Showing 9001 words to 12000 words out of 332344 words

Chapter 4 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14366

na falo naga stand fan ce, ai sunfi akan wannan ta faWa tana nuna fankar Nayla dai bata tanka ba suka fito tare da Mama.

Nayla kalli Jawad ta ce,  Yaya J Ina Yaya ne?.
 Yaya ya koma Lagos, zai yi miki waya ya ce min zai kiraki.
 Allah ya taimaka ta bashi amsa a ta?aice.

Mama ta ce,  To Nayla, mu zamu wuce Kaduna yanzu, amma zan dawo dan ganin halin da ki ke ciki. Kawai sai Nayla ta fara kuka, Jawad ya ?araso ya ri?eta ya ce,  Haba Hauwan Abiy meye na kukan kuma? Allah da na san zaki kuka bazan bari mu zo miki sallamar ba. Ga twiny ki a Kano kullum kuna tare, sannan ga Salma meye na damuwa kuma?.

 Yaya J Ina kewar Abiy, in ka je ka ce ina gaishe shi don Allah.
 Zan faWa masa, kema na san yana kawarki sosai. Ki share hawayenki kin ji?. Ido ta goge, tare suka raka su har gate bayan Jalila tayi mata alqawarin zuwa ta kwana suka tafi.

Tare suka dawo cikin gidan ita dasu Salma, sai ta sake takura kanta, ta zauna shiru babu hira sai dai ta dinga bin su da ido. Shiru suka yi mata suna hira tsakaninsu amma bata saka musu baki. A haka har aka yi sallar la asar, suka tashi suka yi sallah bayan sun idar ne aka sake buga gidan.

Salma ce ta sake zuwa ta buWe sai gata sun dawo da Didi. Nayla na ganin Didi sai ta murmusa domin gabaWaya fuskar Didin ta koma mata ta Omaar. Ganin tayi murmushi sai Didi taji sanyi a zuciyarta ?araso a sanyaye ta ce,  Nayla ya jikin?. Abinda ta fara tambaya kenan tun kafin ta zauna.

Nayla ta ce,  jiki ya yi sau?i Didi.
 Amma na ga fuskarki tayi ja, kuka ko Nayla?. Salma ta ce,  kuka tayi, su Mama ne suka zo yi mata sallama sun koma Kaduna, shine ta sha kukanta son ranta. Didi ta ce,  to ki yi ha?uri. Nayla sai tayi murmushi jin yadda Didin tayi magana a raunane.

Didi ta kalle su ta ce,  Jidda bamu gaisa ba. Jidda ta yi dariya ta ce,  ai baza ma ki kula dani ba, kina ta sirikarki. Didi ta yi dariya suka gaisa gabaWaya kana ta ce,  ya gajiyar hidima?.
 Alhamdu lillah Didi. Ke ma ai za a yi miki ya gajiya, kullum sai kin fito daga wannan unguwar ta ki mai shegen nisa. Didi ta yi murmushi ta kalli Nayla ta ce,  amma dai kin ci abinci ko?.

Nayla ta ce,  na ci Didi. Didi ta girgiza kai bata ce komai ba dan kunya take ji ta rasa abinda zata ce. Sai daga baya sannan ta ce,  ban ma shiga ciki ba unguwarmu ba, nan na fara zuwa mu gaisa sannan na shiga. ?an murmushi suka yi babu wanda ce mata komai.

Didi ta kalli Nayla ta ce,  in akwai abinda ki ke so ki faWa min. Nayla ta ce,  Babu komai Didi, kar ki damu. Didi ta sake yin murmushin ya?e dan gabaWaya ta rasa abinda zata yi. Duk suna lura da ita, ta kasa sakewa ba kamar yadda suka saba ba, su kam basa ganin laifinta ko kaWan kawai dai itace ta tsargu. Hirar littafin baya da ?ura aka fara tsakanin Jidda da Salma har Didi ta saka baki Nayla ma haka sai hira ta buWe gabaWaya suka fara hira da nishaWi.

Har aka yi i sha Didi tana nan, a sake kawo abinci daga gidan Hajja tare suka ci gabaWaya. Harabar gidan suka fita ita da Jidda da Salma zasu rakata zata tafi gisq ta kalle su ta ce,  na ce zan kawo Omar yau gashi bai yi ba ko? Ku yi ha?uri ban ma yi magana dashi ba so nake sai gobe in sha Allah.

Salma ta ce,  Kar ki damu Didi babu komai, iya wannan wahalar da yake saka ki ma ai yana Waukar ha??inki. Ina gani gabaWaya yanzu bakya sakewa damu kamar ba ke ba. Murmushi ta yi ta ce,  Ku dai bawa Nayla ha?uri don Allah, na san bamu kyauta ba nida Omar.

Jidda tacce,  ha?urin me Didi? Omar fa ko yazo ba kallon Nayla zai yi matsayin matarsa ba, zama kana jin motsin wani shine amfaninsa kawai a gidan nan, amma baya ga haka bashi da amfani. Didi ta ce,  zai yi amfani in sha Allah Jidda. Kuma na sanar da yaran sa komai akan auren, babu abu na cutarwa da zai shigo ta ?ofa ya cutar da Nayla in sha Allah. Dan unguwar nan kaf a san nan gidansa ne kuma matarsa ce a ciki, babu abinda zai same ta da izinin Allah.

Salma ta ce,  Allah ya amince.
 Amin Salma. Don Allah ki sake taya ta kwana kin ga bata da lafiya.
 Kar ki damu Didi.
 Na gode, Allah ya bar zumunci. Suka amsa da amin ta fita ta shiga motar mijinta.

Tana shiga motar ta kalle AbdulHamid ta ce,  Wallahi ban ji daWin rashin zuwan Omar ba YallaSai. Ya ce,  ba ina sane na ce ki ?yale shi yau ba, sai dai ko kin je yau Win abinda ki ka bari jiya zaki tarar, ke ki ke faWi min zafin ransa shiyasa na tabbatar har yanzu yana tare da wannan Sacin ran. Gwara a bashi lokaci zuwa gobe, in sha Allah dani dake zamu je mu same shi zamu san ta inda zamu Sullo masa in sha Allah.

Didi ta ce,  to Allah ya sa ya amince.
 Amin, zai amince ma in sha Allah.
 Ni ko ciki ban shiga ba Ina nan tun Wazu.
 Ko wajan Hajjan?.
 Wallahi, kunyar Hajja nake ji ne. Sai an daidai komai sannan zan samu nutsuwa. Murmushi ya yi ya ja motar suka bar unguwar.
KRB3P004
ArewaBooks@nanahaleema11.

Mama da suka koma Kaduna bata tarar da Abiy ba har suka yi baccin gajiya suka tashi Abiy baya nan. Sai bayan sallar i sha ta same shi a zaune a falon sa yana amsa waya. Kafin ya gama wayar ta kawo masa abinci da ruwan lemon da ta san yana sha sannan ta zauna a gefensa. Yana ajjiye wayar ya kalle ta ya ce,  mutanen Kano, ashe kun dawo. Mama ta ce,  mun dawo tun Wazu, lokacin da muka shigo baka nan.

Jalil ne ya shigo a guje yana cewa,  Abiy oyoyo. Abiy ya yi dariya yana cewa,  Autana, ka tafi Kano ka barni ko?. Jalil ya ce,  Zan koma wajan Yaya Nayla sai mu je tare ko?.
 Shikenan Jalil. Ya Kano?.
 Da daWi Abiy. Abiy gidan Anty Nayla mai kyau yana ta ?hamshi. Abiy ya yi dariya ya kalli Jalila da ta shigo ya ce,  Jalila an dawo? Na Wauka ke zaki yi zaman Waki ai. Dariya tayi suka gaisa da Abiy sannan suka fita ita da Jalil.

Abinci Abiy ya Wauka wanda Mama ta zuba masa ya fara ci. Bai ce komai ba abincinsa yake ci hakan ya saka Mama ta ce,  baka ce min ya mu ka baro Nayla ba. Abiy ya kalle ta kafin ya Wauke kai ya ce,  na san ai tana cike da farin cikin auren wanda take so.

Mama ta ce,  hmmm bari kawai. Duk abubuwan nan da suka faru amma Nayla ?aunarsa take yi kamar ta busa masa rai. A gaban idanun mu da yayyen mahaifiyarta aka kira shi jiya aka zauna dan aji ta bakinsa. Babban Wan Hajjan nan da suke cewa Daddy ya ce indai har ya furta baya son zama da Nayla za a warware auren dan baza su bata wanda ba ya son aurenta ba. Yaron nan dan wula?anci duk an taru ana jiran sa amma ya shafe mintina talatin bai zo ba, kuma da yazo ana tambayarsa yana bawa mutane amsa ta rainin hankali. ?arshe idanun wanda ake kira da Daddy ya kalla ya ce shi baya son Nayla ai bai ce a Waura masa aure da ita ba, kuma bai ce yana bu?atar aurenta ba. In ma yana da ra ayin auren to wata ba Nayla ba. Ni abinda yafi tsaya min a rai da ya ce wacece Nayla, yana nufin bai ma santa ba fa kenan Abiy.

Abiy kallon Mama yake yi ta cigaba da cewa,  Har sai da ?anwar marigayiya Sa adatu ta fusata ta ce kai ba fa auren sadaka aka baka ita ba ka ke yiwa mutane maganar banza. Kaga yadda ya yi mata kallon wula?anci yana cewa koma meye shi ba ya sonta. Kamar fa ba iyayen matarsa ba, to ko Nayla ba matarsa bace tunda jininka ce ya cancanci ya girmama iyayenta saboda abinda ka yi masa kwanaki. Amma yaron nan bai yi ba sai zallan iskanci a cikinsa. Kaji masifa da bala in da ya dinga yi kamar wasu sa aninsa? Yana shouting yana sake maimaita baya son Nayla. Na ji daWi da Jawad ko Yaya basa wajan, dan da abin faWa zai zama wallahi, yanayin yadda yake magana dole ya fusata su.

Abiy ya murmusa ya ce,  To ai gaskiya ya faWa, ya ce yana sonta Win ne?.

 Haba Abiy, koda baya sonta faWar wannan kalma a gaban iyayenta ai cin fuska ne. Ba dan Yayarsa Aisha ba wallahi sai ya saki Nayla a jiya. To itace ta ja shi waje suka tattauna sannan ya dawo rai a Sace ko kallon kowa baya yi ya ce ya amince. Duk da wannan abin da ya faru ita Nayla bata so ya furta ya saketa, jikinta rawa yake yi da yake cewa baya sonta, amma yana furta ya karSi auren ta yi ajiyar zuciya. Gaskiya na ji babu daWi akan abin nan na Nayla, haba don Allah, ana nemar mata ?anci tana zubawa mutane ?asa a ido?. Ai sai da na faWa mata Wazu, na ce ni ban ga abin so a wannan yaron ba, sai tayi dariya wai ita har yanzu son da take masa bai ragu ba Mama ta ?arasa faWa a fusace.

Abiy ya ce,  to meye na fusatar? Ki kwantar da hankalinki haka ta zaSa.
 Kasan ko gidan da aka kaita bai je ba har yanzu, ita da Salma suka kwana. Wannan wula?alanci har ina? Kuma ita sam bata gani har yanzu haskensa take gani tana kuma sonsa, abin nan ya taSa min zuciya kamar na yi kuka wallahi ta ?arasa faWa murya har rawa take yi.

Abiy ya yi shiru bai ce komai ba amma zuciyarsa sam babu daWi da jin abinda Mama ta ke faWa, gabaWaya zuciyarsa ta cushe bai ji daWin abinda ya faru ba.

Mama ta katse masa tunani ta ce,  Yanzu batun gwajin jini ake yi, tunda kai ka Wauketa ka bashi ita ba a san matsayin jininsa ba, Ko yana da hiv ma waye ya sani. Mtsww! ni wallahi gabaWaya Nayla ta fi bani haushi a lamarin nan, na san ana nan ana yi dani a dangi ana cewa da yake ba ni na haifeta ba na bari an yi mata irin wannan aure. Ba shiri, ba biki, babu komai an wanke yarinya kamar Nayla an kai masa ko kuWin aure babu balle lefe. Duk wanda ya zarge ni shi da Allah, domin na fi su jin zafin wannan abin da ya faru.

Abiy murmushi ya yi domin kuwa an zargeta Win, dan ?an uwansa ce masa suka yi dan mahaifiyar yarinya bata raye sai ya yi mata abinda ya ga dama, kuma Mama na zuga shi da yake ba Jidda ce ko Jalila ba. Abiy ya kalle ta ya ce,  To yanzu meye na wannan Sacin ran?.
 Abiy abin ne da haushi wallahi. Gidan da aka ajjiye Nayla ko mai aikin gidan nan sai haka, wasu ?ananun da?una kamar akurki.

 ?addararta kenan.
 Da ?addara da kuma rashin jin magana irin na Nayla ba. Bai ce mata komai ba ya yi shiru amma abubuwan da ta faWa sun yi tasiri sosai a zuciyarsa. Sosai yaji ransa ya Saci akan lamarin fiye da tunani, ga shi Nayla ko waya bata yi masa ba, alamu ya nuna ta samu abinda take so ya za a yi ta tuna dashi.

GabaWaya sai abincin ma ya fita daga ransa ya ajjiye ya dau?i lemo ya sha ya tashi ya shige bedroom. Murmushi Mama tayi bayan ya shiga ta ce,  Ba boka, babu malam, babu Wan bori, babu masu tsibbu na yi abinda nayi niya akan Nayla. Burina ya cika ta shiga gidan da zata sha wahalar raguwar aure, har gwara ni kana sona uwar gidanka ce bata sona, amma ita mijin ma baya sonta. Mu je zuwa mu gani, yanzu na fara saka maka Sacin rai akan auren nan na Nayla. Mu je zuwa.

*Kano.*

Omar da Sacin rai da takaici ya kwana ya tashi, ko yaransa da suka ganshi babu wanda ya iya tanka masa dan kana cewa kanzil zai wuce a kanka ko waye kai ko ya ki ke dashi.

Washe gari ranar lahadi da wuri ya fita company ya je ya samu ana ta aikin takalma kamar ko yaushe, gefe Waya kuma ana saka wasu a kwali saboda za a tura garin da aka ce ana so.

Bashir da ya ganshi a zaune sai ya ?arasa ya zauna ya ce,  Barka da zuwa Tiger. Daman Kai mu ke jira akwai abinda ya ?are ana bu?atarsa da gaggawa. ?ago ido ya yi ya kalle shi sai Bash ya saukar da kai ?asa ganin idanun mai gidan nasa yana gani ka san baya cikin walwala.

Atm Winsa ya bashi ya ce,  ku je a siya, in ka dawo ka zo gida ka same ni ya faWa yana tashi ya fita su kuma suka cigaba da aiki.

Gida ya koma kawai ya zauna ba tare da yana yin wani abun ba, gabaWaya komai ya fice masa daga rai baya jin daWin komai ba kuma ya jin daWin aikata komai. Zuciyarsa babu daWi haka yake ji, kamar wanda ya rasa wani abu mai mahimmaci a rayuwarsa haka yake ji. Ya kasa mantawa da batun auren nan, duk yadda ya so da ya ajjiye maganar ya kasa, ko ya ya ya motsa sai ya tuna yanzu fa yana da mata, in ya kawar da tunanin anjima zai sake dawowa cikin kansa.

Tsaki ya yi a bayyane, ko a lokacin Narma bai ji wannan nauyin zuciyar da yake ji a yanzu ba. Ya karkata hakan ga Sacin ran da maganar ta saka masa shiyasa da ya tuna sai ya ja tsaki.

Bashir ne ya shigo suka gama magana, Omarya aike shi shi kuma ya kwanta akan kujera ya rasa abinda yake masa daWi.

Bacci ne ya kwashe shi a haka sai kiran sallar azahar ya ji, ya tashi ya yi sallah yana tunanin abinda ya kamata ace ya ci. Kitchen Win ya shiga yana ?arewa komai na ciki kallo, sai kuma ya ja tsaki ya fito ya Wauki ruwa yana sha cike da jin haushi. Sai kuma ya kuma tashi ya dafa shayi ya dawo yana sha ba tare da ya saka madara ko wani abun ba.

Bayan sallar la asar Bashir da Tk suka shiga wajansa, yana kwance da ya gansu sai ya mi?e ya ce,  Ya aka yi?. Tk ya ce,  Tiger kayan da aka tura Abia state ne wai basu je ba, shine nake tambaya mai motar bai yi maka waya ba?.

Omar ya ce,  Kamar ya basu je ba? Ni babu wanda ya kira ni ya faWa yana duba wayarsa amma bai gani ba. Tk ya ce,  wanda aka turawa kayan ne ya kira ni ya ce driver bai je ba har yanzu, na kira driver a waya kuma baya Wauka amma bara& . Maganar ta katse saboda ganin kiran mai motar sai ya ce,  gashi ma yana waya. Ya faWa yana Wauka suka yi magana kafin ya kashe ya ce,  Yauwa, ya ce yanzu nan ya shiga garin zai kai masa nan da anjima kaWan.

Shiru ya yi baice komai ba. Bashir ya ce,  Damisa Didi ta sanar damu aurenka. ?ago ido ya yi ya kalle shi sai ya sunkuyar da kai yana sosa kai ya ce,  Tuba nake Damisa, babbar Yaya ce ta sanar dani shiyasa na amince da batun. Kuma ta saka har a masallaci an sanar da maganar.

Da mamaki ya ce,  a masallaci?.
 kwari Boss, dan yanzu mutanen unguwa duk sun shaida. ?aramin tsaki ya yi bai ce komai ba Bashir ya ce,  Allah ya sanya albarka Boss, mun so ranar auren ka ayi shagali na gaske, ranar Kano ta san da zaman mu wallahi tallahi. Da ranar kaf unguwar nan sun huta siyan maganin sauro, saboda zamu yiwa unguwar haya?i da ganye mai albarka Boss. Amma hakan ma normal ne, sai dai ba mu san Anty na mu ba.

 Bash ka dakata da yi min wannan maganar ya faWa yana kallonsa.
 Tuba nake, kaina biya wuya na. ?auke ido ya yi daga kallon su amma bai ce komai ba.

Sallamar da aka yi ne ya saka suka kalli wanda ya shigo. Ganin Didi ce da mijinta duk sai suka yi fara a suka gaishe su ta zauna tana cewa,  in aka ga zara za a ga wata, in aka ga Omar za a ganku. Bash ya shafa kai ya ce,  Babbar Yaya muna kewar girki mai daWi wallahi, yanzu sai dai mu dinga yawo mu rasa inda zamu ci. Tayi dariya ta ce,  ba sai ku yi aure ba, shi ogan na ku gashi nan ya yi aure ya bar ku ai.
Bashir ya ce,  Yanzu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login