Showing 81001 words to 84000 words out of 332344 words

Chapter 28 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14429

kalle ta cikin tsananin fusata da Sacin rai, hannunsa yana rawa ya ce, "Ke bana son aurenki, ban taSa ji a zuciyata ina son zama dake ba, Ina zaune dake ne saboda Didi, duk abinda nake yi a gidan nan saboda ita ne. To naga lokaci ya yi da komai zai ?are tunda har abin ya kai ga haka......" Ya dafe kai tare da runtse ido, ya buWe ido ya sake kallon Nayla ya ce,

"A kan aurenki ta Waga hannu ta mare ni, tun ina ?arami muke tare da ita bata taSa dukana ba koda wasa sai yau, yau Win ma a kanki da waWancan munafukan. To ina so ki san bana sonki kamar yadda bana son aurenki, kina zaune dani ne saboda alfarma, Ina kwana a gidan nan saboda dolen da aka yi min a kan ki. Tunda abin nata ya zama haka yanzu komai zai ?are, bazan......." Didi ta mi?e tsaye da hanzari ta katse shi ta ce, "Omar ka dakata!."

"Bazan dakata ba! Bazan dakata ba!. Ni kika Wauki hannu kika mara, tun ina ?arami baki taSa aikata hakan ba sai yau, tun lokacin da nake ji da tantiranci, nake zubar da jinin mutane, nake Wauko miki magana, ki ke yawo a kan titi kina nemana, ki ke zuwa police station belina, ki ke zuwa prison kai min ziyara, baki taSa Waga hannu kin mare ni ba sai yanzu. Akan su da kuma kan wannan aurenta kika Waga hannunki da kike rarrashina dashi ki ka mare ni ko Didi?!" Ya faWa tana kallon ta idanunsa har ruwa suka tara saboda Sacin rai, jikinsa rawa yake yi haka bakinsa. Jijiyoyin kansa sun tashi, duk wata kafa ta gashi a jikinsa ta buWe, fuskarsa tayi ja matu?a.

Didi ta runtse ido, saboda tashin hankali har Wan cikinta sai da ya motsa saboda bala'in Omar. Ta runtse ido ta ce, "Babu ruwan auren nan a cikin maganar nan, na sako shi a ciki ne saboda ka san mahaimmacin su a gare ka."

"To bana son auren ai, na faWa miki tun farko ai ko? Tun kafin azo nan na ce miki bana so kuma bazan karSa ba. Amma me ki ka ce min? Dole ki ka yi min ba dan ina so ba kika jawo ni har nake zama a cikin gidan nan. Didi na gaji da dolen da ki ke yi min, bazan sake aikata abinda bana so ba saboda ke!" Ya faWa yana nuna Didi da yatsa cikin fitar hayyaci.

Ya nuna Nayla hannu yana rawa amma Didi yake kallo ya ce, "Kin tuna? Kin yi min faWa a kanta, kin ce min ina shirme a kanta, kin kore ni daga falon ki akanta, kin yi min dole na karSi aurenta, kin yi min dole na zauna da ita, kin yi min dole ina saurarenta, kin yi min dole ina shiga lamarinta, yanzu kin mare ni ta dalilinta. Me zai saka ni na so ta har na so aurenta? Me zai saka ni na zauna da aurenta!?. Cewa ki ka yi in ban karSi aurenta ba babu ni babu ke shima duk a kanta. Didi ko aljanna zan samu ta hanyar zaman aure da ita na yarda ta wuce ni, ai rahamar Allah tana da yawa, hanyar rabo tana da yawa zan samu a wani kiran rabon ba sai ta dalilin aurenta ba!?."

Didi ta dafe kai ta ?arasa zata ri?e shi ta ce ta ce, "Omar ka saurare ni...." Ya fizge jikinsa ya ce, "bazan saurareki ba, na gama saurarenki Didi, na gama sauraren maganar ki akan abinda bana so har abada. Wallahil azim bazan taSa son abinda ya fito daga hannunsu ba ciki harda auren nan da ita kanta!. Komai ya zo ?arshe, komai ya lalace Didi, komai ya ?are!" Ya faWa can ?asan ma?ogwaro yana kallonta dan jijiyar kansa har harbawa take yi. Didi dafe kai tayi ta zauna ta fara rawar jiki saboda yadda kanta yake sarawa.

Nayla kuwa ta gama ?amewa a wajan tun daga kan maganar da ya kalle ta ya faWa, jikinta ya gama yin sanyi zuciyarta ta gama karyewa a lokacin. Hawaye ya gama wanke mata fuska, jikinta ya gama mutuwa gabaWaya. Shiyasa ta kasa koda motsi, da?yar ta iya ta ri?e Didi tana ganin yadda jikinta yake rawa sosai.

Shi kuma dakatawa ya yi da maganar ganin yanayin Didi ya canja, ransa ya riga ya kai ?arshe wajan Saci, huci kawai yake yi kamar kumurci. Kallon ta yake yi kawai amma ya kasa ce mata komai saboda wutar Sacin rai da ?unar zuciyar da take ruruwa a zuciyarsa. Wai Didinsa ce ta mare shi, mari akan kuncinsa kuma saboda waWanda ya fi tsana a duniya. in ya tuna hakan sai sai ya ji kamar ya kurma ihu. Ji yake kamar ya bankawa gidan wuta, da shi da Didin da Nayla duk su mutu a huta.

"Didi!" Nayla ta faWa a sanyaye tana daga tsaye. Didi bata motsa ba sai rawar jiki da take yi ta ce, "Didi mu je asibiti, baki da lafiya" ta faWa hawaye na sake zubo mata. Didi ta ce, "Nayla ri?e ni mu fita." Nayla ta du?a ta ri?eta, ta saka hijjabinta da yake gefe ta ri?e hannunta suka fita daga falon har lokacin yana tsaye.

Nayla ta buWe gaban mota Didi ta shiga, ita kuma ta ?arasa gate Win ta buWe ?ofa tana duba su Bashir, ganin babu kowa a cikin su wanda zai buWe mata sai ta buWe da kanta ta shiga motarta fita ta bar shi a buWe.

Didi ta ce, "Nayla mu je gidan mu kawai."
"Didi baki da lafiya."
"Ciwon kai ne kawai, mu je gidan mu Nayla, akwai key Win gidan a hannuna." Da yake babu nisa ba jimawa suka ?araso. Nayla ta ajjiye motar ta ri?e Didi har gidan ta buWe mata ta shiga. Gidan yana nan yadda yake ko ?ura babu sosai dan yana zama a ciki sosai.

A kan kujera Nayla ta zaunar da ita, ta Wauki ruwa ta bata tasha ta ce, "ki sha ki kwanta ki huta Didi." Didi ta yi ajiyar zuciya tana kallon Nayla da fuskarta ta tayi ja tana tuna abinda ya faru.

Didi ta sunkuyar da kai bata ce komai ba tana shan ruwan. Ajiyar zuciya ta yi bayan ta sha ruwan tana kallon Nayla, ta jingina da kujera bata san me zata ce mata ba. Nayla ta mi?e ta ce, "Sannu Didi, babu abinda ki ke so?." Kai ta girgiza alamun babu Nayla ta ce, "Ina zuwa" ta faWa tana fita daga gidan.

Motar ta koma ta nufi gidan kai tsaye, ta tsayar da motar a ?ofar gidan ta tarar da an kulle gate Win ta buWe ?ofar ta shiga. Yana nan inda yake a zaune ya dafe kai yana wani irin huci har sautin sa tana ji. Wuce shi tayi bata ce komai ba ta shiga Wakinta ta jawo trolly bag tana zuba abinda ta san zata iya zubawa wanda zai yi mata amfani, ta Wauki laptop Winta da tap Winta, ta jawo jakar tan ri?e da sauran kayan a hannu ta fito.

?arasowa ta yi inda yake, ta kalle shi ta haWWiye yawu Sacin rai ta ce, "Na gode da karSar aurena da ka yi saboda Didi, yanzu ina so ka rabu da aurena saboda nima na ce bana so, ina so ka rabu dani saboda bana so ba dan wani ya yi maka dole ba, bana son zaman auren kamar yadda baka so. Na gode da zaman da muka yi da kai matsayin mata da miji. Zaka iya karSar number wayata a wajan Didi ka tura min saki ba sai ka wahalar da kanka ka rubuta ba! Sai wata rana" ta faWa tana jan jakarta fita daga falon, ta saka jakar a bayan mota ta ajjiye komai na hannunta ta shiga gaban motar taja motar ta fita daga unguwar gabaWaya.
KRB3P026
Arewabooks@nanahaleema11.

Usman Umar shine sunan mahaifin su Omar, asalin kakanin su ?an garin Gombe ne amma iyayen su da shi kansa a Kano aka haife su. Yana da ?an uwa guda huWu har shi biyar kuma dukkan su maza ne dan mahaifiyarsu bata taSa haihuwar mace ba.

Matarsa mai suna Saudat ita kuma asalin su buzaye ne haihuwar ?asar Chad, iyayen su dukkan su a can aka haife su, kana ganin kammanin su ka san ba ?an nigeria bane saboda kyau da gashi. Kasancewar mahafiyar su ta yi aure a nigeria hakan ya saka duk aka haife su a Kano suke kuma zaune a Kano. Su huWu ne mata, sai yayan su namiji guda Waya wanda ya kasance shine babba a cikin su.

Tun farkon haWuwar Usman da Saudat Allah ya ?ulla ala?ar ?auna da soyayya a tsakanin su cikin lokaci kaWan, har ta kai ga ta gabatar dashi a matsayin wanda take so kuma zata aura. Dangin Saudat kowa ya nuna sam baya son Usman, dan kallo Waya zaka yi masa ka fassara shi a mutum mara kirki, sannan a kammani da zubin sa ya nuna hakan.

Saudat ta nuna ita dai shi take so kuma shi zata aura, ?an uwanta da kowa nata ya nuna baya son auren amma ita ta nuna shi take so kuma shi zata aura. Kasancewar inda mahaifiyarta ta fito ba daga nigeria bane da ta ga ta dage akan shi take so bata takura ba ta saki maganar. Dagewar da tayi a kai ya saka dole aka daura musu aure ba dan wani nata yana son wannan aure ba sai dan babu yaddda za su yi da ita ne.

? ?? A gidan gado Saudat ta tare, gida ne da dukka su uku suke aure a ciki, harda space Win sauran biyun da ba su yi aure ba. Gida ne mai Wakuna da yawa amma banWaki biyu ne kacal a gidan kuma a tsakar gida yake. Kasancewar iyayen Saudat suna da rufin asiri sam basu ji daWin wannan gida da ?arsu ta tare a ciki ba.

Bayan auren Saudat da Usman sai asalin halinsa ya fara bayyana, mutum ne mai shaye-shaye, kaf danginsa haushinsa suke ji dan lokacin da aka bashi Saudat har mamaki abin ya basu saboda sun san ba a kintse yake ba. Saudat ta fara shiga damuwa matu?a, dan baya tashi dawowa sai dare kuma a daren da?yar in bai mata duka ba, garin dukan ta da yake yi ta yi Sarin cikin ta ne farko.

Bayan wani lokacin iyayen Saudat suka rasu nasa iyayen su ma suka rasu ya rage basu da kowa sai ?an uwa. A wannan lokacin Saudat ta haifi Aisha wacce Wakyar aka iya rainon cikin ta saboda wahala, duk da bata rasa ci da sha a gidan ba amma ta rasa farin ciki mai yawa. Bayan haihuwar Aisha kamar ya nutsu ya daina komai, amma sai aikin yiwa yaran mutane ba'a da jafa'i, ko wanne yaro Wan iska yake kiransa kuma mara tarbiyya.

Matarsa Saudat sam bata jin daWin wannan kalaman na sa, amma ya riga da ya saba ko magana zai yi sai ya haWa da Wan iska ko tsinanne. Ita kuma tana gujewa Aisha da ta haifa, kar bakin da yake yiwa yaran wasu ya faWa kanta.

A cikin wannan yanayi Aisha ta taso kasancewar yana matu?ar son Aisha babu abinda baya yi mata, komai yana siya mata na yara da duk abinda zata bu?ata. A haka ta fara tasawa cikin kula da tarbiyyar mahaifiya. Sai dai kyara da hantarar mutanen gidan, dan zuwa lokacin sauran mazan duk sun yi aure. Matan gidan sai suka haWewa Saudat kai, saboda ta fi su kyau da jiki mai kyau sai suke ba?in ciki da haka. Babu damar Aisha ta fito tsakar gida koda rarrafe ne sai tsawa da duka.

A haka aka cigaba da rayuwa, Aisha da shekara huWu a duniya Allah ya kawo cikin Omar a lokacin da ba a yi tunanin zuwan sa ba. Da yake Saudat tana fama da rashin lafiya mai tsanani wacce take tashi a kai a kai ba a yi tunanin zata iya sake haihuwa a wannan yanayi da take ciki ba.

Bayan ta haihu aka sakawa yaro suna Omar, sunan mahaifin Usman kenan. Da kanta ta kaiwa ?an uwata shi amma babu wanda ya iya Waukarsa, har gwara ?anwar ta Saroot a lokacin bata yi aure ba yarinya ce, ta nuna ya burge ta saboda ya yi kama da ?an Chad gabaWaya.

GabaWaya ba sa son yaranta, Saroot Win ce kawai ke iya yiwa Aisha wasa har ta Wauki Omar. Haka take zaune cikin yanayi na damuqa kala-kala, ga damuwar miji, ga damuwar zaman gidan yawa, ga damuwar basa sonta, ga damuwa ?an uwanta.

Tana matu?ar son Omar, tana ?aunar Omar saboda yana kama da ita, ?aunar da take masa ya saka take kiransa da Ashiq ko ta ce Habibi saboda son da take yi masa. A haka ta cigaba da rayuwa yau da lafiya gobe babu. Tun bayan ta yaye Omar ciwo ya matsa mata, yau lafiya gobe babu lafiya haka ta dinga rayuwa kamar baza ta tayi rai ba.

A haka har Omar ya kai shekara biyar zuwa lokacin Aisha tana primary school dan ta girma tayi tsaho sosai. Omar yana da shekara shida a duniya mahaifiyarsu ta bar duniya, ?an uwanta sun ji mutuwarta sosai, sun kuma sake tsanar mahaifinsu Aisha saboda a ganin su shine silar raba su da ?ar uwarsu. Kafin rasuwarta ta barwa Aisha amanar ?aninta, duk da yarinya ce amma maganar ta ratsa ta sosai tana ta kuka tana ri?e da hannun mahaifiyarta.

Kaf gidan babu mai kula da lamarin Omar da Aisha sai shi mahaifin na su, babu wanda yake damuwa da maraicin su kowa sabgarsa yake yi dan zuwa lokacin mutum biyu sun tashi gidan ya zama saura mutum uku. Hakan ya saka Aisha take rayuwa cikin kaWaici ba uwa kuma babu dangin da zasu ja ta a jiki su nuna mata ?auna da soyayya. Ita kaWai ke nunawa ?ananinta soyayya, gashi da rigima ita kaWai take iya rarrashinsa tana kuka yana kuka. Wani lokacin baya daina kuka har sai mahaifinsu ya dawo.

Zaman gidan gabaWaya baya yi musu daWi, ga Wabi'ar mahaifinsu har lokacin tana nan bai daina ba hakan ya saka suka zama marayu na asali wanda basu da wani gata sai na Allah. A haka suke cigaba da rayuwa, Aisha tun tana ?arama ta iya dafa abinci saboda babu mai damuwa da sun ci ko ba su ci ba, dole ita zata yi ko dan Omar.

A haka suka cigaba da rayuwa har Omar ya shiga primary school da kuma islamiyya. A cikin wannan yanayi ciwo ya kwantar da Baba saboda shan tabar da yake ta taSa masa hunhu, daga nan bai sake samun lafiya ba har ya bar duniya.

Rasuwar su sai ta sake zamar musu sabon maraici domin kuwa babu wanda yake kula dasu duk da lokacin sun girma ba kamar Aisha. Aisha tana da shekara goma sha biyar, Omar yana da shekara goma da ?an watanni. A lokacin ne Kawu Sulaima kasancewar shi ne na tsakiya a cikin su ya ce zai aurar da Aisha dan bazai iya kula da ita ba, ta dinga kuka tana bata so, a lokacin sai ya ce bazai sake mata magana ba ta zauna a haka har ?arshen rayuwarta.

Haka suka cigaba da zaman gidan babu daWi ko kaWan, abinci ma wahalar samu yake musu saboda sai anga dama za a basu abinci, wani lokacin ragowar da ?an uwan su suka rage za a basu.

Rashin wannan jigogi da suka yi a rayuwarsu da rashin mai nuna musu soyayya sai tarbiyyar Omar ta fara gurSacewa, ga yanayin gidan da suka tashi zagi kamar gidan maguzawa, yara da manya dan su yi ashar ?aramin abu ne a wajan su. Omar sai ya zama in aka tura shi makaranta ba makarantar yake zuwa ba yawo kawai yake tafiya. A haka ya fara shiga cikin yaran unguwa Sata gari yana zama, in Didi tana nemansa ma kai tsaye can zata je kuma zata ganshi.

Omar sai ya zama yana ?ara shekaru yana girma baka iya ka tan?wara shi ba, duk dukan da zaka yi masa ba zai buWe baki yayi magana ba. Ya sha duka a wajan ?an uwan mahaifinsa da matar Kawu Babba wanda ya kasance shine babba. Abu kaWan zai yi su yi masa dukan tsiya.

Baya magana da kowa sai Aisha kawai wacce ya yiwa la?abi da Didi. Ya ji kalmar Didi a wani film na india, ya shiga wajan Kawu Sulaiman ya kira shi ya gama ran?washin kansa, a lokacin ya ji ana kiran Didi sannan ya ji kawun ya fassara ya ce ?ar uwa kalmar ta ke nufi, shikenan ya saka mata Didi bai sake cewa Yaya ba.

Didi ce kaWai take hana shi ya hanu, bayan ita babu wani ko wata da zai iya cewa kar ya yi ya?i yi. Kaf labarin iyayen su da abinda ya faru da yana yaro ya sani a bakin mutanen gidan, ya san komai babu irin ba?ar maganar da basa faWa akan iyayensa, hakan ya saka ya san komai akan dangin mahaifiyarsa da halin mahaifin su da wanda bai sani ba.

Yana cigaba da girma rashin ji yana sake ?aruwa, domin sai ya zama sume manya taqadiran makaranta, in suka saka kara babu wanda ya isa ya tsallake a cikin makaranta. Babu wanda yake tsoro kullum a sai an zane shi a makarantar amma ko a jikinsa gobe sai ya maimaita. Gashi yana daga cikin masu ?o?arin makarantar, har class aka ware musu ana koyar dasu saboda ana yawan yin gasa tsakanin makarantu. Ana koya musu turanci yadda zasu fitar da makaranta kunya.

Islamiyya kuwa da?yar Didi ta saka ya kai aji huWu daga nan ya daina zuwa saboda baya lamuntar a ce za a dake shi in ya yi fashi ko in ya makara, gashi ya fi kowa laifi amma ba a isa a taSa shi ba. Yana aji huWun wani Malami ya dake shi saboda ya makara ai kam ya fasa masa kai da dutse? ya gudu. A ganin sa kan me za a dake shi a gaban ?an aji kuma harda mata.

Akwai wani babban malami a islamiyyar mai suna Malam


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login