Showing 246001 words to 249000 words out of 332344 words

Chapter 83 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14378

yadda ya ce, ki zo mu je ki huta a gajiye ki ke sosai. Da?yar suka lallaSa Didi suka fito Nayla na ri?e da hannunta. Kasancewar asibitin indai kana da visa umra ne free ne ba a karSar komai, basu biya komai ba har magani aka bawa Didi.

Didi kallon masallacin take yi tana hawaye, ta sake Wurkusawa a wajan tana kuka sosai. Wai itace a harabar masallacin annabi, to me zata yi in ba kuka ba? Me ya kamace ta in ba kukan ba?. Nayla ta ri?eta ganin ta sake fita daga hayyacinta, ?aramar motar da suka hau Wazu ce ta zo wucewa Nayla ta yi musu magana suka shiga aka kai su ?arshen harabar masallacin daga nan suka ri?e Didi suka koma hotel.

KB3P094
Nana haleema.

Nayla alwala ta saka Didi tayi sannan ta yi sallar asuba. Bayan ta idar Nayla ta ce,  zaki ci abinci ko sai kin tashi daga bacci?. Didi ta ce,  bana jin yunwa Nayla, ba na son cin komai.
 A gajiye ki ke Didi, na san kina jin yunwa. Rouhii bara na sauka ?asa na siyo mata tea. Hannunta ya ri?e yana kallon ta ya ce,  babu inda zaki je, kema ai kina bu?atar ki huta, sai zirga-zirga ki ke yi kin san ba haka mu ka yi dake ba. Zauna ya faWa yana zaunar da ita cikin bada umarni.

Didi ya kalla da take kallonsa ya ce,  Didi don Allah ki bar wannan kukan kin ga ba lafiya ce da ke ba, in kina kuka sai naga kamar baki farin ciki ba. Didi ta zuba masa ido kawai tana kallonsa, me zata cewa Omar? A ganinta kalaman bakinta sun yi kaWan wajan nuna masa jin daWin ta da farin cikin da take ciki. Tun bayan da tayi aure, Omar ya auri Nayla suka fara zaman soyayya da jin daWi bata da wani buri da ya wuce ta ziyarci Madina. Ko tafiyar da mijinta zai yi sai da taji kamar ta bishi, har ya yi mata al?awari indai yana da rai a shekarar zai biya mata taje. Ga ?aninta da suke ciki Waya ya cika mata wannan burin a matsayin bazata, to in bata yi kuka ba me zata yi?

Ta ri?e hannunsa gam ta ce,  Omar Allah ya cigaba da farantawa rayuwarka, Allah ya kare ka ya cigaba da Waukaka ka zuwa matakin da baka yi tunani ba. Allah ya ji?an iyayenmu, Allah ya raba matarka da abinda yake cikin ta lafiya, Allah ya baka mai faranta maka kamar yadda ka ke faranta min&  ta faWa sabon kuka yana ?wace mata.
KRB3P093
Nana haleema.

Omar ya bita da kallo ?auna da tattali, a sanyaye ya ce, "Amin. Ya isa kukan don Allah. Didi in ban miki ba waye zan yiwa? Ke kaWai nake da ita, ke nake kallon a matsayin uwa, uba, ?anwa, ?awa, sannan Yayata. Kece matakin nasarata, kece silar auren wacce nake so, kece silar zuwana wannan mataki. To in ban saka ki farin ciki ba wa zan saka farin ciki Didi?. In dai ina da rai yanzu ki ka fara farin ciki in sha Allah, a yanzu ne zaki san kina da Wan uwa Omar!. Ki nutsu ki daina kuka" Ya faWa yana ri?e hannunta yana kallon ta.

Murmushi take yi tana kuka tana kallonsa ta ce, "tunda nake a duniya ban taSa farin ciki irin na yau ba, Omar ko ranar da nayi aure ban yi farin ciki irin wannan ba. Ni ce Madina har na shiga masallacin Annabi..?. Allah ya saka maka da alkhairi Omar, Allah ya baka abinda ka ke nema duniya da lahira."
"Amin Didi. Indai kina so na san kin yi farin ciki ki daina wannan kukan, sannan ki nutsu ki huta zuwa anjima sai ki koma masallacin."

Ta share hawaye ta ce, "To Omar na daina."
"Kina jin yunwa?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "mu je ki huta, kin ga Marmerh har ta sake yin bacci." Da kansa ya ri?e ta har Wakin da ta shiga Wazu, sai da Didi ta kwanta ya dawo ya kwantar da Marmerh a kusa da ita ya kashe hasken Wakin.

Bayan ya fito ya kalli Nayla ya ce, "Ashiq don Allah taso mu je ki huta kema." Ta mi?e ta ce, "zan kwanta tare da Didi." Da yake so yake ta kwanta Win sai ya ce, "To ki je." Sai da ya bita ya tabbatar ta kwanta Win sannan ya iya kwanciya shima.

GabaWaya Didi ta sanyaye masa zuciya, rauni da ?aunarta yake ji a cikin zuciyarsa sosai, ya kuma ji a ransa sai yanzu ya fara rama alkhairi akan wanda ta yi masa. Ta sha gwagwarmaya dashi shi kansa ya sani, bata da nutsuwa kullum saboda Wauko mata magana da yake yi, ta saka shi a gaba tayi kuka amma hakan bazai saka gobe ya ?i yi ba. Mahaifiyarsu ta haife shi ne kawai, amma Didi itace uwa a gare shii. Yana son Didi sosai, yana ?aunar tayi farin ciki, ya san zuwa saudia yana Waya daga cikin burinta na duniya shiyasa ya fara mata dashi. Da wannan tunanin shima ya yi bacci.

Nayla ta riga su tashi lokacin ana gab da yin sallar azahar, ta sauka daga kan gadon ta sake yin wanka ta saka hijjabi ta fita daga Wakin. Ba jimawa ta dawo da abinci da kuma paper cup da ta siyo tea ta zauna tana sha. Motsi ta ji a bayanta, ta juya ta kalle shi ta ga ita yake kallo ya ?araso ya zauna kusa da ita ya ce, "Daga zuwa Madina kuma sai ki canja Jidda?." ?aure fuska ta kuma yi ta kawar da kai gefe ta ce, "Ai kaine ka jawo hakan."

"Da na yi meye Ashiq!?" Ya faWa murya a can ?asa yana kallon idanunta. Ta ce, "Budurwar ka mana." Murmushi ya kubce masa ya ce, "yanzu daman duk akanta ki ke ta wanna fushin?. Kamar mun gama maganar nan tun a baya ko?."

Nayla ta ce, "mun gama kaine ka dawo da ita baya." Ya matso kusa da ita sosai yana jin ?hamshin turarenta murya a ?asa ya ce, "to me nayi? Uhum me nayi kuma?."

"Meyasa baka faWa min kun haWu a airport ba?."
Ya Wan buWe ido ya ce,"Shikenan daman fushin?." Ta harare shi ya yiwa idanunta kiss, ya dawo bakinta ya yi kissing sannan ya ce, "Lokacin na so na faWa miki sai sawun guiwa ya take na ra?umi, da na zo zan faWa miki sai ki ka sanar min da kin karSi ajiyata. Jidda ta ya zan tuna da batun wata bayan ina murna zan zama uba?. Daga nan na manta da batun, amma na so na faWa miki."

Nayla ta shagwaSe fuska ta ce, "to me ta ce maka?." Ya shafi fuskarta ya ce, "Ba ki ji abinda ta maimaita ba? Ni ban nuna na gane ta ba Jidda, kuma na gane ta Win amma kawai bani da lokacinta."

"Amma ita tana da naka lokacin, gashi tana cewa tana sonka zata aureka, Har maahifinta yana zancen yana son ganinka." Ya sake ri?e ta a jikinsa ya ce, "Ashiq!." Ya yi shiru ya zuba mata ido yana jujjuya idanunsa a kanta sannan ya ce, "Baki yarda da mijinki ba ne?."

Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "ki bani amsa." Nayla ta ce, "A'a, na yarda da kai." Omar ba tare da ya daina kallon idonta ba ya ce, "To meyasa ki ke tunanin zan iya amsa kiran mahaifinta ko kuma zan iya aurenta?."

Ta yi shiru bata amsa ba ya kuma cewa, "Ki daina wannan tunanin, ni naki ne ke kaWai kawai. Saboda ke kaWai Allah ya halicce ni, ki amince da wannan maganar da nake faWa miki. Inda ina da ra'ayin aure zan sanar dake, kece ta farko da zan fara faWawa zan yi aure lokaci kaza, ko kiji daWin maganar, ko kar kiji ni dai bani da wanda zan faWawa sai ke Win. Kuma koda ina da ra'ayin auren bana tunanin zan iya aurenta. Jidda in nayi gaba bana dawowa baya, in na ce na bar abu na bari kenan har abada!."

Wasa take da azurfar hannunsa tana shafa gashin hannunsa ta ce, "Amma ai nima ka ce baka sona kuma daga ?arshe ka canja, ka ga itama zaka iya canjawa ai."

"Jidda ke daban ita daban, wallahi ban taSa sonta ba, sai da na fara sonki na tabbatar da ita ba sonta nayi ba Jidda. Ki amince dani, ki bani yardarki bazan ci amanarki ba har abada....." ya matse hannunta a cikin nasa cikin taushin murya ya ce, "Jidda koda zaki ganni da mace a Waki Waya kawai ki tuna da yardar da ki ka yi min, ni kuma na yi miki al?awarin bazan ci amanarki ba har abada!. Ni naki ne ke tawa ce, dan ni aka yi ki dan ke aka yi ni. Wata tarkacen ?ar Sen da ma ko wacce mace bata kai Omar ya kalle ta ba, har yanzu sunan yana nan....Tiger! Har gobe sunana ne. A wajan ki kaWai na canja, amma ga kowa haka nake. Ke kaWai ki ke ganin fara'ata ko a yaushe, shiyasa ki ke tunanin zan yiwa matan kan titi, ki tuna damisar da ki ka sani a baya har gobe ita ce!."

Rungume shi tayi da sauri ya yi ajiyar zuciya yana shafa bayanta ya ce, "kin azabtar dani, rabon da na ji ki haka tun a Abuja, don Allah ki daina haWe min rai Ashiq, kina sakawa ina fita daga hankalina." Nayla ta ce, "ina sonka Rouhii, ina kishinka sosai."
"Son da ki ke yi min wasan yara ne akan wanda nake miki. Ina sonki, Allah shaida ne, ina kishinki wanda ban san iyakacinsa ba."

Nayla ta ce, "Alfarmar wannan gari mai albarka, alfarmar wanda yake kwance a cikinsa baza ka yi min kishiya ba, Allah yasa ka cigaba da sona har a aljanna, Allah ya sa baza ka taSa jin sha'awar wata mace ba sai ni kaWai." Murmushi ya yi mai sauti ya ce, "Amin Jidda, Allah ya amsa addu'arki."

"Amin Rouhii."
Ta yi luf a jikinsa, shima bai ce komai ba idonsa a lumshe kafin ya ce, "Ina kewarki sosai Ashiq, aljanun da suke kawo mana ziyara ma suna kewa Jidda." Ta Wago ta kalle shi taga ya marairaice fuska ta ce, "Didi tana nan."

Ya Wan wara ido ya ce, "sai me? Ta san tunda muka zo tare ai dole sai tana rufe idonta." Murmushi ta yi tana kai masa duka a ?ijinsa ta ce, "baka da kunya ne kawai."
"Ke kina da ita ai." Cikinta yake shafawa a hankali ta ce, "na siyo abinci fa, gashi nan."

Bai magana ba sai matso da fuskarsa da yayi kusa da tata, yana kallon idon ta har lokacin yana shafa cikinta ya ce, "kin san in ka aikata aikin lada a ?asar nan Allah ninka maka ladan yake yi ko? To ki yi aikin lada Jidda!." Nayla ta Wan juya kai ta ce, "Rouhii Didi fa tana tare damu, kuma lokacin sallah ya kusa."
"Ashiq abinda nake so kenan, baza ki yi min ba?."
"Ina so Rouhii, amma....."
"Shiiii! Ki yi shiru." Shirun ta yi tana ji ya fara yamutsa ta ya fara kissing Winta a haukace.

Kukan Marmerh suka ji, Nayla tayi saurin yin baya sai ga Didi ta buWe ?ofar ta fito daga Wakin. Nayla ta yi wiki-wiki kamar munafuka shi kansa jikinsa ya saki ya lumshe ido yana sauke numfashi, bai kalli Didi ba ya rufe ido yana shafa kansa a hankali.

Didi ta ?araso tana kallon su, ganin yanyinsu sai ta ji wani iri, duk da bata gansu a tare manne da juna ba amma sai ta ga kamar akwai wani abun da ya saka suka yi mata shiru. Nayla saboda ta katse shirun sai ta ce, "Didi kin sha bacci, ga abinci ki ci an kusa sallar azahar."

Didi ta ce, "Bacci nayi cike da mafarki Nayla, ki sake yi min godiya a wajan mijinki." Nayla ta yi murmushi Marmerh tana mi?awa Omar hannu tana kiran Daddy kamar yadda Didi ta koyar da ita ce masa Daddy. Jin muryar abar ?aunarsa ya saka ya buWe ido, ya kalle ta ya yi murmushin ?arfin hali ya mi?a mata hannu Didi ta bashi ita, Nayla ta ce, "Bara na kawo mana yaji, wannan shinkafar ta su babu maggi" ta faWa tana tashi ta shiga ciki ba jimawa ta dawo.

Tana zama Didi ta ce, "Nayla me yake damun Omar ne? Naga ya canja." Nayla ta kalli Omar da ya kallon ta, ta kalli Didi ta ce, "Didi kin fa san halin kayan ki, babu abinda yake damun shi." Murmushi tayi kawai bata ce komai ba.

Abinci suka fara ci ita da Didi kafin ya ce, "Mun yi waya da mijinki, na faWa masa inda mu ke ya ce da ?ar tazara da inda yake amma zai zo." Didi ta yi murmushi ta ce, "ka ce ku ne ki ka tsara tafiyar nan a haka?." Omar ya ce, "Jidda ce." Murmushi Didi ta yi, Nayla ta kalle shi ta ce, "baza ka ci abincin ba?."

Ya bita da mayen kallo ya ce, "Kin bani ne?." Nayla ta ce, "baka ce ba ai." Mi?a masa ta yi ya karSa yana binta da ido, ta kawar da kai kamar bata gani ba ta koma suna cin abinci da Didi tana bata labarin yadda aka tsara tafiyar. A tare suka gama ya kalli Nayla ya ce, "Wauko min abinda na baki."

Ba musu ta tashi ta kawo masa, kuWi ne na ?asar da suka canja tun a nigeria, ya bawa Didi ya ce, "Didi duk abinda zaki siya ki yi amfani dashi." Bata karSa ba ya Wora mata a kan ciyarta ya sake bata wani ya ce, "ga na marmerh, in kuma ki ka ci kuWinta Allah yana kallonki." Sai ya bata dariya ta ce, "Omar..!." Ya katse ta a kausashe ya ce, "Didi, ni na gaji da kiran sunan nan nawa da ki ke yi, ko yaushe ki ce Omar kamar ke kika raWa min sunan?." Murmushi ta yi dan ta kasa magana.

A tare suka fita zuwa masallaci don yin sallar azahar, bayan sun idar suka dawo AbdilHamid ya zo suka dinga hira duk da rabi godiya take sakawa ya yiwa Omar. Omar ya ce, "To ka dawo nan da zama mana, akwai Waki ai sai ku zauna tare."

"Ai na riga da na biya Omar, kar ka damu."
"Har na makka?."
"Har shi Omar."
"To ai shikenan." Omar ya faWa dan shi gaskiya yana so ya dawo Win ko dan ya dauke hankalin Didi shi kuma ya samu sakewa da matarsa yadda yake so

Nayla ce tayi musu booking shiga ziyara suka samu permit na shiga bayan sallar i'sha. Anan suke zaune har suka je la'asar suka dawo, da suka je sallar magriba ne Nayla ta ce baza su dawo ba sai sun fito daga ziyara. Didi sabon kuka ta fara Nayla na rarrashi a haka suka kammala suka dawo gida. Nayla ta so su fita yawo amma ya ?i ya ce ta gaji.

?iri-?iri ya hanata kwana a wajan Didi. ya tasa ta a gaba har Waki, ita kuma kunyar Didi take ji amma ya shafawa idanunsa toka ya ce sam bai san kunya ba. Haka ta dinga zuba masa shagwaSa tana sake haukata shi, basu fito ba sai cikin dare suka yi alwala gabaWayan su suka tafi masallaci.

Washe gari ma haka ne ya faru, da safe sun je ziyarar masijib ?uba, Uhud da sauran wajan ziyara. Da daddare Nayla ta ja Didi yawo suka tafi kasuwa. Ta dinga kai ta waje kala-kala basu dawo ba sai cikin dare sosai.
KRB3P094
Nana haleema

Narma tunda ta ga Omar ta tabbatar shine ta sake birkicewa, tafiyar da zasu yi ba kenan sai missing flight suka yi saboda zazzaSin da ya rufeta ruf dole suka dangana ga asibiti. Ruwan da aka saka mata ya sakata bacci, Mum da Dad suna tsaye a kanta suna kallonta sai da ta samu bacci sannan suka fito zuwa wajen Wakin.

Mum ta kalli Dad ta ce, "Haka zamu cigaba da barin Narma cikin wannan yanayi?." Dad ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Lamarinta ya dame ni sosai, da gaske take son shi ba wasa take yi ba." Mum ta ce, "kuma da gaske shine C.E.O Win company nan wai?." Dad ya Waga kai ya ce, "Shine."
"To daman ?arya yake yi a lokacin nan ba Wan daba bane?."
"Ba ?arya yake ba, shine."
"To ta ya zai samu wannan cigaban cikin sau?i haka? Ba shi da ilimin komai fa, taya ya kai wannan matakin a rayuwar shi?."

Dad ya ce, "Ban sani, amma abin ya bani mamaki. Wai Tiger da na sani wanda ko karatun secondary school bai gama ba shine ya kai wannan matakin, shine da wannan matsayin da ni da nake da matakin phd ban kai matsayin ba. He speak an English also, ta ya ya samu wannan cigaban within two years?." Mum ta ce, "to daman ?arya yake maka ya kai matakin da ya kai tun a baya, shiyasa yake dabancin mai tsari. Ni tsoro ma nake yi anya ba Dss ba ne?."

Dad ya kalli Mum ya ce, "ki yarda shine Tiger, a baya bashi da wani ilimi ko wani mataki na rayuwa. Ki dawo hankalinki mana."
"Dole na fita a hankalina, kana magana akan wanda China tayi signing contract da shi fa, kuma yanzu ana zancen shine Tiger wanda ya yiwa Narma asiri, ai dole na ruWe." Dad ya kalle ta ya ce, "Wallahi shine, shine wancan shine wannan."

Mum ta ce, "yanzu meye abin yi?."
"Daman can bashi da tsoro kuma baya tsoron magana, ya kalle ni ya ce shine zai bani appointment ba ni ne zan bashi ba."
"To ai ya kamata a san abinda za a yi kafin Narma ta rasa ranta." Dad ya kalle ta a nutse ya ce, "Kin amince ya aure ta kenan?."

Mum ta ce, "indai zai aure ta Win na amince mana."
"Rayuwarsa ta baya fa? Kar ki manta komai yana nan a rubuce."
"Waye zai tuna wani previous abu? ai present ake kallo yanzu a manta da wanda ya wuce.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login