Showing 15001 words to 18000 words out of 332344 words

Chapter 6 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

30854

zaka je? Baka jin ana yi muku nasiha ne?.
 Nasihar mijin ta ki ce na ji da Wan rainin hankali a cikin ta, Allah ya bata ha?urin zama dani ya ce, amma ni bai ce Allah ya bani ha?urin zama da ita ba. Ni ne mai halin banza kenan?.

AbdulHamid ya ce,  Yi ha?uri mutumina, kai ai namiji ne, na san zaka iya yin ha?urin shiyasa ban faWa ba. Ita kuwa mace ce sai an sanar da ita. Yi ha?uri ka zauna. Didi ta jawo hannunsa ta ce,  Zauna don Allah. Bai musa ba ya zauna AbdulHamid ya murmusa ya cigaba da yi musu ta?aitacciyar nasiha.

Ita dai Nayla ba ma jinsu take yi ba, hankalinta yana ga wani wajan daban, amma duk motsin Omar a kan idanunta yake yi, duk abinda ya ce tana ji. Ita kanta dariya ya bata jin abinda ya ce, bata san tayi murmushi ba a ranta tana ayyana mutum sai masifa.

Didi ta ce,  to ka gama faWar duk abinda zance ai, abinda zan ?ara dashi shine Nayla sai kin yi ha?urin da zama da Omar Sai ta kalle shi taga ita yake kallo ta ce,  ka dai na san halinka, nima ha?uri nake yi da kai balle matarka, ka daina kallona sai na faWa. Ta sake kallon Nayla ta ce,  Yana da taurin kai sosai kuma masifaffe ne, sannan yana da hargagin da zai tsorataki lokaci Waya, yana da zafin kai kullum zuciyarsa a sama. Don Allah ina so ki mayar dashi kamar ruwan sanyi, duk wannan zafin kan na sa ya ajjiye ya zama bawan ki. Bai san lokacin da murmushi ya kubbe masa ba jin kalaman Didi, wai ya zama bawanta, shi har yanzu zuciyarsa faWa masa take yi Didi tana da ?ar matsala gaskiya.

Ta kalle shi ta ce,  Omar Nayla bata da matsala ba kamar kai bace, tana da kirki tana da fara a da kuma biyayya. Ta fito daga babban gida wanda ta samu kyakykyawar tarbiyayya ta kuma ta shi cikin nutsuwa. Bana jin Nayla ko kaWan, na san ko ban ce ba ita mace ta gari ce a wajanka, don Allah kaima ka zamar mata miji na gari. Marainiya ce bata da mahaifiya, ga mahaifi ta ma ya yi mata nisa tunda ta bar asalin garin su. Don Allah ka zamar mata uwa da uba, yayanta kuma mijinta. Don Allah Omar kar ka bar Nayla ta zubar da hawaye a zaman ku da ita. Ka bata dukkan kulawar da ka san zaka iya.

Shiru ya yi bai ce komai ba amma yana mamakin kalmar marainiya Win nan da Didi take faWa, shi ba maraya bane kenan ko kuma iyaye sun fi iyaye ne? Ko mutuwa tafi mutuwa ne da zata dinga maimaita masa marainiya ce?. Didi jin ya yi shiru bai tanka ba sai ta ji daWi a zuciyarta dan bata so ya yi abinda rai zai Saci. Didi ta ce,  Allah ya baku zaman lafiya ya Worar da zamanku har aljanna. Da ita da AbdulHamid da salma suka amsa da amin ban da Omar.

Didi ta ce,  to zamu wuce mu dare yana yi. Salma mu tafi sai mu sauke ki gidan Hajja? Ta faWa da sigar tambaya. Salma ta ce,  Eh Didi, bara na Wauko kayana ta faWa tana tashi ta shiga bedroom. Jim kaWan ta dawo Didi ta mi?e AbdulHamid ma ya mi?e tsaye suna yiwa Nayla sallama. Didi ta kalli Omar da bai motsa ba ta ce,  ka zo mu je ka kulle gidan. Ba tare da ya kalle ta ba ya ce,  zan zo.

 Ka taso Omar, nan ba gida ba ne. Mi?ewa ya yi ya bi bayan ta Salma da take tsaye tana su bayan sun fita ta kalli Nayla ta ce,  amarya naga angon na ki ya Wan yi hankali babu laifi. TaS amma Ina tausaya miki shiga hannun wannan mutumin, wannan ai sai ya Salla ki g1da biyu.

Nayla ta Wago ido ta kalle ta, Salma ta ?yal?yale da dariya ta ce,  Amaryar Ango mai zuwa gidan amarya da ?ananun kaya. Nayla sai tayi murmushi kawai Salma ta ce,  Sai mun yi waya ta faWa tana fita da sauri.

Nayla ajiyar zuciya tayi gabaWaya zuciyarta babu daWi haka take jin jikinta. Tayi shiru tana jinjina girman iko na Allah, wato daman ya ?addara zata auri Omar shiyasa ya saka mata sonsa a zuciyarta, sai gashi auren ya zo a lokacin da babu wanda ya yi zato babu wanda kuma ya shirya zuwan sa.

Motsinsa ta ji bata Wago ba ta sake saukar da kai kasa, shi kuwa chakewa ya yi daga gefe yana kallonta yana maimaita kalmar matarsa a zuciyarsa. Nayla bata san yana tsaye ba sai ta Wago ido suka haWa ido tayi saurin sauke kai ?asa, Omar ya taSe baki yana sake girgiza kai. Indai ya kalle ta babu abinda yake zuwa ransa sai faWan da Didi tayi masa a gabanta, yana kallonta abinda yake zuwa zuciyarsa kenan hakan ya saka yake Wan jin haushinta kaWan.

Kallon ?ofar da take bayan sa ya yi yaga Wakin yayi daidai da wanda Didi ta ce masa shine na sa, ya murWa handle Win Wakin ya buWe yana kallonsa ba tare da ya shiga ba. Sake ?arewa Wakin kallo yake yi zuciyarsa gabaWaya babu daWi bai san abinda yake damunsa ba.

Warning yake so ya yiwa Nayla amma kuma ya kasa ko motsawa yana kallon Wakin, zuciyarsa tana faWa masa yaje ya yi mata warning akan zaman sa tare da ita a gida Waya, kar ta shiga harkarsa shima bazai shiga ta ta ba. Samun kansa ya yi da shiga Wakin yana jin wani iri wai shine ya yi aure ya tare da matarsa a gida Waya.

Bai taSa kwana a wani waje tare da wata ba, ya zauna a gida Waya ma na wani Wan lokaci shida mace bai taSa ba sai lokacin Narma da ya taSa zama a gidan da take. Amma kwana dai in ba Didi ba bai taSa yi ba shiyasa yake jinsa gabaWaya wani iri. Lamarin yazo masa ba?o ya kasa sakewa gabaWaya.

Nayla tana ganin ya shiga bai mata magana ba daman bata kawo a ranta ma zai mata magana ba, ta tashi ta shiga Waki tana sauke numfashi. Ita har yanzu tsoronsa take ji sosai, dan da ya yi mata magana lokacin da ya shigo zata iya firgicewa. Ita kanta akwai rashin sabo na keSancewa a gida Waya ita da wani namijin a duniya, sai take ji gidan ya yi mata girma sosai. Numfashi ta sauke ta ?arasa ta zauna akan gadon tana mamaki wai itace matar Omar.

Shima a Sangarensa hakan take, gabaWaya ya kasa sakewa sai kalle-kallen Wakin yake yi. BanWakin da?in ya buWe yana kallo kafin ya bar wajan ya zauna ya harWe hannayensa ya rasa abinda zai yi.

Haka gidan ya zauna shiru kowa yana nasa Wakin yana na sa tunanin da ya damu zuciyarsa a hakan har dare ya yi. Nayla tayi bacci amma shi ya kasa bacci sai juyi ya ke yi saboda gabaWaya shi in ba gidan su ba bai saba kwana a wani waje ba. Da?yar shima bacci ya Wauke shi.

Washe gari Nayla ko da ta farka bata ji motsinsa ba gabaWaya, bata sani ba ko yana nan ko baya nan bata sani ba. Wayarta ce tayi ?ara ta duba ganin sunan Salma sai ta Wauka a nan take shaida mata an aiko abinci daga gidan Hajja ta buWe ta karSa. Fita tayi ta buWe gate Win ta karSa ta kulle ta kuma koma ciki. A kan dining ta ajjiye tana kallon Wakin na sa zuciyarta na wani irin bugawa a hankali. Ajiyar zuciya tayi ta koma Waki ta yi wanka ta shirya cikin shigar doguwar riga ta fito ta shiga kitchen ta dafa ruwan tea ta zuba ta fito tana sha.

Abiy ne ya faWo mata a zuciyarta, ta Wauki waya a sanyaye ta kira shi amma bai Wauka ba, Ta sake kira ba a Wauka ba sai ta ajjiye tare da ajiyar zuciya. Rashin Waukar da Abiy bai yi ba sai jikinta ya yi sanyi, ta rasa abinda yake yi mata daWi, tana kallon wayarta ko kiran Abiy zai shigo amma bai shigo ba.

BuWe ?ofar ta ji anyi an shigo babban falon da mamaki take tunanin daman baya nan kenan, kuma waye ya buWe masa gidan yanzu?. Tana jin motsi da alama ba shi kaWai bane dan taji yana magana cikin bada umarni.

Sai da yazo shiga Wakin da ya kwana sannan ta ji ya ce,  Didi ce ta saka ku wannan aikin?. Muryar Bash taji yana ce,  itace. Tsaki ya yi ya ce,  na rasa meyasa Didi ta raina ni wallahi ya faWa yana buWe Wakin ya shiga suka bi bayan sa da kaya masu yawan gaske.

Ba jimawa suka fito, Bash ya kalli inda Nayla take zaune dan bai kula da ita ba ya ce,  Antyn mu barka da safiya. Nayla sai ta ji wani iri, wai Antynsu bayan tana da tabbaci ya girme mata. Ta daure ta ce,  barka. Fita Bashir ya yi shi kuma ya fito da waya a kunnensa yana cewa,  meyasa ki ke kin haka? Meyasa ko yaushe sai kin yi min dole?. Yanzu meye na saka su Bashir su shiga gida har Wakina su haWa kaya su kawo min? Na saka ki ne? Ko nace ina da bu?atar hakan?. Shiru ya yi alamun tana bashi amsa kafin ya ce,  Ya dai isa haka, na gaji da kawar da kai. Dan kin ga Ina ?yalewa ne ma ya saka ki ke yi min abinda ki ke so.

Shiru ya sake yi kafin ya ce,  Oho yana faWa ya yanke wayar ya saka a aljihu yana kallon wani wajan daban. Yana juyowa suka haWa ido da Nayla da take kallonsa tana mamakin shi wannan Didin ma bai bari ba a fannin masifa. Suna haWa ido ta ji gabanta ya faWi, da?yar ta daure ta ce,  Ina kwana. Kallonta yake yi kamar bai santa ba, ya tsayar da idanunsa ?yam a kanta yana kallo, shi kansa bai san meyasa yake son kallonta ba kawai ya samu kansa a kallon nata. Tsaki ya yi kafin ya janye idanuasa ya yi banza bai amsa ba.

Nayla ta ji babu daWi a zuciyarta ta kawar da kai hawaye na cikowa idanunta. Juya spoon Win take yi a cikin mug Win hannunta jikinta ya yi sanyi akan abinda ya yi mata. Sake kallon ta Omar ya yi kamar mai tunanin wani abu sai ya fita daga wajan gabaWaya.

A bayyane ta ce,  matar cushe bata taSa daraja ta faWa hawaye na sakkowa daga idanunta. Kallon abincin ta yi da aka kawo daga gidan Hajja a bayyane ta ce,  gaisuwa ma bai amsa ba balle na ce ga abinci, nima karanbani ne irin nawa na san bazan amsa ba ta faWa tana goge idanunta cike da tausayin kanta.

Wayar ta ce taji tana ?ara ta kalla ganin Salma ce sai ta Wauka cike da tsokana Salma ta ce,  Amarya, bani labarin first night Win mana, ya komai dai normal?. Nayla ta sauke numfashi ta ce,  ki daina wannan batu don Allah Salma. Salma jin muryarta na rawa sai ta ce,  Nayla lafiya ki ke kuka?.
 Babu komai Salma. Ya Hajja? Bata mu gaisa.
 Muryar ta ki tana rawa zan bawa Hajja? Ki daidaita muryarki sai ku gaisa.
 Bata.

Da aka bawa Hajja wayar ta ce,  Hauwa u kin yini Lafiya?.
 Hajja Ina kwana.
 Lafiya lau amarya. Ya kwanan ba?on waje?.
 Alhamdu lillah Hajja.
 Ma sha Allah. Allah ya baku zaman lafiya mai Worewa. Ki yi ha?uri da duk abinda zaki fuskanta, kin san halin mijin da kika aure tun kafin ki aure shi. Ki daure ki yi masa biyayya kar wani tunani na banza ya shiga ranki, zaman aure ibada ne sai kin daure zaki kai ga nasara.

Nayla da take hawaye ta ce,  to Hajja. hajja ta ce,  yauwa, ko gaishe shi ki ke yi in bai amsa ba ki sake gaishe shi, shima in bai amsa ba gobe ma sake gaishe shi, in bai amsa ba sake gaishe shi, wata rana na tabbatar zai amsa miki. Sai kin yi ha?uri kin jure kin kawar da komai daga zuciyarki sannan zaki ji daWin zaman auren.

Nayla ta amsa Hajja ta cigaba da yi mata nasiha kafin ta bawa Salma wayar. Nayla ta ce,  Salma zaki shigo?.
 Bazan so ba gaskiya Nayla, sai an kwana biyu.
 Shikenan. Daga haka suka yi sallama ta kashe wayar.

Wayar Mama ce ta shigo ta Wauka ta saka a kunne suka gaisa da Mama kafin Nayla ta ce,  Mama Ina Abiyna?. Mama ta ce,  Abiy yana Lafiya lau.
 Na kira shi Wazu bai Wauka ba.
 Wata?ila lokacin bai tashi ba. Nayla ta girgiza kai ta yi shiru Mama ta ce,  Komai dai lafiya ko Nayla? Ina nan sai tunanin ki nake yi.

Nayla ta ce,  Lafiya lau Mama.
 Kin tabbata lafiya?. Mijin na ki yazo?.
 Eh yazo Mama.
 Har na ji daWi, Ina fatan dai komai Lafiya?. Nayla ta yi ajiyar zuciya ta ce,  lafiya lau Mama.
 To haka nake so, In akwai wani abun ki kira ni ki sanar dani. Nayla ta ce,  To.. Daga nan suka yi sallama ta kashe wayar ta ajjiye wayar a gefe ta dafe kanta.

Bata san adadin lokacin da ta Wauka a haka ba, sai kuma ta Wago ta sake kiran Abiy a lokacin ya Wauka cikin hanzari ta ce,  Abiyna, abiyana ina kwana. Abiy jin yadda muryar ta take rawa ssi ya tausasa murya ya ce,  nutsu Nayla, nutsu ki yi magana. Sai kawai ta fashe masa da kuka ya ce,  zan kashe wayata in kuka zaki yi min. Ta yi sauri ta share ta ce,  na daina Abiy. Ina kwana.
 Lafiya lau, kin tashi lafiya?.
 Lafiya lau Abiyna. Ya gida?.
 Komai Lafiya lau ya bata amsa yana jira ya ji me zata ce. Nayla ta ce,  Abiy ka daina fushi dani?.

Abiy ya ce,  ni ba fushi nake yi dake ba ai Nayla. Zata sake magana ya ce,  Ina da ba?i Nayla, zan kira ki in na samu space yana faWa ya kashe wayar. Ajiyar zuciya tayi ko babu komai taji daWi tayi waya da mahaifinta.

Haka ta yini a gidan nan shiru daga ita sai wayar ta har dare. Bayan ta idar da sallah ta yi wanka ta saka kayan bacci riga da wando dogaye masu laushi ta zauna tana shan tea. Tunawa tayi da ta bar kettle a kunne sai ta mi?e da sauri ta nufi hanyar fita da mug Win tea Win da take sha a hannunta. Karo suka yi da mutum shayin ya zube masa a jiki sannan mug Win ya faWi a ?asa ya tarwatse a kan tiles Win wajan.
KRB3P006
ArewaBooks@nanahaleema.

Cak Omar ya tsaya saboda ruwan zafin da ya ratsa rigarsa ya sauka akan fatar cikinsa, ga karon da suka yi ?irjinsu ya haWu waje Waya, ga ragowar ruwan tea Win da ya zube a ?asa ya taSa ?afarsa. Nayla a gigice ta ja baya sai kuwa santsin tea ya kwashe ta tayi baya zata kifa. Kamar ya ?yaleta ta faWi sai kuma ya ri?o hannunta ya dawo da ita ta tsaya cak tana zare idanu.

Hannunsa da ya ri?e nata sai da ?wa?walwarta ta je gutun rabon lokaci, bata Wauka haka zata ji hannun nasa da laushi haka ba, ta Wauka zata ji tauri kasancewarsa na tantari wanda kwalliya ma bata dame shi ba balle har ya san abinda zai saka a hannunsa ya yi laushi. Shima sai da yaji wani iri ri?e mata hannu da ya yi, hakan ya saka ya saki hannun nata cikin sakanin da sanin da bai wuce biyar ba.

Nayla jikinta rawa yake yi kaWan ta buWe baki da?yar ta ce,  ka yi ha?uri ban san ka taho ba. Fuskarta yake kallo da idanunta da suke kiftawa gashin idonta na sama da ?asa kamar munafuka.  Shiyasa ki ka ?ona ni kenan? Ya faWa a Wan kausashe yana kallonta. Nayla ta girgiza kai ta ce,  ban yi ima sane ba, ka yi ha?uri don Allah.

Bai ce mata komai ba ya wuce ya barta a tsaye a wajan tana raba ido. Nayla ta yi ajiyar zuciya tavce,  wai na sha da?yar. Da sauri ta kwashe pieces Win mug Win da ya fashe, ta Wauko mopper ta goge wajan sannan ta kashe abinda zata kashe a kitchen Win ta koma falo tana sauke ajiyar zuciya.

Har lokacin zuciyarta bugawa take yi kamar yana gabanta, ita ta rasa meyasa take jin tsoronsa har haka a zuciyarta. In ta ganshi sai ta gigice ta rasa abinda yake mata daWi, duk ?arfin guiwar da take ji da sun haWa ido sai ya kau daga zuciyarta ta fara tunanin Didi bata nan balle ta taimaketa.

Bangarensa shima da ya shiga Wakin tsayawa ya yi yana tuna idanunta da suke kitfawa da yadda idanunta suka yi waje lokacin da ta zuba masa tea Win. TaSe baki ya yi ya cire rigar yana kallon fatar cikinsa da wajan da tea Win ya zube ya Wan yi ja. Tsaki ya yi ya ce,  ban taSa ?onewa ba ta ?ona min fata. Kaya ya canja kawai ya zauna a Wakin ba tare da yana yin komai ba.

Yunwa ya ke ji sosai amma bai san abinda ya kamata ace ya ci ba, baya son za?ewa da yawa balle ya shiga kitchen ya ce zai yi wani abun, shi da gidan su ya saba kawai, da can ne da ko


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login