Showing 150001 words to 153000 words out of 332344 words

Chapter 51 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14419

ya zama ita ta zama shi, ga tarin soyayayr da yake mata wacce bai san adadin yawan ta ba. In aka ce hakan zai faru a rayuwarsa zai ce ?arya ne, amma gashi ya faru cikin ruwan sanyi, kuma jikinsa da zuciyarsa sun karSi abun hannu biyu.

? ?? ?ago ido ta yi jin shiru ya yi yawa ta kalle shi suka haWa ido alamun kallon ta daman ya ke yi, ta yi saurin sunkuyar da kai. Murya a ?asa ya ce, "meyasa baki son kallona?." Tayi shiru bata amsa ba ya ce, "meyasa." Jin ya maimaita sai Nayla ta ce, "bana iya kallon idanunka, kuma kunyarka nake ji" ta faWa tana rufe fuska da hananyenta.

Murmushi ya yi mai sauti ya ce, "kunya!...." Ya sake murmusawa ya ce, "A karo na farko a rayuwata na ji wani abun kunya, ban taSa ji ba sai Wazu da Didi take min bayani akan Sarnar da na yi a jikinki. Sai na ji nauyinta sosai, amma daga nan komai ya wuce."

Kalamansa ya sake bata kunya sosai, ta runtse ido cikin kunyarsa da kuma kunyar Didi da kunyar abinda ya faru. Bai lura da yanayin ta ba ya Wan yi murmushi ya ce, "Ni fa a kanki na aikata abubuwan da ban taSa aikatawa ba a rayuwata. Tunda ki ka shiga rayuwata abubuwa suke ta faruwa dani wanda basu taSa faruwa ba sai a kan ki kawai." Ta Wago a hankali ta kalle shi ya Waga gira ya ce, "Na lissafa miki?."

Kai ta Waga alamun eh, ya matsa kusa da ita ya ri?e hannunta cikin kasalalliyar murya ya ce, "ke ce mace ta farko da Didi ta taSa yi min faWa a gabanta...." Ya dakata da maganar saboda ?ar dariyar da Nayla tayi alamun ta tuna.

Bata yi magana ba sai Wauke kai da tayi ya ce, "Da gaske kece ta farko, ni ba a yi min faWa a gaban kowa musamman baki. Abu na biyu kuma na ce zan Wauki mataki a kanki akan hakan amma sai na kasa aikatawa, amma da wata ce ba ke ba har abada bazata sake marmarin zuwa gidanmu ba, kin dan waye Tiger a baya ba sai na faWa miki ba. Abu na uku; a kanki Didi ta ce na fita na bata waje, hmm...! lokaci daga Abuja na dawo, ko sannu da zuwa bata ce min ba. Na ji haushinki sosai, ina mamakin meyasa ki ke shiga rayuwata ne har haka?. Na uku; a kan ki ta ce min ina shirme, kuma ke ce ki ka yi min korar shaiWanu ban Wauki mataki ba."

?ar dariya Nayla ta sake yi tunawa da abinda ya faru, sai ya dakata da maganar yana kallonta ganin tana dariyar da ta Wauki hankalinsa. Ya yi shiru bai ce komai ba, ta kalle shi suka haWa ido ya ce, "Kuma tun farko kece wacce Didi take yawan saka ni a lamarinta, haka kawai in ki ka shigo ki ka fita sai ta fara labarinki, sai na ji haushi na ce wai wannan wacece ne da zata ?wace min Yayata?. Ke ce mace ta farko da ki ka fara bani kyauta na karSa har na yi amfani dashi, kin bani kyutar azurfa gata a hannuna, kin bani kyautar turare har yanzu na kasa ?arar dashi saboda son da nake masa, kin bani kyutar riga wacce da ita na kwanta a asibiti a jiya."

Hannunsa ta kalla ta ga azurfar kuwa tana nan, ta Wora hannu a kai ya ri?e hannayen nata ya ce, "Kece mace ta farko da na fara jin nauyi da girman iyayenta a duniya, a gaban Abiy na kasa samun sukuni, nauyinsa ya rufe min idanu, na rasa abinda nake ji. Ke ce mace ta farko da ki ka fara kirana da Yayaaaa!" Ya Wan sauke numfashi kaWan ya ce, "Ya ilahii......!har yanzu na kasa manta lokacin da mu ka je g1danku, ki ka ce Yaya Omar Allah ya kiyaye hanya, a daidai lokacin hawaye ya sakko daga idanunki kuma kina murmushi. Kin tuna?."

Wasu hawayen ne a idanunta, ta Waga kai alamun eh ba tare da ta kalle shi ba ya ce, "kina lissafawa dai? Ni na Sata a lissafin."

Bata bashi ba amsa ba ya ce, "kece mace ta farko bayan Didi da na ci abinda ta sarrafa, Didi ta faWa min lokacin da ki ka dafa awara na ci har naji tayi min daWi. Jidda ke ce mace ta farko da na karSi aurenta, ke ce mace ta farko da na zauna da ita a gida Waya, kece mace ta farko da na ke shiga lamarinta har na saurereta. A kan ki na fara jin kishi tun ban san ina sonta ba, ke ce mace ta farko da na kwana a gado Waya da ita, ke ce mace ta farko da na damu akan rashin lafiyarta, ke ce mace ta farko da na ji a raina in wani abun ya same ki bazan ji daWi ba" ya sauke ajiyar zuciya ya matse hannayenta, ya sake yin ?asa da muryarsa sosai ya ce,

"Ban taSa karya rantsuwa ba, in na rantse na rantse kenan bana canjawa, shiyasa ban cika yawan rantsuwa a rayuwata ba, dan babu halitttar da ta taSa karya min rantsuwa. Ke ce mace ta farko da rantsuwar ta karye ta dalilinki. Ke ce mace ta farko da na ji a raina in na rasa ta bazan iya rayuwa ba, ke ce mace ta farko da na furta mata kalmar ina sonki, ke ce abu na farko da na ce na bar shi amma na kasa bari, ke ce ta farko da nake tsananin ?auna, nake ji kamar na mayar da ke zuciyata. Ashiqaty!" Ya furta can ?arshen ma?ogwaro yana kallon idanunta.

Shiru ya sake yi yana kallon ta, zuciyarsa na cigaba da antayo kalamai kan harshensa ya ce, "Ke ce ta farko da na san meye so a kanta, na banbance soyayyar burgewa da soyayyar gaskiya a kanki. A kan ki na fara sanin mace, da ke kaWai na taSa haWa jiki Jidda, ke kaWai ce ki ka san waye Omar in and out. Kuma ke ce wacce na taSa bawa ha?uri a duniya Jidda!."

Lumshe ido tayi ta kwanta a jikinsa dan farin cikin ya yi mata yawa tana so ta jita a jikinsa a wannan lokacin, ya rungumeta sosai yana shafa bayanta a hankali cikin salo na ?auna. Ya sake yin shiru bai ce komai ba, idanunsa a lumshe yana ji kamar ya buWe ?irjinsa ya saka ta ya huta da bugawar da zuciyarsa take yi masa. Ya buWe ido ya ce, "abu nawa na lissafa?." Nayla ta ce, "nima na Sata a lissafin, amma dai sun fi fifty." Dariya ya yi kaWan ya ce, "to duk ta dalilinki ya faru, na ?ara miki da wani ma guda Waya....a kan ki nake ta yawan murmushin, ko Didi albarka."

Murmushi ta yi tana daga jikinsa yana shafata a hankali cikin salo na soyayya da kwantar da hankali da nuna tsansar kulawa a gare ta. Shiru ya biyo baya, ta yi luf a jikinsa ko motsin kirki bata yi. A hankali ya ji ta ce, "ban Wauka zaka saka azurfar da na baka ba, lokacin da na ganta a hannunka na yi mamaki sosai. Ban Wauka zaka yi amfani da abinda ya fito daga hannuna ba, ganin haushina ka ke ji." Cikin shau?in ?aunarta ya ce, "Haushin na ki shine soyayyar Jidda!. Wannan soyayyar da nake miki ba wacce aka samu a kwanan nan bane. Ni na san ta jima a zuciyata, ban fahimta ba ne sai bayan kin bar ni, kishin kuwa tun shekara goma baya."

? ? Ta Wago ta kalle shi ya Waga gira sama ya ce, "eh mana. Na kuSutar dake daga wanda suka ke ?o?arin yi miki fyaWe, na ji zafi a raina har ta kai ga na yi amfani da wu?a dan hukunci. Jidda daga wannan ranar na fara fitar da jini daga jikin wani, a ranar na yanke masa ?an yatsunsa saboda ya yi ?o?arin taSa min ke. Tsananin kishinki da na ji a lokacin shine ya kai ni ga aikata hakan. Ban fahimta ba, ban kuma gane ba, amma na tabbatar da daga wannan lokacin soyayyarki ta samu gurbi a zuciyata. Tunda aka samu kishi tabbas akwai soyayya, yadda hankalina ya tashi na dinga yiwa Hajja faWa ni kaina abin ya bani mamaki. Kuma gashi lokacin da ?uruciya a tare dani, amma na ruWe a kan abinda aka yi ?o?arin yi miki, in ba soyayya ba meye Jidda!?." ya ?arasa faWa yana kallonta.

Ya Wan taSe baki kaWan yana kallon ta ta ?asan idanu ya ce, "Ashe faWan da na yi akan abinda ya ke mallakina kuma halak Wina ne, ashe na suturta jikinki ne da rigar jikina saboda abinda na rufe Win nawa ne ban sani ba." Kunya ya bata mai nauyi, ta koma jikinsa ta rufe fuska tana murmushi. Murmushin shima ya yi ya ri?e ta yana lumshe ido, bai ce komai ba sai ?hamshin ta da yake sha?a wanda ya zauna daram a jikinta.

Shifa ya Wauka zancen Didi ne da ta ce kalamai suna fitowa daga zuciya, amma yanzu ya tabbatar dan baya sanin mai zai furta sai bayan ya furta Win.

Shiru ya tsara tsakaninsu, sun jima a haka yana shafa kanta zuwa bayanta idanunsa a rufe itama kuma na ta idon a rufe. Gently ta ji ya ce, "?arin wani abu Waya! A kan ki Omar ya fara kwanciya a asibiti. A yadda Allah ya halicce ni ban cika rashin lafiya ba a rayuwata, amma a kan ki nayi zazzaSi da ciwon ?irjin damuwar barinki gidan nan, sannan jiya na kwanta a asibiti saboda ke. Ki ?ara a lissafi." Murmushi tayi ta sake kwanciya a jikinsa ya cigaba da shafa kanta har ya gama maganar idanunsa na kulle.

"Jidda!."
"Uhum!."
"ki yi ha?uri idan son da nake miki yayi yawa, ki yi ha?uri in soyayyar ????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  da nake son gwada miki ta girmi ?wa?walwarki. Ban taSa jin irin wannan soyayyar a baya ba, shiyasa na baki kaina gabaWaya dan bana son na kwantanta irin zaman kaWaicin dana yi a baya. Tabbas zaki iya ganin za?ewata tayi yawa Jidda, ba dan komai ba sai don ke Win kin zama komai a gare ni da rayuwata."

?ago ta ya yi daga jikinsa, ta kalle shi kamar yadda yake kallonta ya ce, "in zamu kwana ina faWa miki mahimmacin da ki ke dashi a rayuwata lokacin ya yi mana kaWan, ko da zamu kwana mu yini mu sake kwana bazan kai ?arshe ba, kawai ki saka a ranki Omar yana sonki, zai rayu dake a duniya, yana fatan rayuwa dake a aljanna."

Murmushi ta yi cikin tsananin farin ciki da ?aunarsa amma bata ce komai ba. Ya tashi tsaye ya ya fita bai ce mata komai ba, bai jima ba ya dawo ya yi shirin kwanciya ya ce, "na shigo?." Rufe ido ta yi da sauri dan rigar jikinsa ?arama ce ita kuma kallonsa ma tsoro yake bata.

A hankali ta Waga kai, ya tako ya shigo ya kwanta a gefenta bayan ya kashe hasken Wakin ya matso da ita jikinsa ya kwantar da ita a ?irjinsa. Gabanta ya faWi sosai, tsoron abinda ya faru jiya ya dawo mata a zuciyata, sai ta yi niyar mi?ewa zaune ya mayar da ita. Calmly ya ce, "bazan yi abinda zai cutar dake ba, na san abinda yake ranki Jidda, a jiyan ma yazo ne ba tare da an shiryawa hakan ba. Ki nutsu!." A sanyaye ta koma ta kwanta amma har lokacin a tsorace take dashi.

"Nifa har da yayanki na yi kishi, da ki ka rungume shi a gabana sai dai naji faWuwar gaba. Kin san ban iya Soye abu a rai ba shiyasa nake faWa miki, amma kishi na yi ba haushi na ji ba." Dariya tayi sosai jin yadda yake maganar a yangance, kuma ba tayi zaton zai sake magana ba sai gashi ya yi, sai abin ya bata dariya, wai kishi na yi ba haushi na ji ba.

Shima murmushin ya yi, a lokacin ya tuna? yayi kishi da Jawad, kuma yana so ya faWa mata kar ya manta. Dan shi bai iya Soye abu a rai ba, kuma yanzu ya na ganin babu wacce ta cancanci ta san duk abinda yake zuciyarsa kamar ita. Bai sake cewa komai ba sai shafa bayanta da yake yi a hankali duk da ya san babu lallai ta yi bacci tunda bata jima sosai da ta shi ba.

"YaMar!" Ta furta a hankali tana kwance a jikinsa ya ce, "Uhum!."
"Lokacin da mu ka je Kaduna, da Abiy ya ce ka dawo masa dani fa?."
"Zan dawo Kano ni kaWai na bar ki a can."
"Ka ce baza ka iya rayuwa babu ni ba....?"
"Rayuwar zata yi min wahala, amma gwara na barki a can da na dawo da ke baya so."

Nayla ta ce, "meyasa?." Ya yi ajiyar zuciya kaWan ya ce, "Zan faWa miki, amma yanzu ki kwanta ki huta." Nayla ta ce, "ni bana jin bacci." Ya ce, "ai baki da lafiya."
"Ni dai ka faWa min."

"Tunda na ce zan faWa miki zan faWa, amma yanzu ki huta." Shiru tayi bata ce komai ba sai daga baya ta sake cewa, "To Narma fa!?." Idanunsa a kulle ba tare da ya kalle ta ya ce, "Wace haka?." Ta kalli fuskarsa, sai ya buWe ido suka haWa ido a cikin ?aramin hasken Wakin, bata bashi amsa ba ta koma ta kwanta a jikinsa shima kuma bai sake cewa komai ba. Ta dole ya saka bacci ya Wauke ta yadda yake yamutsa mata gashin kai da shafa bayanta bata san ta biye masa bacci ya kwashe ta ba.
KRB3P054

A haka suka yini cikin kula da tattali da soyayya mai tsayawa a rai. Babu inda Omar ya je, ko sallah tare suke yi da sun idar ya cigaba da rarrashin masoyiyarsa. Iya kallon da yake yi mata kwantar mata da hankali yake yi, balle in ya buWe baki ya ambaci sunanta sai ta ji kamar babu wata macen a duniya bayanta.

Bayan sallar i'sha tana zaune a falon da ta saba zama tana shan alawar tom tom, idanunta a rufe ta jingina da kujera ta Waga kai sama kamar mai tunani. Bata jin daWin jikinta ko kaWan, ji take kamar iska zata kwasheta ta watsar a wani waje. Ga raWaWin da take ji a cikin jikinta, dauriya kawai take yi amma a takure take.

Motsinsa ta ji a kusa da ita yana, ya zauna a kusa da ita sosai ya ce, "Gata nan." Jin abinda ya ce sai ta buWe ido ta kalle shi kamar yadda yake kallon ta. Ta Wan gyara zama kaWan ta Wauke kai daga kallonsa. Muryar Didi ta ji daga wayar ta ce, "bani ita mu gaisa." A sanyaye ta ji ya ce, "tana jin ki." Didi ta ce, "Nayla!." Nayla a raunane ta ce, "Na'am Didi, ina yini."
"Lafiya lau Nayla, ya jikin na ki?."
"Da sau?i Didi."
"Allah ya ?ara lafiya."
"Amin. Ina Marmerh?."
"Gata nan tana bacci."

Omar kallon ta kawai yake yi, ?hamshin alawar da take bakinta yana shiga hancinsa saboda kusancinsa da ita. Ya lumshe ido yana kallon bakin ta da take motsa shi cikin rauni da shagwaSa. Ta buWe baki zata sake yiwa Didi magana ya haWe bakinsa da nata, wayar hannun Nayla ta suSuce ta faWi a kan carpet, ta zaro ido waje jin yana shanye alawar da take bakinta a nutse. Gabanta faWuwa yake yi, ta motsa kaWan ko zai cikata amma bai sake ta ba sai sake ri?e fuskarta da ya yi.

Omar idanunsa a lumshe yake, za?i da yajin tom tom Win da take bakinta yake haWWiyewa a cikin salo na soyayya da shau?inta da yake mamaye masa jiki. Nayla ?irjinta bugawa yake yi, tsoro da fargaba suka mamaye mata zuciya. Jikinta ya fara rawa ba tare da ta shirya ba, hawaye ya fara sakkowa daga idanunta. ?umin hawayenta ya ji a kan fuskarsa, ya buWe ido ya kalli fuskarta yaga hawaye take yi amma idonta a rufe yake. A hankali ya zame bakinsa ya haWe goshinsu waje Waya a lokacin kukanta ya samu damar fitowa.

Kuka take yi mai sauti jikinta yana rawa, ya rungumeta yana shafa bayanta a hankali tana cigaba da kukan. Yadda jikinta yake rawa ne ya saka shi ya matse ta a jikinsa yana so ya samar mata da nutsuwa da kwanciyar hankali. A hankali kukan nata ya ragu, ta Wago daga jikinsa tana jan numfashi idanunta a rufe saboda kunyar da take ji.

Fuskarta ya Wago yana kallo, ya saka hannu ya share mata hawaye ya ce, "Ina ma Omar zai zama hawayen da suke sakkowa daga idanunki, ina ma ni ne hawayen da yake fitowa daga idonki ya samu masauki a kan kuncin. Inda na kasance a haka da zan fi kowa farin ciki, dan na san zai rage min kewar ki da nake ji a zuciyata. Zan kasance a cikin idonki kullum, sannan in na tashi fitowa zan sakko akan kyakykyawar fuskarki!" Ya faWa yana ri?e da kumatunta yana shafawa da yatsa Waya.

Bata buWe ido ba tana jin abinda yake faWa, a tsorata take dashi sosai, zuciyarta bugawa take ji tsoro ya mamaye ko ina na jikinta. Kafin ta yi magana ya ce, "Me ki ke so ki ke kuka? Me yake damun ki?." Kawai sai ta sake fashewa da kuka ta kwanta a kafaWarsa ta ce, "Ni Kaduna zan je wajan Abiy!." Bai Wagota daga kafaWarsa ba sai hannunta da yake cikin nasa ya ce, "Bakya son zama dani?." Ta girgiza kai alamun a'a sannan ta ce, "Wajan sa nake son zuwa" ta faWa cikin kuka.

A hankali ya Wago ta yana kallon yadda hawayen suke sauka Waya na bin Waya, matso da fuskarsa ya yi kusa da ta ta, ya sanya harshe ya lashi hawayen cikin sacan biyu. Jin Wumin harshensa sai ta buWe ido suka haWa ido, ya Waga mata gira Waya sai ta mayar da ido ta rufe gabanta yana cigaba da haWuwa.

A taushashe ya ce, "Yanzu ki ke so ki tafi Kadunan?." Da sauri ta Waga kai alamun eh. Ya yi murmushi mai sauti ya ce, "Ni kuma sai ki bar ni


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login