Showing 114001 words to 117000 words out of 332344 words

Chapter 39 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14389

gani? Ki goge yanzu sai mu yi magana." Yana faWa ya yanke wayar. Ba jimawa ya sake kira ta ce, "To Omar na goge."
"Na gani. Kar ki sake Wora hotonta a status. Ina Marmerh?."
"To ubana. Ga Mamerh tana bacci a kusa dani."
"Ki shafa kanta a madadina, zan zo na ganta."

Didi ta yi murmushi ta ce, "To sai ka zo, tunda dai kana ta cewa zaka zo baka zo ba." Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba Didi ta ce, "ya dai?." Omar ya ce, "dama ta zo gidanki jiya?." Didi ta ce, "kaima ka san ta ya za a ce bazata zo sunan Marmerh ba?." Ya girgiza kai cike da jin haushi ya ce, "tana ta zuwa inda take so ba tare da izinina ba." Didi ta yi murmushi ta ce, "To ai ita kaga...." ?aramin tsaki ya yi ya ce, "kar ki kira abinda zai Sata min rai don Allah."

Didi ta ce, "shikenan Omar, amma yanzu ya ake ciki da maganar?." Omar ya ce, "Ina gab da kasa jurewa Didi, na yi ha?urin, nayi juriyar amma abin yana neman yafi ?arfina." Didi ta ce, "ka kira ta a waya?." Ya girgiza kai kamar tana gabansa ya ce, "tunda aka ce na bata lokaci shine na bayar, bana son yin abinda za a ga rashin kyautawata shiyasa ni ko waya ban kira ta ba."
"Kana kewarta sosai ko?."
"Fiye da yadda zan faWa miki Didi, ban san me zan ce miki ki gane ba." Didi ta ce, "to ka je gidan ka same ta mana."

"Didi ban son na je ayi min wani abun raina ya Saci wani abun ya faru, a karo na farko ina gudun Sacin raina a wani waje."
"Ranka bazai Saci ba in sha Allah, ka je ka sameta."

"Didi gaskiya bazan je ba." Didi ta ce, "to ai shikenan, sai ka cigaba da jiran tsammani" ta faWa dan ta san bazai iya jurewa ba. Katse kiran ya yi ya nemo number Nayla da har lokacin bai yi saving ba, ajiyar zuciya ya yi kawai ya kira number.

? ?? Nayla a lokacin tana zaune an gama turara mata jiki kenan ta ga ana kiranta, kamar baza ta Wauka ba sai kuma ta Waga ta ce, "Hello." Shiru ya yi bai amsa ba jin saukar muryarta har cikin ?wa?walwarsa. Tsaki ya ji tayi ta katse wayar ya kifa wayar a kirjinsa yana lumshe idanunsa.

Nayla tana katse wayar Mama ta shigo Wakin ta kalle ta ta ce, "Daddy yana ta faWa wai kin yi shiru, na ce masa kin amince kawai muna Wan gyare-gyare ne, yana ta faWa ya ce ki koma a wannan satin."

Nayla ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba, Mama ta ce, "Ko baki son komawa ne?." Nayla ta yi shiru Mama ta ce, "Nayla faWa min abinda yake ran ki, kin ce kin amince amma yanzu ina ganin kamar baki son komawa." Nayla ta ce, "Mama har yanzu ko waya bai sake yi min ba balle ya zo, Ina ganin kamar baya so na koma."

Mama ta yi murmushi ta ce, "Yana so mana Nayla, dan bai yi miki waya ba ko bai dawo ba ba hakan yana nufin baya sonki ba. Tunda har yaje gaban iyayenki yana sonki wallahi, wata?ila bai neme ki ba saboda lokacin da aka ce za a baki." Nayla ta ce, "Mama ni sai nake ganin kamar baya so ne kawai." Mama ta shafa kanta ta ce, "Kar ki damu yana sonki, yana kuma so ki koma da ra'ayin kan ki ba dan tilastawa ba." Nayla ta goge idanun ta bata ce komai ba.

? Da yamma Salma da Jidda suka zo gidan suka dinga rarrashinta amma ta kasa fahimta ita gani take yi kawai ba sonta yake yi ba tunda bai neme ta ba. Salma ta ce, "kema kin cika rigima wallahi, kin san halin mijin nan naki meye zai dame ki? A ganina ai tunda har ya kalle ki ya ce bazai sake ki ba, sannan ya faWa a gaban su Daddy me zai dame ki kuma?." Nayla ta ce, "gani nake kamar...." Jidda ta katse ta ce, "Haba me ki ke so ya yi miki kuma? Ke ki ka ce sai an baki lokaci, an baki lokacin kuma kin damu."

Nayla ta yi shiru bata ce komai ba. Wayar ta ce ta yi ?ara ta duba ta ga number ce sai kawai ta Wauka ta saka a speaker ta ce, "Hello."
"Ina cikin gidan da ki ke, zan iya ganin ki?." Gabanta ya faWi ta kalli su Jidda da suke kallon ta ta ce, "waye ya ke magana?."
"Ki zo zaki gani" yana faWa ya yanke wayar Nayla ta bi wayar da kallo.

Sai kuma ta yi ihu ta faWa jikin Salma suka rungume ta Jidda ta ce, "Wai ke nufin ki Omar Win ne?." Nayla ta ce, "wallahi shine Twiny, ko a mafarki zan gane maganarsa." Jidda ta ce, "to ga abinda mu ke faWa miki ya tabbata." Murmushi ta yi tana goge idanuta.

Salma ta ce, "ya aka yi ya san kina gidan nan? Sananan kuma ya aka yi ya san gidan nan?." Nayla ta ce, "ban sani ba." Jidda ta ce. "yanzu dai a faWawa Mama zuwansa sai ki je ki sha kalaman soyayya ki dawo." Murmushi ta yi ta kalli Mihada da take gefe tana bacci ta shafi fuskarta.

Salma ce ta faWawa Mama batun zuwan Omar ta aika ta ta ce taje ta shigo dashi. Salma ta yi mamaki gani sa a mota a zaune a wajan gate Win gidan dan bai shigo ba. Salma ta ce, "Barka." Kallon ta ya yi sarai kuma ya gane ta, da?yar ya buWe baki ya bata amsa. Salma ta ce, "Mama ta ce ka shigo." Omar bai ce komai ba ya fita ya bi bayanta zuwa gidan. Salma sai gulmarsa take yi a zuciyarta har suka shiga cikin gidan.

Yadda suka gaisa da Mama abin ya burge shi sosai itama ta saki fuska sun gaisa sosai, aka kawo masa ruwa da lemo da bowl wanda aka zubo cincin a ciki da kayan motsa baki. Ba jimawa Nayla ta shigo da sallama ya amsa ba tare da ya kalle ta ba, dan yana so ya yi mata warning akan fitar da take yi babu izininsa, in ya kalle ta tsaf zai kasa aikata abinda ya zo aikatawa.

"Ina yini" Nayla ta faWa a sanyaye ba tare da ta kalle shi ba. Ba tare da ya kalle ta ba ya ce, "Baki tambayi waye ba amma kin fito, in da ba ni Win bane ba fa?." Nayla ta Wago ta kalle shi ta ga ba ita yake kallo ba sai wani basarwa take yi fuskarsa a Waure.

Murmushi ta yi ta sunkuyar da kai ta ce, "Salma ta sanar dani." Omar babu walwala akan fuskarsa ya ce, "Meyasa ki ke fita ba tare da na sani ba?."

Sai a lokacin ya kalli fuskarta ya ga abinda yake matu?ar Waukar hankalinsa akan fuskarta, yadda take kifta idanu kamar mai jin yaji a cikin idom, ganin motsawar idonta yana sakawa ya tsayar da idonsa ?yam a kanta. ?ago ido tayi ta kalle shi ta ga ita yake kallo, ya buWe Wan idanunsa akan fuskarta ya ce, "meyasa?."

Nayla ta sauke kai ?asa, ta daure ta jure dan tana son gwada yanayinsa ta ce, "har yanzu ai ban gama yanke hukunci zama da kai ba." Kai ya girgiza ya ce, "kafin ki yanke Win har yanzu matata sunan ki, kinsan abinda zaki yi ai." Nayla tayi shiru bata ce komai ba. Omar ya zuba mata idanu dan gani ya yi ta ?ara yin kyau sosai, umarnin zuciyarsa kawai ya bi saboda ya kasa jurewa sai da yazo ya ganta, gashi ya zo sai wani shan ?hamshi take yi masa.

"Yaushe zaki dawo?." Ba zata taji maganar kuma a hankali ya furta sai ta kalle shi ya Waga mata gira alamun ina jinki. Nayla ta kawar da kai dan gabaWaya fuskarsa babu walwala kamar ba shine ya je gidan Daddy yana murmushi ba. Nayla ta ce, "bana tunanin zan dawo saboda ka riga da ka gama cire min son zama da kai a zuciyata, gabaWaya ka karya min zuciya."

Kallon ta ya yi yana mamakin kansa, wai shine zaune a gaban wata mace tana faWa masa kalaman da ba su yake da ra'ayin ji ba. Lallai soyayya ta canja shi, abinda ta rage a halayensa kaWan ne ya rage. Omar ya yi shiru bai ce mata komai ba, sai da aka Wan jima kaWan sannan ya ce, "baki ha?uri ba?." Ta Waga kai ta kalle shi ta ce, "ha?urin nake so na yi amma na kasa, tun daga ranar da ka je gidan Daddy baka sake koda nemana ba ta ya zan Wauka kalamanka na gaskiya ne?. Na kasa ha?uri, ina so na ha?ura amma zuciyata ta riga da ta....." HaWa ido suka yi sai ta kasa maganar ta Wauke kai daga kallonsa.

Shi kam Omar bai san me zai ce mata ba kuma, tunda har tana Waukar kalamansa na ?arya ne bai ga abinda zai mata wanda zata yarda ba, gwara kawai ya yi shiru kar ya furta abinda zai tarwatsa mata zuciya. Shiru ya sake ratsa tsakani kafin ya ce, "Kalaman nawa ki ke Wauka na ?arya? Kina tunanin zan zauna a gabanki na yi miki ?arya ne dan na burge ki ko dan ki dawo rayuwata?...Hmm." Nayla ta yi shiru bata ce komai ba, ta Wago ta ga ya zuba mata ido kawai yana kallon ta da alama ya rasa abinda zai ce mata.

Shi kuwa Sacin rai yake ji a zuciyarsa, na farko tana fita bai sani ba, na biyu tana kallonsa tana cewa kalamansa na ?arya ne. Ba dan soyayyarta da yake ji a zuciyarsa ba da kuWi aka ce ta faWa masa abinda ta faWa baza ta iya ba.

Ya girgiza kai ya ce, "ba a haifi wanda zan yiwa kalaman ?arya dan na burge shi ba, haka ba a haifi wanda zan bawa hakuri ba tare da na san na yi laifi Ina so na gyara ba" mi?ewa tsaye ya yi ya kalle ta ya ce, "ki yi tunani yadda ya kamata, ki yi tunani daidai da ra'ayinki da kuma abinda ki ke so. Abu Waya zan sake maimaita miki bazan rabu da ke ba, amma in ki ka yanke hukuncin ki ka ji a zuciyarki kin gama zama dani zan yi abinda ki ke so" yana gama faWa mata haka ya fita dan ransa ya Saci zai iya hargitsewa a gidan mutane gwara ya kama kansa ya bar gidam hakan zai fi alkaihri.
KRB3P042
Arewabooks@nanahaleema11.

Yadda Nayla ta shiga a sanyaye ya saka Jidda da Salma tambayarta abinda ya faru. Zama tayi akan gadon ta kalle su ta ce, "Na faWa mu ku kamar baya sona ma gabaWaya." Salma ta ce, "ya taso ya zo gidan nan saboda ke kuma kice haka? Wai kin manta waye Omar Win ne? A ganina tunda har ya zo zancen so ya kamata ki rufe shafinsa." Nayla ta ce, "gabaWaya babu karsashi da zumuWin son dawowata a gare shi, na Wauka zan ga yana zumuWin na dawo amma sai naga ba haka bane."

Jidda ta ce, "me ki ke so ya yi miki a gidan sirikansa?." Nayla ta ce, "Amma yadda ya yi min magana a gidan Daddy daban da yadda ya yi yanzu. Sai Waure fuska yake yi, wai ina fita ba tare da izininsa ba." Salma ta yi dariya ta ce, "ko a nan baki fahimci soyayya bace ba kenan?." Nayla ta ce, "ni kuma na ce har yanzu ban gama yanke hukuncin zama dashi ba, na Wauka zan ga ya cigaba da bani ha?uri sai na ga akasin haka. Domin kuwa cewa ya yi in na gama yanke hukuncin na sanar dashi zai yi abinda nake so."

Salma ta ce, "Wallahi kina da matsala, yanzu meye na dawo da maganar saki kuma don Allah?." Jidda ta ce, "da kin sani kin bari komai ya wuce, dole ya ce miki haka ai Nayla. Duk da dai zhima ya kamata ya nuna miki soyayya a bayyane." Nayla ta ce, "gabaWaya son komawar ma ya fita yake daga raina." Salma ta ce, "Sai ki yi ai." Nayla dai ta yi shiru bata ce komai ba amma gabaWaya zuciyarta babu daWi.

Shi kam Omar da matu?ar fusata ya koma gidan. Ya tsani maganar sakin nan, ko kusa baya so ayi masa zancen saki, amma shi yarinyar nan zata saka a gaba tana yiwa batun saki dan ta ga ma yana saurarenta.

Ko gidan bai je ba, gidansu ya koma ya zauna yana huci shi kaWai. Masifar da take zuciyarsa yake so ya saukewa wani shiyasa kawai sai ya kira Didi. Tana Wauka ya fara masifa ya ce, "Wai me yarinyar nan ya Wauke ni ne? Tana fita duk inda take so ba tare da na sani ba, tana yin duk abinda ta ga dama da aurena a kanta. Yanzu ni take kallo tana sake yi min maganar saki, dan wai tana ganin na je har inda take ne ko? Ni za a rainawa hankali ko Didi? Dan kawai ina sonta ina kuma so ta dawo rayuwata shikenan kuma sai raini ya shigo ciki!?."

Didi da take jin yadda yake masifa da mamaki ta ce, "Omar to ai ba ni ce Nayla Win ba ko? Wannan masifa da ka ke yi min kamar ni ce Nayla Win?."


"Ai faWa miki ke yi, na gaji da Waukar wannan abubuwan da yake faruwa, tana yin abinda take so ne saboda kawai ta samu dama daga wajena. Na kasa sarrafa kaina na kasa tsayawa akan matsaya guda Waya, ko yaushe cikin ?unar rai nake da damuwa duk a kanta. Har faWa min take yi wai kalamaina ba na gaskiya bane, ita an faWa mata ina yin ?arya dan na burge wani? Ko kuma Ina ?arya ne dan wani yaji daWi?. Ni ban ce ta karya min zuciya ba itace zata ce na karya mata zuciya? Ya yi kyau. Ki zama shaida, daga yau bazan sake maganarta ba, in ta ga dama ta dawo, in bata gama ba tai ta zama har a tashi duniya. Rabuwa da ita ne bazan yi ba, duk inda taje babu sanina kuma ita da Allah" ya faWa yana katse wayar a fusace tare da cilar da ita.

Fusata yake ji da ita har a jininsa, gabaWaya kansa ya kulle, zuciyarsa na bala'in bugawa sai girgiza kai yake yi shi kaWai yana cize baki cikin zallan takaici da ba?in ciki. Ranar ko fita bai yi daga gidan ba, a ciki ya kai har dare. Sai daren ya Wan samu zuciyarta sassuta ya fita zuwa shago, amma babu walwala ko magana tsoron yi masa ake yi saboda yanayin fuskarsa.

Bayan kwana biyu da maganar Nayla da Jidda da Salma suka fita su a lallai yawon siyyayar komawar Nayla suke. Ta layin gidan Didi suka zo wucewa kawai suka tsayar motar a ?ofar gidanta suka shiga.

Tana zaune da Marmerh a hannu suka shiga ta da fara'a ce, "barkan ku da zuwa." Suka zauna Salma ta karSi Marmerh ya ce, "masha Allah, Didi Marmerh tana kyau wallahi, amma ni sai nake ganin fuskarta kamar ta Omar." Didi tayi dariya ta ce, "indai kin ga fuskarsa sai kin ga tawa. Sannan ku da zuwa." Jidda ta ce, "Yauwa Didi. Hanya ce ta biyo da mu muka shigo nan."

Didi ta ce, "Sannun ku da zuwa, ku sha ruwa akwai abinci in zaku ci." Umma Saroot ce ta fito ta ce, "Nayla ku ne tafe." Nayla ta yi murmushi ta ce, "mu ne Umma, barka da yamma."
"Barka dai Nayla, ya mai gidan naki? Omar sarkin ?an rigima." Murmushi ta yi bata amsa ba dan yadda take mata magana ba su san tana gida ba.

Umma Saroot ta ce, "Omar akwai rigima, ina jinsa yazo yana ta wasa da ?arsa." Nayla dai bata ce komai ba sai murmushi kawai. Umma ta ce, "in zaku ci abinci akwai." Salma ta ce, "babu komai Umma, mun ?oshi." Ta yi murmushi ta shiga Waki. Jidda ta ce, "Didi wallahi Umma na da kirki sosai, gata suna kama da Omar." Ta yi dariya ta ce, "maza ya ji ki."

Kira ne ya shigo wayar Didi ta kalli mai kiran ta kalli Nayla ta ce, "Mijinki na kira na, ban san da me yazo ba kuma." Nayla bata ce komai ba sai murmushi da tayi, Didi ta Wauka ta saka wayar a speaker dan ta san bazai wuce zancen Nayla ba.

Daga can Sangaren ya ce, "Didi!." Didi ta ce, "Na'am Omar."
"Kina lafiya? Ya Marmerh?."
"Lafiya lau, Na ga baby swing da ka aiko mata dashi, Omar yana da tsada fa, na yi tunanin siya na fasa saboda kuWin da yawa."
"In bakya so ba sai ki ?ona ba, kuma kar na sake yin abu ki ce min yayi tsada, kuWina ne ai ko?."

Didi ta ce, "na ka ne, amma...."
"Kin ga Didi, ba ke na yiwa ba ai ?ata na yiwa, In ke ce zan ma kalle ki ne?." Tayi dariya ta ce, "Ya na jika haka kamar mara lafiya? Lafiya dai ko?."

Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "GabaWaya na zama mai rauni kamar ba ni ba, ko magana bana so ayi min haushin yarinyar can da nake ji da an yi min magana sai na fara faWa, ita kuma na kasa yi mata faWan. Ni da bani da yawan ciwo amma yanzu kullum da ciwon kai da zazzaSi nake yini, ba kuma komai ne yake kawo min ba sai damuwa."

Didi ta kalli Nayla da take kallon Didin tayi murmushi ta ce, "Wacce yarinya kenan?."
"Wa nake da ita bayan ke da Marmerh?."
"Oh ai na ji kace yarinya ne shiyasa. Me matar ta ka ta kuma yi maka kuma?."
"Meye ma bata yi ba."
"Amma ka ce ka daina yi min maganarta, har ka sakko daga fushin?."

Omar ya ce, "na faWa miki na canja, ni kaina canjin nan yana cutar da ni. Didi na kasa mantawa da ita kamar yadda nayi niya, gashi sai da na kira ki dole na yi maganarta. Amma ita Waukar kalamaina take yi matsayin na ?arya, a duniya akwai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login