Showing 222001 words to 225000 words out of 332344 words

Chapter 75 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

30950

ga mutum yazo ga rashin lafiya amma babu kuWin magani."

Omar ya ce, "to me ki ke ganin za a yi?."
"Mu shiga gobe da daddare, duk mara lafiyan da yake ciki mu basu sadaka, wani ko kuWin abinci ba shi dashi. Ko mutum biyar aka taimakawa mun gode Allah." Omar ya girgiza kai ya ce, "Allah ya kaimu goben."

"Amin ya Allah. Shiyasa ka ke cigaba a rayuwar ka, duk abinda ka samu ka farantawa wani da abin da ka samu wallahi Allah bazai barka ba, sai ya ninka maka ninkin abinda ka samu. Allah ya dafa maka Rouhii."

"Amin Ashiq!. Na tashi da yin sadaka gaskiya, ban sani ba a jinina abin yake ko kuma dan Didi ce ta raine ni ban sani ba. Didi akwai ta da taimako, ta yarda ta rasa inda wani zai samu, ko kuWinta kenan tana iya yin kyautarsa ta ce Allah zai bata wani, shiyasa nima na buWe ido da yi. Kuma Malamina marigayi Malam Salahudeen a duk sanda na je wajansa yana faWa, duk abinda na samu kar naci ni kaWai na kyautatawa na kusa dani, kuma na bawa wanda bashi dashi. Tun bana Waukar nasihar saboda yadda nake a lokacin har ta shiga jikina. Yanzu ina ganin amfaninta sosai, kuma zan iya cewa itace silar nasarata a rayuwa."

Nayla ta ce, "Gaskiya ne, Allah ya cigaba da bamu ikon taimakawa wanda bashi dashi." Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Amin ya rabbi. Mutanen Kaduna sun yi min waya suna ta taya ni murna" ya faWa yana kallon ta da murmushi. Ta yi murmushi ta ce, "Abin murnar ne ya samu, dan ma ?an mata suna ta tanka min kai, ni kam ina ta faWa tabarakallahu asanul khaliqin!."

?? ?an girgiza kai ya yi ya ce, "kin kyauta." Ganin yadda ya amsa mata kawai ta san ba a ?an kirkin yake ba. Ya mi?e tsaye ya ce, "Bacci zan yi." Nayla ta ce, "nima haka." Tare suka kwanta amma hannunsa bai zo inda Nayla take ba, zuciyarta na son kasancewa dashi amma gangar jikinta bata so. Da kanta ta matso jikinsa ta kwanta bai hanata ba ya ?yale ta dan bazai neme ta ba sai dai ta neme shi.

? ? ?? Labari ya baza duniya, ana ta cecekuce ana ta yiwa Omar fatan alkhairi da nasarar da ya samu. Abinda yake trending kenan a media a kwanakin, ba kamar hoton Omar da yake Waukar hankali, kallon farko zaka yi masa ka fassara shi a Wan gata gaba da baya, saboda kyuan da Allah ya yi masa. Abu kamar wasa ig account Winsa ya cika da dms, kuma yawanci duk mata ne, shi abin ma dariya yake bashi ko buWewa baya yi balle ya ce zai basa amsa.
KRB3P83
Nana haleema

Bayan kwana biyu da yin abun ranar Monday Nayla ta tashi da azumin godiya ga Allah, ta yi mamaki da ta ce masa zata yi azumi bai tanka ba ya ce Allah ya bada ikon yi, a nan ta tabbatar da ?warai fushi yake yi da ita. Sai ta ?ure yake ri?e hannunta, amma hugging ko kiss duk ya daina, hakan yana damunsa shi kansa balle ita da take ganin laifi tayi masa.

?? Bayan ta sha ruwa ya shigo falon ya zauna ya kalle ta ya ce, "Kin sha ruwa lafiya?."
"Lafiya lau."
"Ina tunanin jibi zan koma China tunda akwai visa, akwai takardar da zan saka hannu a can, kuma akwai kayan da zan siyo saboda zamu fara tura musu kaya a wannan watan." Nayla ta kalle shi ta ce, "Jibin zaka je?."

"In sha Allah."
"Ka siyi ticket Win ne?."
"A'a ban siya ba, yanzu maganar zuwan ta tashi ke na fara faWawa."
"Allah ya kaimu."
"Amin." Ta sake kallon sa ta ce, "tare zamu je din?." Kallon ta ya yi na wani lokaci, kafin ya janye ido ya ce, "A'a, ina yi miki batun tafiya jibi kina zancen tare zamu je?."

Nayla a sanyaye ta ce, "Amma ka ce baza ka sake tafiya ka bar ni ba." Ya Wan shafa kansa ba tare da ya kalle ta ya ce, "in na je dake yanzu amfanin me zaki yi min? Damuwa zaki ?ara min kawai." Kallon sa tayi da mamaki, kafin ta yi magana ya ce, "A ina zaki zauna in na tafi?." Muryarta ta fara rawa sosai ta ce, "Wajan Hajja."
"Baza ki je Kaduna ba?." Ta Waga kai alamun eh hawaye na sakko mata.

? ? ? Sai ta karya masa zuciya, yana matu?ar ?aunarta yana kuma tsananin bu?atarta amma ya rasa abinda ya yi mata take gudunsa, shiyasa yake bata space bai sani ba ko akwai dalilin ta na yin hakan. Kusancinsu cutar dashi ya ke yi, shiyasa yake baya baya da ita. Ita kuma sai ta ke gani kamar ya canja mata ko ya daina sonta bayan ba haka bane, shi kaWai ya san halin da yake ciki na rashinta.

A hankali ya ce, "Meye na kukan?." Kamar jira take ya tanka ta fashe da kuka mai sauti, ya yi ajiyar zuciya ya taso ya zauna a kusa da ita ya ce, "Jidda!." Bata kalle shi ba ta kwanta a jikinsa bashi da zaSin da ya wuce ya ri?eta a jikinsa amma shi kaWai ya san illar da hakan zai masa.

Bayanta yake trapping a hankali ya ce, "ki bar kuka Ashiq, ko kina so na yi kuka ne nima?." Ta girgiza kai tana kuka ta ce, "ka....dai....na....so....na....Rouhi!."
"Shiii! Har abada bazan daina sonki ba Jidda, da sonki Allah ya halicce, da sonki zan bar duniya, da sonki zan tashi har a aljanna. Babu wani dalili da zai saka na daina sonki, ina baki space ne kawai."

"Ka yi ha?uri!."
"Baki yi min laifin komai ba Jidda, ki daina kukan mu yi magana." Ta Wago daga jikinsa tana kallonsa, ya share mata hawaye ya yi mata kiss a goshi, ta lumshe ido jin Wumin lips Winsa a fuskarta, rabon da ya yi mata haka har ta manta. Fuskarta ya ri?e ya ce, "Kinga tafiyar gaggawa ce ta same ni shiyasa baza mu tafi tare ba, amma in sha Allah tafiya ta gaba tare zamu yi dan na san yanzu zan dinga shiga ?asar a kai a kai."

Ta Waga kai alamun to ya ce, "To ki yi murmushi mana???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?." Bata yi murmushi ba ta zuba masa ido musamman lips Winsa da ta missing sosai, a hankali ta ta matsar da bakinta kusa da na shi ta fara kissing a hankali. Runtse ido ya yi jin tana sake birkita masa nutsuwa, ya san abin yana yim nisa jikin zai fara rawa ta gudu. Kiran sallah aka yi ya saka shi ya janye jikinsa da hanzari, ya kalle ta ya ce, "Ki kwantar da hankalinki, zan je nayi sallah na dawo" ya faWa yana mata kiss a kumatu ya tashi ya fita.

?? Nayla tausayin kanta take ji, tana son mijinta tana kewarsa amma ta rasa abinda yake yi mata daWi, ta rasa me yake damunta har ya canja ta haka. Ranar ya sakar mata fuska duk da daman bai daina yi mata fara'a ba, sai dai rashin kai hannunsa jikinta da ba yayi, kuma bai yi ?o?arin yi mata komai ba itama bata nema ba a haka dai suka yi bacci.

?? Kamar yadda ya faWa ranar talata da safe ya hau jirgin abuja ya sauka a airport na Abuja, sai ?arfe? Waya na rana hau jirgi suka bar Nigeria. Nayla tana gidan Hajja har jirginsu ya tashi, gidan babu daWi saboda babu Salma sai ?ar ?anwar Hajja itama kuma ta girma sosai.

Zaman gidan baya yi mata daWi kawai sai ta tafi gidan Mama Sa'adatu, gabaWaya bata son zama a Kaduna da can zata je haka kawai bata son zuwa. A gidan Mama Sa'adatu ma bata da walwala ta fi ganewa ta keSe kanta a Waki ita kaWai bata son hayaniya.

? ? Bayan kwana uku da tafiyarsa ya tura mata hotunan abinda ya faru a can da hoton da aka Wauka kamar yadda aka Wauka a Kano. Ta taya shi murna amma ko a status bata sakawa saboda mata. Amma da ta shiga X sai ta ga ana ta sake Worawa ana addu'a, masu cewa ya burge su suna yi masu addu'a suna yi. Gajiya tayi da zaman ta Wauki mota ta tafi gidan Didi bayan ta faWa masa ya barta da?yar. Da maganar abinda ya faru Didi ta tare ta itama ya tura mata hotunan, Didi kuwa an saka a status tana addu'a da fatan alkhairi.

? ?? Bayan sun gama gaisawa da maganar Omar Didi ta kalle ta a nutse ta ce, "Nayla sai nake gani kamar kina da damuwa ko?." Nayla ta yi shiru kafin ta ce, "ina da damuwa Didi." Didi ta ce, "me ya faru?." Nayla ta ce, "Rouhii ne yake fushi dani" ta faWa hawaye yana sakko mata.

Didi ta ce, "Nayla na rasa yaushe zaki daina ji da autanci, wannan ai ?aramin abu ne, zama zaki yi ke da shi ki bashi ha?uri ba shikenan ba?." Nayla ta ce, "Didi bana kyauta masa ne, ina cutar dashi ni kaina na sani." Didi da mamaki ta ce, "Kina cutar dashi kuma Nayla? Ta wacce hanya kenan?." Nayla ta yi shiru tana wasa da hannunta cikin jin nauyin maganar da zata furta. Ganin hakan sai Didi ta ce, "kar ki damu in baza ki iya faWa min ba, amma ki samu ku daidaita dashi in ya dawo."

Nayla tayi ajiyar zuciya ba tare da ta Wago ba ta ce, "Didi haka kawai bana so ya taSa ni, in ya taSa ni sai naji kamar zan mutu. Shi kuma tunda ya fahimta ko hannuna bai sake ri?ewa ba sai ana e gobe zai yi tafiyar nan" ta Wago ta kalli Didi ta ce, "Wallahi ban san meyasa ba, ban sani ba ko wata cutar ce ta kama ni."

Didi ta bita da kallo tana zargin wani abu ta ce, "Kuma babu ciwon kai ko zazzaSi?."
"Babu komai, gwara ma dai jiri, ina yawan jiri sosai, in na tashi sai naji kamar zan faWi amma bana jin komai." Didi ta girgiza kai ta ce, "Da mota ki ke?." Ta Waga kai alamun eh ta ce, "Bara na kire YallaSai a waya sai mu je asibiti a faWawa likita."

? ? Cike da gamsuwa Nayla ta Waga kai, Didi ta shiga Waki ba jimawa ta fito da hijjabi Nayla ta Wauki Marmerh suka tafi. Nayla ta ce, "Akwai asibitin da Twiny take zuwa, akwai likitoci sosai bara mu je can." Can suka wuce Nayla ta ajjiye motar suka shiga ciki suka biya kuWin ganin likita aka nuna musu inda zasu je.

? ?? ?akin Nayla ta shiga ta yiwa likitan bayani ya rubuta mata scaning ya ce ta je ta yi. Tare suka je suka biya kuWin da Didi aka nuna mata Wakin scanning Win ta shiga. Ba jimawa aka gama ta fito aka kawo mata result har inda take, ta mayarwa da likitan a lokacin suka shiga Wakin tare da Didi.

Dr ya buWe result Win ya kalli Nayla ya ce, "Hawwa kina da ciki na sati huWu, duk abinda ki ke ji shine ya saka ki ke jinsa. Ba abin damuwa bane wannan yanayin da ki ke ji, daga kin fita daga first tremister komai zai wuce" ya faWa yana mi?a mata takardar.

Nayla kasa magana tayi ta zubawa likitan ido kawai tana kallo, kafin ta kalli Didi da take murmushi sai kuma ta sunkuyar da kai cikin kunya. Magani ya rubuta mata ya bata suka fito ita da Didi ta kasa cewa komai. Mamaki take yi wai ciki ne da ita, babu abinda take ji in ba wannan damuwar ba sai kuma jirin da take ji ba, ashe daman ana iya yin ciki babu laulayi?.

Didi kamar tafi Nayla farin ciki, ta kasa Soye muryarta sai addu'a take yi. Suna shiga mota ta ce, "da na iya tu?a motar ai da bazan bari ki tu?a ba wallahi. Alhamdu lillah, burina a duniya yana ta cika, zan ga Wa ko ?ar da Omar zai haifa." Nayla ta kifa kanta akan sitiyarin motar tana jin kunyar Didi mai tsanani. Didi tayi dariya ta ce, "shi yana can yana fushi bai san abinda yake so ne ya samu ba, dole na yi masa babban albishri."

Nayla ta Wago da sauri ta ce, "Don Allah Didi kar ki faWa masa, ki bari ya dawo." Didi ta ce, "To ai da ki ka shiga wajan likita ya kira ni wai bakya Waukar waya na ce bakya jin daWi muna asibiti, duba wayarki zaki ga kiran."

Kamar jira yake yi tana kallon wayar kiransa na shigowa ta Wauka kafin ta yi magana ya ce, "Jidda Didi ta ce min bakya jin daWi an je asibiti, me ya same ki? Kina lafiya dai ko? Me suka ce yana damunki?. Ki yi magana mana, na kira Didin bata Wauka ba." Nayla jin ya rikice yana jero mata tambaya sai ta ce, "malaria ce aka ce tana damuna."

"Amma da sau?i dai ko? Kwantar dake suka yi ko ruwa aka saka miki?." Nayla ta yi murmushi ta ce, "Babu komai fa Rouhi, magani kawai suka bani."

"In akwai damuwa ki faWa min, kuma meyasa baki faWa min baki da lafiya ba har ki ka ce min kin tafi gidan Didi? Kin san baki da lafiya ina ke ina Waukar mota?. Sannan ba na ce duk inda zaki je ki dinga bari a kai ki ba? In aka sake ?o?arin cutar dake fa?. Meyasa ki ke yi min haka ne Jidda?."

Jin ya fara yi mata faWa sai ta ce, "Ka yi ha?uri."
"Wannan ai ganganci ne, kin san baki da lafiya sai ki Wauki mota ki bar gida? Meyasa baza ki ha?ura ba?. Na hana ki fita ke kaWai amma bakya ji, yanzu da wani abun ya same ki fa?." Nayla ta ce, "to ai nace ka yi ha?uri." Ya yi tsaki ya ce, "ina Didi?." Nayla ta ce, "gata" ta faWa tana bawa Didi wayar.

Didi ta karSa tana ji kamar ta sanar masa amma tunda Nayla ta ce bata so gwara ta ?yaleta ta faWa masa. Ya ce, "Didi don Allah ki kula da ita, kin tabbatar zata iya driving?." Didi ta ce, "Gaskiya nima bana so tayi, bara na kira Tukur ya zo nan ya tafi da motar."

Tsaki ya yi akwai ya kashe wayar, Didi ta kalli Nayla tana dariya ta ce, "A haka ma bai san ciki ne dake ba." Nayla ta yi murmushi, Didi ta kira Tk tayi masa kwantace ya ce gashi nan zuwa. Suna zaune a motar ba jimawa ya zo, Nayla ta fita ta koma baya ya shiga motar ya ja suka tafi.
KRB3P084
Nana haleema.

Sai da aka sauke Didi a gida sannan aka wuce da Nayla gidan Mama. Da suka je ya ajjiye motar ya bata key ya koma a napep ita kuma ta shiga ciki. A falo ta samu Mama da Abbas da Khaleefa, Mama ta bita da kallo ta ce, "har kin dawo?." Nayla ta ce, "eh Mama, jiri nake ji" ta faWa tana zama kafin ta gaishe da su Abbas. Mama ta ce, "Sannu, rana ce ta saka ki jiri, dan yau ta buWe sosai, kuma kamar bazata buWe ba saboda hadarin da ya haWo Wazu."

Nayla ta mi?e ta shiga ciki takardar hannunta ta faWi bata sani ba. Khaleefa da yake kusa da ita ya Wauka yana cewa, "Nayla kin yarda da takarda." Nayla ta shiga ciki bata ji shi ba. Ganin hoton scaning a sama sai ya ja hankalinsa ya buWe takardar, ya kalli Mama ya ajjiye bai ce komai ba. Mama ta kalla ta ga alamun takardar scaning ce ta ce, "A'a Nayla bata da lafiya? scaning taje daman?" Ta faWa tana buWewa tana ganin abinda yake jiki.

Murmushi ta yi ganin abinda yake rubuce a jiki, a lokacin Nayla ta dawo tana cewa, "Mama na yarda takarda......" Maganar ta tsaya ganin result Win a hannun Mama. Mama ta mi?a mata ta ce, "gata nan." A sanyaye ta karSa ta koma ciki da sauri cikin jin kunya. Mama bata ce komai ba suka cigaba da hira kafin ta tashi ta shiga wajan Nayla.

A zaune ta same ta, Mama ta zauna kusa da ita ta ce, "Nayla sannu." Nayla ta sunkuyar da kai cikin kunya ta Wagawa Mama kai. Mama ta ce, "babu abinda ki ke so?." Nayla ta ce, "Babu Mama."
"Kin tabbatar? In akwai ki faWa min kinga ba ke kaWai ba ce." Nayla sai ta kifa kanta a jikin Mama cikin jin nauyin maganar. Mama ta yi dariya ta ce, "ni tunda ki ka zo nake kallon ki kamar mai ciki, ashe shi Win ne. Allah ya inganta Nayla ya raba lafiya." Bata ce komai ba tana jikin Mama.

Mama ta ce, "To meye na kunyar? Kinga Wago ki faWa min abinda ki ke so." Nayla ta Wago ta ce, "babu komai Mama."
"Kin tabbatar?." Ta daga kai alamun eh Mam ta ce, "duk abinda ki ke so ki faWa min." Nayla ta amsa sannan Mama ta fita.

Cikin lokaci kaWan kowa ya san da batun cikin Nayla, har Mama ta Kaduna sai da ta ji labari, Nayla dai bata san waye ya faWa mata ba sai kiran Mama ta ji tana cewa duk abinda take so a kawo mata daga Kaduna ta faWa mata.

Har Abiy sai da ya kira ta ya yi mata ya jiki, ana ta murna kamar a kanta za a fara samun jika. Hajja kuwa kamar ta fi kowa farin ciki, itama waya take sakawa a bugawa Nayla ta ce ta faWi abinda take so. GabaWays ta zama ?ar gata, kowa burinsa ta ce ga abinda take so. Ita kuma cikin bai saka mata wannan kwaWayin ba, normal take harkokinta sai sai jiri da nauyin da kanta yake yi, wani lokacin sai kuma ri?ewar mara.

" " " " " " " " "

"Safna kalli ki ga, kalli Safna, wallahi he's the one, he's my love Faruk, wallahi shine" Narma ta faWa hannunta yana rawa tana nunawa Safna wayarta da take hannunta. Safna ta kalli abinda take nuna mata ta kalle ta cike


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login