Showing 60001 words to 63000 words out of 332344 words

Chapter 21 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14428

?onawa ne. Dariya tayi ta kalle shi ta ce,  Daga tambaya?. Ya kalle ta fuska a cushe yama Waga gira ya ce,  Amsa na baki. Murmushi tayi ta ce,  na gode Omar, Allah ya saka da alkhairi ya sa ka fi haka. A iya laSSansa ya amsa da amin ta kalli Nayla ta ga sai murmushi take yi, ta kalle shi kamar zata yi magana sai ta fasa.

Didi waya ta Wauka tana dubawa kafin ta kalle shi ta ce,  wai wacce mace ku ka samu take yin video product Win ku ana posting ne? ?afarta ma sha Allah ana ta yabo kuma tana kawo muku customers da hakan. Omar ya kalle ta cikin ko in kula ya ce,  ni ban cika bibiya ba, ban sani ba gaskiya, na san aikin su Bashir ne. Nayla tayi shiru bata amsa ba dan ta san ko Didi bata san ?afarta ba ce ba.

Didi ta ce,  Hakan ya yi kyau, na ga a comments section ana yabon kyaun da takalman suke yi mata. TaSe baki ya yi bai ce komai ba dan bai damu da ya san wacece Win ba. Tashi yayi ya bar wajan, bayan ya bar wajan Nayla ta kalli Didi ta ce,  Didi in kuma hira kuna burge ni, sai naga kamar ba shine yake magana ba, sannan sai maganarsa ta dinga fita a hankali babu tsawa.

Didi tayi murmushi ta ce,  wallahi Omar ya saba dake sosai Nayla, kawai izzarsa ce ta saka ya kasa bada damar da zaku yi hira tare. Tunda har nake saka ki a maganar abinda ya shafe shi bai katse ni ba na tabbatar da kin shiga rayuwarsa. Ni har kishin ki ma naga yanayi yi, musamman da nake zancen samarin ki.

Nayla ta ce,  Hmmm Didi babu wani kishi fa, kawai hirata ce baya.
Didi ta ce,  au haka ne? Shikenan zamu gani. Nayla murmushi take yi ko babu komai yau ya ci abincinta, kuma ya zauna ana yi hira dashi duk da ba da ita yake hirar ba.

Yinin ranar yayi mata daWi saboda Didi, duk da tunda ya fita bai dawo ba amma ta ji daWi a zuciyata ita kaWai tai ta murmushi. Da daddare Nayla ta tambayi abinda za a dafa Didi ta ce ta bari akwai ba sai ta yi girki ba bata jin yunwa tasha fruit. Bayan sallar i sha suna zaune suna kallon tv Didi tana shan kankana ya shigo da sallama.

Suka amsa a tare ya kalli Didi da kulawa ya ce,  kina lafiya?. Ta ce,  me ka gani?.
 Kin canja ya bata amsa yana kafe ta da ido.
 Qalau nake. Bai sake cewa komai ba ya wuce ta ce,  ka dawo zamu yi magana yanzu. Bai amsa mata ba aka fara tallan companyn sa da aka bayar. Didi ta kalli hotunan ?afart ta ce,  Hotunan nan suna yin kyau wallahi, ni ?afar yarinyar ce ma take burge ni.

Nayla ?asa-?asa ta ce,  Didi ni ce fa. Didi ta kalleta tana buWe ido ta ce,  da gaske?. Nayla ta ce,  Wallahi. Amma Bashir ne kawai ya sani shine ya ke kawo min sample Win da nake yin video.

Diid ta ce,  wai daman ke ki ke saka takalman ki yi video ayi posting?. Nayla tayi dariya ta ce,  Wallahi ni ce Didi, da yake ina da account Win na su a hannuna da kaina nake posting Win.
Didi ta ce,  ai kam ki dinga tofe ?afarki da lahaula, dan baki ga yadda ake yabon ?afarki ba, ki dinga shan maganin baki.
 Ina gani Didi, harda masu cewa su don Allah a basu number mai wannan ?afar. Didi ta yi dariya ta ce,  ba su san matar Boss ba ce.

Omar yana tsaye ya ji duk abinda suka ce, wayarsa da take aljihu ya Wauko ya shiga ig page Win nasu yana scrolling yana ganin hotuna da video ?afarta dan kusan kaf posting Win videos Win ne. Tsurawa ?afar ido ya yi yana kallo, ?afarta ta tayi haske sosai haka faratanta, sannan gata madaidaiciya mara tudu da tsaho. ?an yatsun ta a jere babu alamun koda jijiya a ?afa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????r sai zallar kyau da haske. Sosai ?afarta ta ke haska takalman matu?a, ko baka da niyar siya zaka tsaya ka kalla saboda kyaun da takalmin yake yiwa ?afarta.

Wani irin abu yake ji mai kama da Sacin rai yana mamaye ilahirin jikinsa da zuciyarsa, haka kawai ya ji ya damu kansa, hannu yana rawa ya danna comments section Win yana karantawa. _Kai ma sha Allah, wannna ?afa ba dai kyau ba. Ko wacce mai ?afar nan Ina matu?ar sonta, saboda ?afar nan zan siyi taklamin nan wallahi._ abinda ya gani kenan a rubuce, ya sake yin scrolling yana ganin irin su babu adadi. Cike da bugawar zuciya ya rufe ido ya buWe yana ji kamar ya je ya kwashe ta da mari.

Numfashi ya sauke ya tako ya ?araso falon ya kalli Nayla ya ce,  ba na hana ki shiga lamarina in ba ni na saka ki ba? Ba na ce ki daina yi min shishshigi akan abinda ya shafe ni ba!?. Da murya mai amo yake magana cikin tsananin Sacin rai. Didi ta ce,  Omar Lafiya? Me ya faru kuma?.

Ya nuna Nayla da yatsa ya ce,  duk ke kika jawo min, ke kika jawo yarinya ?arama kamar wannan ta raina ni har na ce ga abinda za ayi ta tsallake ta ta?i yi. Didi ta ce,  me ta yi ne Omar?.
 Na faWa mata babu ruwanta da shiga rayuwata, na faWa mata babu ruwanta da shiga abinda ya shafe ni meyasa take yi!?.

Ya ruWa Didi hakan ya saka ta ce,  ka faWa min abinda tayi maka Win mana. Ya haska mata fuskar wayarsa ya ce,  ni na saka ta wannan aikin? Na saka ta na ce ta dinga yi min tallan kaya da jikinta!?. Ya juyo ga Nayla a fusace ya ce,  Na saka ki!?. Nayla ta firgita sosai ta yi shiru bata ce komai ba.

Didi ta ce,  Haba Omar; kai fa mijinta ne tana yi dan taimakawa kasuwancin ka. Meye aibu dan ta yi maka talla?. ?asa ya yi da muryar sa amma a kausashe take ya ce,  to na ce ina so ne? Ko na ce mata Ina bu?atar ta aikata hakan?. Didi ta ce,  Dan ta yi hakan ai ba wani abun ba ne ba Omar, taimako ne& & . Tray Win da Didi take shan kankana ya cillar a ?asa ya rabe gida biyu ya ce,  To bana so! Bana so, na sake maimaita!. Kar a sake aikata abu ba tare da na sani ba, kar a sake shiga lamarina ba tare da na ce a shiga ba& . Ya juya ga Nayla ya ce,  Kar ki sake aikata wannan kuskuren, ina ja miki kunne a karo na ?arshe kenan, ki tsaya a iya matsayinki! Ya faWa idanunsa a waje har ja idanun ya yi.

Didi ta ce,  to ka yi ha?uri mana, amma dan an yi posting ai ba wani abun ba ne.
 A ganin ki kenan, amma a wajena wani abun ne, wani abu ne a wajena Didi. Na ce bana so a daina! Ya faWa hannunsa har rawa ya yake yi yana danna wayar yana kiram Bashir.

Bashir yana Wauka ya ce,  duk page Win da ka san ka yi posting wannan video da ake Wauka ba tare da na sani ba a goge, a goge yanzu babu Sata lokaci! Ya faWa yana sauke wayar a fusace tare da lumshe idanunsa cikin Sacin rai. Kai ya dafe yana yamutsa gashin kansa kafin ya shafa gashin fuskarsa yana furzar da iska mai zafi. Ya rasa abinda yake mu?ur?usar zuciyarsa har ya canja shi haka, zafi yake ji yana tasowa daga zuciyarsa yana ratsowa har fatar jikinsa.

Didi karantar yanayinsa take yi sai ta yi murmushi, zata iya rantsuwa babu kaffara Omar kishin Nayla yake yi, kishi kuma ba Wan Wan ba. A hankali ta ce,  Omar dan dai ka nace ne, amma meye laifi dan ta yi video ko hoto ta Wora? A ganina ai ba wani abun bane. Mata nawa ne suke yin hakan akwai abinda ya same su ne?. Kuma ta yi ne saboda a samu followers da masu siya kuma an samu.

Kallon Didi yake yi kawai ya ma rasa abinda zai ce mata jin abinda take cewa. Wai ta yi ne dan a samu masu siya, haka yace mata hana da bu?atar masu siya ne ta wannan hanyar?. Ido kawai ya zuba mata yana kallo kafin ya girgiza kai ya sauke ajiyar zuciya, ya sake kallon Didi yana cize baki ya ce,  ke ki ke zugata kenan ko? Ke ki ka saka take yin abinda ban sakata ba ko?. To na rantse da Allah na sake ganin makamanin hakan ke da ita baza ku kwana lafiya ba!. Zata iya kasuwanci da abinda mu ke yi ta siyar bai dame ni ba, amma wannan bana so!. In kuma aka sake& &  sai ya girgiza kai alamun ku guji abinda zai faru ba tare da ya ce komai ba, ya kalli Nayla da tayi tsuru-tsuru ya ce,  gargaWi na ?arshe! ya juya ya fita daga gidan gabaWaya.

Alhaji Omar kenan>?#?
KRB3P018
Arewabook@nanahaleema11.

Nayla tana tsaye tana hawaye, Didi ta ?araso kusa da ita ta rungume ta tana tapping bayanta alamun rarrashi. Nayla cikin kuka ta ce,  Didi yanzu meye laifin a nan? Ni da zuciya Waya na yi ba da wani abun ba. Amma naga ba yaso na dinga shiga lamarinsa, zan daina in sha Allah. Didi ta ce,  ki bar kuka, ki yi ha?uri.

Nayla ta Wago daga jikin Didi ta ce,  yanzu ba dan kina nan ba da ban san ya zan yi ba, nayi shiru ya ce nayi masa banza, na yi kuka ya ce dukana ya yi da nake masa kuka. Kuma ni naga haka masu siyar da irin wannan kayan suke yi, sai na ce nima bara na yi saboda na taimaka ba dan wani abun ba. Didi ni aurena dashi bana Waukarsa matsayin aure wallahi, Ina yi masa komai ne saboda yana matsayin ?aninki, zan iya yin komai dan ganin cigaban rayuwarsa. Didi shi na lura baya son haka, kawai baya sona shiyasa baya so na shiga lamarinsa.

Didi ta yi murmushi ta goge mata hawaye ta zaunar da ita akan kujera ta ce,  Ba haka bane ba Nayla. Tun farko na san ke kike yin wannan hotunan, Bashir ya faWa min da na tambaye shi, sai ya ce min kar na faWawa Boss kin ce bakya so ki sani. Ina sane na tayar da maganar har ki ka furta da kan ki, Ina so na ga reaction Win Omar. Tun farko ni na bashi wannan shawarar tun kafin auren ku, sai yake cemin ina za a samu macen da za a dinga hoto da ?afarta? Sai na ce masa gani ba sai nayi ba. Nayla hararata ya yi ya ce bazan yi ba, kin san meyasa ya ce baza a yi ba?.

Nayla ta girgiza kai alamun a a Didi ta ce,  Saboda Yayarsa ce ni yana kishin hakan a kaina. Ko da Omar yana da ?anwa na tabbatar bazai bari ta aikata hakan ba, dan shi mutum ne da baya so a raSi abinda yake so. Nayla in muka fita dashi wani ya tanka ni har mu dawo ransa a Sace yake, in na yi masa magana sai ya ce ban san me yake ji bane.

Nayla ta ce,  to laifi ne ni dan na yi kenan?. Didi ta ce,  ni fa Yayarsa ce Nayla, ya nuna baya so nayi saboda yana kishina. Ke kuma matarsa ce, me yanayin Omar ya nuna miki a yanzu don Allah?. Nayla ta ce,  ba yaso na shiga lamarinsa shine kawai.

Didi tayi dariya tana mamakin autancin da yake damun Nayla har da ta kasa ganin kishi a idanun Omar ta ce,  Nayla ba wannan ne a ran Omar ba, wallahi Omar kishinki ya ke yi, kishinki yake kishi mai tsanani ma kuwa!. Ki duba yadda ya fasa tray Win nan ta faWa tana nuna mata yadda tray Win ya tsage har gida biyar.

Damm ?irjin Nayla ya buga ta kalli Didi ta ce,  Didi Kishi fa ki ka ce?. Didi ta yi murmushi ta ce,  ?azu maganar samarinki ake yi ya nuna baya son ji, yanzu hotunan ?afarki ake Worawa ana talla da su ya hargitse har da fasa tray, Nayla in ba kishi ba meye?.
 Tsana ce mana Didi! Ta faWa kai tsaye dan ita bata yarda kishi ba ne ba.

Didi ta yi dariya sosai tana girgiza kai ta ce,  ashe kema irin sa ce, taurin kai gare ku. Yanzu baki yarda Omar kishinki yake yi ba?. Nayla ta ce,  wallahi ko kaWan ban ji hakan a zuciyata ba.

 Shikenan Nayla, zan tabbatar miki nan da lokaci kaWan. Amma daman Wora hotunan ?afarki ana talla dasu bai kamace ki ba, ke ai matar aure ce, ko ya wani yaga gani ya yabi ?afarki za a rubuta miki zunubi.
 Amma Didi da akace mace dukkanta al aura ce an ce banda fuska da tafukanta. Kinga babu ?afata a cikin al aura ko?.

 In ji? Wasu malaman sun ce hatta muryarki ma al aura ce. Ke fa ki ka ce min akwai wanda ya ce a bashi number ki saboda ?afarki ta yi masa, hakan ba zunubi ba ne ba kasancewar ki ta matar aure?. Nayla tayi shiru bata ce komai ba.

Didi ta ce,  Ko bai hana ba daman ina da niyar yi miki magana, ina sane ban yi maganar ba so nake ya magantu kamar yanzu kuma ya yi magana. Abu Waya nake so ki sani, babu wanda ya zauna da Omar ya san halin Omar kamar ni, zaki fi ni sanin halayensa amma ba yanzu ba sai nan gaba, kafin ki zo karatun nake Wora ki a kai yadda kafin ya riske ki kin haddace. Nayla inda Omar bai damu dake ba hankalin sa bazai tashi haka ba, sai ya ji abu a cikin zuciyarsa yake hargitsewa haka, abinda bai kai ya kawo ba baya damunsa har kiga fushinsa kamar wannan. Amma da zarar abin ya ratsa zuciyarsa nan take zai bayyana akan fuskarsa, baya taSa tayar da hankali akan abinda bai shiga zuciyarsa ba. In zaki tuna Wazu da na fara tambyarsa cewa ya yi bai sani ba ?arshe ya taSe baki ya bar maganar, amma da ya ji ke ce fa?.

Nayla tana sauraren Didi amma bata ce komai ba tana tunanin kalaman da Didi ta faWa mata. Didi ta mi?e da kanta ta kwashe tray Win da ya fashe tana cewa,  Wannan tray ya tashi aiki dole sai dai a zubar. Nayla ta mi?e ta ?araso ta ce,  Didi ki bari zan kwashe. Ajjiyewa tayi akan dining Nayla ta ce,  Didi mu je ciki. Tare suka shiga ciki har bedroom Win Nayla. Disi kalli Nayla ganin gabaWaya ta canja sai ta ce,  ki saki ranki don Allah, bana son wannan yanayin na ki.

Ajiyar zuciya tayi aka kira wayar Didi ta Wauka ta fita falo. Ita kuwa bata bari kalaman Didi sun yi tasiri a zuciyarta ba ta cire kaya ta shiga wanka. Lokacin da ta fito sanye da bathrobe tana zaune a kan stool na madubi tana amsa waya.

Didi ce ta shigo ta zauna a gefen gadon tana kallon Nayla. Nayla tana da kyau sosai, tana da madaidaicin jiki mai kyau da kuma kyakykyawar sura mai Waukar hankali lokaci Waya. Ta fi ?arfin Omar ta ko wacce fuska, tazarar su kamar nisan sama da ?asa ne, ita matar manyan mutane ce ba mitstsa irin su Omar ba. Dan Omar bai kai a ce masa ?aramin mutum bama sai dai a ce Wan mitsitsi. Alqalamin ?addara ne ya zana mata rayuwa dashi, in ba dan haka ba da matar minister ce ko sanata.

Kashe wayar Nayla ta yi ta kalli Didi ta ce,  Wai ?anin Salma ne zai yi graduation a London, shine Mama ta kira ni wai ko zan je. Didi tayi murmushi jin abinda ta ce sai ta ce,  to zaki je Win?. Nayla ta girgiza kai ta ce,  na yi ya da aikina? Bazan je ba. Didi tayi murmushi a lokacin Nayla take shafa turare a jikinta sannan ta warware gashin kanta tana fesa turare.

Didi ta ce,  Nayla akwai ki da son ?hamshi, harda turaren gashi?. Nayla ta yi murmushi ta ce,  Khamshi duniya ne Didi. Didi ta murmusa ta ce,  Gaskiya ne.
 Wai kuwa Didi har yanzu kina abincin order?.
 Ina yi mana Nayla, Ina yi sosai dan yanzu har na biki na fara yi. Nayla ta wara idanu ta ce,  waye yake taya ki?.
 Wacce take yi min aiki mana.
 TaS amma kina ?o?ari, da nima na so nayi irin abincin nan wallahi.

Didi ta ce,  Aikin ai ba na ajebo bane irin ku, aikin da wahala baza ki jure ba. Nayla tayi dariya ta ce,  wai ajebo. Ki tura min hotunan spices Win da naga kin fara, ina da masu siya sosai. Didi ta ce,  to Nayla zan tura miki, Na gode. Nayla ta ce,  ke da kike ?aunata kenan, dana ce zan yi miki har kin yarda kin kuma gode, ?aninki kuwa da baya ?aunata, ?iris yake jira na shiga sabgarsa ya zane ni.

Didi tayi dariya sosai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login