Showing 141001 words to 144000 words out of 332344 words

Chapter 48 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14440

?ani na ki anya ba maganin ?arfin maza ya sha ba? Kin ga irin aikin da ya yiwa yarinyar nan kuwa?. Gashi kuma da alama ba ta shiga ko Wan ruwan zafin nan da ake taimakawa amare ba. Duk da dai shima bashi da lafiya sosai, amma ya kamata ace an taimaka mata."

Didi ta yi ajiyar zuciya, kunya duk ta bi ta rufe ganin AbdulHamid yana wajan kuma yana ji, duk da dai sun Wan yi nisa da inda yake amma ta san zai juyo dan ba a hankali take magana ba.

Nurse Win da take tsaye kusa da Dr ta ce, "Lamarin ya dangana ga Winki, amma ba wai sosai can ba, kuma kyau samu ta kwana a nan zuwa gobe ko jibi yadda za a kula da ita in ya so sai ta koma gida." Didi a sanyaye ta ce, "Shi kuma me ya kawo nasa ciwon?."

Dr ta ce, "Ana samun irin haka musamman ga saurayin da ya Wan kwana biyu bai yi aure ba kuma bai taSa sanin mace ba, su kan tsinci kansu a yanayi na zazzaSi da ciwon kai, ciwon gaSoSi da jiri saboda kasancewar su ba?i a wannan Sangare. Wannan shine ya jawo masa na sa ciwo, dan zazzaSi ya kama shi sosai har zafin jikinsa har ya fi nata. Shi ake kira da samartaka in ji manyan mu."

Didi ta girgiza kai cike da gamsuwa Dr ta ce, "in? sun warware ta koma gidan a Wan ?ara mata hutu na at least kwana biyar zuwa sati Waya haka." Didi ta girgiza kai cikin gamsuwa ta ce, "Yanzu tana Lafiya?."

"Lafiya take, ta yi bacci. Shima kuma rashin sabo ne da zarar ya farka zai iya dawowa daidai sai dai rashin ?arfin jikin kawai, itace zata Wan yi jinya kaWan." Didi ta ce, "na gode sosai." Dr ta ce, "babu komai aikina ne" ta faWa suna wucewa suka fita daga wajan.

Didi ta dawo a sanyaye ta zauna cikin kunyar mijinta kamar ita ce ta aikata abinda aka ce. Tunanin halin da aka faWa mata suke take yi, Allah ya sani tunda Nayla ta dawo gidan Omar take tunanin wahalar da zata sha a hannunsa, haka kawai take ji a jikinta Nayla zata sha matu?ar wahala a hannunsa dan Omar bai yi kama da ragon namiji ba. Babban abinda ya saka ta ji daWi a zuciyarta tunawa da bayanin likita, godiya take ga Allah ya kasance Omar bai taSa aikata zina ba, ya gujewa saSawa Allah ya ri?e kansa har sai da aka gama faWan zamansa da Nayla har ya amince da ita ya fara sanin ?a mace a kanta. Hakan ya yi mata daWi sosai, dan yadda zamani ya lalace samarin yanzu kaWan ne basu taSa aikata zina ba, an mayar da ita ado kamar ba ita Allah ya ce kar a kusanceta ba. Amma tausayin Nayla ya gama mamaye mata zuciya, daman ko shakka bata yi akan Nayla, ta san ita Wiyar ?warai ce da ta samu tarbiyya mai kyau. Ajiyar zuciya tayi, a lokacin gari ya yi haske sosai ma'aikata na shigowa asibitin wanda suka kwana kuma duk sun tafi.

AbdulHamid ya kalle ta ya ce, "ko zan mayar dake gida ne kin bar Marmerh a hannun Umma, in ta farka ya za a yi da ita?." Didi ta ce, "to in na tafi waye zai kula dasu gabaWaya? Da ace ma ya farka sai na tafi, amma bai farka ba shima bacci yake yi."
"To yanzu haka za a bar jaririya a gida ba tare da mahaifiyarta ba? Ai sai da na ce ki taho da ita ko?."
"Ban Wauka zamu jima haka ba, bara mu gani zuwa anjima in bai farka ba sai mu je ka kaini na dawo anjima." Bai ce mata komai ba ya yi shiru itama ta yi shiru cikin tausayin Nayla mai yawan gaske.

Ganin ?arfe takwas na safe tayi Didi ta tashi ta shiga Wakin ta same su dukkan su suna bacci dan Wakin mai gado biyu ne. Ajiyar zuciya tayi ta ?arasa inda Nayla take ta dafa goshin ta taji babu zazzaSi a jikinta, ta dawo wajan Omar ta tsaya yana kallonsa.

Dariya ce ta kubce mata ba tare da ta san dallin yinta ba, haka kawai ya bata dariya har sai da ta dara ta dafa goshinsa, a bayyane ta ce, "Bana tunanin Omar ya taSa kwanciya asibiti, kai bai taSa ba ma, amma gashi yau ya kwanta. Alhaji Omar manya, komai na su na manya ne" ta faWa tana dariyar da bata san dalilin ta ba ta fita daga Wakin.

Kallon AbdulHamid tayi tana murmushi ta ce, "Ka yi ha?uri YallaSai, mu je ko?." Ya kalle ta ya ce, "da wa ki ka barsu?."
"Zan dawo anjima sai na taho da Marmerh Win."
"Bai kamata ba, ya kamata ko gidan Hajja ki yi waya yarinyar nan ?awarta ta zo."
"Ka san abinda ya faru na san ka ji me suka ce, bana son kiran mutane azo ana tambayar me ya same su, hakan babu daWi kamar fallasa sirrinsu ne."

AbdulHamid ya ce, "lalura ce ai ba wani abun damuwa ba, babu wanda ya wuce ?addara dan an sani ai ba komai bane. Haramci suka aikata ko me?." Didi ta ce, "mu je dai kawai, ance ai zasu jima suna baccin." Bai ce mata komai ba suka fita daga wajan tare.

Didi koda ta koma a gaggauce ta yi wanka ta yi girki mai sau?i da shayi da sauran abinda ta san zasu bu?ata. Bata fi awa biyu da komawa ba ta dawo ita da Umma Saroot, dan itama hankalinta bai kwanta ba dan Didin bata ce mata ga abinda ya faru ba ta ce kawai basu da lafiya. Har lokacin da suka dawo dukkansu bacci suke yi, suka basu waje suka dawo wajen Wakin suka zauna akan kujera.

Omar sai ?arfe biyu na rana ya buWe ido yana kallon Wakin yana so ya gane a inda yake a kwance. Mi?ewa zaune ya yi cikin rashin ?wari amma ya ji daWin jikinsa zazzaSin ya sauka sai dai rashin ?arfin jiki da bashi da ita. Kallon gefensa ya yi ya ganta a kwance idanunta a rufe da alama bacci take yi.

Sakkowa ya yi daga kan gadon ya mi?e tsaye a hankali yana yamutsa fuska, sai yanzu ya lura a asibiti suke ya Wan ja tsaki kaWan, a rayuwarsa bai taSa kwanciya a asibiti ma amma saboda tonan asiri Didi ta kama ta kawo shi asibiti. ?arasawa ya yi wajan Nayla ya dafa kanta ya ji babu zafi a jikinta gabaWaya, ya taSa wuyanta nan ma babu zafi ko kaWan. Kanta ya shafa da gashin ta yake baje a kan gadon yana kallon fuskarta.

Kiss ya yi mata a goshi yana shafa fuskarta yana ganin yadda take a kumbure har lokacin, ya sauke ajiyar zuciya yana kallon ta. BuWe Wakin aka yi ya kalli wacce ta shigo, ganin Didi ce sai ya Wan yi tsaki ya ce, "Wai daman asibiti mu ka zo? Ni na ce miki asibiti zaki kawo mu?."

Didi ta ce, "ikon Allah, kai ka tashi daga ciwon ma baza ka daina masifa ba? Da ba mu zo asibitin ba ya ka ke so nayi da ku gabaWaya?." ?auke kai ya yi daga kallonta a lokacin Umma Saroot ta shigo jin maganar Omar.

HaWa ido suka yi da ita Marmerh na hannunta ta ce, "Omar ya jiki?." Ransa ya ji ya Saci matu?a, ya kalli Didi ya girgiza kai kawai bai ce komai ba amma haushinta yake ji, daga kiranta dan ta taimakawa Nayla sai kawai ta yi masa gayya? Ya tsani rashin sirri a rayuwarsa, yana girmama sirri sosai a rayuwa, wannan dalilin ya saka bai taSa tunanin aikata zina ba, saboda gani yake duk yarinyar da ya kwana da ita ba tare da aure ba kamar ?arshen rashin sirri kenan. Shiyasa ko sha'awar auren mata biyu ba ya yi, gani yake in yana raba kansa ga mata biyu kamar babu sirri a ciki. Amma daga kiran Didi ta taimaka masa ta kama ta yi masa gayya harda zuwa asibitu. Kallon Didi ya yi ganin tana kallonsa alamun ya amsawa Umma sai ya Wan yi ?aramin tsaki ya ce, "lafiya...." Kafin ta amsa ya kalli Didi ya ce, "Ya jikinta?."

Didi ta ce, "har yanzu ita bata farka ba." ?an dafe kai ya yi jin yana sara masa Didi ta ce, "ka zauna ka daina tsayawa, zata farka itama in sha Allah." Zama yayi akan farar kujerar da take gaban gadon da Nayla ta ke, ya ri?e hannunta ya kulle ido bai ce komai ba. Didi ta ce, "bara na faWawa likitan ka farka, daman sun ce in ka farka na sanar da su."

Fita Didi ta yi ba jimawa ta dawo ita kaWa,? jim kaWan sai ga likita namiji ya shigo ya kalli Omar ya ce, "Sannu ya jiki?." Omar ya Waga kai kawai bai ce komai ba. Likitan ya ce, "Abinda ya kamata ka yi yanzu shine; ka samu ka yi wanka, ka ci abinci, ka huta zaka fi jin daWin jikinka." Omar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "ita fa?." Likitan ya kalle shi ya ce, "itama muna jiran ta farka, in ta farka sai mu san abinda ya kamata mu yi."

Omar ya yi shiru bai ce komai ba likitan ya matsa kusa da Nayla yana duba ruwan da saka mata dan likitan da ta karSe su tayi masa bayanin komai kafin ta tafi.

Omar kallonsa yake yi ta ?asan ido yana jin kishi na mamaye masa zuciya, gabaWaya haushin Didi yake ji, ko meye na kawo su asibiti oho, haka kawai yanzu ga wani banza kusa da matarsa har yana maganar wai zata samu sau?i. Tsakin da ya yi a bayyane ya saka Didi ta kalle shi a lokacin likitan ya fita daga Wakin.
KRB03P50

Bayan fitar likitan Didi ta bishi da kallo tana Soye dariyarta ta ce, "ko zaka kira Bashir ya zo ku tafi gida ka je ka yi wanka? Ko kuma zaka fara cin abinci?, gashi na kawo." Kallon ta ya yi baice komai ba.? Didi ta ce, "ko tea ne ka sha ka ga yanayinka har yanzu bai dawo normal ba, ga toothpaste na tawo maka dashi na san zaka ce baza ka ci abinci ba saboda baka wanke baki ba, gashi don Allah ka wanke ka sha koda tea ne in yaso sai na kira Bashir ya zo ya kai ka gida, zuwa anjima sai ka dawo lokacin ta farka."

"Kawai sai na tafi na barta a nan a kwance?" Ya faWa muryarsa a can ?asa dan kana ji ka san bashi da lafiya kamar mai mura.

Didi ta ce, "ai ni ina nan, kuma ba jimawa zaka yi ba" ta faWa tana Wauko kayan wanke bakin ta mi?a masa ta ce, "don Allah ka tashi." Ajiyar zuciya ya yi ya kalli Nayla, maganganunta na daren jiya suna amsa kuwa a kunnensa. KarSar abin hannun Didin ya yi amma bai mi?e ba Didi ta ce, "ga banWakin nan" ta faWa tana nuna masa ?ofa nan ma bai kalle ta ba.

Sai da ya gaji da zaman dan kansa ya tashi ya shiga ya wanke bakin ya fito, ta bashi tea Win da ta haWa masa ya karSa yana sha yana kallon Nayla. Rabin tea Win ya sha ya ajjiye Didi ta ce, "Ga Bashir Win ya zo, ka zo ku je."
"Kar ya shigo min nan."
"Allah ya ba ka ha?uri, na ce ya jiraka a waje." Banza ya yi mata kamar ba zai tashi ba yana kallon Nayla da take kwance tana bacci a hankali.

Ya kwashe sama da mintina goma sannan ya mi?e Didi ta ajjiye masa takalmi ta ce, "ga shi nan." Bai musa ba ya saka ya fita yana takawa da?yar. Umma Saroot ta murmusa ta ce, "Omar manya." Dariya Didi tayi kawai bata ce komai ba suka cigaba da zama.

? ?? A hankali Nayla ta buWe ido tana kallon Wakin kafin ta ware gabaWaya, zafin da ta ji jikinta ya saka ta yamutsa fuska ta ce, "wash!." Duk da muryarta tayi ?asa haka bai hana Didi ji ba, ta taso da sauri ta ce, "Nayla kin farka? Sannu." Didi ta ri?e hannun Nayla ta ce, "Nayla sannu, ya jikin na ki?." Jin muryar Didi ya saka ta kalle ta ta ri?e hannun Didi amma ta kasa magana.

Didi ta ce, "sannu, bara na kiira likita" ta faWa tana sakin hannunta ta fita da sauri. Ba jimawa suka dawo tare da wata midwife babbar mace ta ?araso kusa da Nayla ta ce, "Sannu, me yake damunki yanzu?." Nayla ta nuna kanta midwife Win ta sake cewa, "bayan shi fa?."

Da?yar Nayla ta ce, "Ina jin zafi sosai" ta faWa tana runtse ido. Midwife Win ta kalle Didi ta ce, "Ku Wan bani guri na duba ta." Ba musu suka fita, ta saka safar hannu ta duba Nayla ta zare safar ta ce, "Ki yi ha?uri, an yi miki Winki ne, zaki dinga jin wannan zafin amma in kina tsarki ruwan zafi a hankali zai ware, yanzu ki tashi ki ci abinci ki samu ki yi wanka."

Nayla hawaye ya sakko mata dan ba ?aramin zafi take ji ba, Allah ya taimaka babu zazzaSin sai nauyin da kanta ya yi mata. Midwife Win ta kira Didi ta shigo ta ce, "kina ji, kamata ya yi kawai ku tafi da ita gida, in aka je gida zata fi samu ta shiga cikin ruwan zafi a nan kin ga babu damar hakan. Duk da ba a son shiga ruwan zafin in an yi Winki yanzu, an fi so ayi tsarki da ruwan ba a shiga cikinsa a zauna ba, amma saboda yanayin ciwon da ta Wan ji da kumburi zata iya shiga, amma ba mai zafi sosai ba."

Didi ta ce, "amma ciwon kan fa?."
"Duk zafin ciwon ne ya kawo ciwon kan, da zarar raWaWin da yake mata ya Wan ragu ciwon kan ma zai daina ciwo. Yanzu bara na rubuta magani ku siya sai ku wuce gida ku je ta shigan ruwa mai Wumi ba mai zafi ba, tayi wanka ta ci abinci ta sha magani, in sha Allah zata samu sau?i."

Didi ta ce, "To na gode." Midwife Win ta ce, "sannan a faWawa mijin nata a bata lokaci ta warke gabaWaya, in ba haka ba za a fama ciwon, a bata kamar sati Waya zuwa kwana goma haka. Sannan ya kasance tana shiga warm water, ba mai zafi sosai ba irin Wan daidai kamar yadda na faWa a farko. Ko bata shiga ciki ba ta yi tsarki dashi."

Didi ta ce, "in sha Allah."
"Yauwa, ki jira na kawo miki" ta faWa tana fita Didi ta koma kusa da Nayla ta ri?e hannunta. Cikin tausayi ta ce, "Sannu Nayla." Hawaye Nayla ta share bata amsa ba ta yi shiru kawai.

Didi waya ta Wauka ta kira Omar amma bai Wauka ba, ta sake kiransa bai Wauka ba sai ta kira Bashir ta ce ya bashi in suna tare, Bashir ya ce ya shiga gida amma in ya fito zai bashi.

Didi ta kalli Nayla ta ce, "zaki iya tashi zaune na baki tea ki sha?." Nayla ta Waga kai dan ta gaji da kwanciyar itama. Da?yar ta motsa tana runtse ido Didi ta jinginar da ita ta ce, "ki kuskure bakin ki sai ki sha tea Win."

Ruwa Didi ta bata ta kuskure bakintata? zuba a dusbin ta haWa mata tea ta bata. A hankali ta sha tea Win, bata sha da yawa ba ta bawa Didi alamun ya ishe ta. Umma Saroot tsaf ta gane abinda ya faru, hakan ya saka ta tausayawa Nayla sosai ta ce, "Sannu Nayla, ya jikin?."
"Da sau?i" ta furta a hankali hawaye na taruwa a idanunta cikin matu?ar kunyar da lulluSeta.

Midwife Win ce ta shigo ta bawa Didi takardar maganin ta tashi ta fita dan ta siyo. Tana fita Omar ya kirata a waya ta Wauka ta ce, "in zaka iya ka taho da mota zamu taho da ita gida, sun ce a dawo gida a kula da ita." Abinda ta ce kenan ta yanke wayar ta siyi maganain ta dawo ta haWe da na Omar dan kar ta manta. Ta ?arasa ta biya kuWin da aka kashe a asibitin ta dawo wajan Nayla.

Suna zaune a daWin, Marmerh na hannun Didi tana shayar da ita ya shigo da sallama. Kallo Waya zaka yi masa ka ga ya rame amma ya yi haske sosai sai gashin fuskarsa ya sake yin ba?i har wani she?i yake yi kamar wanda aka sakawa mai. Sanye yake da manyan kaya na yadi ruwan ?asa kansa babu hula.

Nayla na jin sallamarsa ta yi saurin sunkuyar da kai gabanta ya yanke ya faWi, tsoronsa da kunya suka mamaye mata zuciyar a lokaci Waya.

Didi ce ta amsa sallamar bai ma kalle ta ba ya ?arasa inda Nayla ta ke ya zauna yana ri?o hannunta. Sai jikin Nayla ya soma rawa dan tsoron ya kawo hannunsa jikinta take yi, murya a ?asa ya ce, "Ki nutsu, Ya jikinki?." Bata iya kallonsa ba kawai ta saka masa kuka.

Tashi ya yi tsam ya koma kusa da ita ya zauna, ya kwanto ta a jikinsa yana shafa kanta dan Didi ta saka mata hula ya ce, "Ki yi ha?uri ki daina kuka, Kin ga baki da lafiya ko?." Kuka take a kafaWarsa sosai cikin kunyarsa da kunyarsu Didi. Omar? ya ce, "Ki daina kuka, bana so na ji kina wannan kukan, ki bari baki da lafiya." Numfashi ta koma ja a hankali tana jikinsa ta kasa koda motsin kirki saboda kunya.

"Ashiq!" Omar ya furta cikin murya mai sanyi. Sai a lokacin ta tuna sunan da ya dinga kiran ta dashi kenan a lokacin da take gab da rasa hankalinta, tabbas ta ji yana cewa Ashiq ko kuma ce Ashiqaty, ta manta ne kawai saboda yanayin da take ciki, amma yanzu da ya faWa ta tuna. Shiru ta yi bata ce komai ba abubuwan da suka faru jiya suna dawo mata a cikin kanta, tunawa da kalamansa na daren jiya bata san ta chakume shi ba saboda nauyin da ta ji da kunya mai matu?ar yawa ta lulluSe ta.

"Ki yi ha?uri, Kin ji?" Ya faWa a daidai kunnenta amma bata motsa ba.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login