Showing 261001 words to 264000 words out of 395027 words

Chapter 88 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

har ita hauwa din kuwa.

Ragowa kawai take maki na duban kina sama da ita keko kin dauka hakan kamar tsorone ko shakkanki akeyi to ki sani HAWAYEN KADA KWANTONE GA MAFARAUCINTA.

A yanzu kin tabbatar da hakan don kin fara ganin Barnan Kada a gidan nan dama lokaci aka baki lokaci kuma yayi don hasken rana tafin hannu baya tareshi.

Laila hausatu yau kun nuna min ku din yan asalin gidan malamaine gabana zakizo har kofana kina fada min hakan tunda kin gani zaune ?

Zama kan ai yanzu kika fara Naito tunda baki barin mugun abu a cikin ranki yanzu kike shiri ganin sakamakon ubangiji tun a duniya.

Nama dai an baki naki rabo kuma anki akawo maki dakin ki handame yadda kika sabayi a baya ki hada komai ki tura daki idan anyi magana kice kece uwar gida wanan din shine damuwanki a yanzu ko .

A daidai lokacin suka fado gidan anyi daidai hjy Naito tana wurgo roban naman nata zuwa waje sai a kafan yusuf saura kiris yakai a kafan shi shima ya jaye da sauri yana fadin subbahanallahi.

Kalaman hjy Naito din ne a lokacin ya sanar dasu abindake faruwa a gidan ya juya yana cewa Yusuf baka daiji ciwo ba ko ?

Kai kuwa bata guntule mashi kafan ba ta samu abokin gurmanta ta Allah ba taki ba yar banzan mata kawai kadan kika gani a dakin nan ai.

Dakin mahaifiyarsu ya nufa suna shiga inda ya samesu zaune hjy hauwa din tana bawa danta nono sukai sallama suna gaida ita da kwana ta amsa tana fadin kun samu hjy yau ta tari aradun gidan mu ni nasan da matar nan tana tsaye akai sunan nan jiya da ba,a kwashewa lafiya da ita wanan karon ?

Baiyi magana ba tunda hjy hauwa din ta soma yi mashi bayanin abinda ya kawo fadan sai auna karfin halin hjy Naito da yakeyi a zuciyar shi.

Kai tashi muje don Allah ya fada yana mikewa a hasale don jin yadda Naito din daga kofan dakinta data jawo kafa take aunawa iyayyensa zagi na fitan arziki a bakinta.

Lalai kan ku bargidan nan don yau Allah ya gyara idan banyiwa matan nan karan aiki ta koma zaune ba ko gindin bata iya jawowa zuwa kofa gobe balle tayi cin mutunci.

A,a mama don Allah ku fita zancen ta don kamar abin nan ya taba ta nake gani bani daukanta yanzu mai cikakken hankali don ace mutum ko yaushe cikon masifa haka da mutane ?

Don Allah mama ku kyaleta yadda kowa yasa mata ido a gidan nan ku barta tayi ta fadan mugun abinta dake karewa a kanta ni yanzu banda matsala da ita ko wani a gidan kema kuma haka ummah so kubarta don Allah idan tagaji tayi shiru don kanta.

Wanan maganan nashi yasa hjy matar malam ta fita zancen hjy din sai bayab fitansu take fadin yaran nan abinci sukazo ci kuma basu tsaya sunci ba fa ?

Kyalesu hjy kokin kirashi yanzu bai dawowa gidan nan tunda ya samu ana haka dama da niya tayi hakan da gangan da gangan donta batawa kowa farincikinsa a gidan yau.

A gidan malam dai suka karya inda ya samu kunun gyada yasha sosai don ya kwana biyu da shan kunun ko wani iri daga nan ya fita yacewa yusuf zaije ya dawo idan yai hakan yakan gane baison fita dashi lokacin.

Yaron malam ya kira suka hadu a waje nan suka taka har zuwa gaban gidan mu ya tsaya yana karewa tsohon ginan kallo na dan lokaci suka juya suka koma wajen motarshi.

Har shagon mahaifina ya nufa inda ya zata zai samu shagon irin na zamani duk da yaga wajen idon kasuwane don ya samu ana hada hadan kasuwa a lokacin.

Ba laifi gaskiya saidai ba haka ya zata ba yaga wurin ya hango mahaifinmu da yai zufa zufa yana sharan zufa a lokacin sosai na dan diboshi wajen tsayi amma na darashi haske sosai kuma akwai dan kama a fuska.

Yaja mota ya bar wurin ba tare da abokin tafiyan nashi yasan da abinda ya kawosu ba shidai yayi abinda baban malam din yace yayi mai yazo kwanan gidan ya tsaya don ya ajeshi ya taka zuwa wurinsu.

Kudi ya miko mashi da sauri yaron malam din ya kalloshi yana girgiza kai yana fadin asha baban malam don dan wanan abin zaka ban kudi haka kunfi nan a wajenmu wallahi.

Na sani ban baka don kayi abinda nace ba nasan da wuya mu kara hadu in sallameka dole yasa hannu ya karba yana ta godiya ya bude mai motan zai fita yace ko yusuf ya tambayeka kada ka fada mai komai don Allah kada ka damu wallahi sai idan kaika fadawa wani zancen nan.

Motar ya fisga ya shiga gari ya jima yusuf nata kiranshi a waya saidai yace yana cikon gari yana wani abu hakan yasa shi fitowa yana tambaya dawa ya fita kowa yai shiru.

Hakan yasa ya kama gabanshi saida dare bayan an idar da sallah ya shigo unguwar ba gidan malam ya nufa ba kofan gidan mu ya tsaya da mota.

Yaro ya samu ya tura ciki yace ace ana sallama da Saudat yaron na shiga yayi sallama murya radau yana fadin wai ana sallama da saudat a waje.

Saudat fa inna ta fada tana kallon inda take zaune tana karatu ehh wani mutum ne mai jeep yace in kirata ?

Da sauri yaya murja dake diban ruwa a lungunsu ta fito tana fadin kai wanene ya aikoka yace wani mai motane a waje barin zo tace ta juya dauko gyalenta.

Mamakine ya kama su inna da sauri saudat ta mike tsaye ta figi hijjab din ta tana fadin barin ga ko waye inna ?

Ganin haka inna batace komai ba ta fito tana leke ta karasa tana sallama tare da fadin malam wa kewa sallama ?

Ya dan dube duk a duhune akwai yanayin murya dana tsayin daya gani irin nawa gareta yace saudat mana ko bake bace saudat ?

Nice lafiya dai ko ta fada hakan yasa ya danyi murmushi yana fadin nazo in saceta inkaiwa matata maryam lagos.

Jin hakan ta danyi murmushi tana fadin ina satuwa kuwa duk da wajen yata zaka kaini amma ban yarda ba tunda ni tawa yar uwar batayi aure ai ?

A lokacin itama yaya murja din ta fito tana arba da motar ta karaso kusa tana fadin ke Saudat wake nemankine ?

Gurinki akazone dama eeh yaya Saurayin yayan mu ne yazo ta fada haka kai tsaye ba tare da tunanen komai ba .

Wata yayan taku kenan ta fada tana kokarin karasowa kusa ta duba maishi tace yaya Mairo dai tamu.

Tana jin hakan ta ja baya da sauri ta juya da sauri kamar zata kife don sauri inna dai ta ganta ta shigo da wani irin sauri ta shiga part dinsu ta bita da kallo tana dakon shigowan Saudat din a lokacin .

Inna na ciki ko ta amsa da ehh sannu da zuwa anzo lafiya amma yaya bata fada min zaka zo ba ai yace bata san zan kawo nan ba amma tasan da zuwana kano ai .

Yaya hanya yaya mama da jiki ta sake fada yace hanya lafiya nazo kada tayi min kotafin banzo na dibaku ba na shigo ki gaida inna don Allah wani karon zan shigo mu gaisa insha Allahu.

Ki kira don Allah a tayaki kwashe kayan nan zuwa ciki dan tsarabane kuyi hakkuri dashi don Allah ya fada yana kokarin daga bayan motan nashi dake shake da tsaraba dayace ya riko.

A daidai lokacin baba ya faka mashin dinshi a kofan gidan namu yana dan dube duben motar daya gani din kofan gidanshi tare da son yasan waye tsaye wajen mai motar ?

Sannu da dawowa baba ta fada ta karasa wajenshi tana karban ledan dake hannunshi ya amsa har lokacin yana bin motan da kallo cikin mamaki.

Da sauri tace dashi baba wanan ogan aikin su yaya na can lagos ne yazo gaida ku wai kada ya koma yaya tace ya shigo kano bai zo ba ?

Au daga can gurinsu yake ke nan ta amsa da ehh baba tana dan ja baya shima ganin baba din yasa ya sauko daga motarshi a lokacin yazo suka gaisa gaisuwa kuma ta mutunci irin ta ladabin hausawa asali ga manya don bai yarda ya mikawa baba hannu yadda ya miko mashi ba sai yayi saurin yin kasa yana gaidashi din a cikin ladabi.

Ya amsa tare da fadin haba haba dai ba sai kai hakan ba ai mana yaya ka barsu a can yaya wajensu shi malam Faruq din yana fadin lafiya kalau suke .

Ya kara jefo mashi tambaya da a garin nan kake ko aiki ya kawo ka nan din ya danyi murmushi yana fadin ni dan garin nan ne baba jikan nan gidan Sidine ni a bayanku.

Ikon Allah kai dangidane ke nan Allah mai yin yadda yaso ko kaine kwanaki uwarsu ke fasin zasu duba jikin mahaifiyarka nine baba ya fada cikin matsuwa daya tashi din yadda yaken .

Babako tankar ya ganni ne yake ji a zuciyarshi lokacin don ba karamin dadin hakan yaji har kasan ranshi ba koba komai dai yau dai zuwanshi ya nuna wanda yasanni a can.

Fitowan su Saudat din ya katsewa baba tambayan da yake da niyar yi mashi lokacin ya juya garesu yana fadin yaya ya haka kuma ina zaku hakane ?

Baba munzone mu kwashi kaya shi yace na kira a dauka zuwa cikin dare haba dai kaiko mu ko zuwan nan da kayi wallahi ya wadatar muna don tankar munga matyamune a yau nake ji yau rabon mu da ita shekara hudu ke nan da dan kai kuma ana kasa daya.

A cewan shi uban nata can sai lokacin data kare karatunta yake son zo garin nan don gudun surutun mutane yace ai an kusa baba yan watani ya rage yanzu ta kammala duka insha Allahu.

Allah ya nufa ubangiji Allah ya nuna muna hakan lafiya a kare a cikin sa,a wallahi naji dadin zuwan nan naka ya fada yace ba komai ai baba.

Ya juya zuwa cikin gida a tsaye ya samu inna cikin tsarguwa don saudat ta fada mata baba ya dawo yana can suna magana da bakon.

Tasan idan zancen bai gamsheshii ba yau akwai fitina ke nan a tsakaninsu don ba zai raga masu ba ko kadan akan hakan .

Shigowan baba yayi daidai da shigowan uwale da katon din minerals biyu data aje da karfi tana nishi duk suka dubeta ta juya da sauri ta sake fita.

Har suka kwashe aka shigo da kayan saudat tazo da kudi tana bawa inna tace yace a bawa baba wanan wanan kuma naki wanan namune mu raba.

Ni Ai banda wanan uban kayan dayayo tsaraba haka kudin me kuma zai bada a yanzu don Allah ni kan idan baiyi nisa ba da ku mayar mashi kuce angode.

Ai ya tafi inna don kamar sauri yake ana jiranshi naji yana waya yace a gaidake sosai don Allah .

Ni wanan abin haka kamar za a bude shego wai inna don baki ganshi bane fa saudat din ta fada a lokacin yaya Sahura ta fito daga part dinsu tana fadin innan mairo me muka samune haka ina jin karan yarda abu ina sallah.

Ke dau bari Sahura wai daga wajen yar uwarku yazo gaishe mu shine yayo wanan uban tsaraban kamar za a bude shago dasu gidan nan ?

Ai ko mai nemantane yazo shine naji murja nawa mita a daki ashe kai murja dai bata hankali wallahine ta fita ashe ?

Ta dawo tana mita a daki amma angode kuwa wallahi wanan ai mu duka gidan akaiwa tsaraban nan don za a kwana biyu ana morewa bari ke dai sahura ni abin ma na rasa me zance .

Yaya sahura din ta juya wajen kayan tana haska hasken waya tana fadin a,a,a wanan kan baizo da wasa ba Allah yasa dashi za ayi mukan mu more ?

Fitilan da baba ya hasko daga kofanshi yasata yin shiru baba din ke fadin yana wajene saudatu ta amsa da baba ya tafi yace a gaishe ku yana sauri.

Nan inna ta sameshi tana bashi sako yace madala bayan wanan dawainiyar kuma ya karo wanan laluran haka ya mika hannu ya karbi kudin kadin yaji nauyinsu da kamshin sabbin kudi lokaci guda yace.

Ai wanan ba karamin kudi bane fa dole a kira yarinyar nan yanzu a sheda mata muji ko tasan da zuwanshi kada muyi abu a cikin jahilci ?

Nima shina gani malam baba tasan da zuwanshi mana tunda ita zatayo mai kwatancen gidan nan yazo ai dole tasan da zuwanshi din.

A,a sahura kedai bari ba haka akeyi ba gara dai muji din a bakinta yafi mutunci kada wani abu kuma yazo ya biyo baya muji kunya mun kama kaya daci kamar masu jira .

Shima ya fadi yaya bata san zaizo gidan nan ba ya dai zone kada taji yazo kano baizo ya dubemu ba yasa shi yazo saudat ta fada daga inda take gefeb kayan suna kallo da yaya sahura.

Yaya murja ta fito a cikin shirinta ganin baba din baisa taji darrr din fita ba a lokacin baba din yace ina zaki haka da daren nan ke kuma ?

Iya nan shagon isah zan tsaya insai kati tafada tana tafiya kijema yar jakar uban nan kada ki dauka anfi karfina na yarda kin dawo gidan bai min wahala yanzu in turaki wajen uwarki kije can ku karata da ita da mugun halin ku.

Kowa yayi tsit a lokacin kafin su fara barin wajen daya bayan daya sai saudatce take fadin uwale kama kayan nan mu kwashe zuwa daki.

Abin mamaki saiga yaya murja tasa hannu aka kwashe komai da ita kafin ta juya zuwa part dinsu da yanzu su kadaine acikinsa zaune mama na gida jikin yakiya shi kuma baba yaki mayar da ita dankita duk da yan uwa sunsa baki a zance amma ya kekashe kasa yace ba gidanshi ba.

Don kota dawo ba barin halinta zatayi ba ga likita yace hawan jinine ya kamata a lokacin.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[9/27, 9:01 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊 8️⃣0️⃣ 🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Ringing turne din wayana dana saka wakan Assalamu alaikum ya baba shine keta kara a saman gado ina zaune ina cin corsolow din dana sayo da zan dawo gida kusan shine abincina a yanzu don yana min dadi sosai a bakina lokacin abinci sai jefi jefi nake danci amma ba sosai ba.

Da sauri na daga zuwa inda wayan ke ringing na dauka Saudat dina nagani a rubuce don layin eirtel dinta ne dayan MTN na rubuta my blood.

Na dauka da sallama kafin ya katse muryanta raudau ba tare da amsa sallaman ba a lokacin saboda kaguwa ta fesa min abinda ke bakinta ta amsa da yayanmu .

Nace na,am Saudat kinsan me a,a wallahi yanzu saurayinki nan ya bar gidan nan bakiga alherin da yazo muna dashi ba yau ?

Wani saurayina kuma na katseta da sauri da tambaya cikin mamaki don sam ban ko kawoshi a lokacin ba cikin raina saida naji tana fadin wanda mukaje gidansu mana a satin can ?

Yazo wallahi iyakan haduwa yadda gidansu yake da kyau haka shima yake da kyau da komai nasa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login