Showing 18001 words to 21000 words out of 332344 words

Chapter 7 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14365

tea ya dafa ya sha.

Tsaki ya yi ya ce,  ko meyasa ban je can nayi girki ba oho. Kulle ido ya yi ya buWe yana jin sa wani daban kamar ba shi ba. Fitowa ya yi har lokacin tana zaune jin motsi sai ta kalli wajan a sanyaye ta ce,  ga abinci. Ba tare da ya kalle ta ba ya bar wajan ko amsawa ma bai yi ba.

Nayla a bayyane ta ce,  kema dai Hauwa akwai ki da shishshigi wallahi. Duk sai taji babu daWi ta tashi ta bar falon zuwa Waki. Shi kam fita ya yi ya kira Bash suka siyo masa fruit suka kawo masa ya zauna ya sha sannan yaji daWi. Ya shiga Wakin yana kwaikwayon muryar Nayla yana cewa,  Ga abinci, mtsww shirme ya faWa yana kwnaciya tare da rufe idanunsa.

Washe gari ma haka ta kasance bata san ya fita ba, tana so ta shiga Wakinsa ta gyara amma tana jin tsoronsa hakan ya saka bata ma kalli hanyar Wakin ba. Bayan sallar azahar tana zaune ya shigo da sallama a ciki, ta amsa bai kalle ta ba ya wuce da kaya a hannunsa. Bai jima ba ya dawo ya zauna kamar bai ganta ba ya fito da kayan da ya zo dasu yana Wauka hoto da alama akwai wanda zai turawa.

Nayla ta ce,  sannu da zuwa. ?ago idanunsa yayi ya kalleta tayi saurin kawar da kai dan bata jure kallon idonsa, idanun nasa akwai girma da kwarjini. Bai amsa ba ta sake cewa,  Ga abinci. Ajjiye abinda yake yi yayi ya harWe hannayensa a waje Waya ya kalle ta ya ce,  ke ba a faWa miki bana son shishshigi a lamari na bane? Ina yini, barka da zuwa, ga abinci, na ce miki ina so ne? Ya faWa yana Wan buWe ido yana kallonta.

Nayla jikinta ya yi sanyi ta girgiza kai alamun a a ya ce,  to ki tsaya matsayinki, har gobe sunana Tiger ban canja daga yadda nake ba. Ki yi rayuwarki na yi tawa, babu lallai sai kin yi min magana nima babu lallai sai nayi miki. Mu kwana dubu a gidan nan dan baki min magana ba babu abinda zai dame ni, kema ki koyawa kan ki hakan. Kin ji ai ko?. Nayla ta Waga kai alamun t eh ya ce,  baki da baki?. Murya na rawa ta ce,  Ina dashi.
 Rainin hankali ne ya saka ki ke yi min magana da kai? Ya faWa a Wan tsawace yana buWe idanunsa.

Nayla ta tsorata ta ce,  a a, na ji, na fahimta.
 Dakyau ya furta yana Wauke kansa ya cigaba da abinda yake yi. GabaWaya shi an gama cutarsa, an aura masa yarinya da bai ce yana so ba, yarinyar da Didi tayi masa faWa a gabanta har wani girmansa zata gani.

Tsaki ya yi a bayyane hakan ya saka Nayla ta mi?e jikinta a sanyaye zata bar wajan ya ce,  zauna. A zabure ta zauna ba tare da ta sani ba, dan bata yi tunanin zai yi magana ba ko kaWan, ya kalle ta ya ce,  na ce babu ruwanki da ni ne ban ce ki tashi ba ai, zaki iya zama na ga parlor naki ne ko?.

Nayla kamar zata zubar da hawaye ta ce,  nawa ne.
 Kujerun ma naki ne ko?.
 Nawa ne ta sake faWa kamar ta yi kuka.
 Ni ya kamata na baki waje ya faWa yana mi?ewa ya fita daga gidan gabaWaya.

Nayla ta ce,  na shiga uku, wannan mutum sam baka gane masa, Allah ka sassauta min abinda nake ji a kansa. Wannan abu ya yi yawa, daga wannan sai wannan. Wayarta ce tayi ?ara ganin sunan Didi sai ta Wauka Didi ta ce,  Nayla ya ki ke?.

 Lafiya lau Didi, Ina yini?.
 A a ya naji muryarki na rawa? Omar ya yi miki wani abun ko?.
 Bai yi min komai ba Didi.
 Kar ki ?o?arin kare shi, na san halinsa wallahi. Nima masifa ya gama yi min na saka an kwaso kayansa an kawo gidan. Ki faWa min abinda ya yi miki.

Nayla ta ce,  bai yi min komai ba Didi. Didi ta ce,  ki yi ha?uri Nayla, yana da wahalar sabo amma da kun sana shikenan magana ta ?are. Zai canja miki zaki ga ya koma miki wani Omar Win da ban wanda baki san shi ba, duk da masifa da zafin rai a jininsa yake, amma dariyarsa da hira dashi zai zamar miki ko a yaushe dan na faWa miki yana da hira in kun saba. Ki yi ha?uri, da kun saba shikenan komai ya ?are.
Nayla ta ce,  haka ne Didi. Hira suka yi da Didi sosai kafin ta kashe ta tashi ta koma ciki dan har lokacin bai dawo ba.

Da yamma ?annen Salma suka zo, Nayla ta ji daWi sosai sun sha hira sai da suka yi sallar magriba sannan suka wuce gida har lokacin Omar bai dawo gidan ba.

Shi kam Omar gidansu ya wuce ya cigaba da abinda yake yi, yana yi yana mita yana cewa,  GabaWaya bana sakewa a can gidan, ban sani ba ko dan komai na gidan nata ne oho. Ta saka min ido, Ina yini, ga abinci, sannu da zuwa. Mtsww! Na ce mata ina son gaisuwa ne? Ko ance ina son magana da ita ne?. GabaWaya bana sonta! Ya faWa yana cigaba da yanka da sample Win takalmin hannunsa sai kuma ya dafe kai.

Numfashi yake saukewa a hankali ya ce,  na tabbatar rashin son da nake mata ne ya saka na kasa sakewa. Narma ce ta zo zuciyarsa sai kawai ya yi tsakin da bai san dalilinsa ba ya cize baki yana cigaba da sauke numfashi a hankali.

Wayarsa ya kalla yaga sunan Didi a bayyane ya ce,  sarkin takura ko ne zata ce min oho. Bazai iya ?in Waukar wayarta ba duk fushin da yake yi da ita, hakan ya saka ya Wauka ya saka a speaker ya ajjiye a kusa dashi ya ce,  Wanne dolen za a sake yi min?. Didi tayi dariya ta ce,  Haba Omar Tiger, Ko gaisuwa babu?.
 Kwana biyu bakya bu?atar gaisuwar ne.
 To naji. Ya amarya?.
 Oho ya bata amsa a ta?aice.

Didi ta ce,  Omar kar fa ka cutar da yarinyar nan, ha??in kula da ita yana kan ka na faWa maka.
 Ikon Allah, me kuma akace nayi?.
 Babu abinda aka ce ka yi, ina tuna maka ne kawai.
 Duk wannan sadaukar da rayuwar tawa da nayi saboda auren ba a gani ba? Me ake so nayi kuma?. Didi tayi dariya jin wai ya sadaukar da rayuwarsa ta ce,  kayi namijin ?o?ari Omar. Yanzu kana ina?.

 Gidan mu.
 Omar zaman wannan gidan fa ba naka bane, ga gidanka can da ka biya kudin hayarsa zaman me ka ke yi a nan?.
 GabaWaya kayan gidan nata ne, takura nake yi bana sakewa ko kaWan. Ta cika saka min ido, ina kwana, ga abinci. Na ce mata ina so ne? Bana son shishshigi kema kin sani. Didi ta ce,  Omar matarka ce fa, yanzu kenan ko gaisuwar baka amsawa ko?.

Omar ya ce,  to na saka ta ne? Da ki ke zancen matata ce ni na ce ina sonta a aura min ita ne?. Ban taSa cewa ina sonta ba, kuma har gobe bana sonta. Didi ta kwantar da murya ta ce,  amma dai ba haka ka ke ce mata baka sonta ba dai ko?.

Kamar tana gabansa ya wara idanu ya ce,  To in na ce laifi na yi? Kaji Didi da wani abun, dan na faWa mata bana sonta ai ba ?arya nayi ba, bana sonta kema kin sani. Na karSa ne saboda ke, li?a min ita akayi ta dole ba dan ina so ba.

Didi ta ce,  kar dai ka faWa mata haka, ka cigaba da ri?ewa a zuciyarka har lokacin da zaka so ta Win.
 Hmmm! Shine abinda yace. Didi ta ce,  Ina fatan kana kula da abincinta ko?.
 Jaririya ce ita?.
 Ha??inta ne a kanka.
 Bani da wannan lokacin.
 Omar ka sassautawa zuciyarka wannan zafin kan, Ina sake faWa maka akwai ha??inta a kanka kaima ka sani.

Sai kuwa ta fusata shi ya ce,  Sai maimaita min batun ha??i ki ke yi me ki ke so nayi nata? A baki ki ke so na bata abincin ko farka cikinta zan yi na zuba mata?. Ke ki ka ce min gidansu an kaita da abinci, to me zanyi kuma? Sun nuna min ni ban isa na ciyar da ?arsu ba, sun nuna min bani da kuWin da zan iya ciyar musu da ?a shiyasa suka kaita da abincinta, ba sai ta ci abincin gidansu ba ita kaWai ba? Lallai sai na kula da abincinta!?.

Didi ta ce,  maida wu?ar Omar, abincin da aka kaita da shi daga gidansu shi ake kira da gara, a al ada ba laifi bane kuma ba anyi dan ka gaza bane al adar malam bahaushe ce. In zaka tuna kaima lokacin bikina na karSi kuWi a hannun ka nima kayan abincin na siya na je dashi, bawai dan mijina ya gaza ake yi ba sai dan al adar bahaushe ace a haka.

 Kutmar uban al adar! Ya faWa a fusace cike da jin haushi. Jin zagin da ya yayi Didi ta ce,  A uzubillah! Omar me ya yi zafi haka?.
 Ni ban Wauki hakan a matsayin wani al ada ba tunda ba addini bane, kawai an nuna na gaza ne shiyasa aka kawo ta da abinci. Sai ta aci abincin gidansu, ni ban ce ina da bu?ata ba daman ai.

Didi ta ce,  Ka dai yi min irin wannan zagin bana so. Ana nuna maka gabas kana karkacewa, kai komai abinda zuciyarka take so shine daidai?. Yanzu ya zaka yi ga azumi zamu fara, ya zakayi da abincin shan ruwa?.
 Bani da hannu ne? Zan dafa da kaina a cikin gidan mu ba a gidan haya ba.

Didi ta ce,  ai shikenan Omar. Amma ka bi komai a hankali, da zaka ji ta tawa ka Wauketa kamar ?anwarka zaman zai yi maka daWi.
 Kin ji na ce miki ina so zamana ya yi daWi ne? Ko kin ji na ce daWin zaman nake nema?. Didi ta ce,  kai dai ka sani. Amma ina so ka sani akwai ranar da zaka nemi daWin zaman, Allah Omar sai ka so Nayla fiye da son da ka yiwa Narma.

Omar ya ce,  Tunda ke kika halicce ni sai ki saka min son na ta Win. In kina yi min irin wannan maganar wallahi zan yanke ala?a da ita, gidan ma zan daina zuwa ai ba dole!. Didi tayi dariya ta ce,  Allah ya shirye ka daga haka ta kashe wayar.

Tsaki ya yi ya ajjiye a bayyane ya ce,  wai sai na sota fiye da Narma, to ita Narma har wani sonta na yi? Mtsw Didi akwai kayan haushi ya faWa yana taSe baki yana cigaba da duba kayan. Sai da ya yi i sha a unguwar ya bawa su Bash key Win gidan dan su suke kwana a ciki ya wuce can ransa duk a jagule.

Nayla bata babban falon, ta ji dai alamun ya shigo, bata yi gigin fitowa ba ma balle ta yi masa tayin abinci. Shi kuwa in ya tuna komai na gidan na ta sai ya ji zaman gidan ya fita daga ransa, shi fa a tsarinsa bai yarda da kayan Waki gidan mata su yi ba, a yadda ya tsara in zai yi aure shi zai yi komai da kansa yadda zai yi komai yadda yake so baya so ayi masa iko ba, in ya siyi komai babu wata shegiyar yarinyar da zata ce ai daga gidansu aka kawo abu kaza. Yanayin yadda auren yazo ya saka burinsa bai cika ba shiyasa ko zaman gidan baya so. A haka dai ya kwanta da ya tuna maganar Didi sai ya ja tsaki har ya yi bacci.

Bayan Kwana biyu.

*America.*??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Narma ta rame sosai ta fita daga hankalinta, kai da ka kalle ta sai ka san Narma tana cikin yanayi na damuwa. Komai ya tsaya mata babu abinda take jin daWinsa a zamanta da Ashraf. Ashraf ya ?wace mata waya ya kuma hanata fita, gabaWaya kaWaici ya isheta shiyasa duk take rama.

Tana zaune a falo tayi tagumi ya shigo ya kalle ta ya ce,  Mum tana son magana dake, wallahi in ki ka faWa mata kina da damuwa sai ranki ya Saci. KarSi ya faWa yana mi?a mata wayar a lokacin kiran Mum ya shigo. Ta Wauka ta saka a kunne Mum ta ce,  Daughter me ya same ki? Ashraf ya ce min kin yi rashin lafiya, ko kina da ciki ne? Me ya samu wayarki?.

Narma jin tambayoyin da Mum take yi mata sai ta ce,  Mum lafiya lau nake. Ina Dad?.
 Dad baya nan, ya je Italy bai dawo ba. Kina Lafiya dai ko? Me ya samu wayar ki?.
 Mum na yar da wayar ne kuma kin ga layin Nigeria ne sai na dawo dole na yi swap.
 Amma ki siyo sim a nan mana ki dinga amfani dashi, shirun naki ya ishe ni.
 Babu damuwa Mum, zan yi.
 Haka nake so na ji. Zan shigo America na duba ki. Ta amsa sannan ta kashe wayar ta bashi.

Ya kalle ta ya ce,  kin taimaki kan ki da yau sai kin yabawa aya za?in ta. Narma ta kawar da kai, ba tsoronsa take ji ba ta yi hakan ne saboda duk abinda ya faru laifin su Mum Win ne shiyasa bazata faWa musu tana cikin damuwa ba. Su suka siya mata da kansu da sun yi mata abinda take so da shikenan. Gashi sun kawo ta nan ya mayar da ita tamkar se* machine, kwana biyu da aka fara azumi ne ma ya saka yake iya ?yaleta. Amma kullum a abu Waya ake.

Bayan an sha ruwa ya dawo ya bita da kallo tana zaune tana tauna tosted bread kamar bata so, ya kalleta ya ce,  ki gama malama ina da bu?atar ki. Kallon sa tayi ta ce,  kai wai babu abinda ka iya ne sai s*x?.
 Dan shi na aureki ya bata amsa kai tsaye. Narma ta ce,  kenan daman ba sona ka ke yi ba?.
 Da fari na Wauka ina sonki ne, amma daga baya sai na gane sha awarki kawai nake yi. Na tabbatar da kin bani abinda nake so kafin wannan auren da ba a kawo haka ba.

Narma ta bishi da kallo ta ce,  kenan ka yi satisfying lust Winka yanzu bani da amfani a wajan ka ko?.
 No, har yanzu ina da bu?atarki ai, ban gaji dake ba. Narma ta taSe baki ta ce,  ka ci amanar iyayena, ban yi tunanin haka daga gare ka ba. Ka san ba sona ka ke ba ka amince da aurena?.

Ashraf ya kalle ta yana taSe baki shima ya ce,  laifinki ne, ke kika jawo na aure ki da wannan niyar. A ko yaushe in na ganki sai nayi sha awarki saboda irin shigar da ki ke yi, ko yaushe nude Winki a bayyane yake, kina saka kaya half niked ga ki da sura in kika saka kayan komai sai ya bayyana sosai har hakan ya kai ni ga karyewar alwala. Ban taSa mafarki na kwanta da wata ba sai ke, saboda tayar min da hankalin da ki ke da shigarki. Har wankan tsarki kin saka ni saboda haWa jikin da nayi dake cikin shigar da ki ka saba, ko yaushe ?irjinki a bayyane yake ga ?asanki kin matse da?yar ki ke tafiya, kina motsawa jikinki na rawa, waliyi ne ni da bazan yi sha awarki ba?. Abinda nake ji a kanki shi ne ya saka na Wauka a raina sonki nake yi ashe ba so ba ne ya bata amsa yana kai abinci bakinsa.

Narma ta yi shiru domin bakinta ya mutu da kalmansa, ya sake cewa,  majority ma su sonki ba ke suke so ba halittarki suke so saboda ita suke gani a bayyane. A social media ko yaushe cikin yabon surarki ake saboda a bayyane take ga kowa. Kinga ban yi laifi ba nima dan na mayar dake abin morata ko yaushe, ke kika siya da kuWinki.

Narma ta ce,  Amma meyasa a baya baka taSa faWa min ba sai yanzu?.
 A lokaci a hakan nake son ganinki a lokacin, bana so ki Soye ko wacce halitta a jikinki shiyasa bazan taSa faWa miki ba. Zuga ki ma nake yi akan ke mai kyau ce kina jin daWi, ban yi ?arya ba kina da kyau, kina da sura mai yau Narma. Yanzu kuma na mallaki komai na jikinki, ko bargo zaki Winka ki saka a jikinki ?arewar rufe jiki bazai dame ni ba. Ni ne wanda na yi disvirgin Winki, so ban ga abinda zaki Soye min a jikinki ba, ban ga abinda zai Wauki hankalina a tare dake ba. Nayi mamaki da ki ka kasance budurwa har wannan lokacin, dan wannan shigar da ki ke yi tsaf mutum zai iya sakawa a Wauko masa ke ya yi abiinda yake so dake.

Narma kallonsa take yi har ya gama maganar, ta girgiza kai cikin ba?in ciki ta ce,  Allah ya isa. Ka raba ni da wanda nake so ka zo nan kana wahalar da rayuwata, ni ka ke kallo kana faWawa wannan maganar dan kawai ka gama cutar dani. Kuma wallahi yau


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login