Showing 216001 words to 219000 words out of 395027 words

Chapter 73 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

Ban dauko ba kuma ban fita ba sai da akai kiran azahar a wayana na mike na shiga dan karamin toilet din nayi alwala.

Na fito na shimfida sallayan dana sayo don office tare da hijjab don sallah a nan idan ya kamani ina tsaka da sallah aka turo office din saidai banji motsin fitan maishi ba sai zuwa can naji fitanshi daga office din yayin da sakon kamshin turare ya sanar min dako waye wanda ya shigo a lokacin.

Bandashi banji wani dake amfani da yake shafawa a company asalima dai a garin gaba daya zance.

Sai bayan na idar na dan juya ya fitako a lokacin don haka na karanto addu,oina a tsanake na shafa na mike na nade sallayan na mayar wajen da nake boyewa a office din.

Idan ba bata nayi ba baifi yan kwanaki ba na bar aikin nan mu koma school don hutunmu daya kusa karewa a lokacin.

Wanda har yau kuma paapa ne ke biya min makudan kudin karatuna na ko wani shekara tun bayan daya gane irin abinda anty tayi min a baya.

Wanda a nawa lissafin na dauka cikin punishment ne hakan da tayi min a lokacin bisa rashin fahinta irin nata na karamin kwakwalwa duk da nafi ganin laifin mummyna fati a raina kan zancen.

Ban kai ga kare tunanen ba aka kara shigowa office din shine fuskanshi a daure na dan zauda ina gyara zama ga yadda nake zaune shima waje ya samu ya zauna muna fuskamtar juna dashi ya soma fadin.

A yanzu na yarda da abinda sulaiman ke fada akan mata ku din mayaudarane don wanda bai gane ku ba saiku wahal dashi dama kina tafiya da wanan katon hijjab don ganawa da ubangijinki sai kin gama ki kama yawa kamar doki ana kallonki ko ina ?

Wani dan kallo nayi mai ina dukar da kaina kasa don banda abinda zance a lokacin don nagama fahintarshi don duk ogan kwarai ba zai dinga hakan da yake min ba ?

Ke nan hasashen oga sulaiman akan mu yana son zama gaskiya ke nan kome don gaskiya wanan mutum yana shiga min rayuwa da yawa ta hanyar shammatana.

Gashi a yanzu yana min kwarjini sosai a idona wanda bansan lokacin da hakan ya fara zo min ba ko don yawan ganinshi da nakeyine yanzu oho ?

Koka dai don ya zama ogana a yanzu yasa nakr jin hakan a tare dani duk lokacin daya tsaya min a gabana sai in matsu in kauce a wajen.

Ko yanzuma din ido ya zuba min yana kallona jin shirun yayi yawa na dan dago kai na dubi inda yaken zaune ya soma fadin.

A ina kikai karatun secondary dinki cikin mamaki na kara dagowa ina fadin a kano man na soma yi nazo nan na karasa ss dina.

Kinyi karatu a kano ke nan nayi na fada a takaice don in katse mashi tambayan gaakiya you are lucky don kin samu good foundation sosai dan da farko na zata ba zaki iya wanan aikin ba.

Na dai zabokine don ke hankali na ya kwanta da zaki iya hakan amma banda tabbacin kin iya din sai an baki traning na dai zata iya zaman office da sauran abubuwa kadai zaki iya a yanzu sai gashi ashe kin wuce wanan ke ban sani ba so na gode bisa wanan aikin da kikai min a yau sosai wallahi.

Kallonshi nakeyi kamar a mafalki nake jin zanceshi zakice bashine a gabana a lokacin don na kasa tsayawa in fassara me hakan ke nufine wai lokaci daya ya sauya min daga oga Aley haidra zuwa Aliyu a yanzu.

Anywhere naga kaman baki fahintana a yanzu don nazo maki a wani siffa na daban yanzun din iam Aliyu Ahmed yakubu .

Zaki iya kirana da A A Y don dashi akafi kirana ba kowane yasan da sunana nakwarai ba irin hakan sauran bayani daga baya sannu a hankali zaki fahince don yanzu na fahinci baki sauraron abinda nake fada maki din.

Dan gyara zama nayi daidai lokacin da yake mikewa din naji yana fadin only thing shine ki yarda na sanki tun kina karama a kano a wajen gidan malam Innu,wa na malam hamza kin yarda da hakam ?

An dai fadama hakan da kayi bincke ko ok baki yarda na sanki ba ke nan tunda ban kamaki a lokacin da kike zane min mota da rubutu na tsatsaleki a lokacin da kin tuna dani yanzu ai.

Wani guntun murmushi ya sauka min a fuska jin cewan da yayi ya tsatsaleni nace kamar wanda ya samu yarshi ke nan dai ?

Mata kuna da saurin girma na yarda da hakan akanki son yadda na barki na dawo kuma iske kin girma a nan Lagos shima still kika bi min mota da kallacewa da har na fara zargin keko aljannace dai ?

Ni da aljanace aida kai zan fara tashi irin yadda ka tsaneni din nan har kake min mugun zargi daba shi ba ?

Ni yanzu ina son sanin abinda kake bukata a wajena da kajawoni zuwa wajen nan da bai dace dani ba a yanzu aiki ba takardu ba wani kwakwaran hujja na shedan hakan amma kuma aba mutum aiki haka zikau dole akwai ayar tambaya a lamarin nan.

Ki jira very soon zaki fahinta duk da nasan kina min kallon wani mugu a kasan zuciyar ki abinne ya kai ga hakan dole saina biyo ta wanam hanyar zaki fahinceni.

Yaja kafan shi ya fice ya barmi tsaye ina bin shi da kallo cikin mamaki kafin in sauke ajiyan zuciya ina duban laptop din dake gabana a bude.

Yaki ya ban amsan daya dace da tambayana don abinda na nazarta tsakanin dare zuwa safiya abin ya ban tsoro lokacin sosai .

Ta yaya za a ha,inci mutum wanan miliyoyin kudi masu yawa haka ace bai fahinta ba nikan nasan ba iya haka bane manufashi a wanan aikin dole akwai dai ?

Time nayi na mike na fara tattara kayana dan zuwa gida duk da nasan gidan kona koma bacin raine kawai zanje in sama a gidan kan mommy.

Wace satin ta kusan ukku yanzu da zuwa gidan namu wanda kusan zance zuwanta nice aka kuntatawa ba wani ba.

Dama wancan zuwa tana da lafiyanta illa fitinantane kawai a kaina lokacin wanan ko ta fake ga ciwo tana kuntatamin kuma ga zagi da cin mutunci irin wanda ta iya.

Gidan namu tsit koda na shigo zakice ba kowa a gidan na karasa falon da nasan bai samu gyara ba run bayan wanda nayi da weekend kafin a shiga ranan aiki.

Dagashi kuma sai wani satin idan na fito na gyaraahi ban daukeshi komai ba tunda aikinane tun farko girkine kawai sai naga dama nakeyi yanzu idan kuma ina bukatan cin girkin gida zan tsaya in girka masu mu zauna muci.

Don koda mummy tazo din nan taso sakani wanan aikin wahalan data saba sakani anty ta nuna mata bata son hakan don Paapa ya saka dokan wani aiki a kaina haka yanzu.

Take fadim ehh lalai yarinya dole kiyi takama tunda an kama maki har girkin daya kawoki ma saida ku san munafuncin da kuka hada akanshi.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[9/11, 9:23 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊6️⃣7️⃣🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Idan kinga innan mu a cikin dan kwanakin zaki fahinci sauyin rayuwa a wajenta don idan rayuwan bawa bata a cikin tashin hankali daga gangan jikinsa ake fara gane hakamn.

Don inna har dan haskenta na asali wanda ya dushe a baya a yanzu ya fara dan baiyana mazaunanta da azaban mama ya zubar sun fara dawowa a ganganjikinta.

Kashin wuyan da mama ke samu ta zaga ko agaban kowa a yanzu sun fara dancika suna bacewa daga idanuwa.

Kallon tsab da mama ta karewa inna dake tsaye tana magana da wace tazo sarin turaren kamshin daki wajensu daga unguwar kabo shiyasa maganan zucin mama fitowa a fili.

Wai Ai kece haka ko idona ke min gizo ko kin fara shafa man nan da akace yana sauya halittane kuma irin na yaran zamani ?

Daga inna har matar suka juyo gun mama cikin mamaki suna kallon ta tace Allah gaba daya Ai yau kin canzawa ganina kin koma Aishan ki na baya lokacin malam yana kiraki da wani Aisha can.

Yau kuma yaya sherin da aka tashi man dashi ke nan a gidan in shafama wa mai kuma ni wallahi kinga vasseline din mu can dagani har yaran nan da yarinya ta aiko muna dashi shine nan muke ta murzawa har yaran.

Saidai kamshi kan inkince na shafa wanan kan ina dan murza kamshi a jikina ko wani lokaci tunda kana tsaye kana aiki saboda tsami.

Kamshi kam maman Saudatu ai dole ki shafa shi donko lungun nan naki mutum ya kawo kamshine zai tari hancin mutum ko baki shafaba sai yabi jikinki.

Lafiya dai ta samu dama hakane indai hankalinka a kwance yake ba abinda ya tsayama a rai dole jikinka ya nuna hakan shima ?

Wani nisawa mama tayi daga inda take tana sauraren matar dake zuba kamar an kasa da ita mai abu shiyasan kayanshi don inna ta fahinci sauyin mama a lokacin yasa tacewa matar.

Yanzu hjy za a buga waya ta turo maki da wanan din da kike so kinga sai ki fara tafiya da wanan da aka samu to shike nan don Allah ayi min kokarinshi maman Saudat don mata da yawa suna son wanan turaren yana da kamshin dadi sosai wallahi.

Na tura kasuwa anyi yawo ba a samu irinsa ba yasa na taso da kaina za a kawo insha Allah barin kira ita mai kayan a maiduguri take ai ba nan ba saita sako muna shi da dan yawa a cikin sakon mu tunda ko nan naga anaso ai.

Wuri mama ta samu ta zauna tana sauraren abindake wakana tsakanin inna da bakuwarta har kudin da matar ta zaro masu yawa ta mikawa inna duk a idon mama don zafi daya hanasu shiga daki.

Sukai sallama inna ta bata kayanta ta rakata har kofan gida ta dawo mama na zaune a inda ta barta ta duka zata dauki sauran ta mayar daki taji mama na fadin.

Duniya sabuwa inka fadi ace don me gaskiya mai dacin fada a yanzu danka na cikin bariki yana turo maka da arziki haka gida amma ko a jikin iyayye don son abin duniya ?

Umm,humm yaya ke nan yanzu aiko da bashiga barikin duniya ba ko a dakin uwarshi yake yana bariki nawa akayi muna gani a kullum saidai yarinya ta wanke kafa sai lokacin da yai mata dadi zata dawo gidan .

Da haka ba gara mutum yayi barikin mai lasisi ba data tsiya ko a hakan an godewa Allah don shine mai kaddarawa bawa komai zato kuma zunubine koda ya zamo gaskiya.

To yanzu ni kike kokarin dasawa magana daga fadan gaskiya ikon Allah yaya magana kikayi na baki amsa daidai da zancen ki barikin nan yanzu gidan kowa a kwaishi dakin kowa an aje dan bariki nagani ?

Basai ma ka fita kaje duniya ba a dakin uwarkama sai kayi abinka kiri kiri ba abin kunya bane ita bariki yanzu ai kowa da kalan jerabawan da ubangiji yake jefo mai a dakinsa idan ka ruguma da hannu biyu sai Allah ya sauya ma hakan ya zamo alheri a gana gareka.

Ai, ke nan kodai ba a so sai an fada ko mu nagida bamu fada ba nawaje ba a hanasu fada ai tunda abin fada ya samu dole a fada.

Na alheri ba sai makiyin Allah mai mugun nufi a kasan zuciyarshi dake juya zance kan dan wani gashi da mugun abu a tare dashi yaje kaken zance gun dan wani.

Wai meye haka don Allah ku ke nan don Allah baku girma kullum a jiku a gida kuna fitina ina ruwanki da fada mata gaskiya sun nemi shawarankine mama ?

Kayan haramun din da kike fadi naga idan an kawo kema kina karba kiyi amfani dashi kikan fara zancen ki kenan ya zo ya zama babban magana kuma ?

Innan mairo don Allah kuyi hakkuri abar zancen nan haba dai don Allah ku ke nan dai kullum wanan ya zagi dan wanan da mugun lafazi wanan ma ya rama kuna faman aibanta mu da mugun abu kamar baku kuka haifemu ba haba dai don Allah innan mairo na rokeki haka wanan abu ba girmanku bane don Allah yanzu.

Mu dai kukewa fadan nan a kan mu mu kuma bamuki junan mu ba muna son junan mu kannen mu suna son mu muma muna sin abin mu in zakuyi fadan ku kuyi abinda ya shafeku kubar sakamu a ciki don Allah ?

Ke kuma inna zanje in fadawasu Nane gaskiya ni abin ya isheni wallahi mutun yana cikin damuwan abinda ya dameshi amma kullum ki dauko mashi zagi da cin mutunci ?

Zaki zagi natane ta kyaleki tunda ba kurma take ba don Allah innan mairo kuyi hakkuri hakan da inna taji yasa ta shige daki ba tare data tankawa kowansu ba kuma.

Itama Sahura din daki ta koma bata tsaya kara maganawa mahaifiyar nasu ba don haushi tunda ko tayi tasan baji zatayi ba don tunda taji sallaman wanan matar ta mike ta fito tacewa uwar ina kuma zaki mama ?

Kibar haka don Allah sai a dauka sa ido ke fitar dake da anyi sallama ki fita zaram in wajen ki mutum yazo ai dole ya nemiki irin sa idon nan yana halaka mutum wallahi ?

Bata kula diyan ba a lokacin ta fito abinta zuwa can ko tajo sun fara sababi a tsakaninsu shine har ragaji ta fito ta raba fadan dama itace mai kokarin tsayawa tayi hakan don ita murja idan tana gida kokari takema ta shige fadan tace innan mu tana zaginsu .

Don haka mama diban takalmanta tayi tashiga makwabta ta jima a can bata dawo ba har yara suka dawo daga school kowa ya shiga aikin gabanshi.

Izuwa lokacin inna ta fara saka damuwa a kasan ranta na inma karatu nakeyi hakan nagama nayi aure ta huta da ukuban zargin mama a kaina kullum.

Tun tana fada ba a yarda dole a samu wanda zasu yarda da gaskiya take fada akaina tunda gida daya suke taganine ta fada ai ba karya ta fada ba.

Dole ta zauna da malam idan ya dawo ya tuntubi oga Faruq aji me nake ciki a yanzu lokaci yayi dako matsaya nakai gareshi ko zata samun saukin wani abu da mama din ke mata a kaina hakana.

Don haka da yamma da baba ya dawo misalin tara na dare tayi shimfida a kofanshi tare da fito mai da abincinshi da komai da zai bukata a wajen.

Sai bayan ya kitsa yafito ya zauna ya soma cin abinci lokacin ne mama tazo gaidashi yau da gobe sai Allah sanin halin kowa a gidan ya fahinci mama na busan iska dole akwai abindaya faru bayan fitarshi ke nan gidan.

Sharewa yayi yana saurare ko wani zaiyi magana baiji komai ba hakan yasa ya fita zancen nata don ita mama koda yaro tayi fada saika gane don zata wuni da bacin rai a fuskanta bakin rai yana cinta a zuciya.

Innan muce tazo karshe ta kwashe kayan abincin har tagama kintsa har cikin gida kafin ta samu zama dashi yadda suka sabayi a ranan girkin mutum.

Dan hiran kasuwa baba ya soma yi inda tace dashi nikam malam don Allah ga shawara baka kiran Oga Faruq akan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login