Showing 27001 words to 30000 words out of 332344 words

Chapter 10 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14399

yin abun da bana so saboda ke. In na ?i yi ai ba zunubi Allah zai rubuta min ba, tunda ba haihuwata ki ka yi ba balle ace na saSawa uwata! Ya faWa harararta.

Dariya ya bawa Didi ganin hararar da yake mata da kalamansa, bai taSa faWa mata haka ba tun yana tantirinsa sai yau, tunda ta ji ya faWa tasan ta kunna shi da yawa. Ta danne dariyar ta ce,  ka tashi mu je yanzu.

Kamar bazai motsa ba ta sake cewa,  ka tashi Omar don Allah. Banza ya sake yi mata sai kuma ya kalle ta ganin ta koma kalar tausayi sai ya kawar da kai. Bazai iya ?in yin abinda ta ce ba, duk abinda ta ce masa yayi koda baya so dole ya yi saboda ita Win Sangaren rayuwarsa ne, koda yaso yi mata tijara da sun haWa ido sai ya yi laushi saboda tasirin ?aunar da yake yi mata. Ya mi?e ba tare da ya kalle ta ba ta yi gaba ya biyo bayan ta. Bai kulle gidan ba suka shiga gidan Hajja fuskarsa a Waure dan wallahi ya gaji da wannan abun da Didi take masa, dan yana girmamata yana yin duk abinda ta ce ba hakan yana nufin ta dinga yi masa abinda baya so ba.

A bakin falon ya ja ya tsaya Didi ta shiga tana cewa,  Hajja Omar ne ya shigo yi miki sallama ya kuma tsaya a bakin ?ofa. Hajja ta ce,  Ummaru shigo mana, ka tsaya daga nan kamar ba?o. ?aramin tsaki ya yi takaici ya mamaye masa zuciya, ya cize baki tare da haWWiyar yawun jin haushi ya shiga falon da sallama a ciki.

Hajja ta amsa tana kallon sa tana murmushi ta ce,  yanzu nake tambayar matarka kwana biyu ban ganka ba, dan halak ashe zaka shigo. Shi dai bai tanka ba ya zauna ya ce,  Hajja barka, an sha ruwa lafiya.
 Lafiya lau Omar, ya iyali?.
 Allah ya kiyaye ya dawo daku Lafiya ya faWa ba tare da ya amsa tambayar da tayi masa. Hajja ta ce,  amin na gode Ummaru. Kafin Hajja ta sake magana ya mi?e tsaye Hajja ta ce,  har zaka wuce?. Kai ya Waga kawai bai yi magana Hajja ta ce,  Nayla ki tashi ku tafi dare yana yi.

 Tare mu ka zo?. Duk kallon sa yaga suna yi musmaman Didi da take aiko masa da harara, a lokacin ya fahimci su a ganin su faWar hakan da ya yi kuskure ne kenan. Didi ta ce,  Hajja tare zamu wuce da ita ai, shi wannan ma aiki suke yi na haWa takalman sallah.
Hajja ta ce,  Allah ya taimaka Omar, Takalma suna kyau sosai.
 Amin ya amsa a ta?aice tare da cewa,  Sai an jima ya faWa yana fita da sauri.

Hajja ta girgiza kai ta ce,  Omar kenan. Nayla dai tunda ya shigo bata motsa ba, mamaki ma take yi da ya iya shigowa bata Wauka zai zo ba duk da ta san Didi ce ta saka ta. Kamar ruwa ya tsince ta haka ta yi tsif ko motsin kirki bata yi, duk abinda ya ce tana ji har ya fita.

Diid ta ce,  To Hajja Allah ya kiyaye ya sauke ku lafita ya karSi ibada, ayi mana addu a. Hajja ta ce,  Amin Aisha. In sha Allah za a yi addu a bakin gwargwado. Didi ta mi?e ta ce,  mu zamu wuce. Nayla ma sai ta mi?e ta ce,  Hajja Allah ya kiyaye hanya, ayi mana addu a Hajja.
 In sha Allah za a yi Hauwa, Allah ya baku zaman lafiya da wannan Damisar mijin naki, ya sauke masa wannan abinda yake ji a kansa. Mutum kamar aljani. Dariya Nayla tayi suka fita ita da Didi har Salna da ta raka su gate ta dawo.

Da yake Didi ta cewa AbdulHamid tana gidan Omar yana ?ofar gidan da mota yana jiranta. Da ?afa suke takawa ita da Nayla suna hira. Didi ta kalli gidan su bayan sun fito ta ce,  Nayla Omar ko abinci ba ya ci a gidan ko?.

Nayla ta kalli Didi ta ce,  Didi ni abincin ma nake so a rage ya yi yawa kar ya lalace, ni kaWai ce ba wani abun kirki nake ci ba. Don Allah ki aiko a rage wani abun kar azo ayi asara, ko iya lemo yana nan a jibge ko cartoon ban sha ba har yanzu. Didi jin ta canja maganar sai ta yi murmushi ta ce,  Ai Nayla abincin ki ne ta ya za a rage?.

 To Didi sun yi yawa sosai, ni ko shinkafa ban buSe ba kuma tana nan tafi guda biyar fa. Na dai buWe basmati amma babban buhu ban buWe ba. Don Allah a rage wani abun kar azo ana asara, gwara a rage a bawa masu so. Didi ta ce,  gashi ke kaWai ke ci ko?. Nayla ta ce,  eh wallahi, Ni kaWai ce taya zan iya da abincin nan?. Didi jin amsar da take so ta samu sai ta ce,  Omar baya ci kenan, Allah ya shirya min Omar shirin addini. Nayla ta amsa da amin a zuciyarta.

Didi ta kalle ta suna gab da gidan ta ce,  Nayla na san halin Omar, ki cigaba da ha?uri komai zai zama labari. Wallahi ni kunyar ki ma nake ji. Nayla ta ce,  Babu komai fa Didi, kowa da ?addarar da Allah ya rubuto masa. Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce,  haka ne, Allah ya kawo mana mafita. Ta amsa da amin a lokacin suka zo ?ofar gidan. Nayla ta ?arasa ta gaisar da mijin Didi sannan suka yi sallama Nayla ta shiga gidan ita kuma ta hau mota suka tafi.
KRB3P009
Arewabook@nanahaleema.

Washe gari har ta shirya da safe ta fito harabar gidan bata ji motsin sa ba, ban da Allah ya sa ma taji motsi da asuba baza ta san a gidan ya kwana ba. To ta ji an buWe gate har take mamakin daman yana zuwa masallaci ko yanzu ya fara.

Harabar gidan ta ke a tsaye tana kallon motar tana tunanin ta yadda zata fita da ita da baya, ita ta saba da babban gida wanda zata juya mota kawai ta fita ta gaba ba ta baya ba. BuWe gaban motar tayi ta saka laptop ta buWe mazaunin driver ta shiga. Dafe kai tayi tunawa fa ita zata buWe gaye Win, tayi tsaki ta fito ta buWe gate Win sannan ta shiga motar tana fitowa da baya a hankali.

Kasancewar safiya ce babu jama'a sosai kuma babu abin hawa shiyasa ta fito da motar, ba dan haka ba tsaf sai ta bugawa wani motar. Zata fito ta rufe gate Win ta ga Bashir shine ya kulle gate Win ta kalle shi tana cewa, "Sannu, na gode."
"ina kwana Antyn mu." Murmushi ta yi ta ce, "Ka tashi lafiya? Ya ibada?."
"Lafiya lau." Key ta sakawa gate Win sannan ta shiga shiga mota ta bar unguwar.

Wajan aikin ta je tayi duka abinda ya kamata ta yi kafin ta fara aiki a wajan. Sai la'asar suka tashi tana tashi kuma ta Wauki hanyar Arewa24 a address Win da taji an ce suna wajan. Bayan ta je ta faWi abinda ya kawo ta sun yi mata bayanin yadda abin yaketa karSi number su sannan ta nufo gida a matu?ar gajiye ga azumi.

Tana zuwa ?ofar gidan ta hango Omar shida Bashir da kuma Tk suna tsaye da alama magana suke yi. Motar ta faka a wajan ta fito daga motar tana ji kamar zata fika ?asa saboda gajiya da nauyin da kanta ya yi mata. Bashir ya ce, "Antyn mu barka da zuwa." A gajiye ta ce, "yauwa Bashir, na gode." Tk ma ya yi mata sannu da zuwa ta amsa ta buWe ?ofar ta shiga gidan ta buWe gate Win ta cikin gidan ta shiga da motar. Bashir ya ce, "Antyn mu ki huta, bara na shigo miki da motar." Nayla ta bashi key Winta ce, "ai kam na gode sosai." Daga haka ta rufe ?ofar dan ta gaji sosai.

Shigar mata da motar ya yi ya tarar da ita a tsaye daga can gefe ya bata key Win tayi godiya ta ?araso ta buWe gaban motar ta Wauki jakarta da wayarta da laptop ta kalle shi yana niyar fita ta ce, "Bashir yaushe ku ke available gidan tv zasu zo Waukar video na wajan na ku, na gama magana dasu gabaWaya."

Bashir ya ce, "Ai ko yaushe ma muna nan, amma ki ce musu gobe su zo."
"Ka tabbatar gobe kuna nan?."
"Na tabbata Antyn mu."
"Shikenan zasu zo gobe in sha Allah" ta faWa tana shiga ciki shi kuma ya fita.

Nayla wanka tayi ta canja kaya ta zauna tana sauke numfashi saboda ta gaji sosai. Kanta har sarawa yake yi saboda ciwon da yake yi mata. da?yar ta iya samu ta mi?e ta dafa tea ta ji tana son cin bread amma kuma babu, gashi bata da Wan aike balle tayi aike a siyo. Tsaki tayi a bayyane ta ce, "ko meyesa ban taho dashi ba yanzu oho min."

Ha?ura tayi ta soya doya da ?wai ta dawo falo ta zauna lokacin shan ruwa ya kusa. Da?yar ta iya addu'ar gab da shan ruwa saboda ciwon kai, ana shan ruwan ta sha ruwa ta yi sallah ta zauna tana shan tea a hankali duk da kanta da yake ciwo.? Motsi ta ji bata motsa ba dan ta san shine kaWai yake shigowa ba tare da an buga gate ba, ta tabbatar da key Win gidan ya cire yake amfani dashi wajan fita da dawowa.

Daman ta san ba shigowa inda take yake yi ba hakan ya saka bata motsa ba tana zaune tana shan tea Win kamar an yi mata dole saboda ciwon da kan yake mata. Kamar tsayuwa taji a bayan ta hakan ya saka ta juya ta ganshi a tsaye amma kuma waya yake dubawa ba ita yake kallo ba. Fuskarsa take kallo ta ga yayi mata kyau musamman idanunsa da suke kallon waya hasken wayar ya haske idanunsa sai ya bada haske na musamman.

?auke kai tayi zuciyarta na bata umarnin yi masa barka da shan ruwan, wani Sangare na zuciyarta na hana ta saboda abinda ya ce mata ta san kuma bazai amsa ba. Kallon ta ya yi kafin ya yi magana ta ce, "An sha ruwa lafiya?." Kamar ba zai amsa ba sai ya ce, "lafiya. Ehemm akwai wanda ki ke so?." Da mamaki ta kalle shi ta kasa bashi amsa saboda mamakin tambayarsa. Kallonta yake yi yana ganin mamaki a kwance a saman fuskarta ya wara idanunsa a kan fuskarta ya ce, "kin ji abinda nace ko?." Saurin Wauke kai tayi Allah ya sani in ya buWe ido ba ?aramin tsoro yake bata ba.

Nayla ta girgiza kai ta ce, "babu komai."
"In akwai zaki iya sanar da ni."
"Yanzu dai babu." Ya Waga kafaWa alamun ban damu ba yana niyar fita. Ta kalli abincin da yake gabanta ta ce, "Bismillah ga abinci." Kallon abinda yake gabanta ya yi ya taSe baki ya girgiza kai ya fita daga gidan. Nayla ta dafe ?irji ta ce, "wannan mutum kamar wahainiya ko yaushe canjawa yake yi, wai akwai abinda nake so ka ji fa."

Sai kuma ta yi murmushi a bayyane ta ce, "Ko babu komai ya nuna min ya san ni matarsa ce, hakan ya yi min." Da wannan murmushin ta gama ci ta sha magani aka kiran sallah ta tashi ta tayar da sallah.

Tun daga ranar magana bata sake haWa su ba dan ba bama ganinsa take yi ba, in ta fita tun safe sai yamma shi kuma baya dawowa sai dare wata?ila sai tayi bacci. Kamar yadda suka tsara da Bashir an zo an yiwa company su video ta biya kuWin tayi komai a dan a fara haskawa a arewa24.

Takalman da aka kai Kaduna gabaWaya sun ?are har an sake kai wasu saboda yadda ake rubibin su sosai. Ita kanta wanda ta saka ?afar ta a wajan aiki mutane da yawa sun siya mata da maza, har na yara an siya saboda sallah. Video ?afarta kuwa da take yiwa ko wanne sample Bashir ne yake kawo mata sample tana yi tana tana posting dan tayo log in a dukkan account Win su.

Videon yana Waukar hankalin mutane sosai, ko baza ka siyi takalmin ba in ka ganshi a ?afarta da yadda take Waukar video sai ya burge ka saboda kyaun da yake yi mata. Sun ja hankain masu siya sosai da wannan advert Win da take yi, komai yana tafiya daidai yadda Nayla take so. Cikin ?aramin lokaci suka sake wuce matsayin da suke kai saboda buWin da Allah ya kawo musu ta dalilin Nayla.

Bashir ne kawai ya san me yake faruwa sai su Tk dan tayi musu magana akan don Allah kar su faWa masa. Omar kuma da yake ba kallo yake yi bai ma san ana yin tallah a tv ba, kwana biyu dai ya san yana samun customers sosai daga inda bai yi zato ba amma bai kawo komai a zuciyarsa ba. Manyan mutane daga gari gari suna siyan takalman ana kai musu inda suke. Cikin lokaci kaWan takalmin ya yi suna a social media da kuma tallata shi da ake yi kullum a arewa24 daga ?arfe shida na yamma zuwa shida na safe.

Watan azumi ya raba har an kusa shiga goman ?arshe, Nayla da Omar basu cika haWuwa ba sai dai taji motsin sa amma magana ko ganin sa bata yi. Da yake ta saka addu'a a gaba tana kuma zuwa aiki hakan bai dame ta ba, in ta dawo suna waya da su Salma yana rage mata abinda take ji sosai.

Ranar da aka shiga goman ?arshe aka fara sallar tahajjud kamar yadda ta saba ko wanne watan azumi ?arfe uku ma dare ta ke tashi ta fara sallah har sai an yi asuba. Bayan ta yi alwala ta shinfiWa sallaya sai ta fiton dan ta Wauki ruwa. Kallon ?ofar Wakinsa tayi tana nan a kulle kamar ko yaushe, bata da tabbacin yana ciki ko baya ciki tunda ba jin motsinsa ake yi ba. Zuciyarta ke bata umarnin ta gwada ?wan?wasa masa ?ofa saboda tunasar dashi lokacin sallar tahajjud.

A bayyane ta ce, "Tsoron masifarsa nake ji."? Da?yar ta daure a hankali ta taka zuwa bakin ?ofar ta kasa kunne wai ko zata ji motsi amma shiru babu motsin kowa. Hannu ta kai da niyar ?wan?wasawa kawai aka buWe ?ofar. Baya ta yi da sauri yanayin da ta ganshi ya saka gabanta ya yi mugun faWuwa. Farar singlet ce a jikin sasai brown Win wando three quater wanda bai zo ?arasa guiwa ba, GabaWaya farin jikinsa a bayyane yake, fatarsa har Waukar ido take yi gashi ya lulluSe ko ina na jikinsa.

Ganin ta ruWe tana rawar jiki ta sunkuyar da kai ya saka yake kallon ta. Ita bata yi gaba ba kuma bata yi baya ba, ta tsaya cak kanta a ?asa kamar munafuka. Bakin ta ya fara rawa tana son yin magana tana jin tsoro, shima bai motsa ba kallonta yake yi yana mamakin dalilin zuwan ta wajan har take niyar ?wan?wasa ?ofar.

Nayla ta daure ta ce, "lokacin Tahajjud ne ya yi shine nazo na sanar da kai." Gira ya Wage guda Waya yana Wan girgiza kai ya ce, "oh haka aka ce miki bana sallah sai kin zo kin tashe ni?." Ta girgiza kai ta ce, "tunasarwace."
"Bani da bu?ata, ko kabarin mu Waya da ke?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "to ware."

"Ba a yi masa abin arzu?i, kullum zuciya a wuya kamar ba musulmi ba" ta faWa ?asa-?asa tana juyawa. "Me ki ka ce?." Da sauri ta juyo ta ce, "A'a ban ce komai ba." Bai ce komai ba ya wuce ya Wauki ruwa ya koma ya rufe Wakin. Murmushi ya yi a bayyane ya ce, "Wai kamar ba musulmi ba, yarinyar nan naci gare ta." Kallon sallayar da ya shinfiWa yake yi kana ya ce, "tunasarwa ce" ya faWa cikin kwaikwayon muryarta. Sake murmushi ya yi ya kalli jallabiyar da ta bashi tsaraba ya Wauka ya saka ya tayar da sallah yana murmushi shi kaWai.

Nayla kuwa sai mita take a zuciyarta ta kuma yi alqawarin baza ta sake tashin sa ba komai zai faru. A haka tayi sallah har aka yi asuba, bacci kaWan tayi ta tashi ta yi wanka ta shirya ta tafi wajan aiki.

Shi kuwa Omaar bai fita da wuri ba yana jin fitar ta da mota da yadda take wahalar buWe gate da rufewa, yana tsaye yana kallonta ta window da take Wakinsa yana kallon yadda take kiciniyar rufe gate Win kamar zata yi kuka. Tsaki ya yi ya ce, "shagwaSaSSiyar banza, kalli yadda take taSe fuska kamar wani ne ya sakata zuwa aikin." Tsaki ya sake yi ya bar wajan shima wanka ya yi ya shirya ya fita saboda yanzu aikin yawa yake masa. Yana fitowa falon gidan ya tarar dashi yana ta ?hamshin turaren wuta, ya girgiza kai yana kallon falon dan ya burge shi sosai a shirye tsaf dashi.

Wayarsa tayi ?ara ya Wauko daga aljihunsa yana kallon wayar, ganin ba?uwar number ce sai ya Wauka saboda kwana biyu ana yawan kiransa da sabuwar number. Bayan sun gaisa da wanda ya kira Win ya ce, "Ina magana da C.e.o Exclusive Footwear by tiger?." Omar ya girgiza kai ya ce "shine."

"Kana magana da Usman P.A na Alhaji Mubarak? C. E.O Na kowa Store. Daman akan takalman da mu ka gani muna so ne, muna so a fara kawo mana babban store Winmu da yake Abuja." Omar ya san Na kowa Store, dan a Kano ma akwai store Win, haka yawancin garuruwa akwai Na kowa store. Omar ya amsa ya ce, "babu damuwa, ya za a yi?."
"Ina so mu yi contract ne, amma don Allah kafin mu akwai store ko shop Win da suke karSa a Abuja?."

Omar ya ce, "gaskiya babu."
"Yauwa, Ina so mu zama


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login