Showing 27001 words to 30000 words out of 395027 words
Chapter 10 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
min hanci a gidan nan fa in fadi in mutu ko akan me zan tsaya wani munafuncin nuna damuwa kan haka ?
Nishin da nayi daga daki don gyara kwanciya yasa duk suka juyo suna kallona baba yace kinga Ai shirya ki kai yarinyar nan chemist a duba ta akwai kudi a hannunku ko ?
Yake tambaya kafin mama ta bada amsa ita mama tace inma babu ai sai a fita a nemo yanzu tunda mai bayarwab daya daurewa karya gindi ya gama yaudaransa ya dibi na diba ya kara gaba.
Allah ya bata wanda yafishi ke kuma aniyarki tabi Rakiya yau na tabbatar dawa kike yau kuma na sheda baki kaunana da arziki ashe da ake fadin da hannunki cikin zaman mu haka gaskiya yau na tabbatar da hakan koke wacece?
Ai baka gama sanina ba tukun mu dai zuba daku kun dauka kyau ko farin jinin da kuke kirawa yarku ko da gaskene muryan yarta saudat ce daga kofa take kiran sunanta.
Tare da fasin mama fa mama mama dake nakeyi fa ta juya a hasale tana fadin wai meye baki bari in gama fadawa mutanen abinda suka shuka yau gasu nagani da idona suna girba zaki isheni da kiran tashin hankali haka ?
Ki dai bar wajen na fada maki meye kikeyi haka kamar wace wani abu ya hau kanta don Allah mama ?
Kafinta jefa mata zaki har ta juya ta koma lungunsu da mama ta kewaye da kwano tayi hakanne ala dole saita banbanta kanta da mama.
Hakanta juya bayan ta gama cin mutuncinta da shewa tana fadin indai rigimane junin inna gasa ai kadan tagani ta matsa cusani ga inda bamu kai ba.
Saida dare inna ta kaini chemest akai min allura da yan maganunuwa takaso min kudi har dubu ukku da dari biyar muka dawo gida aka tura kanina dake bi min ya sayo min ruwan shayi shina sha na kwanta a ranan.
Kwana ukku nayi kwance kafin naji sauki kafin na mike din har inna ta zaga unguwa tana fadin ai da naji labari saidana kai kwance don firgici.
Ina tashi daga ciwon washegari sai na shirya zuwa makaranta don gidan ba dadi zama saboda habaicin mama dake damuna inna kuma duk da ta daure bata nuna damuwamta a fili ba kan zancen amma saida tayi dan rama da jikinta ya nuna hakan.
Hakan yasa namike don kada inyi ta daga mata hankali na fita zuwa school don sammakon da nayi ba wanda yasan nazo har saida aka tashi na fito wasu suka gane hakan ina kallon yadda yan unguwanmu ke nunanih.
Gidama dana dawo banyi sanyin bin jiki na kwanta ba na mike na kama aiyu kan daya dace inyi ba kunya mama ke fadin amma yanzu ai saita koma tallanta ko ?
Nan kan inna ta bata amsa don cewa tayi talla kuma akan me yaya shi wanda yayi gaba ai yayi gaba ke nan da yardan Allah saidai in har mutum ya maida kanshi baya.
Ma,ana idan baka iya godiya ga ubangijinka ba daya kawoma jerabawan don wanan ai gwajin imanine a gare mu damu da ita baki daya.
Ooh injin diyar gwalce tafi karfin tallah ba yar gwal bace amma kuma insha Allahu inna isa ba zata koma tallah ubangiji zai rufa muna asiri in Allah ya yarda.
Sun dan kwasa saidai da inna taki biyewa zancen ta tun wanan amsan data bata yasa ta gaji tayi shiru bata samu yadda taso ba.
Ban fasa zuwa school ba don nasihan da innan kan muna a cikin dare idan mun shige dakin mu yasa ban wani ji jiki ba akan zancen.
Ba wai zancen ya fita min a kai ba na dai hakkura na sake tunda bashi kadai bane namiji haka salma bayan ita ai ina da wasu kawayen da muke tare.
Saidai a yanzu yin kawance yana ban tsoro salma da muka taso a waje daya muna tare tun muna kanana barci kawai ke raba mu inji bahaushe.
Ta iya min hakan balle wace ban zauna da ita ba nasan halin ta yasa daga kawayen school da zamu hadu mu rabu a can banda wata kawa kuma da har zan iya zuwa gidanta a yanzu gaskiya.
Zance salis ya fini shiga damuwa a yanzu don salma budurwarshi ce sosai suna zuba soyayya saiji yayi kwatsam wai anyiwa Bello matsaya da salma din kuma shi bai fada mashi ba.
Yakanso idan mun hadu muyi zancen amma sai in share zancen in mayar da komai ba komai bane a wajen asalima kamar har na manta da zancen.
A wurinshi nake jin har an saka rana yace tunda akai abin Bello yabar garin yana Abuja wai a can ya samu aiki ashe ?
Da ace na biye mai da kullum zanji abinda zai daga min hankali a wajenshi sai na dauko dan shareshi daga mun gaisa sai ince sai anjima sauri nakeyi in tafi.
Ranan muna gida ba a zuwa makarata donshine muka tashi da wanki dani da innan mu duk kayan mu muka kwaso muna wanki tun aauba don kayan suna da yawa sosai.
Can mama ta fito daga dakinya zata fita ko kallonta inna batayi ba sai nice na gaida ita da kwana ta amsa min a gurguje ta fita.
Ta jima don har mun gama wanki ina gyaran part din mu ta shigo tana fadin shi dai namiji munafukine tunda naji ta soma fadan hakan nasan da wani abin ta dawo gidan.
Ko kanmu ko kan makwabta da take shiga dagani har inna ba wanda ya kalleta tace Ai wai kiji mijin hjy Tani aure ya kara ashe akai mata girshi.
Bai fada mata ba har aka daura aure kuma auren gida wanan fitsararar yarinyar dake zawarci gaban uwarta ya kwaso mata fa ance kuma bata da kunya ko kadan dama yasota tana budurwa Allah baiyi ba sai yanzu.
Itama Tani din ta faye isa da iko da izzan tsiya tana ganin ita tafi kowa a shiya ai gashi nan yanzu an dauko mata mai hanata rawan gaban hantsi a gida.
Nan innan mu ta tanka mata tace akan me zata hanata rawan gaban hantsi kuma tunda ba ita ta aje taba kowa dai halinsa ya fitar dashi shine zaman gidan miji ai yaya.
Anya yadda naga tani ta daga hankali haka yarinyar nan bata fi karfinta ba ashe tun dazu muna can muna tausan kirji ance gobe amarya zata tare yau zasu gyara mata daki.
Shine duk ta tayar da hankalinta suna ta fitina da miji da yan uwashi itako a kan me wanda ya ginu ai ya ginu ke nan a gida.
Aina manta yanzu akwai yar tsama a tsakanin ku nake fadin zancen ana jin dadi dadi kuma da tayi min me zanji dadin kan abinda ya sameta inna ta fada .
Kallona tayi ina nade kayan da suka bushe muna saita kwashe da dariya tana fadin hoo yar nema yaran nan dadi fa mairo taji an wa Uwar kishiya hakan ?
Jam ita mamu din din bata da kunya kome uwar salma ai uwartace har gobe din mu bamu kulfucesu a ran mu ba munsan Allah keyin ikonsa ai.
To diyan sharifai masu kiran Allah a baki wa za aiya laggo ace wai gashi gashi ta juya zuwa dakin ta sai kuma ta juyo tana fadin kai kishi ba dadi wallahi .
Daga ita har yaran kowa yaci kuka ido yayi ja kamar anyi masu mutuwa don kawai miji ya kara aure nasan akan tana yar uwarsace suka daga hankali haka dukkansu.
Inna dai bata tankata ba ta juya tana fadin muga abinda ita fatin zata zo dashi ai ance dai iyayyenta suna da hali sosai nasan shine ya dagawa hjy hankali ba komai ba.
Sunan da mama ta fadane yasani dagawa inba kuskuren tunane nayi ba sai ince anty Fati ce dake ce min ni daughter dinta mahaufin su salma ya aura
Itamace don kuwa naji ance ba budurwa bace wayewane da iya gayunta yasa zaki dauka ita din budurwace ba bazawara ba.
Saida muka shiga daki nake fadin inna ina ganin anty fatice fa daddy ya aura inna ta juyo tana fadin kin santane ?
Na santa mana koke inna aikin santa anty fati dai na tsaya nayi mata bayani tace haka haka kuwa wanan yar gayune kam dole hankalin hjy ya tashi.
Don ga kurciya ga kyau ga lokaci duk ta hada naga tayi guntun murmushi tana fadin dadina da gobe saurin zuwa .
Ban fahinci hausanta ba amma ina ji a raina in kara bincika ko itace fatin dana sani mahaifinsu salma din zai aura.
Inko itace nasan da sun shiga ukku a gidan don anty fati ba sauki ga lamarinta ko haduwa akayi na dan lokaci sai sunyi fada a tsakaninsu don mama bata sonta .
Takan kirata da fitsarariya mara kunya bata da mutunci takan fada akan anty fati din ashe abinda yasa ke nan taki jinjnta mijjnta ya kwarewa fati din ne ?
Kide kide akai tayi a unguwa da wasanni tunda gida kudane a tsakanin mu muna jin komai dake faruwa ga mama dake kai da koma duk ta dawo sai ta tsaya a tsakar gida ta fesa muna labari anyi kaza anyi kaza a gidan.
Har yarta anty Saudi nacewa mama din wai mama ba kawarki bane hjy Tani kike mata haka kuma haba dai mama ke baki da gwani a wajenki mama ?
To kinji na fadi ba daidai bane ita dinne taki kwantar da hankalinta ayi komai lafiya ta fitar da kishinta a fili a gaban kowa ai dole abin yaba mutum haushi.
Mama ko kecema haka zakiyi a gaban kowa din kilama sai yafi na hjy tani tunda gaku da innan mairo kullum a cikin fitina balle an dauko wata kishiya sabuwa an kawo maku kuma.
Wa ni saidai innan mairo ai yanzu nikan ai bani kuma babanku zaiwa kishiya ba ranan innan mairo zaku ga haukanta na kishi ai.
Abin yaba innan mu dariya tace ai gaki yaya ba sai na tsaya yin nawa ba nakima ya wadatar don kowa ya shafa ai tunda bori daya muke wa bauta a gidan nan.
Ai banda ciki baki kedai Allah ya kawo kudin musha kallo kinsan malam rashin kudi ya dunkuleshi wajen nan da naira suna nan da yanzu ya cika gidan nan aida mata.
Ya tabbata ko anty fati mummy na daddy ya aura don yan gidan da suka shigo wajena yaran da muke kan mu daya idan muje gidan dasu muke komai sune da basu ganni ba suka shigo.
Don su basu da kabarin cewa ga abinda ke tsakanina da salma sai wanan shigowan da sukayi suna fadin mairo bamu ganki gidan buki ba tun jiya muna ta shigowa bamu ganki ba ?
Caraf mama tace ina zaku ganta kuwa tunda saurayi ya hadasu da salma saurayinta salma tayi baiko dashi karya take da zata gidan kuma ?
Tsaye sukayi cikin rashin fahintar zancen nama sai can dayan tace min ko mamman bellon ki ake nufin sunyi baiko da salma take muna rawan kai tun jiya ?
To shine me idan tayi baiko dashi ni ban guji salma ba ita ta gujeni ai tunda ban nuna mata komai ba innan mu ta katseni da fadin baki basu ko wajen zama balle ruwa kin tsaya waje dasu kina zuba.
Ina jin hakan nasan worning din innan mu a kaina na gane zancen dana dauki take son in bari hakan yasa nace dasu su shigo mana daga ciki sukace zasu koma gidan bukin dama sunzo su dibanine ?
Suna komawa sabon zance ya tashi aka fara kus kus kus kan abinda suka ji a gidanmu aka samu wata yar unguwa data karawa aya zaki ta fada masu karya da gaskiya akan zancen .
Nan kuma aka fara tsegumi har can gidansu hankalin anty fati din ya tashi sosai dama takan min worning tace mairo baki isa aje saurayi ba kibi a hankali kada ya yaudareki.
Ashema yaudaran daga gidansu zaizo min takan tayi min nasiha a lokacin tace kyawonki ace kin tsaya kinyi karatu mairo baki san maza bane.
Zai bata maki kurciyane kawai ya bata maki lokaci sai kunyi aure kun zuba diya yace kin tsufa ya nemo wata gara ki dage kiyi karatu ba gamu ba duk da kayi karatun amma baka tsira ba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/28, 7:46 AM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
π
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,
π€³AUNTY ZEE MOM MUJJAHID KATSINA 08262859027π€³
π*INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK WANI DATTIN MARA SANYI MAI HANA HAIHUWA SA WARIN GABA RASHIN NI IMA JIN ZAFI YAYIN MU AMALAR AURATAYYA FITAR FARIN RUWA MAI WARI KAIKAYIN GABA TUSAR GABA KURAJEN GABA TUSAR GABA BUDEWAR GABA CIWON JIKI RASHIN GAMSUWA*
*Maganin sanyi 5k*
π*Maganin sanyi*
*5k*
π*Maganin ciwon Qoda 10k*
π*Maganin HepatitisB ASHA NA TSAWON WATA DAYA MUNBADA ANWARKE DA YARDAR ALLAH 40k
*MAGANINπ MATA KALOLI DABAN DABAN INGANTATTU MASU LAFIYA DA KARA KUZARI AKWAI NA MATA AKWAI NA MAZA UWARGIDA DA AMARE KU GARZAYO WURIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA*
π*INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO MAI TADA KOMADAR NONO DA DUK WATA TAMOWA TA NONO ZAI CIKO DA TUWON NONO YA TADA KOMATSEWARSU BANCE ZASU TASHI BA ZADAI SU CIKO SUYI KYAU*
*Maganin gyaran Nono π8k*
π*MAGANIN RAGE TUMBI KODA YAKAI GIRMAN CIKIN YAN BIYU INSHA ALLAH KI GWADA MAGANIN AUNTY ZEE DA YARDAR ALLAH ZAKI GODE*
π*Maganin Rage Tumbi 7k*
π*MAGANIN BASUR KODA YAKAI GA YIN TSIRO INSHA ALLAH AGWADA ZA ADACE*
*Maganin Basur 5k*
*MAGANIN CIWON SUGARπ CIKIN IKON ALLAH MUNBADA ANRABU DASHI*
*Maganin ciwon Sugar 10k*
*08162859027**
*Location*KATSINA STATE*
*ACCOUNT NUMBER*
*8162859027*
*ZAINAB SHU AIBU*
*OPAY*
*OR*
*3968303018*
*FCMB*
*ZAINAB SHU AIBU*
π*DAN ALLAH IN KINSAN BAKI SHIRYA BA KARKI YI MAGANA DAN ALLAH KIBARI KI SHIRYA AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA TAKUCE SAI KUNZO*
Gaskiyane ko wace uwa da diyantane abokan shawaranta koda yaran nan basu mallaki hankalin kansu ba zasu hangowa mahaifiyarsu mafita a rayuwa koda ace tunanen su baikai su hangoshi daidai ba duk da hakan zasuyi kokarin kare uwarsu.
Irin hakan ne yake faruwa yanzu a gidan Alh yakubu mai Dala don hjy hauwa a yanzu yayanta biyu mata sune suka zamo abokan hiranta da shawara dasu take zama tayi.
Nas,matu da suke kira da Nas,ma don al,adan hausawa na ragewa mutum darajan sunanshi wanda akasari hakan yake faruwa a yanzu ga sunayen yaya sai a ragewa yaro darajan sunanshi don wayewa.
Mama Abba fa ya shigo gasu can suna daga murya da naji kamar maman N tana kuka don haka suke kiran sunayen uwayen nasu da harafin farko na sunansu .
Fa,iza dake saman kujera kwance ta dago tana fadin Nas,ma nana hanaki irin wanan maganan ba yarinyar tayi kasa da kai tana wasa da yatsun hannunta.
Ke jeki ki dibo kayan miya ki daka kafin mu fito Fa,iza din tace ba sai kin fita ba mama bari muyi nida ita tunda na iya bakin mu zamuyi nan.
Jeki mana mama din ta fada tana hararanta ta juya zuwa kitchen din don aikin da akasatayi tsuki uwar taja tana fadin yaushema ya shigo gidan nan ?
Har yarinyar takai kofa ta juyo tana fadin da zan fita naga shigowanshi da sauri shida yaya hashim wai Nas,ma baki zuwa abinda aka sakakiyi don Allah ?
Zanje mama ta fada koda ta shiga kitchen din batayi abinda aka aiketa yiba tsayawa tayi tana leken side din mama N ta window kitchen dinsu.
Muryan maigidanne yadda yake fada yasa suyin shiru a falon suna saurenshi don murya sama yake fada yana fadin.
Wallahi saina daure shi idan bai fito min da kudina inda yakaisu ba kinji ba fada maki jin hakan yasa hjy hauwa da ba,ason taji maganan fita ta dan ja ta tsaya tana kallonsu.
Kamar jira yake ta fito ya soma fadin yaron banza yaron wofi kawai ka kama kudi ka salwantar min da dukiya ka dauka kudin nawane da kuke gani ?
Kuna sata kunaci nayi kamar ban sani ba haka bai isheka ba yanzu zakai min wanan aika aikan me kake nufi da sace min kudi masu yawa haka ?