Showing 294001 words to 297000 words out of 332344 words

Chapter 99 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14836

ya cire kayan ba.

Waje Waya yake kallo a banWakin, duk inda ya kalla babu abinda yake gani sai fuskar Didi tana murmushi. Ko ya ji sautin muryar tana kiran sunansa bayan nan babu abinda yake iya ganewa. Kamar zautacce haka ya koma, ya fito ba tare da ya cire kayan ba ya zauna yana rawar sanyi saboda sanyin ya yi masa yawa amma baya so ya cire.

Bai san lokacin da ya Wauka a haka ba ya dai ji ana buga ?ofar Wakin bai iya motsawa ba a lokacin aka buWe aka shigo. Baba Adamu ne da Mama Zainab suka shigo Wakin da sallama, ya kalle su bai ce komai ba kuma bai motsa ba. Baba Adamu ya ce, "Subahanallah, Omar me ya same ka haka?." Bai ce komai ba yana dai zaune sai ya dafe kai da hannayensa saboda ciwon da suke yi masa kamar zasu tsage.

Mama Zainab kasa ri?e kuka tayi ta fita tana kuka sosai, ba jimawa Baba ya fito yana yi mata faWa akan zata sake tayar masa da hankali in tana kuka a gabansa. A lokacin ya fito ya saka jallabiyya fara mai gajeren hannu suka sauka tare saboda nema sa da ake yi in an zo.

? ? Haka aka kwana uku Omar baya cikin hankalinsa, abun kullum sake gaba yake yi dan baya magana, in an yiwa Didi addu'a dai yana iya motsa bakinsa ya ce amin amma tun a asibiti ba a sake jin muryarsa ba. Zaman makoki ake yi mai capacity, kowa a danginsu Omar bada gudunmawa yake yi na abinci da abin sha. Mutane zuwa kawai suke yi wasu ba a san su ba kawai suna shigowa ne.

Nayla har lokacin tana asibiti ta farfaWo amma ta kasa nutsuwa, jininta ya hau ga kukan da yake yi kullum. Jidda da Salma ne a wajan ta in Mama bata nan, Musliha na wajan su suna ta rarrashi amma bata iya dainawa har sai an yi mata allurar bacci. A ranar kwana na ukun ne ta Wan samu nutsuwa, kukan ya ragu sai ciwon kai da yake damunta. In ta rufe ido ta tuna Didi ta mutu sai ta ji zuciyarta ta buga ta sake gigicewa.

? ? A ranar kwana na huWu suka dawo gida, tana shiga falon gabanta ya faWi ta tuna inda Didi ta zauna ranar da zata mutu sai kuka ya sake cin ?arfinta. Abiy da kansa ya yi mata nasiha yana bata ha?uri amma ta kasa daina kukan jikinta ya zama wani iri ta koma kamar ba ita ba. Bayan ta zauna ta Wan nutsu Musliha tana hannunta Marmerh ta shigo da gudu ta faWa jikinta ta ce, "Mummy ina Ummi?." Nayla ta zubawa Marmerh ido hawaye suka sakko daga idanunta.

Umma Saroot ta ce, "Nayla ki yi ha?uri, wannan damuwar da kika saka a ranki ciwo zasu saka miki, wanda ya bar duniya ya mutu bazai dawo ba, ita ta dace tunda ta samu yabo da kyakykyawar shaida, na tabbatar mala'iku sun Wauki abinda mutane suke cewa da shi zasu yi amfani. Addu'a ya kamata ki dinga yi mata kin ji?." Ta ri?e Marmerh a jikinta ta kalli Umma ta ce, "Umma bacci ta ce min fa zata yi, hannunta yana cikin wannan hannun nawa" ta faWa tana kallon hannunta.

Umma Saroot ta ce, "na sani Nayla, amma ikon Allah ai ya fi gaban wasa. In lokacin mutum ya yi baya ?ara ko second Waya a duniya yake mutuwa, lokacinta ya yi a lokacin da ta ce miki bacci zata yi."

"Meyasa zata mutu yanzu? Meyasa?."
"Haba Nayla me ki ke faWa haka? Kar hankali ya gushe ki yi saSo fa." Hawaye suka sake sakko mata, Marmerh tana jikinta har lokacin ta kasa sakinta. Hajja ta ce, "Hauwa ki tashi ki je ki duba Omar, an ce ya hau sama tun Wazu bai sakko ba." Umma Saroot ta ri?e Marmerh, Nayla ta mi?e a sanyaye ta hau saman memories Win Didi na dawo mata tana kuka.

Halin da ta tarar da Omar a ciki ya saka ta sake gigicewa, domin kuwa yana kwance shima kamar yadda Didi take. Ta ?arasa inda yake a gigice tana jijjiga shi da iya ?arfin da ya rage mata amma baya motsi kamar yadda Didi bata motsi. Ido ta wara tana girgiza kai kafin ta kwasa a guje ta tana haWa steps zata kifa ta sakko tana hakki ta ce, "Shima baya motsi, shima baya numfashi irin Didi, shima yana kwance, baya motsi." A firgice take maganar hakan ya saka hankalin mutanen wajan ya tashi sosai.

? ? ? Nayla ta sulale ta zauna a wajan tana sake maimaita abinda ta faWa, tana ganin su Umma sun hau saman da sauri ita dai ta kasa motsi. Tana gani su Baba Adamu da AbudlHamid suka hau saman, ba jimawa sai su Kawu da cousins Win Omar an hau sama gabaWaya. ?auko Omar aka yi cak aka fita dashi ta ?ofar da zata fitar da kai compound Win gidan ba tare da an shiga ta falo ba aka wuce asibiti.
P115

KarSar gaggawa aka yi masa, aka shiga ceto ransa domin yana cikin mayuwancin yanayi. Sun jima a kan Omar kafin a samu a daidaita komai likitan ya fito repection inda suke zaune ya ga dukkansu kallon sa suke yi alamun ?arin bayani. Dr ya ce, "Akwai abinda yake damunsa ne? Ina nufin abinda ya jefa shi a cikin wannan yana??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????yin. AbdulHamid ya ce, "?warai akwai, Yayarsa Allah ya yiwa rasuwa."

"Allah sarki, Allah ya gafarta mata." Aka amsa da amin likitan ya ce, "gaskiya jininsa ya hau sosai, sannan akwai yunwa a tare dashi wacce ta taimaka wajan sakin jikinsa da galabaitar dashi. A yadda na fahimta akwai rashin bacci, shima ya taimaka wajan hawan da jininsa ya yi."

Baba Adamu ya ce, "Yanzu ya jikin nasa?."

"Numfashinsa ya dawo daidai a yanzu, an saka masa ruwan da zai daidaita blood pressure Winsa. Sannan an yi masa allurar bacci wacce zata saka shi bacci na dogon lokaci, mun yi isolating Winsa a special room wanda ba a hayaniya wajan saboda ana bu?atar ya yi bacci ?wa?walwarsa ta dawo daidai. Sannan an saka masa nasogastric tube, wacce za a dinga bashi abu mai ruwa ta cikinta yana zuwa har cikinsa, kamar tea ko kunu da sauransu. Yunwar da take damunsa ta wuce drip ya yi masa magani gaskiya. So za a samu mutum Waya da zai dinga shiga yana bashi abincin amma ban da hayaniya, in bai samu baccin da ake so ba zai iya samu taSin ?wa?walwa."

A tare kowa ya yi ajiyar zuciya likitan ya ce, "kar ku damu, da ya tashi daga baccin in sha Allah za a samu canji sosai." A tare suka haWa baki suka ce, "Allah ya sa."

?? Tsakanin dangin Baba da dangin Maman su Omar har rige-rigen kula da Omar ake yi, kowa ya ce shi zai zauna saboda halin da Nayla take ciki itama bazata iya kula dashi ba. Da?yar aka bar autan su Kawu a asibitin duk suka koma gida saboda masu zuwa gaisuwa.

Nayla ma tana gida su Mama sun sakata a gaba tana cin dafaffiyar hanta wacce aka dafata da alaihayu, da?yar take iya kaiwa bakinta ta tauna, da tunanin Didi ya faWo mata sai aga hawaye yana zuba daga idonta. Marmerh da take gefe tana bacci ta kalla ta shafa kanta tana kuka ta goge ido tana cigaba da ci a hankali.

? ? Salma ta dafata ta ce, "Nayla don Allah ki daina kuka, addu'a take bu?ata yanzu." Nayla ta kalle ta ta ce, "Salma hannuna yana cikin nata, ashe ta mutu ban sani ba. Ta juyo ta ce min nima fa ina son Omar ba ke kaWai ke sonsa ba, sai ta yi murmushi ta yi dogon salati ta rufe ido. Ni gani nake kamar ba mutuwa tayi ba suka je suka binne ta."

Jidda ta ce, "Haba Nayla, ki daina furta wannan maganar mana, Ana wasa da mutuwa ne? Lokacin ta ya yi wannan maganar itace ta ?arshe da zata yi miki. Don Allah ki kwantar da hankalinki, sai kin nutsu zaki iya kula da mijinki shima yana asibiti."

Ta kalli Jidda da take maganar zata yi magana Mummynsu Salma ta ce, "Don Allah Nayla ki nutsu, rashin nutsuwar da baki da ita ne ya saka ki ke a nan da kina tare da mijinki. Yana can a kwance, in baki nutsu ba ta ya shi zai nutsu?."

Hawaye ya zubowa Nayla ta ce, "To Mummy, in na tuna da Didi ne sai zuciyata ta karye."
"Ha?uri zaki yi, an san zaki ji zafi a zuciyarki amma daurewa ake yi, addu'a take da bu?ata ba wannan koke-koken ba." Nayla ta goge ido ta kalli Marmerh da ta tashi daga bacci ta ce, "Mummy Ummi." Nayla ta ri?eta ta kasa magana sai kuka.

Jidda ce ta Wauke Marmerh ta ce, "Marmerh muje na baki cocholate?." Marmerh ta ce, "Ummi za ni." Jidda ta ce, "zan kai ki, amma ki fara sha ko?." Ta Waga kai sai kuma ta ce, "da daddy." Murmushi Jidda tayi, hawaye na zubo mata itama ta fita da Marmerh kamar yadda Musliha take hannun Salma.

Da?yar aka samu Nayla ta sakko ?asa saboda masu zuwa gaisuwa, in Omar baya nan dole ita za a nema. Nayla dai kallon mutane take yi har lokacin itama bata dawo daidai ba shiyasa ba a tura ta asibitin ba. A haka aka akayi kwana bakwai da rasuwar Didi, gida ya watse har lokacin Omar yana asibiti bai tashi ba.

Ranar kwana na takwas da yamma aka kai Nayla asibitin, Musliha da Marmerh suna wajan Umma Saroot dan ita a wajan Nayla take kwana.

?akin da Omar yake ta shiga ta ganshi a kwance yana sauke numfashi a hankali, shafa kansa tayi da gashi ya taru gashin a kwance, kallo Waya zaka yi masa ka san ya rame sai haske da ya sake yi musamman fuskarsa da ?afarsa. Hawaye ta goge tana kallonsa ta zauna a gefensa tana kallo ?irjinta ma bugawa matu?a. A asibitin ranar ta kwana ita da Umma, wannan dare ya tuna mata Didi, dan da ace tana da rai tare zasu kwana da ita suna kula dashi. Ta sha kuka son ranta ta share hawaye tana yiwa Didi addu'a a zuciyarta.

? ?? Washe gari da safe Nayla tana gefe a zaune a gefensa,Umma Saroot na gefe ita Marmerh da Musliha suna bacci Omar ya buWe ido. A hankali ya juyo ya kalli Umma Saroot da take zaune suka haWa ido sai ta ce, "Omar ka farka? Sannu" ta faWa tana mi?ewa zuwa inda yake.

Nayla ta kalle shi suka haWa ido, yadda idanunsa suka koma sai da gabanta ya faWi ta ri?e hannunsa ta ce, "Sannu." Ido ya lumshe a hankali, ya jima a haka kafin ya sake buWe idon ya kalli Nayla muryarsa dashe matu?a ya ce, "Abinda ya faru mafarki ne ko gaskiya? Nayi mafarki wai Didi ta rasu, da gaske ne?."

Sai kawai Nayla ta fashe da kuka, ta Wora kanta a hannunsa hawayenta na sauka a hannunsa. Omar ya kafa mata ido yana kallo kafin ya kalli Umma Saroot da take tsaye tana goge hawaye ya ce, "Meyasa ku ke kuka? Ba mafarki na yi ba kenan? Ni na ri?e Didi aka sakata a kabari da gaske?."

?? Da sauri Umma ta fita daga Wakin tana kuka, sai da ta daidai kanta sannan ta kira likita kamar yadda ya ce in ya farka a sanar dashi. Kallon Nayla ya yi da take kuka ya ce, "Hajiya ki daina kuka, zaki sake tayar masa da hankali. Kwanciyar hankalinsa ake da bu?ata yanzu." Nayla ta share hawaye likitan ya ce, "sannu." Bai iya motsawa ba likitan ya ce, "Akwai abinda yake damunka?."

Omar ya nuna kansa ya ce, "kaina na ciwo sosai, ?irjina ya yi nauyi sosai."
"Sannu, damuwa ce tayi maka yawa in ka sassautawa kanka zaka ji sau?i, Zaka iya tashi zaune?." Omar ya girgiza kai alamun a'a saboda baya jin ?arfi ko kaWan. Likitan ya ri?e babban Wan yatsansa na ?afa yana matsawa a hankali ya ce, "kana ji ina matsa ?afarka?." Omar ya Waga kai alamun yana ji, ya ri?e Wayar ?afar ma ban ma ya ce yana ji.

Hannunsa ya ri?e ya matsa nan ma ya ce yana ji likitan ya ce, "Zaka iya tashi, gwada." Omar ya motsa da?yar sai ya koma ya zauna ya ce, "kaina!."
"Sannu, in ka zauna zaka ji daWi." Da?yar ya mi?e ya zauna yana jan numfashi da ?yar. Bp Winsa ya auna ya ga jinin ya Wan sauka amma ba sosai ba, ya kalli Omar ya ce, "Kana da bu?atar ka yi wanka sannan ka ci abinci, zaka ji daWi sosai a jikinka." Omar ya lumshe ido bai ce komai ba likitan ya fita dan kawo magani.

?? Umma Saroot ya kalla ya ce, "Ina Didi take? Ban ganta ba." Ya faWa dan shi manta maganar da aka yi a farkon tashinsa. Shiru tayi bata amsa ba ya kalli Nayla da take ta ajiyar zuciya ya ce, "Didi bata zo ba?." Nayla ta zuba masa ido bata ce komai ba. Murmushi ya yi kaWan ya kawar da kai gefe.

A lokacin su Kawu suka zo harda su Mama Zainab, su Kawu ne suka saka shi dole ya yi wanka aka kawo kaya daga gidan aka bashi tea Wan ya sha. Omar duk ya zama wani mai sanyi, komai aka ce masa kai yake Wagawa baya iya mayar da martani.

Da ya sha tea ya ji daWin jikinsa sai nauyin da ?irjinsa yake yi masa kawai. Washe gari aka sallame shi bayan an yi masa hoton ?irjin da yake ta kuka da ya yi masa nauyi. Omar ya zama dan gata wajan dangi, kowa nuna masa ?auna yake yi Nayla ta zama ?ar kallo tana gefe kawai.

? ?? A hankali ta shiga Wakin ta same shi a tsaye yana kallon hotonsu tun lokacin da suke yara wanda ya Wauko daga gidansu. Jin shigowar Nayla ya saka shi ya kalle ta ya ajjiye hoton yana kallonta kamar yadda take kallonsa. Ya yi ajiyar zuciya ya kalli hotonsu shida ita da suka yi a madina ya ce, "Da gaske Didi ta rasu?."

Nayla ta Waga masa kai ta ce, "Didi ta tafi ta bar mu." Ya dafe kai yana salati ya ce, "Meyasa a lokacin da ta ri?e hannuna a asibiti na cire hannun na tashi? Meyasa ban zauna ri?e da ita har ta mutu ba?. Meyasa Didi zata mutu bayan ni ya kamata na fara mutuwa? Ta san ya rashinta zai yi min illah?. Jidda Didi ce uwata, Didi ce ubana, Didi ce yayata, Didi ce ?awata. Ta ya zan iya jure rashinta? Ta ya zan yi!" Ya furta a sanyaye yana kallon Nayla da ta fara hawaye.

Nayla ta taka zuwa inda yake ya sake kallonta ya ce, "Didi ce ta raine ni, itace komai nawa. Yau magana ake ta kwantanta goma a kabari, ni kuma gani ina rayuwa a duniya. Anya na yiwa Didi adalci Jidda!?."

Nayla ta kasa magana sai kuka da take yi, ya sake cewa, "Meyasa da ta ce tana son jin Wumin ?aninta ban rungumeta ba Jidda? Meyasa na bari ta bar duniya da kewar hakan a ranta? Na tabbata inda ni ne baza ta bar ni ba, zata saka ni a jikinta ta samar min da abinda nake so, amma ni na gaza!" Ya faWa yana kallon window cikin tsananin rauni.

Sai kuma ya juyo ya ce, "Da wannan hannun nawa na ri?e Didi aka sakata a kabari, ni...ni nayi mata wanka. Kenan ta tafi kenan? Ta tafi har abada bazan kuma ganinta ba?. Meyasa Didi zata mutu? Ta sha wahala dani, sai yanzu da lokacin jin daWi yazo zata tafi ta barni? Meyasa na bari ta rasu Jiddaaaa....meyasa?" Ya faWa da rauni sosai muryarsa rawa. Nayla ta kasa ri?e kukanta ta saki kuka mai ?arfi sosai, taka da guje ta faWa jikinsa ta rungume sa. Wata irin runguma ya yi mata mai ?arfin gaske, ya matse ta gam a jikinsa kamar zai shigar da ita jikinsa.

"Didi ta tafi ta barni, ta tafi ta bar ni Jidda. Shikenan ni da ita baza mu sake ganin juna ba, bazata sake bani shawarma ba, baza mu sake faWa ba, baza mu sake zama waje Waya ba Jidda, bazan sake kwana biyu ban kulata ba, baza ta sake bani hannu mu gaisa ba, bazan sake jin muryarta ba, bazan sake ganin dariyarta ba Jidda!. Shikenan komai ya ?are, shikenan....!" Ya fashe da kuka mai sauti yana sake matse Nayla a jikinsa hawaye na ambaliya daga idanunsa.

"Didi....didi...ta...."ya kasa magana saboda kuka, itama Nayla kuka take yi ya matseta ya hanata motsi a jikinsa, jikinsa na rawa kamar yadda muryarsa take rawa. Dukkansu kuka suke yi cikin rauni da bugawar zuciya, ji suke kamar a ranar Didi ta mutu, ji suke yi kamar babu wanda ya kai su ?unci da ba?in ciki a wannan lokaci. Sun kwashe mintina talatin a haka, tsayuwar sam bata ishesu ba saboda basa cikin hankalinsu.

Omar tunda ya fara kuka bai daina ba, kuka ya ke yi da zuciyarsa da gangar jikinsa, ya matse Nayla a jikinsa, jikinsa yana rawa kamar an jona masa wutar lantarki. Nayla ce ta motsa ta Wago daga jikinsa ta ri?e hannunsa zuwa kan kujera, ta ri?e kafaWunsa ya zauna sannan itama ta zauna a kusa dashi, ya sake kwantar da kansa a ?irjinta tana shafa a kansa a hankali.

Hawayensa a fatar jikinta yake sauka, ta yi shiru bata ce komai ba kamar yadda bai ce ba, sai dai ya rage sautin kukan sai hawaye da yake yi kawai wanda ya?i tsayawa. Ya Wago ya kalli Nayla yana lumshe ido saboda ciwon kai, ta goge masa hawayen idanunsa ya girgiza mata kai ya ce, "kar ki tafi ki barni kamar yadda Didi ta tafi kin ji Jidda. In kika barni haukacewa zan yi koda ban mutu ba. Ki bari na rigaki mutuwa kin ji? Ki bari na fara mutuwa kafin ke. Ke da Didi kawai nake da su kawai, ita ta tafi saura ke, kar kema ki tafi ki barni Jidda....in kika tafi haukacewa zan yi...." Ya faWa a rikice yana sake rungumeta a jikinsa sabon kuka na cigaba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login