Showing 105001 words to 108000 words out of 332344 words

Chapter 36 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14821

banza kenan, meye amfanin soyayyar da take masa ana irin wannan abum?." Daddy ya ce, "mu bi komai a hankali Ali."

"Assalamu alaikum, Alhaji barka da yamma" aka faWa daga bakin ?ofar falon. Daddy ya ce, "Wa'alaika Salam, Aminu shigo mana." Aminu ya shigo ya dur?usa ya ce, "Alhaji ba?o ka yi, ya ce don Allah nazo na sanar da kai." Daddy da mamaki ya ce, "Ba?o kuma? Yana Ina?."
"Yana waje dan bai shigo gidan nan ba." Daddy ya ce, "ya sunansa?." Aminu ya ce, "ya ce sunan shi Omar, wani saurayi haka fari kyakykyawa."

Daddy ya kalli Abba dan tashin farko Omar Win Nayla ne ya zo zuciyarsa, ya kalli Aminu ya ce, "jeka ka shigo dashi, ka rako shi har falon nan." Aminu ya amsa ya fita da sauri. Daddy ya kalli Abba ya ce, "ka ga abinda nake faWa maka, mu bi komai a sannu gashi ya kawo kansa." Abba ya ce, "gwara da Allah ya sa ina nan, dan na san halin ka baza ka buWe masa wuta yadda ya kamata ba, tunda ya same ni kuwa ya haWu da daidai shi." Daddy ya yi murmushi a lokacin Aminu ya yi sallama suka shigo.

Omar akan carpet ya zauna kamar yadda Didi? tayi masa nasiha, Aminu da ya rako shi ya fita ya barsu su uku a zaune. Daddy ya kalli Omar da fara'a ya ce, "Malam Omar barka da zuwa." Omar kuwa tunda ya shigo falon nauyi da girmansu ya gama mamaye masa zuciya, ya rasa abinda zai yi balle ya iya magana. Da?yar ya iya furta, "Barkan ku da yamma." Daddy ya mi?a masa hannu ya ce, "bismillah ,mu gaisa." Hannu ya bayar kamar yadda Daddy Win ya mi?o masa hannu, suka gaisa harda Abba da yake ta kallonsa dan gani yake Omar ya canja masa.

Daddy ya ce, "Ya aiki ya kuma Yayarka?." Omar ya ce, "Alhamdu lillah."
"Ma sha Allah haka ake so." Omar ya yi shiru ya rasa ta inda zai fara, shi fa wallahi bai san ta inda zai fara bai ma san me zai ce ba, sunan da zai yi amfani dashi wajen kiran Daddyn ma bai sani ba hakan ya saka shi yin shiru.

Abba ya kalle shi ya yi murmushi ya ce, "Malam Omar ka yi shiru baka ce komai ba." Omar ya Wan sauke numfashi ya ce, "Alhaji ayi ha?uri da abinda ya faru." Daddy ya yi murmushi ya ce, "Omar ai mu ba laifi aka yi mana ba, Nayla ta dawo ta ce ita ba faWa ku ka yi ba kawai tana so ka saketa ne ta gaji da zaman auren."

Omar ya lumshe ido ya tsani kalmar sakin nan da ake faWa, in dai za a ambaceta sai yaji kamar an soka masa mashi a zuciyarsa. Ya buWe ido ya ce, "laifina ne duk abinda ya faru." Abba ya ce, "yanzu kana nufin kazo a baka ita a karo na biyu kenan?." Omar ya Waga kai alamun eh kana ya ce, "abinda nake nufi kenan." Daddy ya ce, "Omar bamu san abinda ya saka Nayla ta ce haka ba, baza mu yi gaggawar cewa zata dawo wajanka ba dan wata?ila tana da dalilin da? baza ta iya faWa mana meye shi ba."

Omar ya sauke numfashi kaWan ya ce, "laifina ne kamar yadda na faWa, ni ba mutum ne mai ?arya ba zan sanar daku gaskiyar abinda ya faru. Da farko ban karSi aurenta ba gaskiya, a ranar da aka sanar dani in zaku tuna na furta bana so kafin yayata ta ce zamuyi magana a keSance, itace tayi min dole har na amince da auren amma ba dan ina so ba.? Itace ta yi min dole ta saka nayi mata al?awarin bazan taSa rabuwa da ita ba koda mahaifinta ne zai kira ni ya ce na rabu da ita, hatta zama a gidan da nake yi Didi ce tayi min dole ba dan ina so ba. Ina da wahalar sabo, shiyasa abubuwa suka dinga faruwa har ta kai ga ta kasa jurewa ta ce zata dawo."

Abba ya ce, "kace da gaskiyarta gwara ayi sakin a huta, meye amfanin zama da wanda baya sonka bai karSi aurenka ba?. Har gwara ace itace take zaune da kai bata sonka da ace kaine baka sonta, ka ga zaman da ku ka yi zaman cutuwa ne da Sacin rai da kuma ba?in ciki." Daddy ya girgiza kai cikin gamsuwa ya ce, "gaskiya ne, tunda har abin ya zama haka yanzu ka rubuta mata takardar sakin kawai zai fi alkhairi."

Omar ya Soye ruWaninsa ya nutsu sosai ya ce, "A'a Alhaji, bana tunanin ko duniya zata taru ta ce na saketa zan iya sakinta, ko meye zai faru a yanzu sai dai ya faru amma wallahil azim bazan iya rabuwa da ita ba. A yau na zo da kaina da cikin umarnin kaina ba dan umarnin yayata ba, na ji a raina in ban bata dawo gidana ba bazan sake yin farin ciki ba a duniya. Alhaji da gaske nake wannan zuwan na kaina ne ba na umarni ko dole ba, a shirye nake na zauna da ita zama na har abada. Na san mahimmacin da take dashi a rayuwata, a baya ma ban gama fahimta ba shiyasa har hakan ya faru, amma a yanzu na gane mahimmacin da take dashi a rayuwata bazan iya rabuwa da ita ba. Ina sonta, ina ?aunar zama da ita har abada."

Daddy ya yi murmushi domin kalaman Omar sun burge shi sosai, kai tsaye yake magana babu ruwansa da wani kara ko kunyar surukai. Daddy ya ce, "in na fahimce ka yanzu ka amince da auren, sannan zaka zauna da ita a matsayin matarka?."

Omar ya girgiza kai ya ce, "haka ne." Abba ya ce, "kuma ba umarnin ta sake baka ba kuwa? Anya ba dole aka sake yi ba?."

Omar ya yi murmushi ya ce, "ko Waya, itama ta san ta gama yi min dole a duniya. Da kaina nazo kuma saboda son raina ba dan ita ba, nakasa jurewa ne kawai, duk yadda na so na jure rashinta na kasa, duk yadda naso na ?aryata kaina akan ina ?aunata na kasa. In da dole tayi min da tare zamu zo da ita, kuma baza ta taSa bari nayi magana ba, kafin nayi magana Waya tayi goma saboda tsoron kar na furta abinda bata so. Kamar yadda na ce ni ba mutum ne mai Soye gaskiya ya faWi ?arya ba, wallahil azim da ace bana ra'ayi labarina ma baza a sake ji ba balle har nazo da kaina. Wallahil azim ina sonta, babu halittar da nake so a duniya kamar yadda nake sonta."

Abba ya yi murmushi mai sauti cikin jin daWin kalaman Omar ya ce, "Haka ne Malam Omar, na amince da gaske yanzu kana son Nayla ba dole aka yi maka ba. Amma kamar yadda aka baka dama a wancan lokacin aka zauna dakai aka tambayeka ra'ayinka akan auren itama za a bata dama, a lokacin baya ba a tambayeta ba saboda muna ganin kaine ba a kyautawa ba an baka aureta ba tare da ka sani ba. Itama zamu bata dama kamar kai, in tana ganin zata iya cigaba da zama da kai shikenan, in baza ta cigaba da zama da kai ba Omar babu wanda zai yi mata dole, sai dai mu ce ka yi ha?uri."
KRB3P036

Omar ya Wago a hankali ya kalli Abba, ya sake sauke kansa ?asa yana maimaita kalmar sai dai mu ce ka yi ha?uri, bai san ko duniya ce zata taru a kansa ba bazai saki Nayla bane shiyasa yake faWar haka. Ya yi ajiyar zuciya amma bai ce komai ba dan ?irjinsa bugawa yake yi in ya tuna su Win iyayenta ne. Daddy ganin yanayin da ya shiga sai ya murmushi ya???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? ce, "na amince a yanzu baza ka bar Nayla ta yi kuka ba Omar, tabbas a yanzu na amince a zuciyata Nayla tayi aure ta auri wanda yake ?aunarta. Amma kamar yadda ?anina Ali ya faWa maka za a bata dama kamar yadda aka baka, daman mahaifinta ne ya yanke hukunci a kwanakin baya shiyasa mu ka tambaye ka dan kaine ba a kyautawa ba, amma yanzu za mu tambayeta mu ji me zata ce."

Omar ya girgiza kai cikin rauni ya ce, "To. Amma zamana da ita a wannan lokaci bazai taSa zama na cutarwar ba balle har ta kai ga dawowa gida ba, ko a baya ban taSa cutar da ita ba balle kuma yanzu da na san mahimmacinta. Sai ka rasa abu ka ke gane darajar da yake dashi da adadin ?aunarsa da ka ke yi masa, bazan sake bari hakan ta faru ba a yanzu ko a nan gaba."

Suka yi dariya tare Abba ya ce, "Dakyau Omar! Haka nake son mutum mai faWar asalin abinda yake zuciyarsa, bana son mutum bai Soye gaskiya ya faWi ?arya dan farantawa wani rai. Tabbas ba dan na san iyayenka ba da sai na ce ni na haife ka."

Omar ya murmusa kaWan amma bai ce komai ba. Daddy ya ce, "Tunda yanzu ka amince da auren naku za ka karSi shi hannu biyu, maganar gwajin jinin da mu kayi tun kwanakin baya yanzu muna da bu?arta shi gaskiya." Omar ya sauke numfashi kaWan ya ce, "in sha Allah za ayi."

"Kasancewar ka mai gaskiya na baka dama ka je duk inda ka ke so ayi maka ka kawo min, na san baza ka Soye min komai ba, dan na amince da kai Wari bisa Wari." Omar ya sake yin murmushi, sosai yake jin girman mutanen a idanunsa, yadda suka karSe shi hannu biyu, suka sakar masa fuska lamarin ya yi masa daWi.

Daddy ya ce, "Naylan tana gidan nan, sun zo duba ni ita da Mamanta saboda na Wan yi fama da mura. Yanzu zan turo maka ita ku gaisa kafin gobe in Allah ya nuna mana mu zauna da ita mu tattauna dan mu ji ra'ayinta."

BuWe baki yayi kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Abba da ya kula da hakan sai ya ce, "kar ka damu Omar, faWi abinda yake bakinka." Omar ya ce, "in da dama a tambayeta a yau.....don Allah" ya ?arasa faWa murya a ?asa. Daddy ya yi murmushi haka Abban ma, gabaWaya Omar Win ya canja musu ya koma wani daban kuma ya basu nishaWi matu?a.

Daddy ya ce, "ka kwantar da hankalinka, mu jira gobe in Allah ya kaimu." Omar ya sauke kai ?asa bai ce komai ba amma ba haka ya so ba. Abba ya ce, "ka kwantar da hankalinka kaji Omar, Ina bayanka nima a yanzu, zan taya ka ya?in dawo da Hauwa in sha Allah." Murmushi ya sake yi amma bai kuma magana ba.

Daddy ya Wauki waya ya saka a kunne ya ce, "ki turo min Nayla parlour." Babu jimawa Nayla ta shigo da sallama, bata lura da Omar ba amma gabanta ya faWi sosai ba tare da san dalili ba. Kusa da Daddy ta je ta ce, "Daddy gani." Daddy ya kalle ta ya ce, "mijinki ne yazo, gashi a zaune ku gaisa" ya faWa yana tashi tsaye, Abba ma ya tashi suka fita zuwa harabar gidan.

Nayla tsam tayi a inda take zaune ?irjinta ya buga sosai, lumshe ido tayi domin kuwa sai yanzu ta sha?i ?hamshin turarensa mai matu?ar sanyi da kashe mata jiki a duk sanda ta sha?e shi. ?irjinta bugawa yake yi da matu?ar ?arfi, wani abu take ji yana shiga jijiyoyin jikinta kamar tafiyar ruwa. Kewarsa da kwarjininsa ya cika falon gabaWaya, ta kasa koda motsin kirki ta yi shiru tana jin sautin bugun zuciyarta. Shiru ya ratsa parlour dan ta ?asan ido ta ga inda yake zaune, kanta yana ?asa bai ce komai ba itama kuma haka.

Shi kam Omar kallonta yake yi kallon da bai taSa yi mata irin shi ba a duniya, kallon ?urilla yake yi mata yana kallon yadda idanunta yake ?iftawa kamar wacce wani abun ya faWa mata cikin idon, duk da hakan sabon ta ne amma sai ya ga na yau yafi Waukar hankalinta.

Lumshe ido ya yi ya buWe a kanta, sai a lokacin ya sake tabbatar da ba ?aramin kewarta ya yi ba, a karo na farko a rayuwarsa da yake ji yana son haWa jikinsa da mace, ji yake kamar ya tashi ya mi?ar da ita tsaye ya sakata a ?irjinsa ya mayar da hannunsa ya rungumeta ko zai ji sau?in bugun zuciyarsa take damun sa dashi.

"Ba magana...?an mata!" Ya furta cikin wata irin murya mai sanyi da daWin saurare, a can ?asa ya yi maganar cikin wani sabon salon da bai san yana dashi ba.

Nayla sai da ta sauke ajiyar zuciya jin yadda muryarsa ta daki zuciyarta ta ratsa jininta ta zaga ko ina a jikinta. Hawaye taji yana taruwa a idanunta, hawayen soyayyar da take masa da tsnatsar kewar ganin fuskarsa da jin muryarsa suna taruwa a idanunta. A hankali ta Wago ido ta kalle shi daman shi kallonta yake karaf suka haWa ido, da sauri ta sunkuyar da kai dan bazata iya jure kallon fararen idanunsa da suke yawo a kan a fuskarta ba. Wani irin abu mai kaifi take hange a idanunsa a karo na farko, bata taSa ganin hakan a idanunsa ba sai a yanzu.

"Ina yini" ta furta a sanyaye ba tare da ta kalle shi ba. Omar ya yi murmushi jin muryarta da yadda ta ratsa ?wa?walwarsa ta kaiwa kunnensa ziyara. Bai ce komai ba sai kallon ta da yake yi kamar ya jawo ta jikinsa ya matse ta har sai ya samar mata da nutsuwa haka yake ji.

Nayla jin shiru sai ta turo baki gaba tana mita a zuciyarta, daman ta san ba zai amsa ba tunda ya riga da ya saba yi mata haka. A hankali ya furta, "Kina lafiya?." Nayla ba ta amsa ba ta ce, "Ka bawa su Daddy takardar sakin ko yanzu zaka faWa min?."

TaSe baki ya yi tare da kallonta ya ce, "Daman ni na ce zan kawo wani abu ne?." ?ago kai tayi suka haWa idanun ya Waga mata gira, hawaye suka sakko akan kuncinta amma bata ce komai ba. Omar kallon ta yake yi ganin hawaye yana sauka akan kuncinta. Sauke ido ?asa tayi sai ya ce, "ni ban ce zan kawo komai ba, kawai na zo na koma dake."

Zuciyar Nayla bugawa take yi matu?a, har a kunnenta tana jin yadda zuciyar ke bugawa sosai. Shi kam Omar gabaWaya ya rasa abinda zai ce mata, shi ba iya magana ya yi da mace ba, sannan ba iya rarrashin mace ya yi ba, ko lokacin Narma itace take rarrashinsa ba shine yake rarrashinta ba, shiyasa ya rasa abinda zai ce mata. Tunawa ya yi Didi ta ce ya faWi duk abinda yazo zuciyarsa, hakan ya saka ya kulle ido ya buWe ya ce, "Jidda!." Wani irin dum Nayla taji a zuciyarta, a karo na farko an kira ta da Jidda, duk da ta san sunanta ne amma ba dashi ake kiranta ba. Bata san ta Wago ta kalle shi sun sake haWa ido ba, tsayar da ido tayi a kansa na na wani lokaci kafin ta sauke ido ?asa.

Omar ya sake tausasa murya ya ce, "Ki yi ha?uri!." Ba Nayla ba, shi kansa da ya bada ha?urin sai da ya ji sautin a zuciyarsa, fit ya ji kalmar ta fita ba tare da ya shirya ba. Bai taSa bawa wata halitta ha?uri daga zuciyarsa ba sai ita, itace mace ta farko da yake furta mata kalamansa suke fitowa daga zuciyarsa har kan harshensa

Nayla ta rufe ido ta buWe tana jin kamar ana Waureta da igiya, ta kasa koda motsin kirki sanyin da take ji yana mamaye jikinta kamar mai zazzaSi. Omar ya sake cewa, "Na Wauka barinki a inda nake shine zai zama maganin matsalata, amma da na zauna bakya nan sai na fahimci kece maganin matsalar. Ina so ki dawo mu cigaba da rayuwa ba irin wacce mu ka yi a baya ba, Da gaske nake ina so ki dawo rayuwata Jidda!

Nayla ta muguWa cikin sanyin murya ta ce, "Ba zan dawo ba, bayan kace dole aka yi maka ka zauna dani."

Omar ya yi murmushin farin ciki, ji yake kamar ya jawo ta jikinsa amma bashi da wannan ?arfin guiwar. Ya kalli fuskarta da take a ?asa ya ce, "in ji waye ya ce haka?." ?ago kai tayi ta kalle shi ta shagwaSe fuska ta ce, "kaine ka ce." Sake kashe masa zuciya tayi da salon maganarta, ya runtse ido da ?arfi yana murmushin da ya?i barin fuskarsa ya ce, "a baya haka ne Jidda, amma a yanzu ba haka bane."

Nayla ta kawar da kai cikin dakiya da dauriya ta ce, "ni bazan komai ba, Ina jiran sa?on saki daga gare ka. Bazan iya cigaba da zama da kai a haka ba, bani da daraja a idanunka, bani da ko wanne mahimmaci a gare ka. Ko lamarinka na shiga cewa ka ke yi baka saka ni ba na tsaya a iya matsayina. Ka kalle ni ka ce baka sona baka son zama dani, ka ce ka tsane ni, ka tsani aurena, babu abinda zai saka ka so auren. Gwara a ha?ura kawai, bazan iya zama da wanda baya sona....baya son aurena ba. Na san ba da sanin ka aka aura maka ni bani, sadakata aka baka shiyasa ka samu damar faWar duk abinda ya zo bakinka......" ta kasa ?arasa maganar saboda kukan da ya taso mata. Ta share hawaye ta ce, "Ka bawa su Daddy takardar sakin, ni bazan sake zama da kai ba" ta faWa tana tashi tsaye zata tafi.

Mi?ewa tsaye shima ya yi, rauni yake ji a zuciyarsa saboda jin kukan ta har cikin ruhinsa, in da a baya ne take faWa masa wannan maganar tsaf zai iya sakinta amma a yanzu bazai iya ba, sakinta daidai yake da barazana ga numfashinsa.

Omar murya a sanyaye ya ce, "Bazan iya sakin ki ba Jidda! Yanzu na fara rayuwa dake in sha Allah. Bana tunanin ko duniyar nan zata taru akan na sake zan sake ki, bazan iya ba!.." Cak ta tsaya daga shiga cikin gidan da take yi, ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login