Showing 321001 words to 324000 words out of 332344 words

Chapter 108 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14415

da kansa ya je har gida ya nemo alfarmar ?anwar Mamansa akan ta zauna da Nayla. Ai kuwa hakan ya yi mata daWi sosai, ta yi farin ciki ta kuma ji daWin abinda Omar ya yi mata sosai.

Ranar da ta kwana uku da haihuwa tana zaune a falo tana faWa da ?a?anta, a lallai sai sun Wauki sa, ta rufe ido ta fara yi musu faWa cikin tsawa dan sun dame ta. A lokacin Omar ya shigo, jin muryarsa sai suka tafi wajansa a guje suna kuka. Ya ri?esu ya ?araso ya zauna ya ce, "Jidda lafiya? Me ya faru haka suke kuka?.
"Ina fa lafiya, sun zo sun ishe ni sai na basu shi, ina yi musu magana kuma sun ?i ji. Ko ta ya zasu iya Waukarsa oho musu.

Ya kalle ta cikin rashin jin daWi ya ce, "shine kuma zaki yi musu wannan tsawar? Haba Jidda, tun kafin na shigo na ji tsawar da ki ka yi musu, ai sai ki tsorata su, har nawa suke da za a yi musu wannan tsawar?. Nayla ta kalle sa da kallon mamaki baki buWe, dan ta lura sam baya so ayi musu faWa komai sai abinda suke ga dama suke yi, musamman Marmerh da take babba kuma mai ?iriniya, baya so ya ga Marmerh tana kuka ko kaWan yanzu sai ya damu kansa kamar wani babban abun ne ya same ta. Nayla ta kawar xa kai gefe ta ce, "?an nawa haihuwar kwana ukun zan bawa waWannan yaran? In suka yar min dashi fa? Haihuwarsa na yi fa, ba bacci nayi na farka na gansa a gefena ba. Kawai dan kar su yi kuka sai na basu shi? Sun daWe basu yi ba.

Omar ya Wan yi murmushi ya ce, "Eh na san haihuwarsa ki ka yi ba ajjiye miki aka yi ba, amma ki daina yi musu irin faWa haka, ki duba har kuka suke yi fa. In kika yi musu magana a nutse ai zasu fahimta, tsawar nan tsorata su ki ke yi wallahi. Nayla bata sake magana ba ta Wauke kai ta cigaba kallon Wanta da yake kwance a jikinta. Omar ya kalle su da suke kwance a jikinsa ya ce, "Kar ku daina kuka kun ji, ku karSa ku jr ku yi wasan ku ya faWa yana basu kayan za?in da ya shigo musu dashi, suka karSa suka fita zuwa inda aka tanadar musu domin wasa.

Ya bisu fa kallo har suka fita, ya kalli Nayla da ba shi take kallo ba tare da yin ajiyar zuciya ya ce, "Ban samu mun yi magana ba sai yanzu, bana samun zama sai ta kama. Ta kalle sa fuska babu walwala ta ce, "ka yi busy ai, ni Win ma ba ganin ka nake yi ba" ta faWa tana Wauke kanta daga kansa. Ya Wan shafa kansa zuwa gashin fuskarsa ya ce, "Abubuwa sun yi min yawa ne wallahi, kwana biyu kuma bakya rage min aikin ne shiyasa. Na saba wani abun ke ki ke yi shiyasa abubuwan suka tarar min sosai. TaSe baki ta yi bata ce komai ba. Ya nutsu yana kallon yanayin ta dan sai ya ga kamar fushi take yi ya ce, "wai fushin me ki ke yi ne haka? Ina magana kina kawar da kai kina Waure fuska. Bata kalle sa ba ta ce, "ni ba fushi nake yi ba."
"Amma meyasa ki ke Waure fuska? Maganar ma kamar bakya so ki ke yi, da farko na Wauka saboda yanayin jikin ki, ne amma yanzu na lura kamar akwai wani abun a ranki.

Nayla ta ce, "GabaWaya yanzu ka zama baka da lokacina, ko yaushe kana office baka dawowa sai dare, kuma da ka dawo zaka cemin bacci ka ke ji ka gaji. Abinci ma ba ko yaushe ka ke ci ba, in na ce a aiko maka dashi office ka ce a'a. A haka ka ke so ka ganni kamar daaa?. Kaima ai ba kamar da Win ka ke ba yanzu.

Tunda ta fara magana yake kallon ta har ta gama, ya girgiza kai cike da mamakin rigima irin ta ta ya ce, "Jidda aiki ne yake yi min yawa kin fi kowa sani, ke da kan ki kina taimaka min wajan rage min wani abun. Kuma ina sane nake cewa kar ki aiko da abinci saboda yanayin da ki ke ciki, yanzu kuma kin haihu, in ki ka huta sosai zuwa gaba zan ce a kawo ai. Ta ya zaki ce bani da lokacinki? Ina da wanda zan bawa lokacina in ba ke ba?.

Ajiyar zuciya ta yi tana Wan taSe baki alamun bata yarda ba ta ce, "Haka ne." Ya yi murmushi yana kallon ta ya ce, "baki yarda ba kenan ko? Baki yarda da abinda nace ba?.
"Hmm ni ban ce ban yarda ba, tunda ka faWa ai dole na yarda ko bana so. Amma batun canji ka canja fa, a daa in na Wauki wayarka baka damuwa, har fita ka ke yi ka barta a hannuna, wani lokacin ni ce ma nake aiko maka da ita saboda kar a neme ka. Amma yanzu da na Wauka sai ka ce na baka zaka yi amfani da ita, ko da kaga zan yi amfani da ita sai ka riga ni Wauka kamar wacce take yi maka bincike a ciki. Kafi kowa sanin ba bincike nake yi maka ba, inda bincike nake yi maka a wayar da ka sani. Babban abinda yake tsaya min a rai meyasa baka so na ri?e? Meyasa baka so na Wauka bayan daa baka damuwa?.

"Saboda bana so ki ga abinda zai Sata miki rai ne." Da mamaki ta kalle sa ta ce, "Meye a wayar da zai Sata min rai? Yaushe aka samu abinda zai Sata min rai a cikin wayar?.
"Ba wani abun bane a, amma wayar tana hannunki message zai iya shigowa wanda baza ki ji daWi ba in kika gansa, ta ko wacce kafa messages da hotuna nake samu, ko nayi blocking wani zai zo. Duk da ba amsa nake bayarwa, ba amma in kika gani ranki bazai yi daWi ba, na san halin ki. Saboda haka nake kiyaye Sacin ranki, shiyasa bana so wayar ta jima a tare da ke.

Ta zuba masa ido tana kallonsa, kafin ta janye idanunta ta kalli gefe bata cr komai ba. Omar ya mi?a mata wayarsa ya ce, "karSi." Bata karSa ba ta cigaba da kallon Wanta tana shafa kansa. Ya Wan yi shiru na wani lokaci, kana ya ce, "Jidda kina zargin ina da ?an mata a waje ne ko kina zargin na fara bin matan banza?." Da sauri ta kalle sa ganin so serious ya yi maganar, ta langwaSar da kai a raunane ta ce, "A'a,ni ban ce ba."

"To meyasa ki ka damu dan ina karSar wayataa hannunki? In akwai abinda nake aikatawa wanda bana so ki gani ai bazan ma bari ki Wauki wayar ba ko da wasa. Da rufe ta zanyi na saka mata security wanda baki san sa ba. Na san kuma ba bincike ki ke yi min ba, sai amfanin ki Wauka Win ya zo ki ke Waukar waya. Amma saboda gujewa Sacin ranki da jin babu daWi a zuciyarki ya saka nake karSa. Amma ke naga zargina ki ke yi, zargi ki ke yi ina aikata wani abun mara kyau shiyasa.

Da sauri ta tare shi ta ce, "A'a wallahi, ni ba zarginka nake yi ba, har abada bazan taSa zargin ka ba ta faWa a raunane tana kallonsa. Ya zuba mata ido yana kallon ta kana ya ce, "To me yasa kika damu kan ki har ki ke fushi?." Nayla ta ce, "Kawai zuciyata ta kasa aminta da hakan ne, na riga da na saba da yadda muka fara tun farko, ganin wannan canjin zai saka min shakku a zuciyata.

 Shakku, a kaina Jidda?.
 A kan wayar ba kai ba ta faWa tana rausayar da kanta.  To waye mai wayar in ba ni ba?.
 Allah ba haka nake nufi ba.

Ya Wan yi murmushi ya ce, "Ni dai ina faWa miki, babu abinda zan Soye miki a cikin rayuwata da wajenta. Jidda ko budurwa na gani ina so zan aura you're the first person da zan fara faWawa, ko ya yi miki daWi, ko kar ya yi miki daWi, ni dai na faWa miki saboda kece komai nawa, dan bani da wata bayan ke. Daman ke da Didi ne, to ita bata duniya sai ke kaWai, dole ki jure abubuwan da zan dinga zuwar miki dashi dan wani bazai yi miki daWin ji ba. Ina so ki ri?e wannan, bisa kuskure na aikata wani abun mara kyau wallahi sai na faWa miki Jidda, ko mai muninsa sai kin sani.

Ta yi ajiyar zuciya a raunane ta ce, "balle ma baza ka ga budurwar har ka fara so ba, kuma baza ka aikata wani abun ba." ?an murmushi ya yi kaWan yana lumshe idanunsa akan fuskarsa kana ya ce, "ki kwantar da hankalinki, wannan Omar Win na ki ne ke kaWai in sha Allah, babu wata mace da zata yi miki over taking a wajena. Dan na san duk akan kar ki je ina da wata a waje ki ke wannan abun, to babu Jidda, har gobe da jibi kece kaWai. Abu Waya nake so a gare ki...." ta Wago ta kalle sa kamar yadda yake kallon idonta ya ce, "Yarda! Ki yarda dani kawai Jidda, bazan taSa cin amanarki ba in sha Allah. Yadda kika ri?e min amanar kan ki nima bazan ci amanar ki ba, zan ri?e miki kaina da zuciyata, babu wacce zata shiga zuciyata domin fadar ki ce. Murmushi jin daWi da walwala tayi, ya shafa kumatunta yana ja kaWan ya ce,  keda kishi aminan juna ne. Ta kwantar da kanta a kafaWarsa ta ce,  kai kuma fa?. Bai bata amsa ba ya kalli Babyn da yake jikinta ya ce, "da Abiy zamu dinga kiran sa?."

Da mamaki ta ce, "Sunan Abiy Win ne? Na Wauka sunanka ne."
"Sunan sa ne, in Allah ya kawo wani sai a saka sunan nawa." Ta yi murmushin jin daWin karar da ya yi mata ta ce, "Na gode YaMar." Ya Waga gira sama yana binta da kallo ya ce, "da aka yi me?." Murmushi ta yi bata bashi amsa ba, ta shafa kan yaron ta ce, "Allah ya raya mana Mufty."

Ya bita da harara ya ce, "kin cika iyayi, daga Musliha an samo Mufty. Ko da yake ?ar gayu ce ke, dole ki saka sunayen ?an gayu. Ta yi dariya ta ce, "kuma dole ka faWa ba, haka lokacin Musliha ka ce baza ka faWa ba, sai gashi yanzu shi ka ke cewa har ka sana." Ya yi murmushi ya ce, "zan fita, ki yi lisaafin abinda za a siyo da abinda ki ke so, babu lallai na dawo da wuri. Ta amsa da to bai jima a zaune ba ya tashi ya fita.

_Jiya na yi kuka sosai, na gama editing ina burin yau na yi update gabaWaya na huta, ina shiga naga ya dawo farko=?-? over 10k words, haka na gama kukana editing ya dawo farko. Na so na gama uptade yau amma ba zai yu ba, sai zuwa gobe in sha Allah._


Nana Haleema.
P128

? ? ? Haka aka cigaba da karSar ?an barka, mutane Kaduna zuwan su daban ne musmaman da suka ji sunan Abiy aka saka. An yiwa yaro hidima sosai kuWi da kaya kamar ba a so. Ranar suna aka raWa masa suna Abdallah aka yi hidimar taro kamar lokacin Musliha. Sai dai wannan lokacin an fi Sarnar kuWi, an fi kashe kuWi kamar ba nema ake yi ba, an yi Sarnar kuWi a sunan Mufty, dan sai da ya kai ya kawo duk wanda ya zo sunan bazai tafi ba sai da atamfa da takalmi da mayafi da dubu ashirin na Winki. Ga abubuwa manya-manya na rabo da aka raba a wajan, an yi hidima sosai kowa ya yi farin ciki. (Can na hango ?an Kiran Rabo comments section an hau layin karSar Souvenirs, ?an arewapen har sun fi ?an whatsapp za?ewa, ana ture su suna komawa).

Bayan suna da kwana sati uku ya kama sati huWu kenan da haihuwar Mufty, Umma Saroot ta shiryata koma gida bayan ta gama shirya Nayla ta gyara ta yadda ya kamata. Dan ta lura Wan nata fitinanne ne, tunda ya lura Nayla ta samu tsarki babu zaman lafiya, har inda Umma take zai zo ya ce tazo, sai dai in taje ta gudo. Shiyasa tayi mata haWin da ba a yi mata a haihuwar Musliha ba, an yi mata gyara mai kyau sosai.

Kyautar mota Omar ya yi mata ban da kaya da kuWi da aka haWa mata, ba dan ya biya ta abinda tayi ba sai dan ya kyautata mata ya saka ta farin ciki. Ai kam ta yi farin ciki sosai, ta ji daWi tayi masa addu a sosai. Dan a yanzu iyaye yake yi dasu, Umma sama Umma ?asa yake faWa cikin girmamawa da nuna su Win dangin mahaifiyarsa ne, in zai gaishe ta kuwa har ?asa yake dur?usawa. A ?an uwansu babu wanda bai kira sa ya yi murnar kyautar da ya yi ba, shi kansa daWi yake ji a zuciyarsa, daWin alkhairin yake ji a duk lokacin da yaga ya aikata ana farin ciki ana yi masa addu a, sai yana ji ina ma tun Didi tana raye ya bar komai ya wuce haka da bai san farin cikin da zata yi ba, Allah bai nufa zata gani ba.

Ranar da Nayla ta kwana arba'in ranar suka bar bar Nigeria ita da mijinta da ?a?anta. A ?asar Canada suka yada zango, a cikin HoneyRose hotel. Babban hotel?ne a ?asar, hotel ne da ya yake cikin five star kuma yake cikin top ten a best hotel in honeymoon. Hotel Win yana Sangaren VIP, standard da kuma luxury. A vip suka yi reserving room, suka Wauki one parlor and two bedrooms, Waya kids room, Waya kuma couples room.

Nayla ta buWe kids room Win, ta ga akwai toys na yara da aka tanada a ciki saboda yara su yi wasa. Nayla da take kallon Wakin ta kalle sa ta ce, "Zaka iya bari su kwana su kaWai Win ne?." Omar da yake bayanta ya yi ?ar dariya ya ce, "ba dole na ba, shiyasa aka tanadi wannan Wakin."
"Daman kaine ai baka so su kwana su kaWai, kamar wani abun zai same su."

A nan suka kwantar da Marmerh da Musliha da suka yi bacci, kasancewar wheather da suka samu ?asar ta show ce akwai sanyi sosai, sai da suka kunna wood stove Win Wakin, Nayla ta saka musu safa a ?afarsu saboda sanyi.

Sai da ta gama shirya su sannan ta shiga nasu Wakin, babban Waki ne mai girma, wanda aka zagaye ko ina da glass kamar kana waje. Kana ganin korayen furani da suka zagaya glass Win. Bata tsaya ?arewa Wakin kallo ba ta shiga wanka. Saboda sanyin garin ko Mufty bata yiwa wanka ba, ta canja masa kaya ta goge masa jikinsa da baby oil. Tana gama shirya sa Omar ya fito daga wanka, ya shirya suka yi sallah sannan ta dawo ta tarar da Mufty ya yi bacci. Pecking Winsa ta yi a goshi ta ce, "Allah sarki Abiyna, har ya yi bacci."

Kallon Mufy ta yi ta kalli Omar ta ce, "Wallahi babu ta inda Mufty ya bar ka, komai irin naka sak. Wannan in ya girma gabaWaya kamannin ka zai yi." Murmushi ya yi yana daga zaune ya ce, "Haka ake ta cewa, Nima dai ina ganin kamar sosai. Lokacin da ake cewa ina kama da Didi bana gani ko kaWan, in na kalle ta sai naga babu wata kama, amma shi kam ina ganin kamar sosai."

Ta yi murmushi ta ce, "gaskiya kam kuma yi, har ya danne Musliha gabaWaya. Ko nimeyasa basa yin kama dani oho."
"Ina ki ke da ?arfin jinin da zasu yi kama dake? Ai daman da ni ya kamata su yi kama ba da ke ba."

"Saboda me?."
"Saboda ni nake yin cikin, ke aikin ki haihu kawai." Ta yi ?ar ?aramar dariya ta ce, "to da yi da haihuwar wanne ne mai wahala?." Ta faWa tana kafe sa da ido kamar yadda yaka kallon ta.

Ya Wan yi tunani kana ya ce, "eh to, gaskiya haihuwar tafi wahala. Ni fa na firgita a lokacin da kika fara na?udar haihuwarsa, gabadaya kin fita hankalinki, kin ri?e min hannu zaki kara ni. Wai daman haka ki ke da ?arfi ko duk cikin ciwo ne?."

Dariya tayi sosai harda ri?e ciki, ta dawo kusa dashi ta zauna ta ce, "Wallahi zafi ciwon ne kawai Rouhi, haihuwa ai ta wuce tunaninka. Shiyasa nake so da zaka bari mu yi family....." ai bata ?arasa ba ya ce, "wallahi ba za a yi ba, kuma ki daina yi min wannan zancen na faWa miki bana so. Yau zan samar da mai sunan Hajja in sha Allah."

A firgice ta kalle shi ta ce, "Allah bazai yarda ba in sha Allah, wannan wanne irin fata ne? Kwana arba'in da biyu da haihuwa ka dinga yi min zancen ciki? Dan baka san ya ake yin haihuwar ba sai ka dinga yin min wannan mugun bakin?. Haba don Allah, ka bar faWa don Allah, wallahi gabana faWuwa yake yi ta faWa a sanyaye tana kallon sa. Hannunsa ya Wora a saitin zuciyarta ya ji yadda take bugawa alamun tsoro da fargaba ya ce, "To shikenan na janye, Allah ya bamu kamar yadda aka samu bayan haihuwar Musliha." Ta kalle sa idonta ya ciko da hawaye ta ce, "Akwai wahala Rouhi."

"Ke da kike jaruma? Haba ni ai bana jin ki, nasan zaki iya." Ta harare sa ta ce, "yadda baka son zuga nima bana so, ka daina zuga ni, ba wata jaruma." Dariya ya yi ya jawo ta zuwa jikinsa ya ce, "To na daina. Kar ki yi min kuka mana, kin ga dai amarci zamu ci, ki adana wannan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login