Showing 246001 words to 249000 words out of 395027 words
Chapter 83 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
/>
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Tunda na dawo na kwanta ban fito dakina ba sai dare idan da sabo sun saba da wanan halin dana dauko a yanzu.
Ban faye damuwa da surutu ba dama ba yawan maganan nake dashi ba haka to yanzu sai na kara canzawa a gidan gaba daya ina taka tsantsan don ban son abinda zai kawo fitina da hajja yabi data sakoni a gaba da sherinta a yanzu.
Kitchen na nufa don dafa ruwan zafi insha ko shayine a cikina kafin in kwanta ina dauraye tukunyar da zan dora sai gata kitchen din ban kulata ba don ba magana mukeyi a tsakanin mu ba dama.
Wai jaraban lake ke nan kazo ka zauna a gidan mutane kace kai sai abinda kaga dama zakaiwa mutane a gida don samun waje aini yanzu ban mamaki tunda na gano bakin zare.
Na juyo na dubeta tana a tsaye wajan fridge ta bude take wanan maganan ban kulata ba nayi kokarin hada gas din gabana na dora takara fadin wai kaddara mace ki dauko mace haka gidanki don rashin sanin ciwon kanki takoma baya tanaci maki miji don kaddara.
Kece babban kaddara Yabi babba dake haka tsofai tsofai kin shigo masu rayuwa kina takurawa bayin Allah.
Aike kaddarace babba wallahi don kowa ya ganki gidan nan sai a dauka ke yar maigidance don ba mai zaton ke matarshi ce haka ?
Da an dubi uncle ansan zaman kaddara yakeyi dake da hakkuri don sam ke din kin wuce sa,an aurenshi saidai ko babanshi ko kuma babban yayanshi.
Kin dauka kowa irinkine a watse saida kika gama cin mazan saudiya suka izoki gida babu ko guzuri akazo kano aka yasar dake a wullakance kokin dauka bansan rayuwanki bane wai ?
Ki matsa min sheri na fallasaki gun uncle nima har abinda bai sani ba game dake wallahi saina fada ya sani kuma kazafin da kikai min dashi ban yafe maki ba kema aikin haifa zakiga abinki dama kin saba ganin hakan kuma zaman takarinki a saudiya fa ina da labarin komai .
Tunda ni kaddarace sai kiyi maganin kaddaran yau kisa a koreni daga gidan nan bashine fatan ki ba ki bude ido kiga nabar gidan.
Idan na bari sai ki gani idan na kwana a titi irinki da kika fake da sunan gudun hijara kina yawon cin mazan mutane.
Nayi tsuki na harareta itama bawai bakinta yayi shiru bane a lokacin tana jefo min amsa daga bakinta na zazzaro mata magana masu zafi da take boyewa tana dauka bamu sani ba.
Na juya gun gas din na juye ruwan zafina a cup na fito muka hade da antyna a kofan kitchen din.
Kallona tayi take fadin meya faru kuma haka kuma wai ?
Na soma koro mata abinda ya faru har amsan dana bata ban boye komai ba na fada mata gaskiya tare da karewa da fadin ta zata ko ba,a san tarihinta bane ?
Ta maida kallo cikin kotchen din ta juya gun yabi tana fadin haba haba ina wanan maganan ya fito haka kuma don Allah a bakinki ?
Tana soma daga muryawa anty dake tsaye sororo cikin mamaki tana kallon Yabi din paapa dake gidan ba wanda yasan da shigowanshi sai a lokacin yayi gyaran murya .
Lokaci daya gaba dayan mu duk muka mai da kallon mu gareshi yana zaune ya harde kafa saman kujera.
Yabi ta soma kauce zancen tana fadin ni zakuyiwa taron dangi don kunga ina kyaleku zaki dinga turota tana min iskanci har ta fada min abinda taga dama ?
Don kunga ana kama mata idan tayi min a hanani magana da kizo da kanki mana tunda kina jin haushine aiba sai kin turo min yarinya ba ?
Mamaki ya kama antyna lokaci guda don yadda yabi din take kokarin juye zancen lokaci guda haka saboda iya makirci irina tsofin mata.
Ya nunata yace dama yabi haka kike makira munafuka ana fada ina dauka kazafi kawai ake maki don ba a kaunarki ?
Ke din nan zaki iya kashe mutum ki bizneshi a dauka bakece kikayi ba na dade da fahintar hakan amma ina jiran wanan ranan da zan kamaki haka dumu dumu gashi kuwa ?
Ke nan yanzu nice mai lefin keko son fada tunda an hade min kai don anga kana yarda da duk abinda akace maka nayi gidan nan.
Me zaki fada min yanzu bayan wanda idona da kunnuwana suka gane min a gabana kowan ku ya mayar da zance shi.
Don kin daukeni sauna gani wanda uwarshi tayi haihuwan baza gani sha,sha wanda aka sha ruwan zafin banza a kanshi zaki fara tsara min makircinki da kika iya.
To naji komai yadda yarinyar nan tace ta barki ga Allah nima hakane yabi na barki ga Allah ubangiji ya saka min wanan bakin kazafin da kike kokari min kan yarinyar nan a yanzu.
Kuka ta soma tana fadin ai fadane ta fada min mai zafi nima na mayar mata da mai zafi irin wanda take fada min a kullum sai ya zamo kazafi a gareni ko ?
Shi dai ya juya kawai ya shige dakinta antyna ta juyo ta dubeni ruwan dake hannuna ta sauke idonta a kai tana fadin ai ruwan yai sanyi saiki kara dafa wani ?
Na juya zuwa kitchen din ina tsaye na sake jin hayaniya wai ashe Paapane ya dauko kayanshi daga dakinta yakai dakin antyna hakan na nufin wani abu ke nan zai faru a tsakanin su idan namiji yai hakan ga matarshi.
Dakina na nufa ban tsaya bin ta nasu ba na rufo kofa ban san ya suka karata ba don na kunna waya ban ma son in saurari wanan shirmen nasu a lokacin.
Na kasa shan shayin dana hada din don bacin rai da wanan matar ta saukar min a lokacin haka na kwanta da kyar barci ya daukeni a ranan sai mafalkai da nakeyi abinda yasa ban tsaya wahal da kaina ba da zancen Yabi shine.
Idan baki manta ba mai karatu antyna ma tayi min zargin irin haka don haka yanzu da yabi zata fada sai bai zama sabon abu a wajena ba koma meye aina hadiyi wanda yafi nata zafi a lokacin.
Don zancen daga gidan mu irin maganan nan ya soma har ake fada min hakan a yanzu don haka ban yarda na wahal da kaina ba .
Tunda na fahinci a na matukar hassada da kyashin yadda Paapa yake min dawainiya haka alhalin niba wata yar uwarsa bace ta jini sosai haka ba amma yake kashe min kudi kan karatuna.
Sun kasa gane yana hakane don cika alkawarin daya daukowa mahaifina na cewa karatu sai idan ninace na gaji dashi lokacin.
Washegari na shirya don fita school duk da safiyane amma hankalina yana kan wanan mutumin da baya da lafiya.
Ina son inji ya yakwana da jikin nasa a ranan don yadda naganshi akwai alaman ya rame a lokacin sosai.
Saida muka fito breafast na samu sukunin kiranshi inji ya jikin nashi a lokacin koya dauki wayan ko bai dauka ba dai na dai kira din zai kuma san dalilin hakan ance ka nunawa wanda ya damu dakai damuwa idan bukatan hakan ya taso gareshi.
Don iya abinda zakaiwa mutum yasan kana kaunarshi shine kulawa don haka iya hakan zan nuna mashi yasan na damu dashi.
Kamar yadda shima yake nuna ya damu dani yana kula kuma da lamarina kamar wani dan uwa na kusa a gareni.
Wuri na samu na zauna ina lalubo wayana daga cikin jakkata na dauko na shiga call numbershi yana kusa yasa na danna kira sai dai kamar an katse kiran naji a lokacin.
Ban hakkura ba na sake danna kiran aka sake irin hakan na sake a karo na ukku a dan hasale an dauka ba a magana a lokacin hakan yasa na kara a kunnena.
Murya can ciki ciki naji muryanshi yana tambayan waye wanan saurayin na bashi amsa da cewa wanan ta jiyane da tazo take kira naji yace miko min wayan ya karba a cikin karfin hali yake fadin hello maryam.
Sir oga har yanzu jikin ne na tambaya a dan kidime cikin nuna damuwa a baiyane ina gyara kara wayan a kunnena lokacin.
Da sauki maryam ya ban amsa a takaice daga bangarenshi sai kuma jikina yayi sanyi don yadda naji muryanshi na fita a lokacin.
A hankali cikin taushin murya na furta sir meke damunka ne meya sameka ?
A jiyan zuciya naji ya sake kafin ya soma fadin maryam abubuwane sukaiwa rayuwana yawa ya saukar min da stressed a jiki amma likita yace ulcer ce tayi min mugun kamu a yanzu kuma .
Ulcer kuma sir baka cin abincine ina matarka take data bari ulcer ya kamaka haka haba dai ulcer ai ciwom yunwace mana .
Tana nan bata kusa dani yanzu kila kulan da ban samune yadda ya dace yasa ulcer din kamani a yanzu katseshi nayi da fadin .
Ayya sorry sir amma laifin na tare dakaine da basu baka kulawan daya dace hakane kuma kila don ban samu mai kula dani bane din yadda ya dace .
Kinji yadda kirjina yake min suya yana zafi wani lokaci sai inji kamar bam cikin hayacina idan yana min ciwo na lumshe idona cikin jin ciwon kamar a jikina yake lokacin .
Na saki ajiyan zuciya karo na barkatai ina fadin sorry sir Allah ya baka lafiya ya amsa da amin tare da fadin wallahi jiya banyi barci ba daughter sai yanzun nan barcin na dan soma jinsa amma na kasa yi.
Gashi kirjin ya matsa min da ciwo sosai na rasa mema zanyi in samu relief akansa ya matukar min suya sosai tun safe haka na tashi da wanan matsalan .
Murya a sanyayye na soma fadin kuje asibiti mana ko a kira likita ya dubaka zaifi ai da zama gida haka da ciwo a jiki ?
Ba sai naje asibiti ba don babban likita makwabcinane koda safen nan ya shigo ya dubani ya rubuta min magani da kuma abinda zanci sun dafa min basu iya ba sun cika mai a cikinsa one spoom kawai nayi naji kamar raina zai fita.
Eyyah sorry sir bai kamata suyi haka ba ka daina cin abinci mai mai ko yaji ko abinci mai nauyi haka sai somethings liquid ko soft ,,,,,,
A ina duk zan samu wanan abinda kike lissafa min din kamar ya a ina zaka samu mwye amfanin matarka daba zata dawo ta kula dakai ba sir ?
Ko tazo a yanzu ai zuwan baida amfani tunda ciwo ya riga daya shiga jikina ko haka dai zan ta maneji har Allah ya ban lafiya hakane .
Amma ba zaka zauna da yunwa ba sir a dai samu wani abin kaci ko zai dan zauna a cikin ka nagode ya fada sai naji hakan ya kara ban tausayi naji ya kashe wayan a lokacin.
A hankali ya lumshe idonshi yana sauke ajiyan zuciya tare da dafe saman kirjin nasa da hanunshi duka biyu a haka Abdul daya shigo da kayan karin kummalo ya sameshi yayi mashi sannu yana fadin ga breakfast ya kawo mashi.
Ya sake sakin ajiyan zuciya yace bar abincin nan Abdul kirjin nan yana damuna sosai sai zuwa dan anjima idan ya lafa min kadai sake min AC naji dan sanyi ko zan samu relief.
Sannu yallabai Allah ya baka lafiya ya fada ya nufi wajen remote yana kara mashi sanyin Ac dake aiki a dakin .
Tun bayan gama wayan mu dashi hankalina yayi mumunan tashi na shiga halin damuwa lokaci guda maman Toyi mai maganin agumo irin kakadiro din nan na yarbawa dake sayar da sayyu ko wani irin matsala.
Kai tsaye namike na nufi hanyar fita daga school din sai unguwansu nayi sa,a tana shirin fita shago sai gani muka gaisa nayi mata bayanin irin maganin da nazo nema a wajenta tace in zauna in jira ta hada min saidai akwai kudi da yawa zan kashe kudi zaikai dubu biyar.
Ba matsala Allah yasa mu dace na fada ina zama a inda ta nuna min din na zauna na dan jima a zaune kafin ta fito da irin gorunan nan da ake zuba magani a cikin sa kuda ukku tare da wasu sayyu ta zauna a gefena tana miko min ta fara min bayani daya bayan daya na bude jakkata dubu bakwai na dauko na bata .
Ta kirga ta dago kai tana fadin dubu bakwai na bata ai nace eeh mama kici goro da dubu biyun ta soma min godiya ta dafani tace tana zuwa ta shiga ciki da sauri ta sake fitowa da wani dan karamin kwalba tana fadin na karba ta soma min bayani yadda zanyi da maganin.
Na karba na mike ina mata godiya tare da duba time a cikin wayata karfe daya da wasu mintuna na nufi titi drop na dauka wanda ya zamo min habit a yanzu tunda nake jin dan canji a tare dani din nan ban harasan kashe dubu uku ko zuwa biyar ga mai taxi.
Ban bace ba a layin duk da ginnan gidajen duk kusan dayane gasu da tamgama tamgaman get a kofofinsu a kofan gidan muka tsaya na fito na sallami mai taxi din na nufi kofan gidan gadan gadan .
Ga abin kallo baja baja unguwar amma tashin hankali bai bari na ba ido abincinsa ba don damuwa don ba gidajen ne a gabana ba lokacin.
Kamar jiyan yau ma din kofan na dan kwankwasa ba,a jima ba aka bude daga ciki yana ganina ya shedani maigadin gidan ke da shima bahaushene dan uwanshi ya dauka saima ince shidai yana da kishin kasanshi na hausa sosai a zuciyarshi.
Sai baya nashigane na dan fara gaisawa da mai gadin tare da tambayan shi ko maigidan yana ciki ya soma fadin ai yana nan kwance nima ciwon oga ya fara damuna tun ranan daya dawo daga kano bai kara fita wajen gidan nan ba dan dama jiyan nan da kikazo ya leko nan haraban .
Wucewa nayi direct ban tsaya jin karashen zancen shi na nufi kofan gidan kai tsaye saidana dan fara taka step din da zankai kofa naja na tsaya kuma a waje daya.
Ina murda kofan ya bude katon falone da yaji manyan kujeru farare masu nauyi sai center table dinsu babba haka ya baje a falon don girma.
Ga tv daya mahe bangon da wasu manyan falawa masu kyau sun saka tv din da sauran na,uransu a tsakiya.
Wanan Abdul din yana zaune yana waya na turo kofan zubur ya mike yana fadin ashe kina tafe sannu da zuwa oga fa na tambaya ba tare da mun tsaya gaisawa ba dashi.
Yana ciki kwance yace yana son ya samu barcine ya fada dan kallonshi nayi nace yana ina ?
Idan kin shiga zaki iske wani dan corridor a ciki dakuna biyune a ciki kofa mai kallon ki na hannun dama shine master bedroom dinsa .
Da sauri na nufi hanyar daya nuna min din ba tare da tunanen komai ba ina jin yana fadin amma dakin bari har ya tashi idan ya fito ki ganshi.
Ban juyo ba sai zagin dana dura mashi kasan zuciyana da dan iska da dan uwankane aiba zaka ce in tsaya ba sai idan ya tashi.
Kofan da yayi min kwatance na bude ina budewa nayi arba dashi a kwance kasa saman carpet yana dafe da kirjinsa .
Jikinshi dan singlet da irin wandon jiya saidai wanan brown ne da sauri na dan taka sai kuma naja na tsaya a waje daya ina kare mashi kallo.
Na karasa takowa zuwa gabanshi na dan duka na kasa furta komai don na kasa fahintar idonshi biyu ko barci yakeyi a hakan ?
Baifi dan second ba naga yana cire hannunshi daya daya kare fuskanshi dashi ya dago kai tabbas ni dince a durkushe gabanshi ya gani don tantama yake da kamshin turaren da yaji yasa ya bude fuska.
Sannu sir na fada a sanyayye yana kokarin karfin halin mikewa yace my daughter kece kuma ba akwai school ba yau ?
A sanyayye na amsa da hankalina bai kwanta bane na baro school din inzo in duba ka don yadda naji muryan ka dazun din ?
Ya karasa dagawa yana fadin sorry na daga maki hankali ko shiyasa ban son daukan waya don kada hankalin mutane ya tashi tundai ke da ummah