Showing 327001 words to 330000 words out of 332344 words

Chapter 110 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

30877

sane har kallon ka ake yi, saboda ko baka san sa a fuska ba sunansa ya zaga duniya. Duk abinda ya taso a dangi musamman wanda basu da ?arfi wajan Omar ake zuwa, kuma yana yi baya gajiyawa, sai dai yau da gobe ta Wan adam.

Umma Saroot, Mama Zainab da Anty Aisha sun zama kamar sune iyayensa, duk wani alkhairi da ya samu baya mantawa dasu sai sun san ya samu. Zuwan su Saudia ta dalilinsa kam ba a cewa komai, haka kawai zai ce musu wani satin zasu tafi, har ta kai ta kawo ?a?ansu da jikokin su ma sun je ta dalilin Omar. Su a wajansu mutuwar Didi alkhairi ta zama a gare su, har a wajan Omar Win ta zama alkhairi, tunda gashi ta silar barinta duniya yake yin aikin alkhairin da lokacin baya baya yi.

Arzu?i ya zauna, albarka ta samu, cigaba ya samu, abinda ba a yi tunani zai faru ba ba ya faru domin. Omar ya zama fitattce a duniya, haka kamfaninsa ya zama mafi ?ololuwar daraja a Nigeria da wajen ta. Babu abinda yake cewa Allah sai godiya, yana kuma fatan Allah ya ji?an iyayensa da Didi Yayarsa. Mijin Didi har shi albarkar Omar bai bari ba, ba ma iya shi kaWai ba, har yayyen Marmerh da suka haWa uba Waya dasu alkhairisa bai tsallake su ba. A cikin shekarun Allah ya yiwa Hajja cikawa, an yi kuka rashi kuma an yi mata addu'a, dan Nayla ta sha kuka sosai, har ta so ta fi Salma shiga damuwa duk da Salma itace suka rayu tare.

Anyi bikin Jalila ?anwar Nayla, su Nayla an sha hidima a Kaduna, babu damar ta yi hoto sai dai ta ga yana yawo a social media ana rubuta Mrs Exclusive Footwear by Tiger. Nayla ta sake haihuwa ta haifi namiji, ta yi tunanin sunan Omar W???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?in za a saka kamar yadda Didi ta ce, amma sai ya ce a saka sunan mahaifinsa. Yaro ya ci suna Usman ana kiransa da Muhsin.

*****

? ?? Nayla tana zaune a falo, Marmerh da Musliha sun dawo daga makaranta tana koya musu assignment. Marmerh tana rubutu tana kuka saboda laifin da ta yiwa Nayla ta zane ta. Tsaki Nayla ta yi cikin faWa ta ce, "Allah Marmerh in baki daina kukan nan ba zan sake dukan ki, zan yi miki dukan da zaki yini kina kuka wallahi."

A lokacin Omar ya shigo da sallama, Nayla ta amsa tana kallon sa. Omar jin Marmerh tana kuka sai ya ce, "Marmerh lafiya ki ke kuka?." Jin tambayar da ya yi mata sai tashi a guje ta ri?e sa ta ce, "Daddy Mummy ce ta dake ni." Ya kalli Nayla kamar zai yi magana sai ya fasa, ya ?araso ya zauna yana share mata hawaye ya ce, "in kun gama ku je ku kwanta ku huta tunda babu islamiyya yau." Marmerh ta raSa ta wuce a tsorace kar Nayla ta sake dukanta, ta shiga Waki Musliha ma ta tashi tabi bayan yayarta. Ya kalli fuskarsa babu walwala Nayla ya ce, "Ina Mufty?."
"Bacci yake" ta bashi amsa a ta?aice.

Ya Wauki Muhsin da yake ta yi masa dariya yana mi?a masa hannu, ya Wan yi shiru na wani lokaci kafin ya kalle ta ya ce, "Jidda bana son duka na faWa miki ba tun yau ba, in zaki yi musu faWa ki yi amma ban da duka. Akan ne zaki daki Marmerh don Allah? Me yarinyar nan ta sani da zaki yi mata dukan da zata yi wannan kukan?. Gaskiya bana so, kar na sake ganin haka. Bana so naga suna kuka ko kaWan, bana so na gansu a damuwa balle su zubar da hawaye."

Nayla ta bisa da kallon mamaki ta ce, "laifi tayi min, shiyasa na dake ta."

"Har laifin me zata yi da zaki dake ta? Har wanne laifi Marmerh zata yi miki da zaki saka hannunki a jikinta?. Ki daki Marmerh ki ce kin daki me? Ko tausayinta baki ji ba, dukan yarinya kamar Marmerh kamar rashin tausayi ne. Kar ki sake dukan ta na maimaita miki. Ki yi mata faWan da ya kamata amma ba wai duka ba." Nayla bata ce komai ba jin ya fara magana cikin faWa ba kamar farko ba, tana tankawa birkice mata zai yi su yi kaca-kaca baza su kwana lafiya ba. Shiru ya sake ratsa tsakaninsu, cike da jin haushi ya kuma cewa, "kin yi na farko na share ban yi magana ba, kin yi na biyu ban nuna miki ba, kuma dan kinga ina yin shiru ko kunyar idanuna baki ji sai ki ka kuma yin na uku. Komai Marmerh, Marmerh, Marmerh? Ko wanne laifi ki ce Marhmerh, ko yaushe itace take yi miki abin duka sauran basa yi. Musliha ko Mufty basa yin laifin dukan ne sai ita?" Ya faWa cikin faWa sosai yana kallon ta.

Nayla ta Wago ido ta kalle sa suka haWa ido, ta girgiza kai tana binsa da kallo mamaki da ba?in ciki fuskarta babu walwala ko kaWan, Sacin rai ya mamaye fuskarta gabaWaya ta ce, "Ohhh kana faWa min bana dukan wanWanda na haifa sai wacce bani na haifa ko?." Shiru ya yi bai amsa ba yana kallon ta, Nayla ta ce, "ashe akwai ranar da zaka ce ina nuna banbanci tsakanin su? Ashe akwai ranar da zaka nuna min na fifita ?a?an da na haifa akan Marmerh? Ashe akwai ranar da zaka ce indai aka yi laifi Marmerh nake cewa tayi saboda ba ni na haifeta ba?. Ashe daman kallon da ka ke yi min kenan, kallona ka ke yi matsayin wacce take nuna banbanci a tsakanin su ko?."

"Kinga Jidda, ni ba haka nake nufi ba, kar yi deflecting maganta. Ina...." Ta katse sa a fusace cikin Sacin rai ta ce, "oh deflecting maganarka ma nayi kenan ko? Cewa ka yi meyasa ko yaushe ita nake duka bana dukan sauran, cewa kayi ko yaushe ita nake cewa tayi min laifi bana cewa sauran sun yi min. Kana nufin ina banbanta Marmerh da ?a?ana, ina zaluntarta tunda ba ni na haifeta ba. Kai tsaye kace min bana tausayin ta, daman ta ya za a yi na ji tausayinta tunda ban ji zafi a lokacin haihuwarta ba?......" ta Wan girgiza kai ta ce, "Haka ka ke nufi, haka maganar ka take nufi babu zancen deflecting" ta faWa tana kallon sa cikin Sacin ran da taji yana mamaye mata zuciyarta.


Zai sake magana ta hana sa, cikin murya mai sauti dake nuna Sacin ran da take ciki ta ce, "Ka kyauta, na gode sa sakamakon da na samu daga gare ka. Amma ina so ka san abu Waya, wallahi Indai baza a saka Marmerh kuka ba, indai duk duk abinda tayi sai dai a ?yale a zuba mata ido saboda tsoron kar ta yi kuka zaka lalata mata tarbiyya, zata tashi babu kwaSa babu wanda zai faWa mata ta ji. Al?awarin da ka yiwa mahaifinta akan zaka bata tarbiyya zai bi rariya, sannan Didi baza ta yi alfahari da ri?eta da ka yi ba wallahi."

"Nima na tashi babu uwa, yadda ake tsawatar min ana saka ni kuka ya saka na tashi da tarbiyyar da har nake bawa ?a?ana irinta a yanzu. Indai a haka rayuwar Marmerh zata tafi nan gaba zaka yi danasani, domin har kai Win baza ka taSa iya sarrafata ba wallahi. Ice tun yana Wanye ake tan?wara sa, in ya bushe sai dai a saka gatari a sara sa bazai taSa tan?waruwa ba. Kuma ka yi ha?uri, ni na Wauka ina ri?e Marmerh daidai da yadda nake ri?e Musliha, na Wauka itama kamar ?ata take zan iya yi mata hukuncin da nake so, hukuncin da nake ganin shine zai taimaki tarbiyyarta yanzu da nan gaba. Ashe ba haka abin yake ba, ashe ita daban su Musliha daban. Na Wauka yadda take ce min Mummy na zama mahaifiyarta, tunda yanzu ni ta sani matsayin uwa a gareta. Amma tunda kana ganin ina nuna banbanci a tsakaninsu ka yi ha?uri, bazan sake yi mata faWa ba balle har na daketa ta zubar da hawayen da zaka ji zafin zubarsu a zuciyarka. Tunda baka so na daina in sha Allah, zan yiwa ?a?ana dana haifa hukuncin da nake so, tunda su ni na haifesu ko a wuta na saka su na ?ona kowa ya san nawa ne, ni na sha wahalar haihuwarsu ba wani ba, babu wandai tuhume akan meyasa nayi hakan. Ita kuma tunda ?ar Yayarka ce ba Yayata ba bazan sake yin abinda zai sakata kuka ba, faWa akan tayi ba daidai ba bazan sake yi mata ba balle har tayi kuka, in sha Allah bazan kuma ba" tana gama faWar haka ta tashi ta bar masa wajan ranta a Sace sosai.

Omar ya bita da kallo har ta Sace, sai zuciyarsa ta karye ya ji babu daWi ko kaWan, shi ba da wani abun ya faWa ba wallahi, itace ta fassara zuwa haka. Ta ya zai ce tana nuna banbanci bayan sai ta hana Musliha abu ta bawa Marmerh? Ai bai yi mata adalci ba, kuma sai Allah ya tsayar dasu ya saka mata indai har ya ce tana nuna banbanci. Duk wanda ya tambaye ta cewa take ?a?anta huWu duk ita ta haife su, bata taSa cire Marmerh cikin ?a?anta ba, in ta faWa kuma yarda ake yi saboda Marmerh da Didi take kama, Didi kuma jinin Omar ce. Ajiyar zuciya ya yi cikin rashin jin daWi, daga yadda take magana ya san ta fusata sosai. Ya mi?e a sanyaye ri?e da Muhsin ya fita daga falon. Bai shiga inda take ba dan yana so ta huce sai ya bata ha?uri, dan yaga ta yi fushi.

Nana Haleemad'?d'?d'?
09030398006.
P131

Sai gab da lokacin sallar magrib ya shiga kitchen ya same ta a tsaye tana aiki, ya jima a tsaye a bayanta yana kallon ta zuciyarsa babu daWi akan abinda ya yi mata. Ya sauke ajiyar zuciya ?arasa inda take a sanyaye ya ce, "Ashiq!." Juyowa tayi ta kalle sa taga yana takowa inda take. Gefenta ta kalla sai ta Wauke kai ta cigaba da abinda take yi. Omar ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya ce, "i'm sorry Jidda." Matsowa yake inda take a hankali yana taku kamar mai sanWa. Ganin ya kusa tarar da ita sai ta Wauki wu?ar da take gefenta ta nuna sa ta ce, "kar ka matso kusa dani, ka ja baya kar ka zo inda nake."

Omar ya zuba mata ido yana kallon ta yana cigaba da matsawa kusa da ita a hankali bai dakata ba. Nayla rai a Sace take nuna sa da wu?a ta ce, "kar ka zo inda nake, kar ka sake ka ?araso, wallahi in kazo inda nake zan yanke ka da wu?ar nan." Omar ya Waga hannu sama alamun surrender, Calmly ya ce, "Indai abinda ki ke so kenan ki yi Jidda, indai shigar wu?ar nan jikina ki ke da bu?ata ki aikata kawai indai zaki huce" ya faWa yana matsowa kusa da ita sosai. Idonta yana rufe suke gam, da gaske bata son ganin fuskarsa ko kaWan, muryar tasa ma a dole take shiga kunnenta ba dan tana so ba. Baya take yi yana matsowa har ta kai ?arshe ta jingina da cabinet, har lokacin bata daina nuna sa da wu?a ba ta ce, "Ka daina matsowa inda nake, wallahi soke ka. Ka bar kitchen Win nan, ka fita bana son ganinka!."

Omar ya wara idanu ya ce, "bakya son ganina Jidda?..." sai kuma ya ce, "Ni kuma Ina son ganinki Jiddana, ki soke ni kawai indai zaki wuce ki yi, kin ji!" Ya faWa a tausashe yana kallon fuskarta da idanunta suke a rufe. Ganin ta kasa yin komai sai idanunta da suke a rufe gam, sai ya kai hannu zai ri?e ta firgita ta kamar wacce wuta zata taSa ta ce, "kar ka taSa ni, kar hannunka yazo jikina."

Hannu biyu ya sake Wagawa sama yana kallonta ya ce, "bazan taSa ki ba, kin ga hannuna yana sama."
"Ka fita daga wajan nan bana son jin muryarka, bana so na buWe idona na ganka, kar hannunka yazo inda nake, bana so ka taSa ni, don Allah ka fita."
"Ba taSa ki zanyi ba Ashiq, tunda bakya so bazan taSa ki ba" ya furta a cikin sanyi yana kallonta.

Nayla ta fashe da kuka mai sauti, ya Wan yi ?aramin tsaki cikin sigar rarrashi da kwantar da murya ya ce, "kin ce in na matso kusa dake sai kin soke ni da wu?a, kin ce bakya so na taSa ki, kuma gashi kina kuka. Ta ya zan iya jure wannan uhum! Ta ya zan iya jure ina tsaye kina kuka Jidda?. Dole na taSa ki Ashiq, i'm sorry, bazan iya ganin kina kuka na ?yaleki ba. In caka min wu?ar zai saka ki huce ki yi Ashiq....." ya faWa yana saka hannunsa guda Waya ya zaga dashi ?ugunta, ya jawota jikinsa da ?arfi ya haWa jikinsu waje Waya

Kiciniyar ?wace kanta take yi ya hanata saboda ri?eta da ya yi, ya zare wu?ar hannunta ya ajjiye ya matse ta sosai a jikinsa ta yarda baza ta iya ?watar kanta ba. Ya kai bakinsa kusa da kunnenta yana sauke mata numfashia hankali, kafin ya ziea harshensa a kunneta ya Wan juya kaWan, sannan ya yiwa kunnen kiss kana ya ce, "I'm sorry, i'm sorry Ashiq, bazan sake ba, ki yafe min ba haka nake nufi ba. Ki yi ha?uri jidda, ki yi ha?uri Ashiq!" Ya faWa cikin salon rarrashi yana sake matseta a jikinsa sosai.

Kuka take yi sosai a ?irjinsa cikin zafin kalamansa, tunawa da kalamansa a kanta sai ta cigaba da son ?wace jikinta shi kuma ya ?i bata wannan damar. Cikin kuka mai ?arfi ta ce, "Ka sake ni, ka sake ni!."
"A'a bazan iya ba, ina son na jiki a jikina! Ina so ki zubar da hawayen da na zama silar zubarsu a ?irjina. I'm sorry, bazan sake faWar abinda nace ba, ki yi ha?uri Jidda" ya faWa yana Wan sassauta ri?on da ya yi mata.
"Ni bana so! Ka cika ni!" Ta faWa da ?arfi tana ?wance jikinta daga nasa tana harararsa.

Omar ganin hararar da take aiko masa sai ya sake motsawa zai kamo ta ya ce, "Jid..." ai kafin ya ?arasa ta fita daga kitchen Win tana kuka ta barsa a wajan a tsaye. Kai ya dafe cikin rashin mafita, gabaWaya nadamar kalamansa ta kama sa, shi bai faWa da wata manufa ba ko kaWan, Allah yana gani ba da wannan manufar ya yi maganar ba itace ta canja mata ma'ana. Ajiyar zuciya ya yi ya fita jin ana kiran sallar magrib dan ya je ya yi sallah.

Da daddare bayan sallah i'sha suna zaune a dining room kamar ko yaushe suna cin abinci, bayan an gama Nayla ta ta saka aka yi azkhar kamar yadda suka saba, duk da ?arfin yin ita da Marmerh ne sai Musliha da take Wan taya su. Aka gama aka shafa ta ce a tafi Waki aje a kwanta Sai da ta kai su har Wakinsu ta kwantar da Marmerh da Musliha akan gadonsu da yake gefe ko wacce da na ta. Ta kwantar da Mufty akan nasa, dan bai yi girman da za a ware masa Waki ba. Tayi musu addu'a sannan tayi pecking Winsu a kumatu. Ko wacce ta maimaita abinda Nayla tayi musu sannan suka, "Good night Mummy." Ta kashe hasken Wakin ta fita zuwa Wakinta.

Muhsin ta Wauka da yake ta dariya, ta yi dariya tana jan hancinsa ta ce, "kai dai akwai arhar dariya." Zaunar dashi tayi akan gado, ya fara rararafe. Ita kuma ta shiga wanka bata jima ba ta fito, ta canja kaya zuwa nightwear ta zauna tana danna waya. Dan fushi take da mai gidan balle ta je inda yake. Diaper ta canjawa Mushin, ta canja masa kaya ta kwantar dashi tana yi masa wasa yana dariya tana dariya itama.

BuWe ?ofar aka yi aka Wauko, sai ta Wauka su Marmerh ne ta Wago tana cewa, "Marmerh baki yi....." ganin baban Marmerh sai ta yi shiru bata ?arasa ba, ya kulle ?ofa ya tako zuwa inda take ya zauna a gefenta.

?aukar Wanta ta yi ta ri?e a hannunta, shi kuma yana so gudu wajan babansa. Shiru ya tsara tsakaninsu na wani lokacin. Omar ne yayi breaking silence Win ya ce, "I'm sorry Jidda, ban faWi abinda na faWa da wata manufa ba, ke kika fassarata a haka amma ba haka nake nufi ba Jidda. Har abada bazan taSa cewa kina nuna banbanci a tsakanunsu ba, ke uwa ce a gare su gaba da baya, ke mahaifiyarsu ce dukkan su Jidda. Ki yi ha?uri, na ga ranki ya Saci har kina cewa zaki yanke ni."

Nayla ta yi ajiyar zuciya ta share sa bata ce komai ba. Omar jin ta yi shiru sai ya ce, "Jidda!." Nan ma ta share shi bata ce komai ba sai kallom hannunta da take yi. Calmly ya ce, "Jidda please!."

Nayla ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Dole raina ya Saci ai, ni ina ganin na ri?e Marmerh daidai da Musliha ashe kai kana ganin banbanci nake nunawa. In na cutar da Marmerh wacce riba zan samu? Kuma na faWa maka ko ba auren ka nake ba ni mai ri?ewa Didi Marmerh ce. Amma kai ganin ka ke ita nake duka bana dukan sauran, kace bana tausayinta, zaluntar ta nake yi. Baka san me ta yi ba kawai ka yanke min hukunci.."

Ya wara idonu waje ya ce, "Ni Jidda? Yaushe nace kina zaluntar ta Jidda? Yaushe nace bakya jin tausayinta?." Ta kalli idanunsa yadda suke a waje sosai ya saka ta Wauke kai daga kallonsa ta ce, "in ranka ya Saci daman kana faWar maganar da baka san ka faWa ba ai."

Ya ri?e hannunta guda Waya ya ce, "Shikenan naji, duk da na san ban faWa ba amma ki yi ha?uri, na karSi laifin duk da ba haka nake nufi ba amma ki yafe min." Nayla ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Allah na ji haushin kalaman ka sosai, raina ya Saci matu?a, na ji a raina ban kai wani matsayi a wajanka ba, tunda har ka ke


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login