Showing 84001 words to 87000 words out of 332344 words

Chapter 29 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14412

Salahudden, tun a lokacin babban mutum ne mai cikar kamala da son wasa da dariya. Shi kaWai Omar yake jin maganarsa, hakan ya saka Aisha ta je ta same shi ta ce don Allah ya dinga koyawa Omar karatu ta san zai zauna. Ai kuwa haka aka yi, da ya kira Omar bai ?i zuwa ba, ya ce masa kullum da yamma ya dinga zuwa wajansa zai dinga yi masa karatu da kansa. Babu yadda ya iya haka ya amince bayan Aisha ta dinga yi masa magiya kamar ita zata yi karatun.

Omar baya son makaranta amma yana da ?o?ari da sauri iya karatu, ya tsani makarantar boko har gwara islamiyyar tunda yanzu shi kaWai ake koyawa. Boko kuwa da?yar ya kai SS3, tunda aka fara batun jarabawa ya falle bai sake koma ba. Shiyasa ya kan ce ai ya gama sakandiri jarabawa ce kawai bai yi ba. Yana da skills a fanni daban-daban, yanzu zai fara zana fuskar mutum kamar yana wasan ?asa kuma ya fitar da komai. Ko ya Wauki wani abun ya yanka sai ya bada wani abu mai kyau wanda kai kana gani kasan aikin Wan baiwa ne. Haka gyara socket na wuta ko wani abu da ya shafi aikin wuta duk yana yi, kuma ya haWa ya gyara abu ya tashi ya cigaba da amfani.

Tunda ya shekara sha biyar sai abun na sa yayi gaba dan yana daga cikin waWanda basa jin magana unguwar gabaWaya, yana wannan shekaru har yara ne dashi da suke take masa baya saboda ya ri?a. In ya Sata mata rai haka zata kai ?ararsa wajan Malam Salahudden, ya kira shi ya yi masa nasiha ya kuma zaunar dashi ya yi karatu.

Inda karatun Omar ma bai kai ace ya sani ba Malam Salahudden ya sanar dashi, kuma abinda yake burge Malam yadda yake Wauka ya kuma haddace. Zaman sa da Malam ya koyi tsayar da sallah da yin ta a cikin mutane, har hakan ya zamar masa jiki indai za a yi sallah zai shiga masallaci saboda mahimmacin hakan da Malam yake faWa masa.
KRB3P027
Arewabooks@nanahaleema11.

A hankali ya fara taSa shaye-shaye saboda zama da masu yi, tun ba ya sha'awar yi har ya ji a zuciyarsa zai iya gwadawa. Haka Didi zata saka shi a gaban tana kuka sosai, babu mai tsawatar masa sai ita Win, dan jama'ar gidan ba shiga harkarsa suke yi ba dan bashi da kunya. Wannan raunin na kukan Didi da nasihar Malam yake sakawa ko yayi niyar shan wani abu in ya tuna da zata yi kuka sai ya fasa. A hankali sai abin bai bi jikinsa ba, da taimakon Allah da taimakon addu'ar Malam ya daina amma yana taSa shan sigari musamman in ransa ya Saci.

Kaf gidan nan tsoronsa suke ji dan babu wanda yake Wagawa ?afa daga mazan har matan, dan zuwa lokacin ba a rasa shi da ?aramar wu?a a jikinsa, kana yi masa ba daidai ba zai yi maka barazana da ita dan bai taSa fitarwa da wani jini ba har lokacin. Nan da nan sai aka fara cewa daman gadon baban yayi, ya za a yi barewa tayi gudu Wanta yayi rarrafe. Wasu kuma su ce jafa'in da ubansa yake jawowa Wan wani ne ya faWa kan na sa Wan. Ita dai Didi kullum addu'a take yi masa tana kuma yi masa faWa amma baya ji.

Didi ta girma dan ta kammala makarantar secondry, tana son cigaba amma babu gata babu wanda zai kula da karatun ta balle ta yi dole ta ha?ura. Ga samari su dinga biyota ana cewa ana so, da zarar mutanen unguwa sun ga wanda ya ce yana sonta duk yadda za su yi sai sun yi sun kore shi.

Dangin mahaifiyarsa ma ganin abinda Omar ya zama sai addu'a suka sake ?yamatar su, dan a ganin su da babarsu bata auri babansu ba da hakan bai faru ba.

A haka aka aurar da sa'anin Didi amma ita tsoron ma yi mata magana ake yi saboda shi, dan in ko a gidan yaga kana kula ta in ka yi maganar da bata yi masa ba ka shiga uku. Makaranta kuwa tuni ya daina zuwa, Malam Salahudden ne kawai in ya aiko a kira shi baya ?in zuwa, hakan ya saka ya samu ilimi wani lokacin shi yake yiwa Didi gyara.

Yana da shekara sha bakwai aka fara kama shi cikin Sata gari, Didi ce zata je ta yi belinsa, wani lokacin a bata shi wani lokacin a wula?anta ta. Ganin har ya fara zama a a cell sai gidan matan gidan suka haWa yadda zasu kore su daga gidan dan ya zamar musu fitina. Baka isa ka yi abinda baya so ba sai ya yi abinda zai tsoratar da dake. Rashin kunya kuwa kana faWa yana faWa, ka Waga hannu zaka dake shi shima ya Waga nasa. Babu wanda yake cewa tsaya ya tsaya sai Didi sai Malam Salahudden.

Ai kuwa suka haWa masa sharri suka ce ya nemi ?ar Kawu Sulaiman mai suna Ramla da sunan zai yi mata fyaWe. Matar Kawu babba ce ta dinga hira wutar abin, yadda take kambaba maganar sai ka Wauka ya faru a kan idanunta. Wannan dalilin ya saka Omar ya tsaneta tsana mai muni.

Kowa da ya ji maganar bai musa ba dan an san zai iya aikatawa, kuma suna sane suka zaSi Ramla ?ar Kawu Sulaimn dan yana da zafi sosai. Ai kam mazan gidan suka taru suka yiwa Omar dukan da ya kasa motsawa, suka fasa masa jiki, shatin bulalar ta ko ina a jikinsa, suka kuma ce sai sun bar gidan su tafi duk inda zasu ne.

Kawu Sulaiman da Kawu Babba suka Wauko abinda suka gada daga mahaifinsu har ma da na mahaifiyarsu suka watsa musu a fuska, Kawu Sulaiman ya ce su bar gidan basa bu?atarsu har abada sun bar musu gadon. Duk da Omar bashi da lafiya haka ya saka Didi ta Wauko abinda zata
Wauka suka bar gidan kai tsaye dangin mahaifiyarsu ta ce suke. Omar ya nuna baya so suje, amma ta nuna basu da wani wajan sai nan dole suka tafi gidan Yaya Adamu.

Zuwan su gidan bai canja komai ba, ya dinga faWa yana cewa shima Omar bazai lalata masa yara ba gwara su tattara su bar gidan bazai zauna dashi ba halin ubansa ya yi. Didi tana kuka tana bashi ha?uri amma ya ?i ji. Suka tafi gidan Mama Zainab babar Yayar su Mamansu, itama ta ce bata da inda zata ajjiye su. Ta dinga yi musu wuala?anci kala-kala, tana ambato sunan mahaifinsu tana zagi, tana zagin Omar da kalmaai marasa daWin ji.

A gidan Saroot suka zauna kafin ta samu Yayan na su da maganar a san abinda za a yi. Daga ?arshe dai Yaya Adamu ya karSi duk abinda suka mallaka ya tattara ya ?ara da wani abun? ya je ya siya musu g1da ya ce su je su zauna ita dashi.

Haka suka tafi gidan, Omar zuciyarsa ta gama cika da tsanar dangin nan guda biyu, a haka suka fara rayuwa a cikin gidan ita dashi. A haka suka saba da Hajja har ya zama duk ta san labarin su dan farkon tarewar su ma Hajja ce take basu abinci kafin su san abinda zasu yi.

Daga wannan lokaci Omar sunan ya sake yin tambari a garin Kano, dan har gida ya saka aka je gidan Kawu aka yi musu dukan tsiya kamar yadda suka zane shi, daga wannan lokacin ne suke yi masa la?abi da Damisa ?i sabo. Bayan wannan abinda da ya saka aka yi ya sake sakawa aka tarewa Kawu Sulaiman a hanya aka kwace masa mashin ya kuma saka yaransa suka shi tafiya a ?afa, Kawu yana tafiya yana hawaye saboda nisan tafiyar.

A wannan lokacin ne Nayla tazo hutu gidan Hajja, da daddare ta fita ba a sani ba aka yi ?o?arin yi mata fyaWe dan lokacin abinda ake fama dashi kenan.

Allah ya kai Omar wajan ganin abinda yake shirin faruwa ya dakatar da aikatawa, rana ta farko ya yankewa wanda yake ?o?arin yi mata fyaWen Wan yatsa Waya, kuma ya cire masa kunne. Duk sun yaga mata rigar jikinta sai kuka take tana kiran sunan Hajja. Rigar jikinsa ta sama ya cire ya saka mata sannan ya Wauko ta kamar jaririya ya kaiwa Hajja ita dan yaji tana kiran sunan Hajja, kuma yaji ana cewa jikar Hajja ta Sata.

Haka ya dinga masifa a gidan Hajja, yana cewa ta ya za a bar yarinya ta fita ita kaWai da daddare bayan an san ba?uwa ce ita, aka dinga yi masa godiya da abinda yayi sai kuma hukuma ta shigo maganar akace ya Wauki doka hannunsa sai an hukunta shi.

Sun so a kai shi prison zaman jan kunne amma Abiy ya shiga ya fita aka ?yale shi, ya sake yi masa godiya sosai akan abinda ya yiwa ?arsa. Daga wannan lokaci kuma Omar sai ya zama jan wuya kamar yadda suke masa take da sunan, dan sai ya zama babba kuma madugu a unguwar. Kullum Didi tana hanya wajan ?an sanda, ko nemansa tayi ta rasa da ta samu labarin an yi kame in taje yana ciki.

Da farko ya fara aikin yin takalma a wajan wani mutum da Didi ta takura masa, da yake ya iya yanka fuskar takalmi in ya yi aka haWa sai ka kalla saboda kyau. Allah ya saka masa albarka ya iya aikin sosai dan sai da ya zama baban yaron mutumin saboda yadda ya ?ware in dai ya ga dama zai yi. Amma daga baya sai ya watsar ya cigaba da harkar abinda ya saka gaba.

A cikin wannan lokaci ne suka sake canja gida suka karSi wanda yafi wancan kyau amma bai kai na su girma ba, suka sake zama ma?otan Hajja sosai dan da sun Wan yi nisa. Ragowar kuWin Didi ta fara sana'a ta kuma shiga makaranta tana NCE. Daga wannan lokaci Omar abin sa komai gaba yake yi, sai dai shaye-shaye ne baya yi, kuma bai taSa kashe rai ba amma duk wani abu da ya shafi daba Omar ya zama babba kuma Jan wuya a wannan fanni. KuWi yake samu sosai saboda ?an siyasa da suke amfani dasu, musamman ma shi da aka san bashi da tsoro, kowa a cikin kiransa yake yi domin a bashi aiki.

Omar ya taSa zaman prison saboda faWa da akayi tsakanin yaran sa da yaran wani jan wuya kamar sa, har ya kai ga yaran sun yi kisa da aka zo duk sai aka kama su gabaWaya. Su aka yanke musu hukunci life in prison, su kuma su Omar aka yanke musu hukuncin wata Waya a gidan yari. Haka Didi take yawo a hanya wajan kai masa ziyara, duk ta rame saboda rashinsa, ko yaushe cikin kuka take.

Sai da watan nan ta cika sannan ya fito, maimakon ya yi hankali sai kuma abin na sa ya sake yin gaba dan sai ya zama kaf arear Yakasai da ?ofar mata ?an daba iri sa na wajan basu isa su shiga area sa ba. An taSa kawowa Didi hari a kan hanyarta ta dawowa daga makaranta, Omar da ya ji labari kashe yaron ne kawai bai yi ba, amma azaba ya gana masa ita. Ya yayyake shi, ya yi masa kaca-kaca da fuska. Tun daga kansa babu wanda ya sake ?o?arin hararar Didi, sannan ko makaranta zata je akwai wanda zai saka ya rakata.

Zaman sa ya kawo security sosai a unguwar, dan ba a ?wacen waya ko wani abu mara kyau a areasa, dan in kayi ma sai ka kamo ka kuma sai ya kai ka gaban yan sanda. Dabanci yake yi mai tsafta wacce in baka taSa shi ba babu ruwansa da kai, in kayi laifi kuma ya kai ka ga hukuma, in hukuma bata Wauki mataki ba to tabbas shi zai Wauki mataki.

Zafin kai, zuciya, Waurarriyar fuskarsa ya saka kowa shakkar sa yake yi, dan baya Wagawa kowa ?afa. Hatta babban yaronsa na farko da aka samu da ?wace waya shi da kansa ya kai shi gaban hukuma aka yi masa hukunci. Wannan ya saka suke masa take da Damisa ?i sabo. Omar bashi da sabo ko kaWan, bashi da saurin sabo ko kusa, kafin ku saba a za a jima sosai. Yana da ri?o sosai, ya kasa manta abubuwan da iyayensa suka yi masa, duk daga baya dukkan su sun nemi yafiyar su gabaWayan su amma ya kasa karSar su a matsayin danginsa.

Ita kanta Didin ta kasa sakin jiki da dukkan su, sai dai duk abinda ya tashi tana zuwa amma shi ko mutum Waya ma baya ganewa a cikin su. Rayuwarsa yake yi shi kaWai daga shi sai Didi.

Omar mutum ne da baya son ba?o ko kaWan musamman daga cikin unguwar da suke, maganar da suke yaWawa akansa da Didi ya saka baya so kowa ya raSe ta sai shi kaWai. ?an aike almajiri bata dashi, duk abinda take so ya gwammace ya aika yaransa su siyo da dai wani ya shigo gidan.

Su ma mutane da yawa tsoron shigowa suke yi dan gamuwar bata zama alkhairi. In kaga Omar yana dariya to Didi ce a kusa dashi, in ka ga Omar na hira sosai Didi ce, in ka ga Omar na bada labari Didi ce, in ka ga Omar cikin rauni Didi ce, in ka ga Omar cikin damuwa damuwar Didi ce, in ka ga Omar ya yi Didi ce, in ka ga Omar ya bari Didi ce. In dai ba ita ba babu mai saka shi babu mai hana shi, sannan babu wanda ya isa ya yi masa magana balle su yi hira. Bashi da aboki ba shi da kowa daga Didi sai wayarsa dan masoyin danna waya ne. Duk wani platform Omar yana shiga, ya san ta kan social media sosai kuma tsabar shige-shige ne ya kai shi.

Shekarar Didi talatin da biyar amma har lokacin bata taSa yin aure ba, duk masu zuwa ba da aure suke zuwa ba ?an iskan zamani ne. Dan akwai wanda ya taSa zuwar mata da iskanci. Labarin ya kai kunnen Omar ya Wauki yaransa aka tarafa shi suka ce sai sun sake masa kaciya. Bawan Allah ya dinga magiya yana kuka, sai da suka taso shi har gaban Didi ya bata ha?uri, amma duk da haka basu ?yale shi ba sai da suka aske masa gashin kansa tass suka kuma yi masa Salli-Salli a mazaunai.

Tun daga kansa in da iskanci ka ke tafe ba ka sauke shi a gidan Didi sai dai wani gidan, in kazo da wata maganar ta kirki ma sai ka tsorata, in ya dinga tsare ka da ido in ba mai gaskiyar gaske ba ne sai ka kwafsa.

Didi tana sana'ar yin abinci ta siyar in an saka order kuma Allah ya saka mata albarka sosai take samun riba fiye da tunanin mai tunani, shiyasa gidan su kullum kamar gidan amarya duk abinda ta gani tana so tana siya, tun tana ajjiyewa matsayin na aure har ta kwaso su duka tana amfani dashi a ganin ta kamar bata da rabon aure a duniya.

Didi kullum cikin yiwa Omar addu'a take yi na neman shiriya, kuma babu laifi akan Wan samu canji musamman yadda ya daina faWa sai yana da dalili mai ?arfi. Ko gonarsa aka shiga sai dai ya kai maganar ga hukuma wani lokacin kuma ya yi hukunci da kansa. ?an unguwar suna son Omar kuma basa sonsa, suna sonsa saboda zaman sa unguwar ne take da tsaro babu Sarayi balle masu ?wace. Basa son zamasa saboda babu wanda yake shiga harkarsa kuma ko waye kai kayi masa sai ya rama.

A haka Didi ta yi aure da duk abinda ya biyo baya. Wannan shine dalilin da ya saka Omar ya tsani ahlin su, ya tsane su tsana mai muni. Baya girmama kowa a cikin su, baya Waga kai ya kalle su ma balle su samu damar magana daga gare shi. Yana da matu?ar ri?o, shiyasa ya kasa mantawa da abubuwan da suka faru duk da an kwana biyu da faruwar su.

Wannan kenan!.

Kuna ganin dangin Omar Sun cancanci tsana daga wajansa& ?
KRB3P028
ArewaBooks@nanahaleema11.

Nayla tunda ta fizgi motar a guje ta bar unguwar take gudu duk da kasancewar yamma ce akwai chunkoson abeben hawa. Sai da ta Wan yi nisa sannan ta ganganara kan titi ta kifa kanta akan sitiyarin motar ta saki kuka mai karfin gaske.

Kuka take yi mai sauti cikin shashshe?a, ciwo take ji a zuciyarta sosai, wani abu take ji ya cure a zuciyarta ya dun?ule waje Waya. Daga cikin zuciyarta kukan yake tasowa ba tare da ta shirya masa ba, hakan ya saka hawayen ya?i tsayawa sai sauka yake wani yaka bin wani.

Kalaman Omar in ta tuna sai ta ji duniyar na juya mata, tun farko ta san ba sonta yake yi ba amma bai taSa kallonta ya faWi wannan kalmar mai Waci da sanya bugawar zuciya ba, kalmar baya sonta da ya furta ta fi komai Waga mata hankali. Jingina tayi da kujerar tana hawaye tana sauke ajiyar zuciya ?irjinta ta yana Wagawa a hankali yana sauka a hankali. Ta jima a zaune a haka tana hawaye, kanta ya yi nauyi kamar yadda zuciyarta take da wannan nauyin. Kiran sallar da ya karaWe ko Ina ya saka ta mi?e zaune sosai, ta gyara zama tana kallon glass Win motar ta gaba.

Bata gani sosai saboda ciwon kai, ta saka gefen mayafin ta goge idanunta ta sake kallon gaba ta ta ga tana gani amma ba sosai ba. Ajiyar zuciya tayi ta ja motar a hankali tana tafiya.

Allah ne kawai ya?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? kaita gidan Mama Sa'adatu lafiya, zuwa lokacin zazzaSi ya gama rufeta sai sanyi da yake ratsa ?asusuwanta. Kanta yayi zafi ga nauyi, da?yar take iya buWe ido saboda ciwon da kanta yake yi mata. Yadda take danna horn Win a kasalance zai saka ka san tana cikin rauni da rashin lafiya. Mai gadin da ya buWe ya ga motarta ce sai ya buWe mata gate ta shiga ta ajjiye motar a tsakiyar gidan.

Da?yar ta daidaita kanta ta buWe motar ta fito saboda ciwon kan da ya ke barazanar tarwatsa mata ?wa?walwarta, ga zazzaSi ya gama mamaye mata jiki. Tana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login