Showing 6001 words to 9000 words out of 332344 words

Chapter 3 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14367

kwana kawai?. Didi ta ce,  a a Jidda, mijin ki zai yi mamakin ganin amarya a tare dake. Masalaha kawai ta bi ni Win muje ta kwana, ba a barta ta kwana ita kaWai ba ko?.

Salma ta girgiza kaita ce,  gaskiya Omar bai kyauta mana ba Didi, ki yi ha?uri da abinda zance. Omar ya daina ganin kamar sadaka aka bashi Nayla, Allah na tuba ba dan wannan abin da ya faru ba wallahi Nayla ba sa ar aurensa bace, Nayla matar manya ce ba ta ?ananu ba wallahi. To ?addara ta riga fata, da kuma sharrin so.

Didi tayi ajiyar zuciya ta ce,  na sani Salma, na sani ki daina bani ha?uri gaskiya ki ka faWa ai ba ?arya ki ka yi ba. In ba dan sharrin soyayya ba ina Nayla Ina Omar? Ba tsarar aurensa bace, tazarar su na da matu?ar yawa.

 Nayla Win ce ya kamata ace tana wannan abinda yake yi ba sai shi. Gaskiya ni haushinsa nake ji wallahi, meyasa bazai karSi ?addara a yadda tazo ba? Ita Nayla ba ?addarar ta ?arba ba har take zaune a gidan nan? Salma ta faWa a Wan fusace dan haushin Omar take ji sosai.

Jidda ta ce,  duk ba wannan ba, meye mafita?.
Didi ta ce,  Ku lallaSata tazo mu je gidana mu kwana, ni kuma zan saka Omar ya dawo gidan nan gobe in sha Allah. Salma ta ce,  Didi babu tabbacin dawowarsa.
 Gaskiya babu tabbas Salma, za a kai ruwa rana dashi a wajan dawowa gidan nan, musamman in ya san daga hannun waye gidan nan ya fito. Amma zan yi maganinsa, zai zo in sha Allah.

Salma ta ce,  Ku je kawai ni zan kwana nan, zan faWawa Hajja bata da lafiya ne shiyasa akace na kwana saboda zan saka mata ruwa. Daman kamar na san hakan zai faru na ce Mima ta kwana a gidan Hajja, dan haka ba wata damuwa.

Didi ta ce,  kina ganin hakan ya yi?.
 Ya yi Didi, kar ki damu. Kema duk ya saka ki a damuwa da zullumi da fargaba. Didi ta ce,  Hmmm bari kawai Salma, b??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????aza ki gane ba kawai, amma ni kaWai na san waye Omar. Amma in sha Allah silar wannan auren shine silar canjin halayyarsa. Ina so ya so Nayla fiye da komai a duniya, ita kuma duk wannan hawayen da yake sakata a lokacin nake so ta fanshe.

Suka yi dariya Jidda ta ce,  Wallahi nima Didi Ina ji a raina auren nan nasu ba mai mutuwa bane, haka Allah ya ?addarar zuwansa shiyasa hakan ya faru. Amma dai zama da Omar Win ne sai an shirya.

Didi ta murmusa ta ce,  Allah ya sa hakan, in hakan ya tabbata ba wani shirin da zata yi, a hankali zata mayar dashi yafi ruwa sanyi. Suka amsa da amin suka fito ita da Jidda. A harabar gidan suka tsaya Didi ta ce,  Salma kwana ku biyu babu hatsari?. Salma ta ce,  unguwar su Tiger ce fa, kuma matar tiger Win ce a gidan kar ki manta.

 Amma waye ya san ita matarsa ce? Ko na yiwa su Bashir magana wani yazo yana zagawa?. Salma ta ce,  kar ki damu, babu abinda zai faru in sha Allah. Didi ta amsa suka fita ta shiga motar AbdulHamid, Jidda ta shiga ta mijinta suka bar cikin unguwar.
KRB3P003
Arewabooks@nanahaleema11.

Salma a sanyaye ta koma bayan ta rufe gidan yadda ya kamata, tana shiga falon ta kulle falon ta shiga bedroom Win da Nayla ta shiga ta kwanta. Tana shiga Nayla ta Wago kai ta kalle ta ta ce,  Baki wuce ba?. Salma ta zauna ta ce,  a na zan Kwana ai.
 Hajjan fa?.
 Na tura Mima ta faWa tana zare Wankwalin kanta.

Nayla tayi ajiyar zuciya tare sa lumshe idanunta. Gata daina gidan wanda take matu?ar so take kuma ?aunar rayuwar dashi a matsayin matarsa amma shi baya nan yana wani wajan daban, sai an lallaSa shi ma sannan zai iya zuwa gidan. Meye amfanin ma son da take yi masa oho, gashi duk wannan abubuwan da suke faruwa bata jinta daina sonsa, sai dai wani lokaci tashin hankali ya kansa ta ji komai ya fita daga ranta amma da ta nutsu soyayya sa zata motsa.

 Nayla ki samu ki yi bacci, ko zaki ci abinci?. Nayla ta girgiza kai alamun a a kana ta ce,  a ?oshe nake Salma, bacci nake so yazo ya ?i zuwa gabaWaya. Salma ta ce,  zai zo in sha Allah. Wutar solar ce a gidan nan ko nepa?. Nayla bata amsa ba ita kuma fita dan ta duba. Tunani kala-kala Nayla tayi shi kafin bacci ya Wauketa saboda kanta da ya yi mugun nauyi bata san lokacin da tayi bacci ba.

Washe gari bata farka ba sai sha biyu na rana, ta buWe ido ta ganta a sabon gida ba gidansu ko gidan Hajja ba. Ajiyar zuciya tayi ta mi?e zaune a lokacin Salma ta shigo ta ce,  Mrs Omar kin tashi? Ga ruwan wanka can mai zafi na juye miki a boket sai ki je ki yi wanka. Kin san gidan babu water heater, babu bathtub, babu shower glass sai dai bokitin. Kuma Mama ta yi ?o?ari har bokiti an ajjiye miki a ciki.

Nayla ta kalle ta itama ita take kallo, Salma ta ce,  ki tashi ki yi wanka zaki fi jin daWi, kayan ki na saka miki a wardrobe in an kawo sauran daga Kaduna sai ki ?arasa sakawa dan wannan basu da yawa gaskiya. Akwai Sabon brush da toothpaste suna ciki duk na ajjiye miki. Kai ta girgiza ta mi?e tsaye ta saka slippers Win da yake bakin toilet Win akan doormate ta shiga.

Sabo da irin toilet Win gidansu masu shegen girma sai ta ga wannan Wan ?arami, duk da bashi da ?an?anta, yana da girma amma a idonta ?arami ne sosai. Har towels da bathrobes akwai a ciki, ga washing machine babba a gefe, an yi ?aramin bathroom cabinet me kyau a gefe an jera mata towels, bathrobes, showerl gels, soaps, shampoos da sauran kayan banWaki. Harda ?aramar hand dryer a ajjjiye a gefe.

Abin ya bata mamaki ganin shower gel Win da take wanka dashi a banWakin, bata tsaya godon tunani ba tayi wanka tare da alwala ta fito. Lokacin Salma ta sake shigowa Wakin Nayla ta kalle ta ta ce,  Salma na ga shower gel Wina, waye ya siyo?.

Salma ta ce,  ni ce na shiga sahad kafin ki tashi, bana so ki nemi komai ki rasa har ki ji babu daWi a zuciyarki shiyasa na siyo komai na amfani. Har pad na siyo miki na ajjiye saboda ko amfaninta zai tashi kusa. Murmushi Nayla ta yi ta ce,  na gode masoyiya. Murmushi itama tayi ta ce,  bathroom Win naki mai kyau wallahi, ya burge ni, kin san ina son bathroom mai komai fari. Matsalar kawai babu water heater, amma akwwi tank ina jin gidan akwai borhal, in kika kunna shower ruwan sanyi ne zai antayo.

Nayla bata ce komai ba sai murmushi da tayi, Salma ta ce,  Yanzu dai ki shirya ki yi sallah ga abinci.
 To ta furta a ta?aice tare da zama tana kallon Wakin.

Kai da ganin furniture Win Wakin ka san masu tsada ne, sai Waukar ido suke yi kasancewar su sababbi. ?akin yana da madaidaicin girma dan ya cinye komai kuma bai matse ba ya yi yadda ake so, ga kuma center carpet a tsakiyar Wakin a Wora ?aramin table a kai wanda aka yi masa ado a kai. Daga can ?arshen Wakin akwai ?aramar cousion guda Waya wacce take kusa da carpet Win da aka ajjiye. Ga cabinet na ajjiye takalmi da jaka a gefe.

Duk ta san tsarin Mama ne wanann, amma tayi matu?ar mamaki da aka iya tsara komai a cikin kwana biyu kamar an jima ana shiryawa hakan. Wardrobe Win ta kalla ta ganta a gefe mai ?aton mudubi a jikinta. Saman Wakin ta kalla ta ga fanka ce gata nan tana ta aiki har lokacin bata Wauke ba. Salma da take tsaye tana kallonta ta ce,  gidanki ya yi kyau ma sha Allah, ki gama sai mu fita har gate ki gani.

Mai ta shafa wanda ta san shima Salma ce ta siyo ta shirya cikin atampa Winkin da saba ko yauahe, ko bubu ko Tbubu ko kuma Ashape.

Ashape ce wannan ta yi mata kyau duk da bata cikin walwala ko kaWan. Sabon hijjab ta gani sai ta kalli Salma ta ce,  ke wai har nawa ki ka kashe a wannan siyayyar? Naga sabon hijjab.
Salma tayi dariya ta ce,  Ga sabuwar sallaya nan ma, ki yi sallah ki zo mu je falo ki ci abinci. Amsawa tayi ta tashi tayi sallah ta idar sannan suka fita falon.

Sai yanzu take kallon falon, shima ya yi kyau cikin kujeru milk da adon golden a jikin su, labulayen ma milk colour ne. Hatta dining table Win irin kujerun falon ne, ga turkish carpet a shinfiWe komai dai ya yi kyau gwanin sha awa.

Salma ta kawo mata tea da ta dafa ta ajjiye ta ce,  sauran abincin daga gidan Hajja aka kawo, gashi nan sai ki ci ta faWa tana ajjiye mata ita kuma har lokacin kallon falon take yi.

Salma ta ce,  falon ya yi kyau sosai Nayla, gashi babba ma sha Allah. ?aramin nan na ciki wanda muka zauna jiya shima yayi kyau amma wannan yafi kyau. Naga daga wajen ?ofar falon harda public toilet. Yanzu kenan wannan shine Wakin Omar Win? Ta faWa tana nuna wata ?ofa da take hanyar da zata kai ka ?aramin falon.

Sai da gaban Nayla ya faWi jin ta ce Wakin Omar, kafin tayi magana Salma tami?e ta ce,  bara na shiga na gani, dan wata?ila iya yau Win nake dashi, gwara na shiga na gani kafin ya fara kwana a ciki ta faWa tana wucewa. Ita kanta Nayla sai ta ji tana so ta ga ya Wakin ya ke amma bata motsa ba.

Ganin fitowar Salma ta yi tana cewa,  Nayla ai har yafi wanda muka kwana a cikin girma, kuma shi funiture Win ciki irin komai na wannan falon nan ne, kenan set Waya ne da kayan falon. Toilet Win ma yafi naki girma, kuma naga harda water heater a ciki, akwai shower glass sannan shima da washing machine. Su Omar an samu banza ta faWa tana ?ar dariya tana kallon Nayla. Nayla dai bata yi magana ba, amma tana tunanin kenan dai gidan two falo ne kuma two bedrooms. ?aya bedroom Win a falon farko Waya kuma a falo na biyu.

Tea Win ta shanye tas, Salma ta bata magani ta sha ta zauna tana ta jan ta da hira wai dan ta sake. Buga gate Win ake yi hakan ya saka Salma fita dan ta buWe, tare suka dawo da Jidda ta shigo tana cewa,  Gaskiya ne, wannan khamshi haka? Lallai gidan amarya ne wannan ta faWa da fara a tana ?arasowa.

Nayla ta kalle ta ta ce,  Twiny baza ki daina yawo ba ko? Kina ta wahalar mana da Babyn mu. Jidda ta zauna ta ce,  Shima ya san na yi busy ai. Ya jiki?.
 na samu sau?i sosai, ko ciwon kan babu.
 Har na ji daWi wallahi, daman da ke na kwana a raina. Salma gidan nan fa ya yi kyau wallahi, na lura kuma har da solar ko? Ta faWa tana kallon Salma.

Salma ta ce,  solar ce, kuma har fridge za a iya Wora mata. Yanzu nake maganar gidan nima, na ce wallahi ya yi kyau daidai zaman mutum Waya.
 Amma na so three bedrooms ne ba two ba, two ya yi kaWan ai.
 To ita da waye? Daga ita sai shinfa. Jidda ta kalli Nayla da bata ce komai ba ta ce,  ga kayan kitchen Win ki can na kawo miki suna mota, na gaji da ajiya, yau Allah ya yi zan kawo miki kayan ki.

Ta kalli Salma ta ce,  Lokacin bikina da muka je siyayya duk abinda ya yi mata sai ta Wauka ta ce ta siya na ajjiye mata. Haka ta saka ni ajiyar kaya kamar yar cirani, yanzu gasu can a mota na kawo mata, lokacin amfanin su ya yi. Nayla ta Wan yi murmushi kawai amma bata ce komai ba.

Jidda kallon Nayla tayi cikin tausayi, in ban da ikon Allah gida mai falo biyu da bedrooms biyu ai Nayla ta fi ?arfinsa, irin sa Abiy yake bawa ma aikatan gidan sa in zasu yi wani, wani ma yafi wanda take ciki kyau da girma. Da Allah ya tashi ikonsa sai ga Nayla a gida irin wannan, ko a mafarki ta san bata yi tunanin hakan zai faru ba. Lokacin da aka kai Jidda gidanta Nayla cewa tayi ita gidan yayi mata kaWan, duk da sama da ?asa ne babban gida iya ganinka amma Nayla tace ita nata sai ya ninka haka. Da yake baka canjawa kanka ?addara ga inda Allah ya kawo Nayla matsayin gidan aure.

Salma ce ta mi?e jin ana sake buga gidan ta fita, jim kaWan suka dawo Mama da Jalila da kuma Jalil harda Jawad.

Nayla ganin su ya saka ta mi?e da sauri ta ?arasa jikin Mama ta rungumeta. Mama tana murmushi ta ce,  Kar dai ki yi min kuka amarya. Nayla ta fara goge ido ta kalli Jawad da yake kallonta yana murmushi ta ce,  Ya J sannu da zuwa.
 Yauwa Nayla amarya ya faWa da tsokana yana kallonta.

Zama suka yi duk aka gaisa, Mama ta kalli Nayla da take hawaye ta ce,  da na san kuka zaki yi Allah da bamu zo ba. Nayla ta goge ido bata ce komai ba. Jawad ya kalle ta ya ce,  Inyee amarya, wannan gida mai kyau haka.

Murmushi tayi kaWan ya sake cewa,  kar ki damu ki kwantar da hankalinki, komai zai wuce ya zama tarihi in sha Allah. Ni a zuciyata ma ji nake na amince da wannan auren naki, dan ina so ki saka ni a tsagin masu goyan bayanki, nima na shigo team Win Omar and Nayla forever& . Dariya ya bawa Nayla ta yi dariya tana kallonsa.

Yayi murmushi ya ce,  Wallahi da gaske nake miki Nayla, dan haka kar ki bar komai ya dame ki, komai zai wuce kamar bai faru ba. In na koma gida zan saka a kawo miki motarki, na kuma yi al?awarin sabuwar mota za a kawo miki Kano ba wacce kika bari a gida ba. Sannan batun transfer na wajan aikinki mun fara maganar yadda za a yi, zaki cigaba da aikin ki kamar kina Kaduna.

Murmushi tayi cikin jin daWin ganinsa ta ce,  To Yaya J. Na gode sosai.
 Kar ki damu. In akwai zaSin motar da ki ke so ki faWa min sai a siya miki ita. Jidda ta ce,  lallai Yaya J ni fa?. Harararta ya yi ya ce,  motar da ki ke hawa tafi tawa tsada, ai ke mijinki ya shagwaSaki, kinfi ?arfina yanzu. Dariya tayi ta ce,  ta sa daban ta ka daban. Murmushi ya yi bai ce komai ba sai kallon Nayla yake yi cikin tausayinta.

Mama ta ri?e hannunta ta ce,  ta so mu je Waki. Nayla ta bi bayan Mama har Waki ta zaunar da ita akan gado ta ce,  komai na gidan ya yi miki?. Kai ta Waga alamun eh Mama ta ce,  in akwai abinda bai yi miki ba ki faWa min sai a siyo a aiko miki dashi. Turaren wuta duk an saka miki na wajan wacce muke siya Win nan daga Sudan. Spices da komai akwai a kitchen dan akwai kayan abinci da aka kawo duk suna store.
 To Mama ta amsa a sanyaye.

 Zuwa jibi Baba Salisu zai kawo miki ragowar kayanki da abinda na san zaki amfani dashi a Wakin ki. In akwai abinda ki ke so shima sai ki faWa min. Kai ta Waga kawai Mama ta sake cewa,  kar ki damu kin ji? kar ki dinga ajjiye damuwa a ranki, duk abinda yake damunki ki sanar dani. Omar Win ya zo kuwa?.

Kai ta girgiza alamun bai zo bac Mama cikin damuwa ta ce,  ya Allah! Ke kaWai ki ka kwana a gidan nan?.
 Ni da Salma ta bata amsa hawaye na sakkowa daga idanunta. Mama ta ce,  duk abinda yake faruwa ki dinga sanar min dan ba komai zamu dinga jurewa mu zuba idanu ba, duk abinda ya faru ki sanar dani ni kuma zan san abinda zan yi. Nayla ta Waga kai dan magana wahala take mata. Mama ta ce,  kar fa ki ce zaki Soye min, in baki faWi damuwarki ba baza ki ji daWi ba.

Nayla ta ce,  to Mama. KuWi Mama ta ajjiye mata ta ce,  ga sadakin auren ki nan, sannan ga wannan ki ri?e a hannunki, zan haWo har Atm card Winki a kawo miki. Nayla ta ce,  To Mama, an gode.

Mama ta ce,  kina son housemaid a kawo miki daga Kaduna?. Nayla ta ce,  E Mama.
 To zan duba na gani, ko Khajida ce jikar Uwani ta gida wacce take yiwa Abiy ?osan sadaka sai a kawo miki, naga kuna shiri da yarinyar. Sai dai babu Wakin da za a ajjiyeta. Nayla bata ce komai ba Mama ta ce,  zan san yadda zanyi dai.

Mama ta ?arewa Wakin kallo tana taSe baki ta ce,  zaki sha zafi, naga gabaWaya gidan babu ac, iskar fanka me take sakawa banda mura da ciwon kunne?. Har gwara ma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login