Showing 54001 words to 57000 words out of 395027 words

Chapter 19 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

sallah.

Ashe wanan yasa anty din bata wasa da kamshi daga gidanta har waje kamshine ita kuma kamshi na daban mai bada ma,ana don tun kayan hadin na madara take diba kafin ai masa mixed a gaskiya naji dadin abinda na gani ance tafiya bude ido nako bude naga yadda suke hadin turaren kamshi kala kala na daki na jiki na toilet da sauransu na tufafi duk wanan fitan naga hadinsu.

Agabana suka fara wani zance kome tsohuwar ta gani saita mike gami da kiran yar nata suka shige uwar daka din suyi siri a tsakaninsu irin da da uwa.

Yayin da zaune nake ni kuma ina tunanen wanan sana,an dana sama sunayi yanzu ga inna da kwazon nema ace zata samu wanan sana,an na tabbatar da tabar aikin wahalan dahuwan da takeyi tunda asuba na dama kunu da yin fanke don masu saya.

Abubuwa a nan duk na gansu sukan sa in tuno da mahaifiyata da kuma irin yanayin tsangwaman dana barsu ciki na mama saboda na dai san mama ba fasawa zatayi ba.

Nakanyi tunane akan salma ko yanzu sunyi aure ko kuma dai da saura dolene zancen Salma da Mammam Bello ya tsaya min a rai don yadda sukai min basu dubi haracin dake tsakanina dasu ba suka yarda da hadin da ake cewa wai itayyensune suka hadasu ba yin kansu bane suma abinda yam gida su salma ke fada ke nan idan an tambaye me yasa tayi min hakan ?

Da gani wani abu mai muhinmaci mukazo yi gidan nasu a lokacin daga dakin uwar inda take zaune ta kwala min kira tana fadin inzo da sallama na sameta a dakin nayi mamakin ganin yadda tsarin dakin yake da tarkace saidai hakan ba hana dakin kamshin dadi ba.

Ki kwashi kayan nan ki kai min cikin mota ta fada na dula na fara jidan kayan zuwa mota na bude ina sakawa a bayan mota ta samu ta mike da kyar bayan na fada mata na saka take fadin mu zamu tafi mummy.

Nima a lokacin nake fadin sai anjima mummy ko kallo bam isheta ba na fita simi simi na bar gidan inawa mutanen gidan sai anjima.

Wanan matar mai goyo a cikinsuce tabiyomu tana miko min leda tace yar gidan anty ga wanan kyayi amfani dashi ko sai lokacin anty dake cikin bacin rai tayi magana tana fadin haba dai Yaburi dakin barshi kada mummy tayi fada.

Ko tayi dai ai kun wuce a lokacin tare fa mukai aiki da ita yau ace ba a bata ba na dan saci kallon anty take min nuni dana karba na durkusa ina mata godiya.

Tafiya mai dan nisa mujayi a motar ba wanda yai magana a cikin mu saida muka kusa kai unguwarmu ta soma fadin .

Yau kinga mahaifiyata ko maryam mummy fada gareta shiyasa idan zan tafi ban taba zuwa dake ba sai yau ko yau din madai don kada na barki a gida ke kadai yasa naje dake.

Tace sai na mayar dake a samo min wata ni kuma a yanzu kin kwanta min a rai sosai wallahi ina jinki maryam kamar kanwata ta jini ban san dalilin dayasa kowa ke yawan ce min nayi sakacin yarda a dauko min yarinya daga bangaren mijina.

Koda yake nasan don Allah yayi maki zubin halittan irin hakane suke ganin wata rana zaki iya fin karfina ko wani abu dai koma dai meye ba zan mayar dake gida yanzu ba sai kin gama karatun ki insha Allah.

Kiyi hakkuri anty na iya fada don ni abin yana daure min kai bakin jini irin nawa ya soma yawa banda boyar Allah nan duk inda naje sai an tsaneni kamar yadda naji mama na fada a gida.

Idan dan fada ya hadasu da inna zakiji tana fidin bakin jinin innan shine ya shafi duk yayanta don haka kadan ta soma gani har na yarta ya gama baiyana mun zauna gida mjn zunbule mata a daki saboda bakin jini.

Yaya in ma wani abin kikai muna ina neman tsarin Allah akan hakan garesu tundaga wanan ranan ban sake jin ta fadi makamanxin maganan nan ba kuma

Kafin mu karasa gida takwas na dare yayi lokacin nan haraban gidan muka samu Paapa a tsaye yakai gwauro yakai mari saboda rashin dawowan mu gidan akan lokaci.

Fada sosai yayi da ita akan me zata je ta zauna har dare yayi muna haka shikan gaakiya ba a kyauta mashi ba don an tayar mai da hankalinshi.

Nice na tsaya na kwashe kayan zuwa ciki dashi ko a falon dana samesu zaune har lokacin sai fada yakeyi yana fadin me take son yanzu aci tunda bamu dawo da wuri an hada abinci ba.

Kayan na aje kitchem na fada na hada wutan abinci ban kwants ba ranan sai wajajen sha biyu na kammala na kwanta agjiye sai barci .

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[7/9, 11:10 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

1️⃣9️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,

🀳AUNTY ZEE MOM MUJJAHID KATSINA 08262859027🀳

πŸ‘*INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK WANI DATTIN MARA SANYI MAI HANA HAIHUWA SA WARIN GABA RASHIN NI IMA JIN ZAFI YAYIN MU AMALAR AURATAYYA FITAR FARIN RUWA MAI WARI KAIKAYIN GABA TUSAR GABA KURAJEN GABA TUSAR GABA BUDEWAR GABA CIWON JIKI RASHIN GAMSUWA*

*Maganin sanyi 5k*

πŸ‘*Maganin sanyi*

*5k*

πŸ‘*Maganin ciwon Qoda 10k*

πŸ‘*Maganin HepatitisB ASHA NA TSAWON WATA DAYA MUNBADA ANWARKE DA YARDAR ALLAH 40k

*MAGANINπŸ‘ MATA KALOLI DABAN DABAN INGANTATTU MASU LAFIYA DA KARA KUZARI AKWAI NA MATA AKWAI NA MAZA UWARGIDA DA AMARE KU GARZAYO WURIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA*

πŸ‘*INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO MAI TADA KOMADAR NONO DA DUK WATA TAMOWA TA NONO ZAI CIKO DA TUWON NONO YA TADA KOMATSEWARSU BANCE ZASU TASHI BA ZADAI SU CIKO SUYI KYAU*

*Maganin gyaran Nono πŸ‘8k*

πŸ‘*MAGANIN RAGE TUMBI KODA YAKAI GIRMAN CIKIN YAN BIYU INSHA ALLAH KI GWADA MAGANIN AUNTY ZEE DA YARDAR ALLAH ZAKI GODE*

πŸ‘*Maganin Rage Tumbi 7k*

πŸ‘*MAGANIN BASUR KODA YAKAI GA YIN TSIRO INSHA ALLAH AGWADA ZA ADACE*

*Maganin Basur 5k*

*MAGANIN CIWON SUGARπŸ‘ CIKIN IKON ALLAH MUNBADA ANRABU DASHI*

*Maganin ciwon Sugar 10k*

*08162859027*

*09070027627*

*Location*KATSINA STATE*

*ACCOUNT NUMBER*

*8162859027*

*ZAINAB SHU AIBU*

*OPAY*

*OR*

*3968303018*

*FCMB*

*ZAINAB SHU AIBU*

πŸ‘ƒ*DAN ALLAH IN KINSAN BAKI SHIRYA BA KARKI YI MAGANA DAN ALLAH KIBARI KI SHIRYA AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA TAKUCE SAI KUNZO*

Shekaruna bai hanani sanin abindake faruwa dani ba na tsanan danake samu daga mutane.

Duk da hakan ba tsana bace a wajena sai bakin jini da kiyayya wanda wani lokacin sai kaci karo da jerabawan rayuwa a cikin lamarinka.

Watau na kasance irin kamar mai daukan kan nan ne idan kayin min farkon gani zaki dauka ina da izza da jiji da kai da son nuna ni watace irin dai haka din nan.

Amma dakin zauna dani zaki fahinci sam ba haka nake ba ina matukar saukin kai da daraja dan adam iya ka dai ko yaushe fuskata yana a daure din nan ban faye saurin sakewa da mutane ba irin haka .

A zatona wanan yasa mutane ke saurin fassarani da wata manufa da har suke ganin rashin dacewa na da zama tare da Anty Sariya don suna ganin zata iya samun matsala dani nan gaba.

Saidai ita data fahinceni tasan ko yaya nake kila shiyasa bata yarda da zugan mutane da suke mata a kaina din nan duk ko yaushe tana cikin jamin kunne akan abubuwan da kowa ke fadi a kaina.

Takance dani maryam wallahi tausayi kike ban nasan duk abinda mutane suke jiye min a kanki maryam suna duban nan gaba zaki iya ha,inta saidai ni wanan bai dameni ba maryam don rayuwata ban daukeshi da zafi ba.

Nasan duk abinda Allah ya rubutawa bawa bai isa ya kyatare hakan ba a kansa amma ki kula din Allah kada ki yarda wani mugu abu ya shiga tsakanina dake na gaba maryam.

Yanzu haka maryam mahaifiyata ta umurceni da in mayar dake da mun dawo gida kuma ni ba zan iya hakan ba gareki don alkwari na dauka na rikeki amana a gidan nan.

Zan fada mata koda ta gane hakan cewa Paapa ya hana in mayar dake don haka ina son ki kara natsuwa saman wanda kike dashi don Allah har muga abinda hali zaiyi nan gaba.

Haka ya farune a tsakanin mu kwana biyu da dawowan mu daga gidansu mai nisa da muka kai masu ziyar wanan yasa na shiga halin damuwa a kwana biyun bayan zancen mu.

Na rasa meyasa hakan keta faruwa a kaina da mutanen anty din kowa ya kyala ido ya ganni tare da ita zai bata shawaran cewa ba irin mu ake riko ba ai ?

Wasu suce bata da hankaline zata dauko kamata a cikin dangin miji da sunan riko ita meya hau kanta da zata kullawa kanta sheri da hannunta ?

Ban karasa fahinta ba sai wata rana da wata kawarta tazo na dawo daga school da rana tsaka na samesu sun baje a falo nayi sallama na shigo.

Matar da yaranta biyu suna ta tsale tsalensu a falo tunda nayi sallaman matar ta kafeni da idanu anty ke fadin maryam kun dawo ya school din ?

Alhamdullahi anty saina durkusa inawa kawar nata sannu da zuwa ta amsa tana fadin kai kai sariya ina kika samo wanan fine baby din haka ?

Itace mana nake fada maki naji anty na fadan hakan budan bakin matar naji tace kai wanan ce dama ake magana akanta ashe ?

Itace dai ta fada tana murmushi sai naji tace banda abinki don Allah wanan ai kina ganinta kinsan sai anyi daga a kanta .

Koda ace ko bata waye ba balle wanan data samu waje haka nan gaba ba karamin fafatawa zakusha da ita ba gidan nan dolene mum tace kiyi gagawar mayar da ita inda ta fito tun idon mijinki bai sauka a kanta ba besty .

Kema kin yarda ke nan nasan zai iya amma kanwarashice fa ita din Allah yasa ciki daya suka fito dashi na rabaki da namiji kinji su fa basu san abin kunya ba gaba suka bashi ba baya ba karewa ke nan .

Daki na karasa na zauna a hankali na fara cire safan kafana don zancen bakuwar daya tsaya min a rai yau ta fito fili ta fadi abinda ake fada garan da garan a gabana bata tsaya sakayawa ba ita.

Watau abinda yan uwa da abokan arzikinta ke hangowa ke nan a gareni suke kokarin kashe min kasuwa a wajen uwar dakin nawa tun zuwana garin.

Ai hakan ba laifina bane to donko itace ta koya min tsabta da iya kakale idan zan fita koma a gida nake saboda tace bata son kazanta a tare dani.

Ya Allah ka tsareni daga duk wani fitinan da mutanen nan suke min hasashe a kanshi yanzu a rayuwata ba mijin Sariya ba ko wani namijin ina neman tsarin ubangijina daga gareshi don inda sabo da horo na horu a kunnuwana da zuciyana yadda na taso cikin hudubar iyayyena a gida.

Ya zama dole in kara taka tsantsan a gidan nan daga ranan na tsiro zama daki idan mijinta yana gida tunda nasa lokacin dawowashi saina kiyayye hakan haka kuma nasan ranan da bai fita sin haka nakan fito inyi aiyukana in koma in kwanta a daki lokacin da suke a falo suna shan iska.

A bangaren karatuna na samu cigaban da ban taba mafalkin samunshi ba a rayuwata saidai kash abu yazo ga tallaka ba wanda zai fahinci irin baiwan da Allah yai min balle yai prounding da kasancewana a hakan da nake abin alfahari.

Banda anty Sariya banda wani wanda har ya damu da halinda nake ciki a lagos dan garama ita watarana can ba a rasa ba idan ta bushi iska zata fito ta zauna tana min tambayoyi akan cigaban karatuna din.

A lokacin na gane a rayuwa bawa baida wani gata idan ba a gaban iyayyensa ko yan uwa yake ba shi uban rikon nawa duk da matarshi na ikirarin fadin dan uwanane a gaban kowa bai taba damuwa da yasan wani abu daya shafi rayuwata ba.

Inma yana min dai ta bangaren matarshi abin zai fito har yakai hannuna don haka kinga ba zance yasan damuwana ba ko akasin hakan.

Rayuwan daulan da nake lasa ta arzikinsu yanzu yasa komai ya canza min ta bangarena a yanzu tun daga suturu na da duk wani motsina ya koma irin na hausawa mazauna kudu din.

Tun ina kyamar shiga irin tasu har yakai yanzu na daina na koma saka tufafi irin na rayuwan can din na saje dasu har Allah yayi anty ta tashi da nakuda wata rana.

Ranan naga mamaki don zakice mijin nata ba irin mazan hausawan mu bane don irin tabaran da sukeyi tun kafin su fita zuwa asibiti.

Don kamar ya cire cikkn a jikinta ya mayar a jikinsa har muka sakata mota suka tafi ni aka barni a gida ina zaman sauraren albishir din haihuwa a cikin damuwa.

Ba waya a hannuna don basu ban waya ba nima kuma ban damu dashi ba balle ko in kirasu inji halin da ake ciki a asibitin ga dare ya tsala a lokacin hakan yasa na tashi a cikin tsoro na rufe gidan.

Ranance ta farko dana fara kwana ni daya a gidan don saida safene suka dawo da yar jaririyarsu da aka haifa a nade cikin showel fari gwanin bam sha,awa da ita.

Nayi murna sosai saidai matar da suka dawo gida a matsayin yar rakiyan anty din wace nake kyautata zaton daga wajen mahaifiyata tazo kamar bata son in taba yarinyar a lokacin.

Hakan yasa na kama kaina dasu din ban yarda kuma na kara cewa a ban ba saidai duk wani aikin wahala nice maiyinshi a gidan.

Tun daga abinci gyaran gida ruwan wanka da su wankin kayan jego duk ni wanan matar take jibgawa su a cikin gidan.

Ban yarda na taba nuna gazawa naba ga duk abinda zasu sani yi din don anty nayiwa basu ba nice dai tsaye ina kula da komai daya dace.

Na zata yan kanon mu zasuzo sai gashi har dareb suna ba labarinsu saida mijinta ya dawone nike jin wai yan uwansa aiba zasu zo sai sune idan an kwana biyu zasuje arewa sukai baby a ganta.

Inda baby din taci sunan Safiya amma uwarta ta soma kiranta da Nawal nida makwabta kuma muka kama fadan hakan.

Zance zaman wanan matar dake kula da Nawal yaso ya kawo min matsala a lokacin don kuwa matar bata kaunata ko kadan dan laifi kadan zata fara min fada wanda ban saba da hakan ba a rayuwanta.

Saidai in shige daki inyi ta kuka ina gaji in fito haka ranan bayan na gama abinci na shirya ina son zuwa school gashi ina makara a lokacin don aikkn dake min yawa.

Har na fito da dan saurina ina sallaman anty but ta fito daga dakin da take tana fadin ni wanan yarinyar bansan meke damunta ba wallahi.

Yarinya sai kace alhuda huda wajen karatu oya maza ki debe kayan nan ki kwashi wanki gaya can na tara kin wani shirya waike zaki school a yanzu kamar wace kararun zai amfana gaba.

Aiya sory anty karama kamar yadda suke kiranta na fada nace wallahi na makara anty kuma gashi yau muna da test da zamuyi idan ban tafi a cikkn lokacin ba akwai matsala .

Ke ina wasa da kene nace ba zaki ba yau ki mutu oya jeki cire kayan na oloshi omo burku olo popo kina wani simi simi dake kamar mutumiyar arziki can.

Haka na juya simi simi zuwa dakina saidai kafin inkai dakin kuka yazo min mai karfi na fada dakin na karasa sakewa cikin takaici.

Daga anty har mijinta suka fito cikin tashin hankali suna tambayan ba,asi nan take fada masu cewa yarinyar nan munafukace ta gaske.

Wai don nace ba zata school ba ta tsaya tayi wanki shine ta azawa mutane kuka don shagwaba kinga irin abinda muke fada maki ko baki yarda. ?

Haba Anty ki barta taje makaranta indai Maryam ce da tadawo zata wanke komai koba a fada mata tayi ba ai sai tayi cikin anty nawa da fada a cikin harshen yarbanci


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login