Showing 90001 words to 93000 words out of 332344 words

Chapter 31 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14403

wanda zai miki dole, abinda ki ke so shi za a yi."

Nayla ta ce, "Mama ba ya son zama da ni, gwara a raba auren a huta." Mama ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Shikenan dalilin?." Nayla ta Waga kai alamun eh, Mama ta bita da kallo tana hango damuwa sosai a tare da Naylan, sannan tana hango soyayyar Omar har gobe a idanunta. Amma tunda har ta buWe baki da kanta ta ce a raba auren tabbas duk abinda ya yi mata ya taSa mata zuciya sosai. Mama ta ce, "Ina shi Omar Win ya ke?."

"Ban sani ba."
"Ya san kin taho nan?." Ta Waga kai alamun e Mama ta ce, "shikenan. Ki kwantar da hankalinki, gobe zan je na samu Daddyn sai na yi masa bayani. Yanzu ki ta shi ki yi wanka zaki ji daWin jikinki." Nayla ta Waga kai ta ri?e hannun Mama ta ce, "Mama a raba auren da wuri kin ji?." Mama ta ri?e hannunta itama ta ce, "kar ki damu, Tashi ki yi wanka zan saka Ummimi ta kawo miki kaya sai ki saka."

Nayla ta ce, "Mama na taho da kaya suna mota." Mama ta ce, "to bara na saka a Wauko miki" ta faWa tana fita daga Wakin.

Ba jimawa sai ga Ummimi ta shigo da wayar Nayla da laptop da sauran kayan ta ajjiye ta fita. Nayla tana wanka tana kuka, ta dole ta iya furta a raba ta da masoyinta ba dan tana so ba, ta kai zuciya nesa ta ga kuma abinda ya kamata tayi kenan shiyasa ta aikata. Gwara ta bashi space tunda har ya buWe baki ya ce mata ba ya sonta, ido da ido ya kalle ta ya faWi haka, ya kuma ce har abada bazai so aurenta ba, gwara ta ha?ura duk da son da take yi masa.

A haka ta fito ta buWe kayan ta saka doguwar riga ya zauna a gefen gadon. Wayarta kalla ta ga tana haske, ganin sunan Salma sai ta share bata Wauka ba ta jingina da fuskar gadon idanunta a lumshe.

? ? Ranar da ta fara ganin murmushinsa ta tuna a gidan Didi, da ranar da suke je Kaduna ya yi mata murmushi da ranakun da suka biyo baya. Zuciyarta harbawa take, in ta ce bata son Omar ?arya take yi amma ya zata yi? Hakan shine mafita a gare ta da rayuwarta.

Ranar tare suka kwana a Wakin da Mama kasancewar mai gidan baya nan. Duk motsin da Nayla zata yi sai Mama ta buWe ido ta ce lafiya, hakan shine yake yiwa Nayla daWi take jin Mama kamar Ummanta da ta bar duniya.

?? " " " Da safe wanka tayi ta shirya, sai dai kallo Waya zaka yi mata ka hango damuwa da ramar da tayi lokaci Waya. Ummimi ce ta shigo ta kalle ta ta ce, "Yaya Nayla ki fito falo in ji Mama." Nayla ta girgiza kai ta fito zuwa falon a sanyaye ta sakko daga saman. Dukkan su suna zaune wani yana danna waya wani kuma yana shan tea. Kafin Nayla ta ?arasa sakkowa? aka yi sallama aka shigo falon.

Wacce take bin Abbas ce da ake kira da Yaya Zahra da yaranta guda biyu suka. A guje suka taho wajan Mama suka faWa jikinta suna murnar ganin ta. A lokacin Nayla ta sakko daga saman ta ce, "Yaya Zahra sannu da zuwa." Anty Zahra ta kalleta tayi murmushi ta ce, "Naylan Mama."
"Na'am Yaya, sannu da zuwa."
"Yauwa Nayla, lafiya ki ke naga fuskarki ta Wan kumbura?." Mama ta ce, "bata jin daWi ne."

Nayla ta kalli Abbas da Khalid ta ce, "Yaya Abbas Ina kwana, ya Khalid ina kwana." A tare suka amsa Abbas ya ce, "ya jiki? Ina fatan baki kwana da zazzaSin ba." Nayla ta ce, "Eh ban kwana dashi ba, tunda Yaya Khalid ya yi min allura ya sauka." Khalid ya ce, "Amma fuskarki ta kumbura, kuka kika kwana kina yi ko?."

Nayla bata ce komai ba Khalid ya ce, "Nayla kar ki stressing kan ki da yawa fa, ko meye yake damunki ki kwantar da hankalinki ki sanar da Mama in ba haka ba zaki jawowa kan ki ciwo da ?arancin shekarunki, ki kwatar da hankalinki ki faWi duk abinda yake damu ki bazai gagari iyayen mu ba in shaAllah." Nayla ta Waga kai alamun to.

Yaya Zahra ta ce, "A nan ta kwana kenan, Mama lafiya dai ko?." Mama ta ce, "eh to lafiyar dai zan ce. Abbas in baza ka je aiki ba anjima zaka kaini gidan Daddy." Abbas ya amsa da to amma ya damu da ya san damuwar da ta saka Nayla a wannan yanayi.

Mama ta ce, "Nayla tashi ki je ki ci abinci." Bata musa ba ta tashi sai gata ta dawo da tea a hannunta zama tayi tana sha suna hira a falon sama-sama. Nayla ce ta mi?e tsaye a sanyaye ta ce, "Mama bara na Wauko wayata a sama." Mama ta amsa mata ta hau saman da kofin a hannunta.

Yaya Zahra ta ce, "Wai ne ya same ta ne? Ba dai sakinta ya yi ba?." Mama ta yi ajiyar zuciya ta ce, "bai saketa ba, amma ta ce sakin take so, ita kar a Wauki lokaci kawai ya saketa ta gama auren, shiyasa zan je na samu Daddy anjima." Yaya Zahra ta ce, "Tofa, ita da kanta ta ce ta gaji da auren?." Mama ta amsa mata Yaya ta ce, "ba a san dalilin ta na faWin hakan ba, tunda har ta furta da kanta gwara a raba auren."

Mama ta ce, "shiyasa zan sanar da Daddy, ta inda aka hau ta nan ake sauka." Yaya ta amsa suka cigaba da hira har Abbas da yake zaune.

Kamar Yadda Mama ta ce bayan sallar azahar Abbas ya kai ta gidan Daddy, ta same shi a falo ta yi masa bayanin yadda suka yi da Nayla. Abin ya bashi mamaki sosai, ya ce aje a kawo masa Naylan. Abbas aka saka ya koma ya Waukota.

Lokacin da ya koma a zaune ya same ta tana waya ita da Salma, ya kalle ta ya ce, "Nayla ta so mu je, Daddy yana son magana dake." Kashe kiran ta yi ta ce, "To bara na Wauko mayafi" ta faWa a sanyaye tana wucewa ta hau sama ba jimawa ta dawo suka tafi.

A falo ta samu Daddy da Mummyn su Salma da kuma Mama. Ta shiga suka gaisa gabaWaya ana tambayarta ya jiki ta amsa musu da ta ji sau?i. Daddy ya ce, "Hauwa na ji abinda Maman ki ta ce, auren kawai ki so a raba?." Nayla ta Waga kai a hankali kamar mai ciwon wuya. Daddy ya ce, "wani abun ne ya faru?." Nayla ta girgiza kai ta ce, "Babu komai Daddy." Daddy ya ce, "Haka kawai ki ke so a raba auren babu abinda ya faru?."

"eh daddy." Daddy ya ce, "to shikenan. Yanzu a wajan Maman ki zaki zauna har sai an raba auren?." Nayla ta Waga kai alamun eh Daddy ya ce, "babu laifi, shiga wajan ?an uwanki ku gaisa." Nayla ta mi?e ta shiga cikin gidan.

Mummy ta kalli Daddy ta ce, "Jikinta a sanyaye yake duk yadda aka yi dole ce ta saka ta furta wannan kalmar Daddy, kamar ba a son ranta ba." Mama ta ce, "Kamar a gabanki akayi Mummy. Jiya tana faWa min jiya tana hawaye alamun abun yana yi mata ciwo sosai, ni da farko na Wauka ma sakinta ya yi."

Daddy ya yi ajiyar zuciya ya ce, "mu jira mu gani in mijin na ta zai biyo sahu, in dai ya biyo sahunta matsalar ba mai girma ba ce, in kuma bai biyo sahu ba matslaar mai girma ce wacce yake nuni da wata?ila bai karSi aurenta ba ne har yanzu."

Mama ta ce, "haka ta ce min daman wai baya sonta." Daddy ya yi murmushi ya ce, "shiyasa na faWa miki, in har yazo nemata matsalar ba mai girma ba ce, zai biyota dan ni dai bazan neme shi ba, amma indai bai zo ba za a raba auren kamar yadda Naylan ta nema. Daman dukkan mu ba son zamanta dashi mu ke yi ba, babu yadda zamu yi ne ya saka muka amince tunda tana so kuma mahaifinta ya zartar da hukunci. Zan kira mahaifinta na sanar dashi yanzu dan ya san abinda yake faruwa. Ni dai bazan nemi Omar dan naji abinda ya faru ba, tunda har ya san ta baro gida zan saka masa ido na bashi lokaci naga zai nemeta, kamar yadda na faWa in yazo daidai ne, in bai zo ba ma daidai ne."

Mama ta ce, "hakan ya yi, gwara ma da hakan ya faru ko babu komai ta huta a gida, har ga Allah wannan auren nata ba wani kwanta min ya yi ba."

Daddy ya murmusa ya ce, "kar dai ki shiga tsakanisu ki zo ki ji kunya, babu ruwanki da nuna mata bakya son aurenta, babu ruwanki da nuna mata bakya son mijinta, ki tsaya a tsakiya kawai, in tayi ruwa rijiya in bata yi ba masai. A yanayin da take magana Sacin rai ne ya saka ta ce a raba auren, mu bata lokaci ta warware daga baya sai komai ya biyo baya."

Mama ta ce, "Allah dai ya kyauta kawai." Aka amsa da amin. Sai bayan sallar magriba sannan Nayla da Mama suka koma gida.

" " " " " " "

Abiy yana zaune yana amsa waya, Mama na gefensa sai Jawad kamar ko yaushe yana cewa, "To Alhaji Junaid duk abinda ku ka yanke ai daidai ne, dani da ku duk Waya ne a wajan Nayla, dukkan mu iyayenta ne, abinda ku ka ga daidai ne ku aiwatar kawai babu Sata lokaci ko jiran umarnina."

Murmushi ya sake yi ya ce, "Na baka wu?a da nama a wannan lokacin ma, duk abinda ka yanke ka ke ji a zuciyarka daidai ne ka yi kawai." Abiy ya sake cewa, "babu komai ai duk Waya ne. Allah ya zaSa abinda ya fi alkhairi." Daga haka suka yi sallama Abiy ya yanke wayar.

Mama ya kalla da take kallonsa ya ce, "?arki Nayla ce ta bar gidan mijinta ta koma gidan ?anwar mahaifiyarta." Mama ta ce, "Akan me?."
"Wai ta bar auren, ita ta gaji." Mama ta ce, "Subahanallahi! Allah ya sa ba wani abun ya yi mata ba. Kai wannan yaro an yi shaiWani wallahi."

Abiy ya murmusa kawai bai ce komai ba. Jawad ya ce, "Abiy akan me take so a raba auren to?." Abiy ya ce, "ta ce kawai ita bata son zaman auren a raba shi."
"To ina mijin na ta?."
"Ni ban sani ba Jawad, na basu wu?a da nama duk abinda suka yanke daidai ne. In sun raba auren daidai ne, in ba su raba auren ba ma duk Waya a wajena."

Mama ta ce, "Wannan aure babu abinda zai raba shi, in sha Allah Nayla sai ta cigaba da rayuwa a cikin sa!" Mama ta faWa tana kallon Abiy.

Abiy da Jawad duk kallonta suka yi cikin mamakin kalamanta, ganin suna kallon ta da alamun mamaki akan fuskarsu sai ta ce, "Yarinya ?arama da ita ace ta zama bazawara? Ina amfanin wannan auren tun farko amma ta dage sai da aka yi?. Bana so a raba auren nan saboda an lalata mata ?uruciyarta, tana yarinya da ita a ce ta zama bazawara abin sam bai yi ba. Duk wacce take amsa matsayin uwa a wajanta bazata so auren nan ya mutu ba."

Jawad ya ce, "ni kam Mama ban ga aibun hakan ba, in hakan shine mafi alkhairi Allah ya tabbatar, abinda ya kamata ki ce kenan." Ta harari Jawad ta ce, "Baka da hankali ai, baka san meye zawarci ba. Dan rashin hankali auren da bai wuce wata shida ba ace ya lalace?."

Abiy kallon ta yake yi kamar mai karantar wani abu, ta kalle shi suka haWa ido ya dau?e kai ba tare da ya ce mata komai ba. Shima Jawad Win shiru ya yi yana mamaki, ko meyasa Mama bata son auren Nayla ya mutu oho, tun farkon aure ita kaWai ce mai goyan bayan auren har yanzu. Ya rasa meyasa take haka, yau kaga tana goyan bayan auren, gobe ka ji tana kushewa.

Mama tashi tayi ta bar wajan zuwa Wakinta. Hannu na rawa ta kira waya ana Wauka ta ce, "Ke komai yana shirin lalacewa, Aziza wai Nayla ta bar gidanta ta koma gidan ?anwar mahaifiyarta, kuma na san halin dangin babar nan nata, sonta suke yi kamar su Wiga mata rai, tsaf zasu iya kashe auren nan ban cimma burina ba. In auren nan ya mutu yanzu ribar me na samu? Bayan kyau da Naylan ta ?ara yi a gidan? Tunda aka fara irin wannan yajin so nake a cigaba daga nan har a tashi duniya."

Aziza ta ce, "kwantar da hankalin ki Yayata kuma ?awata, Yanzu Ina ita Nayla Win?."
"Tana Kano na faWa miki."
"Shikenan ki kira ta, ki karya mata zuciya da kalaman da zata sake lulawa cikin duniyar qaunarsa. Ki kashe mata zuciya, ki tayar mata da tsumin soyayyarsa. ?awata ki yi mata laga-laga da zuciyata, ki dasa mata raunin da zata ji tana so ta koma masa. Daga nan in ta koma ya kamata mu yi wani abun da zamu jefawa yaron tsanarta a zuciyarsa, yadda ubanta ya ce kar ta zo masa gida shi Omar Win ya dinga cin ubanta kinga bata da wajan zuwa."

Mama ta ce, "Aziza na san Sa'adatu farin sani, babu lallai ta bar kalamaina su yi tasiri a zuciyar Nayla."

"Haba Zeenatu kamar ba ke ba? Ki gwada sai ki zo ki bani labari. Ai tunda har aka Waura auren nan wallahi baza mu bari a raba shi ba, in aka raba ma kenan itace da riba ba mu ba. Duk wahalar da Bilkisu ta ba ki shikenan ta tafi a banza? Matar nan har shara da wanke-wanke ta saka ki da cikin Ahmad wata tara. Ba tausayi balle imani kuma mu sai mu bar ?arta ta yi walwala a gidan miji?. Ni fa na so mai mata ta aura, da ace yana da mata zuwa zamu yi mu haWa kai da uwar gidan, in ta kama mu biya uwar gidan ta dinga cin uwar Nayla yadda zata girbi abinda uwatta ta shuka."

Mama ta sauke numfashi ta ce, "Aziza ina son Nayla, amma bana son Nayla tayi walwala a gidan aurenta. Yadda na assasa auren nan har aka yi bazan ?yale ya lalace a banza ba, zan iya yin komai dan ta koma masa."

"Ki samu ta koma Win, in ta koma zamu canja taku ne, domin kuwa akwai wani malamin su ?awata ban taSa zuwa wajansa ba amma akan wannna maganar zamu je. Za a yi aiki akan mijin nata, a sake jefa masa dabi'ar shaye-shaye da wannan faWan daban yadda zai ci uba ta da hujja."

Mama ta yi dariya ta ce, "Aziza ke muguwa ce wallahi." Aziza ta ce, "Baza ki gane ba Zeenatu, uwarta ta wahalar da ke sosai, har ni da nake ?ar zaman Waki ba ?yale ni tayi ba. Shegiya mai ruwan aljanu, ana cikin kabari ana girbar abinda aka shuka, an bar mu a duniya muna walwala da jin daWi, ga kuma ?arta a duniya zata girbar mata abinda ta shuka kafin ta she?a barzahu."

Mama ta ce, "in na tuna lokacin da nake nakuWar Ahmad tana kallona ina juyi jini yana gudu yana bin ?asa amma baiwar Allah nan ta Wauke kai ta kuma ?i sanar Abiy abinda yake faruwa. Ba dan Allah ya kawo ku a lokacin nan ba da yanzu Ahmad bashi da rai. Ke ba a banza Alalh ya Wauki ran Bilkisu ba, barinsu a duniya ma mugun iri ne wallahi. Sai bayan ta gama aikata sharrinta wai yafe mata, an?i a yafe Win."

Aziza ta ce, "kuma a haka zamu bar ?arta tayi zaman aure lafiya?. Ai Allah yana so ki Wauki fansa ne shiyasa ya Wauki ranta ya bar ?arta a hannunki, duk abinda ta aikata miki sai gashi ta mutu ta bar ?a Waya tilo da ta mallaka a hannunki. Sai abinda ki ka ga dama zaki yi mata, kin ma yi ?o?ari da kika iya rainon Nayla wallahi."

"Ina son Nayla na faWa miki, ina jinta kamar Jidda. Biyayyar da Nayla take yi min Jidda bata yi min ita wallahi, kuma na ri?eta tsakani da Allah da zuciya Waya, kawai burina ta girma a zo wannan gaSar, bana so ta ji daWin aure ko kusa Aziza."

"Zaman aure mai daWi ai sai Jidda da Jalila, su ne zasu yi rayuwar aure mai kyau da farin ciki amma ba Nayla ba. Yanzu ki kira ta ki yi mata laga-laga daga nan sai ki bani labari." Sallama suka yi Mama ta kashe wayar ta kira number Nayla kai tsaye.
KRB3P030
Arewabooks@nanahaleema11.

Nayla tana zaune ita da Mama Sa'adatu da Salma da Yaya Zahra kiran Mama ya shigo wayarta. Kallon wayar tayi kamar bazata Wauka ba sai ta Wauka, da yake wayar na nesa da ita sai ta saka a speaker ta ce, "Mama Ina yini." Mama ta ce, "Nayla kina lafiya? Ya na ji muryarki haka?." Nayla ta ce, "kaina ne yake ciwo Mama, Ina Jalila? Yaushe Twiny zata dawo?."

Maa ta ce, "Nayla ba wannan ba. Yanzu Abiy yake faWa min abinda ya faru, da gaske kin bar gidanki Nayla?." Nayla ta ce, "eh mama."
"To akan me Nayla? Me ya faru, meyasa baki faWa min ba?. Ba na ce duk abinda ya faru ki dinga sanar dani ba?."
"Mama ni kawai na bar auren ne."
"Akan me zaki bar auren bayan kina son mijinki?? Ko dai zuga ki ake yi akan ki kashe aurenki?."

Nayla ta ce, "A'a Mama, da kaina na gaji kawai." Mama ta ce, "to ki faWa min abinda yake yi miki mana har kika gaji Win, dukanki yake yi?." A gajiye Nayla ta ce, "ni bai taSa dukana ba" ta faWa kamar zata yi kuka.

Mama ta ce, "kin ji ko, ni na san kina son mijinki gashi nan muryarki har ta fara yin rawa. Nayla kar ki sake auren nan ya mutu, in ki ka bari hakan ya faru kin rasa masoyinki wanda ki ke so na har abada. Omar shine wanda ki ke so, shine wanda ki ke


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login