Showing 186001 words to 189000 words out of 332344 words

Chapter 63 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14376

lokaci ba ya ri?e a tsam-tsam ya ce, "Zan yi kewarki Jidda, ba dan ba?i da zasu zo anjima ba ni zan kai ki da kaina."

Ta ce, "nima zan yi kewarka Rouhi, har na fara kewarka tun kafin na tafi."
"Allah ya kai ki lafiya ya dawo min dake lafiya. Amma magana ta gaskiya zan yi kewarki fiye da yadda ki ke tunani, zan shiga halin maraici gaba da baya Ashiq. Ina tausayin gangar jikina da ta saba rayuwa dake, ko ya zata kasance a cikin kwanakin nan ban sani ba."

?agowa ta yi daga jikinsa ta sumbace shi a fuskarsa ta ce, "Nima zan yi kewarka, zan yi aljanun dare" ta faWa tana Waga masa gira. Dariya ya yi mai sauti ya buWe idanunsa ya ce, "Allah da gaske? FaWa min adadin kewar da zaki yi." Sai kuma ta rufe ido ta koma jikinsa ta kwanta cike da jin kunya. Itace ta saka sunan aljanun dare, in ita da Omar Win suna kashe juna da soyayya sai ta ce Omar yana maganganu da rawar jiki kamar wanda aljanunsa suka tashi, shima ya ce itama kamar mai aljanu.

Ya Wago ta ya ce, "sai kin faWa min adadin kewar da zaki yiwa aljanunki." Dariya ta yi bata ce komai ba, ta kalli idanunsa sai ta sake yin dariya ta ce, "zan dawo da wuri in sha Allah." Murmushi ya yi ya sumbace ta a goshinta ya ce, "Mu je." Tare suka fito ta shiga mota suka wuce ta bar shi da kewarta.
KRB3P068
Nana haleema.

? ? ? ? Da wuri suka shiga Kaduna, kowa ya yi mamakin ganinta dan babu wanda faWawa zata zo. Abiy ma sai ganin ta ya yi, ya nuna tsananin farin cikin ganin ta suka gaisa kafin ta shiga wajan Mama. Nayla har Wakin Mama ta shiga ta ce, "Mamana kina ina? Na yi kewarki." Mama ta kalli Nayla ta ce, "Gani nan Nayla, saukar yaushe?." ?arasa tayi ta rungumeta ta ce, "Na yi kewarki sosai Mama. Laifin me nayi miki bakya Waukar wayata kuma bakya kirana? Hankalina ya tashi, shiyasa na zo na ji laifin da na yi miki."

Mama ta yi murmushi ta ce, "ki je ki ci abinci ki huta zamu tattauna." Nayla ta fita tana cewa, "Shikenan Mama ina dawowa." Wanka ta yi ta shirya ta sha baccin gajiya, basu haWi da mutanen gidan ba sai bayan sallar i'sha. Ta fito ta zauna kusa da Mama ta ce, "Ya J angon Salma." Da mamaki ya ce, "Ke kuma saukar yaushe?."

Ta kwanta a jikin Mama ta ce, "tun Wazu."
"ina ki ka baro Omar Win?."
"Gida mana."
"Lallai Hajiya Nayla, wannan kyau haka ai sai na kasa gane ki." Dariya tayi sosai ta kalli Abiy da yake ta murmushi ta zuba abinci tana ci suna ta hira da Jalila da Jawad har suka gama.

Nayla ta ce, "Abiy ka taya ni bawa Mama ha?uri, na yi mata laifi ko wayata bata Wauka, duk na damu wallahi." Mama ta kalle ta a sanyaye ta ce, "ni nace miki kin yi min laifi ne Nayla?."
"To Mama bakya Waukar wayata kuma bakya kirana, in ba laifi na yi miki ba me nayi miki?." Mama tayi ajiyar zuciya ta ce, "ni na yi miki laifi ai Nayla, ki yi ha?uri ki yafe min." Nayla ta ce, "Mama ni kika yiwa laifi? Ni babu abinda ki ka yi min Mama, Don Allah ki daina faWar haka" ta faWa dan a tunaninta akan zuwa gidanta da ta yi ne.

Mama ta ce, "Nayi miki laifin ne ai Nayla, kunyarki ma nake ji shiyasa gabaWaya ko wayarki bana iya Wauka saboda ban san ne zan ce miki ba Nayla. Har bana so na haWa ido dake saboda irin abinda na yi miki."

Nayla ta yi sak jin abinda Maman ta ce, ta taso ta dawo kusa da Mama ta ri?e hannayen Mama ta ce, "Mama me ki ke faWa ne haka? Me kika yi min da zaki kasa Waukar wayata? Mama ni fa ?arki ce, laifin me zaki yi min?." Mama ta ri?e hannayenta ta ce, "na yi miki Nayla, nayi miki, amma don Allah ki yafe min. Duk abinda ya faru a lokacin aurenki da Omar ni na haWa, ina so ki aure shi saboda wani buri nawa da na saka a zuciyata, shiyasa ki ka kasa gane kan mahaifinki a lokacin, saboda ni nake Wora shi akan abinda ma bai faru ba, ki yi ha?uri kin ji Nayla."

Nayla ta fara hawaye jin kalaman Maman babu daWin ji ta ce, "Mama ni ko me ki ka yi min ba laifi bane a wajena, kuma lokacin ai kina so ki samar min da abinda nake so ne shiyasa ki ka yi haka, kin yi dan farin cikina ne ba dan ki cutar dani ba." Mama ta ce, "A'a Nayla dan cutarwa nayi hakan, na raine ki na baki tarbiyya da rayuwa mai kyau, amma ina burin ki yi aure a gidan da zaki sha wahala Nayla. Kuma bani da wani dalili mai ?arfi akan hakan sai akan abinda ya wuce, saboda wani saSani da ya shiga tsakanina da mahaifiyarki a shekarun baya. Kuma kafin ta rasu ta nemi afuwata tun kafin ma a haifeki, ta nemi tafiya na yafe mata mun zauna lafiya mun cigaba da rayuwa. Amma shaiWan ya saka ni har nake so na ga kema kin shiga irin saSanin da ya shiga tsakanina da maahifiyarki. Ki yi ha?uri Nayla, don Allah ki yi ha?uri. Na gane kuskurena a lokacin da mahaifinki ya ganar dani, na kuma yi nadama, har zuwan da na yi gidanki ma ki yafe min kin ji?."

Nayla ta gigice bata ma jin me Maman take cewa, hangowa take yi Mamanta na neman afuwarta, ganin hakan take kamar babban saSo ne a wajanta. Ta ce, "Don Allah Mama ki bari bana jin daWin wannan maganar da ki ke yi, Kuma ai Allah ne ya ?addara faruwar komai baki da hannu a cikin duk abinda ya faru. Don Allah ki daina bana so."? Mama zata sake magana Nayla ta ce, "don Allah Mama ki bar maganar nan, ki yi ha?uri ki bar maganar bana son ji ko kaWan" ta faWa tana toshe kunnenta tana kuka.

Abiy da yake jinsu? ya ce, "Zo Mamana." Ba musu ta koma kusa da Abiy ya share mata hawaye ya ce, "Ki nutsu."
"Abiy kana ji me Mama take cewa fa, in ma laifin ta yi min ba uwata ba ce meyasa take neman afuwata? Wanne laifi Mama zata yi min da zata ce kunyata take ji har na dinga kiranta ta?i Wauka?."

Abiy ya ce, "neman afuwarki yana da kyau tunda laifi tayi miki Nayla, amma tunda kin ce bakya son ji shikenan." Nayla cikin muryar kuka ta ce, "Ni bana so."
"To ai an bari" Abiy ya faWa cikin rarrashi dan ya san halinta.

Jawad dai bai ce komai ba sai ma tashi da ya yi ya fita Jalila ma ta tashi ta bar wajan. Nayla ta kalli Mama ta ce, "Mama ni baki min komai ba don Allah ki daina faWa, in kina so nayi farin ciki ki daina cewa na yafe miki."

Mama ta yi murmushi ta ce, "Na daina Nayla."
"Baza ki sake ?in Waukar wayata ba?."
"Bazan sake ba Nayla."
"Kuma a Wakinki zan kwana."
"To Nayla" ta faWa da murmushi tana kallonta amma a zuciyar ta gabaWaya babu daWi, ta rasa me ya kai ta har ta yi ?o?arin cutar da Nayla wacce ta raina da kanta. Ina ta tuna hakan sai zuciyarta karye ta fara zubar da hawaye.

Nayla tashi ta yi ta shiga Waki, Mama ta kalli Abiy ta ce, "na san ban kyauta ba da na biyewa zuciya, amma yanzu wallahi na yi nadama bazan sake ?o?arin aikata abinda na yi ba, ka yi ha?uri. Tun ranar da aka yi maganar nan ban samu ?arfin guiwar baka ha?uri ba sai yau." Abiy ya ce, "ta ya zaki bani ha?uri kin koma wasan Suya da mutanen gidan?."

Mama ta kalli Abiy tana hawaye ta ce, "Kunya ce Abiy, kunyar haWa ido da kai nake yi, kunyar su Jawad lulluSe ni take yi da zarar na ji maganarsu balle na haWa ido dasu. Nayi kuskure, na so na aikata abinda zan bar baya da ?ura, duk da na aikata Win amma na gane kuskurena wallahi. Ka yi ha?uri ka yafe min."

"Ni baki min laifi ba ai, in ma kin yi Allah ya hukunta ki tun ba a je ko ina ba, iya kunyar ?a?anki da ki ka ji babbar jarabawa ce a gare ki, baza su taSa mantawa da wannan abun da ki ka aikata ba har abada. Na Waga miki ?afa tun farko saboda na san ke ?ar adam ce, dole ki yi kuskure a wani Sangaren. Amma in aka duba alkhairan ki ga Nayla sai alkhairin ya shafe kuskuren da ki ka aikata. Tunda kin gane abinda ki ke ?o?arin yi ba mai kyau bane ai shikenan, Allah ya yafe mana gabaWaya. Kar ki sake yiwa Nayla maganar ki ?yaleta kawai, bata fahimce ki yadda ya kamata ba kawai ki bar maganar. Mijinta kuma duk ranar da ku ka haWu ki yi ?o?arin wanke laifin da ki ka aikata." Mama ta ce, "in sha Allah, Na gode." Bai ce komai ba ya tashi ya hau sama ita kuma ta shiga Waki.

? ? ? Nayla tana Wakin ta wanda aka gyara mata daga zuwanta, ta Wauki waya da niyar kiran Omar ta ga kiransa har sau biyar tun tana bacci. Murmushi tayi zata kira shi kenan wayar ta yi shutdown. Dafe kai ta yi da sauri ta Wauko charger ta saka sai ta bar wajan ta tafi Wakin Mama da niyar ta dawo.

? ?? Da ta je Wakin ta zauna ta dinga jan Mama da hira har ta Wan sake kaWan suna hira da dariya kafin ta koma nata Wakin. Number Omar take kira amma bata shiga ta gwada yafi sau goma amma bata tafiya. Ta yi masa text message ta fita zuwa Wakin Mama a can tayi kwanciyarta.

? ? ? Washe gari tana tashi Omaar ne yazo ranta, ta Wauki wayar ta duba ga mamakin ta babu kiransa ko Waya. Ta kira shi ji tana ringing, ta yi murmushi saboda ta yi missing voice Winsa tana jira ya Wauka amma sai ta ji an katse kiran, abin ya bata mamaki ta sake kira aka sake katsewa ?arshe sai wayar ma ta daina shiga.

? ? ? ? Tunani ta tsaya yi me hakan yake nufi kenan? Yana sane yake katse kiran ko kuma network ne?. Tunanin ta ya bata network ne kawai dan ta san babu wani abu mai mahimmacin da zai saka ya katse mata kira. Bayan sun karya sun yi wanka suka fita ita da Jalila. Shagon su ita da Tiwny suka fara zuwa,? Nayla taga shagon da yadda aka sake faWaWa shi komai ya yi kyau sosai kuma ana ciniki ma sha Allah. Daga nan sabon shagon Omar na Kaduna ta je ta ga yadda yake daga nan suka wuce gidan Yaya Ahmad da ya yake ya zo hutu yana Kaduna.

? ?? Nayla gwada kiransa take ta yi amma bata shiga duk ta damu, ta yi message bai bata amsa ba gabaWaya hankalinta ya dawo Kano cikin damuwa. Wayar Jalila ta karSa ta kira shi abin mamaki wayar ta shiga, bata gama mamaki ba sai da taga ya Wauka daga can Sangaren ya ce, "Hello." Nayla jin ya Wauka sai jikinta yayi sanyi da tunanin kenan wayarta ce bazai Wauka ba ko me?. Jin ya sake maimaita hello ya saka ta ce, "Rouhii!." ?it ya katse kiran ba tare da ya ce mata komai ba.

Nayla hankalin ta ya tashi, ta kira ta ji ya saka number Jalila a inda ya saaka numberta. Nan da nan ta rubuta message ta tura masa a wayarta amma har suka baro gidan Yaya babu reply.

GabaWaya ta shiga damuwa, koda ta dawo sai da Mama ta tambaya me yake damunta ta ce babu komai. Tana ji Abiy yana faWawa Mama ai Omar ya kira shi yana faWa masa sun buWe shago a garin, Nayla bata ce komai ba tana mamakin kenan itace dai bazai Wauki wayarta ba kenan ko me?. GabaWaya sai zaman ya dame ta, da?yar ta iya kaiwa ranar juma'a da safe Baba Salisu ya Wauko ta zuwa Kano.

Bai san zata dawo ba baya gidan ya fita, Allah ya taimaka da key Win gidan a hannunta ta shiga ta tarar da komai tsaf kamar ko yaushe, ta shiga Waki ta yi wanka ta yi sallah ta dafa abinci ta ci ta ajjiye masa nasa. Shiru babu labarinsa har dare, sai tara na dare sannan ta ji motsin shigowarsa. Da hanzari ta fito falon a lokacin da yake shigowa kawai ya ganta a tsaye. ?auke kai ya yi daga kallon ta ta ce, "YaMar!." Kallon ta ya yi ya watsar kamar bai gane ta ba, bai ce mata komai ba ya raSa ta ya wuce.

Nayla ta shiga damuwa, jikinta a sanyaye kafin ta shiga ciki ta same shi a zaune yana amsa waya yana kuma rubutu da alama abinda ake faWa masa yake rubutawa. Yanke wayar ya yi ya ajjiye bai kalle ta ba ta ce, "Rouhii!." Banza ya sake yi mata bai kula ta ba, zata sake magana ya riga ta ya ce, "Ya isa! Fita ki bani waje bana son surutu!" Ya faWa fuska a Waure.

Nayla da mamaki take kallonsa jin abinda yace, ta ce, "Rouhii ni ka ke cewa baka son surutu?."
"To ke Win wace? Uwata...?" Ya faWa yana buWe mata ido. Nayla gabanta ya faWi, ta Wauke kai daga kallon sa ta ce, "Rouhi me ya faru?." Bai kula ta ba ya sake share ta, ta ce, "laifin me nayi maka haka?."

"Baki ji me na ce ba kenan?." Zata yi magana ya Wago ya watsa mata idanunsa yana Wan buWe su kaWan a kan fuskarta, sai ta yi shiru ya nuna mata ?ofa ya ce, "ki bar Wakin nan."

Nayla ta haWe fuska cikin shagwaSe ta ce, "Ban san laifin da na yi maka ba, kuma...." Cikin murya mai kaushi da tsawa ya ce, "na ce ki fita ko?." Duk da ba tsawa ya yi mata sosai ba amma sai da jikinta ya yi rawa, domin kuwa ya canja mata daga Omar ya koma mata Tiger wanda ta sani a baya. A sanyaye ta fita ya yi ?aramin tsaki ya Wauke kai bai bari ya cigaba da tunanin ba ya cigaba da abinda yake yi.

Ta jima da fita bai ji motsinta ba, duk sai ya damu da rashinta dan ya yi tsananin kewarta, yana so ya nuna mata kuskuren da ta aikata ne ko dan saboda gaba. Zuciyarsa umarni take bashi akan ya je wajanta, nauyin zuciya yake ji saboda kewarta da yake ji a jikinsa. Ajiyar zuciya ya yi tare da kulle idonsa, a lokacin ya ji ta buWe ?ofar ta shigo Wakin. Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke cikin farin cikin ganinta, bai nuna mata ba yana kallon ta ta gefen ido. Da ta shigo bata kula shi ba ta itama je ta kwanta a inda ta saba kwanciya, shi kuma yana daga zaune a inda ta bar shi. Jin bai yi mata magana ta gyara kwanciya amma hasken ya dame ta.

Kukan shagwaSa take yi ?asa-?asa, tun baya ji har ta kai ga yana jin kukan, ya Wago a fusace ya ce, "Ko ki daina yi min kuka ko ki tashi ki fita, dama ban gayyace ki ba ko!?." Shiru Nayla tayi ta rufe ido bata ce komai ba, ?irjinta bugawa yake yi dan ta saba da sabuwar rayuwar da suka fara, wannan Wabi'un nasa ta manta dasu, gashi yanzu ya dawo mata Omar Win da ta sani a baya. Omar ya yi tsaki ya cigaba da abinda yake yi. Bai jima ba ya tashi ya kashe hasken Wakin ya kwanta bai kalle inda ta ke ba.

Yana jin duk motsinta da kukan da take yi ya bai saurareta ba duk da tarin kewarta da ya yi. Itama ganin yana share ta ba tare da ta san laifin da ta yi masa ba sai ta daure ta yi baccin ta bata sake ce masa komai ba. A haka ta yi bacci cike da takura shima haka. Ko da asuba daga gaisuwa ya amsa mata da?yar bai kuma yi mata magana ba sai ta shiga damuwa amma ta yi ?o?arin Soyewa.

? ? ? ? Washe gari asabar, abincin da ta dafa masa a daren jiya sai zubarwa tayi dan ya lalace, tana so ta dafa wani tana tsoron kar ya ?i ci a sake yin asara. Sai ta dafa tea da abincin kaWan yadda ko bai ci ba zata iya cinyewa. Bai ma fito falon ba gabaWaya, yana ciki Waki yana aiki ba tare da ya neme ta ba. Ganin bai fito ba ya saka ta shiga Wakin da sallama ya amsa a ciki.

Ta ?arasa ta zauna tana ri?e da mug Win tea ta ce, "Ga tea." Zata ajjiye ya ce, "Wauke kayan ki, ai ban ce ina so ba ko?." Nayla ta bishi da kallo ce, "wai me nayi maka haka don Allah? Ka faWa min abinda nayi maka sai na baka ha?uri. Tun a Kaduna bani da kwanciyar hankali ka ?i Waukar wayata, nayi messsage ka ?i ka yi reply. Haka kawai ka fara fushi dani ba tare da na san laifina ba? At least kafin ka fara fushin ya kamata ace na san laifin da na yi maka, ban san me nayi ba ka daina Waukar wayata, na dawo ka ?i kula ni kuma baka ce min ga kuskuren da na yi ba" ta faWa cike da jin haushi tana kallonsa.

Yana jin abinda take faWa yana mamaki, sai ya faWa mata ma zata gane kuskuren ta kenan. Ya girgiza kai ya ce, "in kika cigaba da yin magana ba tare da na baki izini ba sai na watsa miki tea Win nan!. Ki Wauke kayan ki bana sha!." Ya sake faWa ba tare da ya kalle ta ba.

Ajjiye masa tayi a gabansa ta ce, "duk da ban san abinda na yi ba, ka yi ha?uri." ?an ture mug Win ya yi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login