan nake shaida maka Abiy Ina Kano wajan Hajja, Ina son Omar Abiy, Ina matu?ar sonsa, na kasa jure abinda kai da Yayanmu ku ka cewa shiyasa na yanke hukuncin tafiya Kano ko dan na samu nutsuwa. Ka yi ha?uri in na Sata maka rai Abiy, sai anjima._

Ahmad gumi ya wanke masa jiki da?yar ya kai ?arshen sa?on, ya Wago a hankali kafin ya yi magana Abiy ya ce, "akwai wani ma, duba Ahmad." Bai musa ba ya sake scrolling ?asa ya sake ganin wani message Win kamar haka;

_Abiy in dai baka amince na auri Omar ba wallahi Allah sai na shiga duniya, sai na Sata maka suna, sai na yi video na Wora a social a media na ce ka hana ni auren wanda nake so, wallahi Abiy sai na lalata tarbiyyata yadda baka yi tunani ba. In har ba a aura min shi ba zan shiga duniya na lalace, in na shiga duniya bazan sake dawowa gare ku ba har abada. Inda ace? mahaifiyata tana da rai da hakan bazai faru ba, ita ai tana sona baza ta wula?anta ni ba. Abiy zan aikata abinda nace akan soyayya, zan iya kashe kaina a kan son da nake masa. Ka yi ha?uri Abiy, na san zaka ji babu daWi, zaka ga kamar ni Nayla da ka ke cewa Mamanka kamar na yi disappointing Win ka ne, ba haka bane Abiy, soyayyar Omar ce. Zan zauna dashi ko da zai dinga yankar naman jikina kullum, a haka nake sonsa nake ?aunarsa. Ka yi ha?uri!._

Ahmad ya Wago a sanyaye suka haWa ido da Abiy, Abiy ya karSi wayarsa yana nuna Mama ya ce, "Duk aikinta ne, ita ta saka aka yi hacking account Win Nayla aka turo min wannan." Ajiyar zuciya ya yi mai nauyi ya ce,

"Na rasa me ya shiga kaina a lokacin har na amince Nayla zata iya rubuta wannan sa?on ta turo min, na kasa yarda ni da kaina ni ne na amince Nayla ta rubuta wannan sa?on ta turo min. Ban yi mata adalci ba, bai kamata na yankewa Nayla hukunci akan abinda nake da tabbacin bazata aikata ba. Ba tarbiyyar da na bata ba ce, ba halinta ba ne. Amma ?addarar aurenta da Omar ta gifta, shiyasa na amince lokaci Waya ba tare da tunanin komai ba."

Ya kalli Mama da ake jin sautin kukan ta a Wakin ya ce, "da kin kwantar da hankalinki baki haWa wannan makircin ba Omar dai shine mijinta, da kin tsayar da hankalin ki waje Waya ko baki nemo auren ba zai kawo kansa saboda shine mijinta. Amma sai ki ka yi shigar sauri, ki ka Wauki alhakin marainiyar Allah wacce bata tsare miki komai ba. Kin bani kunya, kin bani mamaki wallahi!."

Shiru ya ratsa Wakin, babu abinda yake tashi sai kukan Mama wanda take yin sa cike da dana sani da kunya mai yawa. Abiy ya kalli ?a?anta ya ce,

"Ku yiwa mahaifiyar ku faWa, ku nusar da ita duk ladan da ta samu na kula da Nayla wallahi ya zube, ta bar shi ya bi rariya saboda banzan kuWurin da yake zuciyarta. Ku yi mata faWa ta canja hali ko dan saboda Jalila da bata aurar ba. Jidda ma da ta aurar bata tsira ba indai bata wanke zuciyarta ba. Sannan ku faWa mata in sha Allah zaman Nayla da Omar baza ta yi kuka ba, zata yi farin ciki fiye da wanda ta yi a gidan nan, zata samu walwala wacce bata so ta samu. Na yi shiru da maganar ne saboda bana so Nayla ta san babarta ce ta shirya komai na auren nan, ita Nayla umarninta kawai take bi saboda ta yarda da ita a matsayin uwa ta san baza ta cuce ta, ashe ita da biyu take yin hakan. Bana son Nayla ta ji maganar nan balle danginta, baban abin kunya ne a gare mu gabaWaya ace daga gidan nan aka ?ulla wannan kitumurmurar. Sannan ko dan Jawad da yake neman aure a ahlin babar Nayla!. Fitar wannan maganar babban abin kunya ne a gare mu baki Waya!" Yana faWa ya fita ya barsu jiki a sanyaye duk suna kallon mahaifiyarta su zuciyarsu babu daWi.
KRB3P062

Ahmad da yake tsaye jiki a saluSe ya kalli ?an uwansa ya kalli Mama ya ce, "Mama abinda mu ka ji bai dace da ke ba ko kaWan." Mama ta Wauke kai bata ce komai ba. Jalila da take kuka ta ce, "Yaya sai da na cewa Mama ta bar abinda take faWa a gidan Anty Nayla, Anty Nayla tana kuka amma Mama bata daina faWawa mijinta magana ba." Jidda ta ?araso da Mihada a hannunta ta ce, "Mama me Nayla ta yi miki haka? Ta taSa yi miki wani laifi ne?."

Mama ta goge idanunta bata ce komai ba dan bata san me zata ce musu ba, kunya ta gama rufe ta ko haWa ido bata so ta yi dasu. Jawad ya ce, "Mama Nayla ta taSa yi miki wani abu ne? Meyasa ki ka zama silar aurenta da Omar don Allah?." Mama bata ce komai ba dan kunyarsu take ji sosai.

Ahmad ya ce, "Koma meye a zuciyarki don Allah Mama ki ajjiye shi a gefe. Meye laifin Nayla? In ma laifin marigayiya Umma ne ya shafeta sai ki yi mata adalci, lokacin da abin ya faru ba ma a yi tunanin za a samu Nayla ba, kuma matar nan kin ce kin yafe mata tun kafin ta bar duniya, to meye na dawo da maganar nan kuma Mama?."

Mama bata ce komai ba sai kawar da kai da tayi, a tausashe ya sake cewa, "Ke ki ka raini Nayla, ki ka bata tarbiyya daidai da wacce ki ka bawa Jidda. In ba faWan aka yi ba babu wanda yake Wauka Nayla ba ?arki ba ce, saboda bakya banbanta ta da Jidda wacce ki ka haifa. Mama laifin da ki ke tunani an yi miki har zaki Wauki fansa a kan Nayla ita ta san anyi? lokacin da abin ya faru tana ina?. Kuma Mama kin ce kin yafe mata tun kafin ta bar duniya, ku ka cigaba da zama na aminci da jin daWi da kuma walwala, meye na dawo da hannun agogo baya....?. Kina fushi akan abinda ta yi miki a gidan nan, daga ?arshe kuma ta mutu ta bar ki da gidan, da mai gidan, da kuma ?a Waya da ta haifa a duniya. Mama ko iya wannan ya ishi bawa ya yi darasi, amma ki ka zobe ladanki, ta hanyar son ganin Nayla ta wahala, meyasa Mama?."

Yaya Ahmad ya sake cewa, "yanzu Mama wacce riba zaki samu in Nayla ta wula?anta a gidan mijinta? Don Allah da me hakan zai amfane ki?." Jawad a sanyaye ya ce, "babu."

"To meye amfanin hakan? Yarinyar nan tana kallon ki matsayin uwa a gareta, ta yarda da ke ta amince baza ki cutar da ita ba, ashe duk abinda ya faru a ?ar?ashin umarninki ne, tana bin umarninki saboda yardar da ta yi dake meyasa haka Mama?. Yanzu Mama da kan ki kika rubutawa Abiy wannan dogon message Win ki ka tura masa kawai saboda cikar burinki a kanta. Allah sarki baiwar Allah, shiyasa ta fita daga hankalinta, ta gigice, ta kasa gane me ta aikatawa mahaifinta ya yanke wannan Wanyen hukuncin a kanta. Mama ko ha??inta da ki ka Wauka in bata yafe miki ba wallahi sai ya bibiyeki, bata san laifin da ta yi aka yanke mata hukunci cikin fushi. Kuma Mama ta ce miki ta ha?ura da auren Omar ki ka ce a'a kar ta ha?ura, saboda uwa ki ke a gare ta sai ta amince da duk abinda ki ka ce, saboda bata da mahaifiya ke take kallo a wannan matsayin. Mama anya Nayla ta cancanci wannan hukuncin daga gare ki kuwa?."

Mama dai bata ce komai ba, ta sunkuyar da kai kamar tana saurarensa, yadda yake magana a tausashe ratsa zuciyarta maganar take yi. Ahmad ya ce, "Mama in aka cutar da Nayla akwai Jidda, akwai Jalila, in aka yi fatan ta auri wanda zai wahalar da rayuwarta muna da tabbacin rayuwar Jidda a gidan mijinta zai Wore da farin ciki? Ko kuma muna da tabbacin ita Jalila zata je inda zata yi farin ciki?. Annabi Muhammad S.A.W cewa ya yi ka so wa Wan uwanka abinda ka ke so wa kanka. Yanzu gashi kin so rayuwar Nayla ta kasance cikin ba?in ciki, sai gashi tun ba a je ko ina ba ta fara kasancewa cikin farin ciki da walwala a gidanta. A nan me Allah yake ke nunawa? Allah ya nuna mana shine yake da iko da bawansa a kan komai a kuma ko yaushe, duk yadda ka kai ga son cutar da wani sai Allah ya yarje maka, haka duk yadda ka kai ga son faranwata wani sai Allah ya yarje maka. Kuma inda mutum yake kai ka a rayuwa Allah ya kan canja in babu shi a cikin ?addararka. Tun farko Omar shine a zanen ?addarar Nayla, kawai kin zama silar aurensu ne Mama, wallahi ko babu goyan bayanki sai ta auri Omar saboda shine mijinta. Mama meyasa ki ka yi gaggawa baki bari Allah ya yi ikonsa ba? Meyasa ki ka shiga lamarin ubangiji..?. Tunda mahaifinta yana yi mata addu'ar samun miji na gari na tabbatar da Nayla bazata taSa yin kuka a gidan mijinta ba, saboda wannan miji na garin da yake ro?a mata shi Allah ya bata."

Ya ri?e hannunta duka biyun ya ce, "Don Allah Mama ki bar wannan tunanin daga zuciyarki, ki manta dashi, ki goge shi daga zuciyarki, indai da gaske kin yafe Win to ki bar Nayla ta yi rayuwarta a inda Allah ya ajiiyeta. Don girman Allah Mama kar ki sake aikata wani abun da zai saka Nayla zubar hawaye, ke uwa ce a gare ta, jin wannan maganar babban abin kunya ne a garemu, in dangin mahaifiyarta suka ji labari kamar mun Wauki wu?a mun cakawa kan mu ne Mama. Kamar yadda Abiy ya faWa, Jawad yana son Salma ?ar uwar Nayla da aure, in maganar nan ta je kunnen danginsu abin bazai yi daWin ji ba. Muna ro?on ki don Allah ki bar wannan tunanin ya wuce, in ma akwai wanda yake zuga ki wallahi ba hanyar arzu?i yake kai ki ba Mama. Ki yi ha?uri, tunda kin yafe a bar shi an yafe Win komai ya wuce don Allah."

Mama har lokacin bata ce komai ba tana jin duk abinda yake faWa. Ahmad ya tashi ya kalli su Jawad ya yi musu alamun da su fita su ?yaleta, ai kam duk suka fita har Jidda da saukarta a Kaduna kenan ta ji abinda yake faruwa. Mama da kallo ta bi su har suka fita ta rufe ido kawai tana tunani kala-kala.

" " " " " " "

Nayla ta Wau kwaliyya cikin straight gown ta lace mai matu?ar kyau, ta Waura Wankwali ta saki gashinta a baya, ta sha turare sai ?hamshi take yi. Tana zaune a falo da yamma Salma ta yi mata waya gata a bakin gate. Tashi ta yi ta je ta buWe mata suka shigo. Tunda Salma ta shigo take ?are mata kallo sai da Nayla ta gaji da kallon ta ce, "Dallah kallon na meye?."

Salma ta ?yal?yale da dariya ta ce, "Ke wai me nake gani haka? Kin ga wani uban kyau da ki ka yi kuwa?." Nayla ta harare ta ta ce, "Daman can da kyauna."
"Na san akwai, amma wannan kyaun na musamman ne. Ke wai mai Omar yake baki ne haka? Kin ga yadda ki ka canja Nayla." Nayla ta yi murmushi tana fari da ido ta ce, "me zai bani da ya wuce soyayya?."
Salma ta wara ido ta ce, "Shi wannan har wata soyayya ya iya yi? Ba ni labari don Allah, yana iya abin kirki kuwa?."

Nayla ta ce, "ban sani ba, ?ar rainin hankali."
"To shi da magana ma sai ya ga damar yiwa mutane ina zai iya soyayayr balle har ya aikata?."
"Ke ki ke ganin sa haka, mijina


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login