Showing 159001 words to 162000 words out of 395027 words
Chapter 54 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
gaskiya ba maryam ta dauki kira bashi bane a kan layi tunda naji tace ekale Alaja fausa ?
Nagane hjy hafsat ce da suke kira da Fausa ota din matan wani ogan su anty dinne matar mai kudice sosai suna shiri sosai da iyayyen gidan nawa tun zuwana a tare na samesu suna hurdansu har zuwa wanan lokaci.
Nan naji ta soma zuba magana a cikin harshe yarbanci kafin inji tayi shiru da alama rarashinta akeyi yadda naga tana kada kai kamar a gaban Alajan take lokacin.
Saida ta gama wayan na nisa ina fadin anty kiyi halkuri komai lokacine idan kikai hakkuri komai zai zama labari wata rana.
Ko bai fada maki ba koya fada dai da kudinshi zaiyi hidiman nan ai don haka kiyi hakkuri yadda Alaja ta fada ayi taro nan lafiya.
Ki san dai zama da yare masu nasu al,adan ya bata wanan bawan Allah wai sai yanzu za ayi sunan yaron da a ka haifa mashi dan wajen Yabi .
Wai hakan ba komai bane su a wajensu sai lokacin da mutum ya samu hali ko ince zarafin yin sunan lokacin ne mutum zai shirya ya tara mutane ayiwa yaro taron suna wano iya shegen sai a bariki.
Inda arewane ai tuni yaro ya tsufa da sunan shi ko idan kuma aka kara ko yan kwanakine an samu abin gori da sheri a cikin gari ana gulma ga abinda ya faru da matar wani ta haihu.
Amma shi din yashigo bariki yanzu ya kwashi akidan yan kabilu yana koyi dasu hakan kuma gashi sai girshi yake fadawa antyna cewa wai za ayi taron sunan yaron nan nasa da Yabi ta haifa mashi.
Alhalin matar nashi na jiranshi ya bata kudi mai tsoka yadda suke alkawarin zai bata kudinta da zaran kudi sun shigo mashi.
Sai gashi ya zo mata da wani zance na suna saida ta gama saurarenshi take tambayanshi kudinta fa?
Nan fada ya barke shine yakai karanta wajen Alaja don tace bar mashi gidanshi zatayi ta gaji bata iya zama dashi kuma a yanzu.
Zancen data shigo fada min ke nan sai ga wayan Alaja din data dinga rarashinta tace bayan ta gama wayan take fadin ita gaskiya ta gaji ba zata iya irin wanan auren ba.
Gara kawai su rabu din kowa ya kama gabanshi thank god ma diya daya na haifa dashi d only thing shine idan na tuna ta hada jini da muranen ku na arewa sai inji raina ya baci.
Don ina barin gidan nan ba kasan nan zam tsaya ba gara in ketara zuwa wani kasan zaifi min sauki.
Ido na zuba mata ina mata kallon kanta daya kuwa daga zancen sunan dan kishiya sai zancen fita anya kuwa sunsan darajan aure kuwa ?
In hakane kuwa ashe matan aurewa suna hakkuri su da za a auro masu fiya da biyu a tara gida daya ga kofa ga kofa ana rayuwa a waje daya kuma kowa da yaranta haka za ayi rayuwa a cunkushe da juna.
Gaskiya tayi karami hauka lokacin da Fati tayo mata waya tana fada mata cewa taji kyasham din cewa za a baiwa Paapa maryam ya aura bata tsaya jin zancen ba ta fara fada sosai a lokacin har Fatin saida taji tsoro ta kashe wayanta.
Kwana biyu ta kasa kunne taji ance na dawo bataji hakan ba tacigaba da addu,a tare da fatan kada Allah yasa hakan ya kasance din.
Sai taji shiru a lokacin saida aka dan kwana biyu ita antyna din ta kira Fatin da kanta tana labarta mata halin da muke ciki.
Inda anty Fati din ta nusar da ita da tabari suyi bincike a hankali ko zata gano idan da gaskene amma idonta ya rufe a lokacin kishi ya hanata sarauraranta .
Hakan yasa anty Fati din dana sani furta wanan zancen ga anty don taga rashin kyautawan hakan gareni ko yayane ba zataso ace itace tayi silan raba mu.
Yau gashi ba don banda riko ba da bata san yadda zatayi ba da kunya tunda Paapa daya tashi sai yayi mata bazata ya dauko mata wanan matar mai bakin baki irin yan duniya din nan da angasu ba sai ka tambaya ba.
Sam ita bata da hayaniya gaskiya bata son yawan surutu asalima bata damu da irin kishin mu na hausawa ba don da ace hajja yabi zata bita da zasu zauna lafiya a fahinta na saidai ina hajja Yabi irin matan nan ne masu yadda magana any how akan kishi ita kuma bata saba da hakan ba.
Wanan yasa take ganin barin mijin a yanzu shine daidai don bata iya jure hakan a rayuwanta tun lokacin da naji hakan a gareta hankalina ya daga sosai da jin huluncin da take kokarin yankewa kanta din lokacin.
Tana gama babatun ta a waya nake fadin kina nufin idan kinyi hakan taci galaba akanki ke nan anty ?
Barini Maryam taje tayi taci gara in matsa in bashi wuri ban iya wanan haukan nasu don Allah shiya sani maryam dana barshi ina gama idda zan samu wani mijin daidai dani.
Dakin ga boni na fada a raina a fili kuma cewa nayi da ita haba dai ballema ba inda zaki anty saidai ita datazo ta sameki ta tafi ko su canza gida.
Maryam ki barni kawai kome zaki fada a yanzu ba jinki zanyi ba na riga dana yankewa kaina hukunci ko ba za ayi haka ba anty ki dai kara daurewa.
Kamata yayi daya fada maki hakan aida baki nuna mashi bacin ranki ba sai ki nuna kinji dadin hakan a gaban shi daga baya sai ki nuna kema kina bukatan wani abu a wajensa mai muhinmaci kinga aida kunya yace ba zai maki ba.
Hakane amma dai barshi kawai dai gara na dan gusa daga nan din yafi tunda ya gaji dani a yanzu hakkuri nayi ta bata budan bakinta tace.
Wai kinsan me da ace nasan hakane da zugan dana dunga dauka akanki maryam da ban yarda na maki hakan ba da lalabashi zanyi yama aure ki don ko yayane ba zaki min wanan iskancin ba ai.
Ni god forbid bad things anty hakan ma ba zai taba yuyu a kaina ba in rasa wazan aure sai mutumin da nake kallo a matsayin mahaifina ?
Nidai naci gaba da bata hakkuri kan komai mutum ya gani a rayuwansa daga Allah ne Allah ya rubuto maku hakan a zaman ku sai kiyi fatan kada Allah ya baki ikon da zaki cuta masu su duka din su biyu amma kice zaki fita kibar mata gida hakan take ai dama yasa take maki iya shegen nan.
Shigowan Paapane dayazo ya daga labulen dakin nawa saidai bai shigo ba daga kofa ya tsaya yana bin mu da kallo a yadda ya samemu zaune din da ita.
Nina samu da kyat bakina ya bude ina mashi sannu da dawowa a lokacin ya amsa a sanyayye yana fadin na dauka bata nan ne ai ?
Kenan hakan yana damunshi ya dauka ta tafi din don a gaskiya tana da niyar tafiya kamar yadda ta fada din don a wullakance ta dago tana fadin aiba zan tafi baka ban takardana na ba.
Kinji ko ya juyo yana fada min kinji shirmen antyn baki ko maryam tun jiya muke wana rigiman da ita don Allah yana yuyuwa maryam ace banwa yaron nan suna ba ?
Yaron nan fa jininane nina haifeshi donshine ma nazo dasu don ayi komai a gabanta ta zama shedu ammata ki fahintana ta gane sai tashin hankali take min ita zata bargida.
Cabdi jam lalai namiji namijine na fada a zuciyana saidai a fili cewa nayi dan Allah kuyi hakkuri uncle Paapa wanan abin baikai na aji kanku ba yadda kuke da anty .
Itama sai a kamanta ai mata abinda ya dace a zauna lafiya amma don Allah ayi hakkuri uncle na juya wajenta tare da hada hannayena a waje daya ina fadin Obinu anty edakun naji ta fada a sanyayye murya kasa kasa sai taban tausayi sosai a lokacin.
Shima ya juya yana fadib to tayi mi list din abinda take bukata har ku kafin taron ya juya ya fita kafin wanin mu yace tak a dakin mukaji muryan hajja Yabi tana fadi.
Abin kunya mace ta tsaya tana jan namiji haka don baisan ciwon kanshi ba komai bakin ciki dai sai anyi abinda ba a son ayi banji ya tsaya kukata ba ya fice mun kai wani lokaci zaune a dakin muna hira da anty din.
Sam na manta da zancen Ozil ina faman tausan antyna din in daiga ta fita zancen duk abinda zasuyi waina sunan dan nasu.
Nikan akan Paapa nasan ashe duk namijin daya bar arewa ko wani tambada zai iyayi a rayuwansa da sunan so don kuwa ga paapa dai mutum har mutum amma son zuciya yakaishi gayin abinda ba daidai ba.
Watau shine hikimar iyayyen mu nacewa aiwa mutum auren farko a garinsu da namiji ke nan iyayye sunfi son a fara da auren yargida kafin ayi auren bariki.
Don abubuwa da dama a rayuwan mutum yanzu shi Uncle dai ba mace ta gari guda daya da zai nuna a matsayin mayar kunya daga cikin matayenshi saidai in saukin kaine antyna tafi sauki kai sosai da Yabi.
Zaune nake a aji ina karatu don akwai rana irin mai kudan kai din nan na Lagos hakan yasa na zabi zama a cikin aji ina bitan aikin da mukayi karshe.
Dan firgita nayi don yadda ya kada min hannayenshi daidai kunnena na dan harareshi ina murmushi kazone ka ban tsoro kawai ?
Ya zagayo ya zauna kusa dani yana fadin na duba chamber banga kin fito ba yau nayi tunanen kina a zaune na dan ware ido ina fadin akwai zafi yau garin sosai .
Hakane nima naji dadi dana sameki a nan din don mu tattauna akan zancen da nayi maki don lokacin haduwan naku yana gabatowa gashi bamuyi shirin komai ba har yanzu daga bangaren mu ?
Zancen me ke nan na tambayeshi cikin basarwa yace zance akan maganan da nayi maki last week akan mutanen da zaki gana dasu.
Abar zancen nan Oga Ozil nan ya fara fadin No No No don't do that please meye matsalanki kudi ko kariya kinsan duk wanan ba matsalanki bane a wajena ai ?
Kawai yardan ki muke so don ke din me sa,ace a cikin mutane bamu taba shirya abinda kikai fail din muba yasa nake matukar mutunta lamarinki.
In ma wani abu kike tsoro daga gareni kisa a ranki cewa ba abinda zai sameki kan hakan don mu din bamu abinda kike tsamani don haka for my sake ki daure kiyi muna wanan aikin koda hakan zai zamo na karshe da zaki muna please ?
Shiru nayi na dan lokaci ga irin taimakon da Ozil yayi min a baya ba zan iya fitowa fili in nuna mashi kiri kiri ban iya taimakonshi ba a yanzu kuma.
Yayin da wani sashe na zuciyana ke tuna min da irin worning din da paapa yayi min kan wanan harkallan na shiga kaddara da mukeyi.
Inda ya tsaya min a rai shine bhhhe da yake fadin a tunane ba amfani suke dani suna cin riba ba fiye da dan abinda suke bamu din dake rudin mu idan na jawo rikici gida zai kira ya sheda masu.
Muryan Ozil dake fadin mena yanke a yanzu ya kureni da ido yana son jin amsa,na a lokacin banda tace yadda naga yanayinsa ya nuna idan nace ban masa zai dauka bamu da halarci mu hausa donshi na bude baki ina fadin is Okey Allah ya kaimu.
Farin ciki ya nuna sosai yake fadin yau din nan idan an tashi daga school zai daukemu nida linda muje ayi muna sayayya duk wani abinda zan bukata na sakawa da sauransu dato na amsa mai ya tafi ya barni a tsaka mai wuya ina zullumi a raina.
Ni bawai kudin a yanzu nakewa ba mutumcin da yai min a baya kawai nake duba na sani ba wani aikin kasada bane na dauki hakan da farko.
Amma yanzu da aka tsoratani yasa na gane akwai hatsari a cikin harkan komai wayau na Paapa ya fini sanin abinda ke cikin har duk da iyaka zamuje mu zauna da mutum mu mika mai takardan wajen ya duba sai daga baya mu biyo mai da bayani yadda zai fahinta in hakan yayi mai sai in hadashi da manyan wajen shine kawai aikin namu dasu wanda muke samun kudi masu yawa ga hakan.
Kudin da sai dan tsakwara nakeyi ban komai dashi iyaka na sai dan wani abin sakawa a jikina wani lokacin shike nan abinda nakeyi da kudin nawa.
ZAINAB IDRIS MAKAWA[8/26, 10:11 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
5️⃣1️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15_ HAWAYEN KADA🐊
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Ban boyewa antyna yadda mukayi da Ozil din ba na fadane don ta fadawa Paapa kada yace na kyatare zancen shi kuma.
Don a gaskiya a yanzu in ban tausaya mashi ba baku zanso in jefashi cikin wani tashin hankali ba kuma ai duk da ina addu,a sosai kan lamarin bayan addu,an da nakeyi kafin naje sai nabi almajiran layi na raba dan sadaka nakan tafi.
Wata kila hakan ne ke jawo min sa,a a rayuwana da suke gani kamar wani isimine gareni dake jawo min sa,a da nasaran da nake samu.
Ranan bamu samu fitan da zamuyi ba sai washegari muka fita dasu din kamar yadda yace haka dinne don kuwa sayayya yayi min na alfarma na kece raini daga sutura har zuwa handbag da shoes masu tsada.
Karfe shidda da wani abu na yamma na dawo gida dakina na nufa da kayana duk da suna zaune a falo gaidasu nayi na fada dakina.
Wanka nayi tare da alwala kamar kullum na fito na tayar da sallah don kiran da ladani uguwan mu keyi bayan na idar da sallolinane ina zaune wayana yayi dan kara..
Tun kan in duba nasan mai iya min hakan Saudatce a kullum aikinta ke nan yi min flashing a waya na dauka na fara fadin ke kenan baki iya kira sadai ki dannowa mutum hasken waya ?
Yayan mu innace ke son magana dake ta fada na dan gyara zama ina fadin bata waya a daidai lokacin Amira tashigo dakin tana min magana a cikin yarbanci yana da wuya kiji yarinyar tayi hausa ko tayi din ma bai zuwa daidai.
Inna ina wuni na fada ta amsa muryan ta da damuwa tana fadin meke faruwane wai sai yau yaran nan ke fada min abinda ya faru ai ban sani ba.
Name inna tace abinda Fatin gidan Alh iliya tayi maki mana wai ashe yaya taje da wani zance gidansu ita kuma bata bincika ba takira tafadawa uwar dakinki ?
Inna bakomai bane fa kada hankalinki ya tashi ai zancen ya dade nan dai na dan fada mata kadan kuma nace komai ya wuce a yanzu tunda sun gane ba gaskiya mama ta fada ba.
Ba zan kyale ba in abin baiyi har yakai suji magana haka ba bincike ki dawo gida yar yaya inna zan dawo gida ai amma yanzu karatu nakeyi yasa duk dadewan nan ban zo ba ai.
Anan din nake fada mata zancen auren Paapa din tace to kin gani nasan shi yayan taji saboda sheri ta kira ta tayarwa mutane da hankali.
Gaskiya Fati ta ban mamaki da bata tsaya bincike ba ta daga waya ta kira matar nan da wanan zance wallahi fati tasa ban yarda ds kowa ba yanzu .
Abinda