Showing 45001 words to 48000 words out of 332344 words

Chapter 16 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14393

dawo jikinta, Abin ka da abinda zuciya take so.

Kafin ta yi magana ya sake shan tea Win sannan ya ajjiye. Magani ya Wauka ya Salla ya saka a baki, da sauri ta bashi ruwa a glass cup ya karSa ya sha ya ajjiye. Kulle ido ya sake yi ya yi shiru bai ce komai ba.

Nayla tea Win ta Wauke da ruwan da ya gama sha ta kai dining ta dawo a hankali ta ce,  YaMar ka ci koda irish Win nan ne aka ji daWi, ka ga baka ci komai ba tun jiya. Bai ce komai ba ta zauna nesa dashi tana kallo kamar ta dawo da ciwon kan jikinta haka take ji. Duk da ba wani shiri suke yi dashi ba in yana da lafiyar hakan bai hanata ta ji kamar ta rage masa ciwon ta hanyar kawo shi jikinta ba.

Yana kallon ta ta ?asa ido yadda ta marairaice fuska tana kallonsa, alamun tausayawa ya bayyana ?arara akan fuskarta. Mamaki ta bashi ganin yadda ta damu da ciwon sa haka, sai ya ji daWi a ransa ko babu komai bayan Didi ya samu wacce ta damu da rashin lafiyarsa a karo na farko.

Har aka fara kiran sallar i sha suna a haka, bayan an gama kiran sallar ne ya mi?e zaune sosai ya buWe ido ya mi?e ya fita. Sai sannan ta iya tashi ta yi sallah kasancewar babu tarawee tunda ga watan sallah. Tana idarwa shafa i wutir ta yi, bayan ta idar ta dawo falon ta zauna dan ya dawo a kan idanunta. Ba jimawa sai gashi ya shigo ta amsa sallamar da ya yi ta mi?e tsaye tsaye ta ce,  YaMar ya ciwon kan? Ka samu ka ci abinci zaka fi jin daWi.

Ganin ya yi shiru ya ?araso inda ya zauna ya Wauki wayarsa da ya bari a wajan da kuma wani abun a leda. Nayla ta ?arasa ta zuba masa fried rice da kazar wacce ta rage zata ci, ta ?araso a lokacin zai bar wajan ta ce,  don Allah ka ci abinci. Kallon abincin ya yi ya kalle ta ya ce,  na ji sau?i, na gode abinda ya ce kenan ya wuce ta.

Nayla sai taji daWi ya mamaye mata zuciya, ko bai ci abincin ba iya wannan godiyar da ya yi mata ta fi ya biya mata aikin hajj saboda yadda ta ji daWi har cikin zuciyarta. Murmushi tayi cikin jin daWi ta ajjiye plate Win ta shiga ciki zuciyarta cike da farin ciki.
KRB3P014
Arewabooks@nanahaleema11.

Washe gari da wuri Nayla ta tashi tayi wanka ta shirya cikin Waya daga cikin lace Win da ya bata. ?inkin ya yi mata kyau Winkin doguwar riga mai faWi kuma mai kyau sosai, daga ciki wajan ?irji an kama rigar kaWan amma daga ?asa sai tayi faWi, daga baya kuma a buWe take bata kamata ba ko kaWan. Kallon kanta take yi a madubi dan tayi kyau lace Win ya amshe ta. Waya ta Wauka a lokacin ?arfe bakwai da wani abun na safe, ta yi selfie tana murmushi.

"In dai akwai masallaci a kusa gaskiya zan je sallar Eid" ta faWa ita kaWai tana kallon kanta a madubi tana murmushi. Key Win motarta ta ke nema tana dube-dube bata ganshi ba sai ta fito falo tana dubawa.

Turus Nayla tayi ganin Omar ya fito daga Waki cikin men lace fari mai ?ananun zane, kansa Wauke da? hula rantsatstsiya mai shegen kyau sai ?yalli take yi, gashin kansa ya kwanta a baya sai kyalli yake yi ya sake yin ba?i sosai. Fuskarsa a washe yana murmushi da waya a kunnensa, hakan da ya yi sai ya bayyanar da kyau da kwarjinin da Allah ya yi masa. Hatta takalmin ?afarsa fari ne, ya haska ?afarsa sosai ya fito sak a matashin Alhaji, in ka ganshi, ka kalle shi sai ka so ka sake kallonsa.

Nayla zuciyarta narkewa tayi a kallonsa ganin yadda ya yi mata kyau fiye da kullum a duniya. Ya yi kyau matu?a wanda ya wuce tunaninta har bata san ta tsaya cak tana kallonsa ba. Cikin sanyin murya taji yana cewa, "Eid bana ya shiga tarihi, Didi bata tashe ni zuwa masallaci ba na tashi har na shirya zan tafi." Maganarsa ce ta dawo da Nayla hankalin ta, ganin yadda yake amsa wayar ya tabbatar mata da Didi yake yin waya shiyasa yake murmushi.

Juyowa ya yi suka haWa ido, shima sai ya yi sak yana kallonta ba tare da ya san ya tsaya Win ba. Yadda ta ga ya yi mata kyau shima abinda ya gani kenan a tare da ita, bai lalace a kallonta kamar ita ba taji ya ce, "Gata nan." Jin abinda ya ce ta san Didi ce take tambayarta, bata gama mamaki ba taga ya mi?a mata wayarsa ?irar iPhone 14 pro max. Nayla kallon wayar tayi ta ga seconds suna tafiya ga sunan Didi a rubuce a jikin wayar.

Hannu ta saka ta karSa ta saka wayar a kunne Nayla ta ce, "Didi Ina kwana." Didi ta ce, "Kin tashi lafiya Nayla? Ya Shirin zuwa sallah, amma dai zaki je masallaci ko?." Nayla ta ce, "Ina tunanin zuwa."

"Ya kamata dai ki je Win, ai rai ne ya kawo mu. Da farko da na tambaye shi ya ce min bai san kina ina ba, ashe kuna tare."
"Yanzu na fito na ganshi."
"Na kira na tuna masa yau fa da masallaci, duk da na san aikin ki ne. Ayi ha?uri na tuna waccen shekarar ne shiyasa na kira shi."

Murmushi Nayla ta yi ta ce, "kin kyauta Didi. Babu inda zaki je anjima nazo?."
"Zan je gidan su yallaSai, a ka'idar gidan su ana haWuwa duk ranar sallah. Sai dai gobe in Allah ya kaimu."
"Allah ya kaimu Didi."
"amin. Maza ki shirya ki tafi masallaci, nima yanzu zan tafi" ta faWa tana yanke wayar.

Tunda ta fara wayar tana murmushi yake kallon ta, a rayuwarsa bai taSa ganin wacce murmushi ya ke yiwa kyau kamar ta ba, da zarar ta murmusa dimples Winta sun bayyana akan kumatunta, siraran ha?oranta masu haske sun fito waje sai yaga kamar duk duniya babu wacce murmushi yake amsar fuskarta kamar ta. Murmushi na ?awata fuskarta sosai, da zai iya da ya faWa mata ta cigaba da yi yana samun masauki mai kyau a fuskarta. Ga murmushin nata da arha ko yaushe yi take yi, amma in tayi sai ka sake kallo saboda yadda yake haska fuskarta.

?ago idon da tayi hakan ya saka ya Wauke ido daga kallonta, ta tako kusa dashi ta bashi wayar, ya kalli wayar da take mi?o masa ya mi?a hannu zai karSa idanunsa ya yi karo da zanen ba?in henna da yake hannunta. Jiya ya kula dashi a hannunta, amma da yake bashi da lafiya bai kula sosai kamar yau ba.

Kamar bai gani ba ya karSi wayar ta kalle shi ta ce, "Ina kwana, ya jiki? Ina fatan ka ji sau?i." Bai kalle ta ba ya ce, "da sau?i" ya faWa tare da motsawa zai bar wajan. Sai ya tuna bai Wauki sallaya ba, Wakin ya koma da niyar Waukowa sai ya ga sallayar bata yi masa ba duk da babu abinda tayi, ba dauWa ba komai amma bata yi ba.

Fitowa ya yi yana kiran wayar Bash yana Wauka ya ce, "Fito min da sallaya zan tafi masallaci." Kafin ya ?arasa fita Nayla ta juya da sauri ta koma ciki, ta Wauko sallaya mai kyau da laushi harda feda mata turare ta dawo ta tarar dashi zai fita daga gate Win gidan.

Tsayawa tayi ta ce, "YaMar!." Sai dai ya kulle ido ya buWe jin sunan har ?wa?walwarsa sai da ta harba. Kamar kar ya juya sai kuma ya juyo a hankali ta ?araso ta ce, "Ga sallaya." Kallon hannunta yayi da take mi?o masa ya kalli fuskarta ta ce, "don Allah" ta faWa kamar zata yi kuka.

Ganin ya?i karSa sai ta tako gab dashi ta rataya masa a kafaWa ta juya da sauri ta koma ciki har tana gudu. Murmushi ya yi ya kalli sallayar kafaWarsa itama fara kamar kayan jikinsa, ya Wauke ta daga kafaWarsa ya ri?e ya fita daga gidan.

Tana kallon sa ta window har ya fita tayi dariya ta shiga ciki a guje ta Wauko mayafi ta yafa akan ta kasancewar rigar jikinta zata yi sallah. Key Win mota ta Wauka sai kuma ta tuna akwai babban masallacin juma'a a gaban layin ba za a rasa yin sallar Eid ba. Ajjiye key Win tayi ta fito ko sallaya ita bata nema ba ta kulle gidan ta tafi a ?afa.

Ai kam babu nisa daga gidan, ta tarar har za a tayar ta shiga sahu ta samu space na wasu mata da suke tsaye ta shiga ciki aka tayar da sallah. Bayan an idar tana ta gani ana ta hotuna amma ita murmushi take yi mutanen sun burge ta. Kowa ya sha kwalliya ana murnar sallah, ko iya ganin mutanen ma ai rahama ne.? A hankali take takawa wasu mata su biyu baza su wuce sa'aninta ba suna bayan ta suna ta gulamarta.

"Na rantse da Allah itace matar Tiger, kan bala'i daman haka take kyakykyawa?. Ita kuma Wan daba take so? Amma dai ta cuci kanta, ko da yake kyaun fuskarsa ta aura."

Nayla tana jin su tayi murmushi tana cigaba da tafiya a nutse. Juyowa tayi ta kalle su duk sai suka Wauke kai cike da jin kunya bata ce komai ba ta saka key ta buWe gidan ta shiga ciki.

Nayla hutawa tayi a gida kafin ta kira mutanen Saudia tana yi musu barka da sallah. Abiy ta fara kira bayan sun gaisa ta yi masa barka da sallah ya amsa daga nan ta kira kowa har su Hajja da Salma. Bayan ta gama ta koma ta zauna tana ajiyar zuciya tana tuna abinda mata nan suka ce, taSe baki kawai ta yi ta cigaba da danna wayar ta.

Cousins Winta ne suka zo hakan ya saka ta farin ciki suka zauna suna hira suna hotunan sallah. Omar ko da ya dawo ya zo shiga ya ji hayaniya zai ya koma ya fita daga gidan gabaWaya dan shi baya son ba?i Allah ya sani, ya fi son rayuwarsa shi kaWai kar wasu su dame shi. Sai dare suka tafi ta ji daWin zuwan su sosai tare suka yi girki aka ci gabaWaya. Har glaze donut suka yi mai daWi ta saka sauran a fridge saboda ba?i.

Bayan sallar i'sha Omar ya shigo da sallama kai tsaye inda take zaune ya ?arasa yana kallonta. Nayla ta kalle shi ta ce, "Sannu da zuwa." Bai amsa ba sai gyaran murya da ya yi ya ce, "Kin raina ni ko?." Gaban Nayla ya faWi ta kalle shi alamun me na yi kana ta ce, "me na yi?."

"Kar na sake yi miki magana akan kuWin nan, in na sake yi miki magana baza ki ji daWi ba." Nayla tayi ajiyar zuciya dan tayi tunanin laifi tayi masa ta ce, "ai na yi lissafin, daman so nake ka zo na faWa maka."

"Uhu hum" ya faWa alamun yana jiran cigaban maganarta ta ce, "dubu Wari biyu ne" ta faWa kawai dan bata san ne zata ce ba, ta kashe kuWi a kalla ya yi miliyan Waya da wani abun, amma saboda kar ya ga kamar ?arya take in ta faWi asalin kuWin, kuma tsakani da Allah ta yi masa shiyasa ta ce haka.

Bai ce komai ba ya wuce zai bar wajan ta ce, "Akwai abinci." Ko kallon ta bai yi ba ya wuce cikin Waki. Ta bishi da kallo ta ce, "wannan ka rasa gane kansa."

Washe gari kasancewar an tafi sallah break babu batun zuwa aiki sai ta yi niyar zuw??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a gidan Didi da kuma gidan Mama Sa'adatu. Didi ce ta kira ta a waya ta ke sanar da ita kar ta ce zata je ta shigo cikin gari ita da AbdulHamid. Ranar gabaWaya bata ganshi ba, ko motsinsa ma bata ji ba, duk ta damu tana so taji ko ciwon kan ne ya sake dawowa bata sani ba. Kuma ita bazata iya shiga Wakinsa ba, gwara ta zauna ta jira shi in y fito sai su haWu.

Tana zaune gab da sallar azahar ita kaWai tana cin donut din ta na jiya aka yi knocking gate Win gidan. Hijjabi ta saka akan atamfar jikinta ta fita ta buWe. Bin matan take yi da kallo kamar ta san fuskarsu amma bata gane su ba, suna yi mata kama da wanda ta taSa gani amma sai ta kasa tunawa saboda basu yi kama da hausawa ba ko a shigar su.

?aya daga ciki ta yi murmushi ta ce, "Sannu ?ata, Don Allah nan ne gidan Omar?." Nayla ta yi murmushi ta ce, "eh nan ne."
"Na san baki san mu ba, Mu dangin mahaifiyarsa ne." Nan da nan fuskar Nayla ta washe da annushuwa ta ce, "Lah sannun ku da zuwa, bismillah ku shigo."

Suka shigo ta rufe gate Win daya daga cikin mutane ukun ta ce, "Allah yasa baya nan." Nayla ta ce, "baya nan, mu shiga" ta faWa tana yin gaba suka biyo ta a baya. A falo ta sauke su da fara'ar ta kaso musu ruwa da drink harda ragowar cincin da donut, ta haWo da fruits kankana da apple harda ?ar ?aramar wu?a ta yanka apple duk ta kawo musu ta ajjiye.

Zama tayi ta ce, "Ina yini." Suka amsa da fara'a suna tambayarta anyi sallah lafiya, ta amsa da lafiya lau. ?aga daga cikin su wacce ta kasancr babba a cikin su ta ce, "Ni sunana Zainab ni Yayar mahaifiyarsa ce, dani da mahaifiyarsa uwa Waya uba Waya, ni take bi. Wannan ?anwar mahaifiyarsa ce sunan ta Aisha mai sunan Yayarsa kenan, wannan kuma sunan ta Saroot."

Nayla ta yi murmushi cike da jin daWi ta ce, "ina ta tunanin inda na san fuskar, ashe a bikin Didi ne na Wan ganku kaWan.." murmushi suka yi? wacce tayi magana ta ce, "Tun farkon auren ku muka so mu zo sai aka shiga azumi, shiyasa yau na ce tunda mun shigo cikin gari zamu zo mu gaisa. Na san duk baki san mu ba, baki san kuma labarin mu ba. Ganin da ki ka yi mana a bikin Aisha ai baki san su waye ba, kin Wan gan mu ne kaWan kin wuce." Nayla ta girgiza kai cikin girmama su ta ce, "gaskiya na ji daWi sosai."

Saroot ta ce, "mu ma mun ji daWin ganin ki, ko babu komai zamu dinga zumunci. In ba haka ba za a iya haWuwa a hanya kowa ya wuce bamu zan juna ba, hakan kuma babban abin kunya ne a gare mu." Nayla sai murmushi take yi Saroot ta ce, "ki saka min number ki a nan." Nayla ta karSi wayar ta saka mata number ita kuma ta kira ta dan Nayla ta ga number.

Mama Zainab ta ce, "Ya sunan ki?." Nayla ta ce, "Hauwa, amma Nayla ake ce min."
"Ma sha Allah, ga ki kyakykyawa kamar mijin naki, ina ta so na gano dake dashi waye ya fi kyau." Murmushi tayi tana sunkuyar da kai ita a lallai tana gaban sirikai. Mama Aisha ta ce, "An ce ?ar Kaduna ce ke ko?." Nayla ta ce, "eh a Kaduna nake, iyayena kowa yana can."
"Ma sha Allah. Allah ya ba ku zaman lafiya ya baki ha?urin zama da Omar."

Ta amsa da amin tana murmushi tana mamakin kenan shi kowa ya san halin sa. Nayla ta mi?e tana cewa, "bara na kawo abinci." Mama Zainab ta ce, "ki barshi Nayla, ki yi zaman ki yanzu zamu wuce."
"Don Allah Mama ku tsaya ku ci."
"Zamu ci wata rana, yanzu sauri mu ke yi." Nayla ta zauna ta ce, "to ga cincin ku ci don Allah Mama." DaWi Mama Zainab nake ji jin matar Omar na ce mata Mama hakan ya shiga har zuciyart.

Cincin Win suke ci har da donut Win sun Wan taSa, Umma Saroot ita duk tsorace take bata so Omar ya shigo ya yi musu abinda ya saba shiyasa ta ?agu su bar gidan duk da kirkin Nayla ya kwanta mata a rai. Tsarabar kayan ?hamshin gida dana jiki suka bata, Nayla ta karSa tana godiya dan da yawa kuma akwai ?hamshi sosai.

BuWe ?ofa suka ji anyi tare da shigowa duk suka juya kalli wanda ya shigo. Nayla ta san shine kawai yake shigowa ba tare da ya buga gate ba, shiyasa tana jin an shigo ta san shine hakan ya saka ta kalle shi tana so ta ga wanne irin farin ciki zai shiga. Dangin mahaifiya ai ba wasa ba ne, ko ya ka ga naka sai ka ji daWi zuciyarka; balle su ace a kaf dangin sa sune ziyarar farkoa? gidan.

Nan da nan ya Waure fuska tamau ganin wanda suke zaune a falon, ?are musu kallo yake yi Waya bayan Waya kafin ya kalli Nayla da take kallon sa da murmushi. Wani irin Sacin rai ya ji ya mamaye masa zuciya, ya rufe ido ya sake buWewa yana kallon su. Fuskar Zainab ya kalla nan take lokacin da suka kore su shida Didi ya dawo idanun sa, da yanayin wula?ancin da suka dinga zazzaga musu kamar ba jinin su ba ya cigaba da yawo a idanunsa.

"Omar barka da zuwa, da fatan an yi sallah lafiya." Mama Zainab ta faWa tana kallonsa da murmushi duk da ta san bazai amsa ba. Ai kuwa bai amsa Win ba sai ma wucewa da ya yi ba tare da ya ce pim ba. Mama Aisha ta mi?e ta ce, "Kun ga ku zo mu bar gidan nan tun kafin ayi abinda aka saba, gidan su ma in mun je ba wanyewa lafiya ake yi dashi ba balle kuma cikin gidansa. Nayla zamu dinga zumunci a waya" ta faWa tana fita.

Nayla sai ta ji wani iri ganin irin abinda Omar Win ya aikata, dangin mahaifiyarsa kuma yayar mahaifiyarsa ce ma tayi masa magana ya yi mata banza ya wuce. Sai ta ji sam bata ji daWi ba kuma bai kyauta ba, da tana da iko dashi da ta nuna masa yayi kuskure babba.

Mama Zainab ta kalli Nayla tayi murmushi ta ce, "A yanayin yadda auren ku ya zo babu lallai ki fahimci


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login