Showing 114001 words to 117000 words out of 395027 words

Chapter 39 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

muke dashi ba da nan amma sai make ganin kamar hakan zaifi maki sauki ai.

Amma antynki tace a,a jeka kadawo zakiyi bata yarda ki dinga kwana a can ba tafi bukatan kina gida tunda amananki muka dauko.

Ni abinda nake so shine ki kula da kanki sosai ki mayar da hankali ga karatunkikin daiga yadda akayi kan zancen ki gida don haka yanzu kowa ido ya zuba muna ya gani.

Fada sosai na jan kunne yai min inda a karshe yace zanga sako gun matarshi din in tashi in koma daki nayi godiya na dauki Amira muka koma dakin mu inda muke kwana da ita.

To nidai wanan sakon da Paapa ya ambata har rana ita yau da nake bako labarin nan yar uwa sakon da bangani ba ke nan a wajen uwar dakina din duk da ina da yaknin cewa yabayar kamar yadda ya fada.

Saiya kasance na fara karatu a cikin wani yanayi na lumci da dawowan mu gida na fara fuskantar hakan a wajen uwar dakina amma haka na dake ina karatuna sosai.

Da safe idan na shirya da wuri Paapa zai saukeni dawowane nake shiga taxi in dawo gida inda Allah ya taimakeni ke nan don koda zai saukeni zai kawp kudi ya bani yace in rike a wajena don lalura su zan samu inta tsankwara don yan hidindumun makaranta.

Na kula sosai da sabon sauyin da anty take min yamzu na rowa amma hakan bai damuna a fili tunda a fuska tana nuna min muna nan a yadda muke da ita babu wani sauyin da aka samu amma ni nasan dole akwaishi gaskiya.

Farkon shigana school din na dan sha wuya kadan saboda alkunya irin tamu ta yan erewa da muka gada daga kakanin mu fulani.

Zakiga mutum indai dan arewane musulmi ko kiristan yana da alkuya a cikin sauran al,umma muna da kawaici da jin nauyin abu a bainan jama,a.

Su sai su dauka mu jahilaine bamu san komai ba balle ni da suke ganina ko yaushe a cikin katon hijab wanda ke baiya asalina a fili garesu.

Ganin hakan sai suke min daukan doluwa bagidajiya yar kauye wace bata waye ba gani nan dai a cikinsu sai su nemi raina min wayau kinsan yaruba sunfi ibo wuyan kai kafin ki fahincesu sai kin sha wahala sosai don su ba kamar iyamurai suke ba.

Gashi kuma bahaushe yafi yarda da bayerabe nasan don mafi yawansu musulmaine a gauraye suke da kamar bahaushe nasan wanan yasa mukafi saurin yadda dasu amma suna da wuyan sha,ani sosai ga mu,amula.

Kokarina a aji ya kwaceni daga hannunsu wanda har malaman namu da farko suna min kallon kumju takwala mara kokari bagidaji sai yake sa suna yawan tambayana amsan tambaya idan zasuyi don sun ganni a cikin hijjab ko yaushe.

Wanan budanwan da nakeyi wajen kokarin bada amsa ya jamin kima a idanunsu suka bar kallon da suke min saidai ba ruwana da kowa ko break bani fitowa yi sai tashi.

Ana tashi kuma zan nufo titi in samu abin hawa da zai kaini jection din unguwar mu don kinsan lagos kamar kano ce ko wani unguwa suna da kalan abin hauwansu.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

YAURI KEBBI STATE

[8/8, 10:15 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,



3️⃣7️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15- HAWAYEN KADA🐊 1000.

_Account No._

_*ZAINAB IDRIS MAKAWA*_

2254380105

ZENETH BANK

PHONE NO.

08036959257

Rayuwa idan kana jin wani abu kamar tatsuniya don saika tsanmaci ba a iya hakan a rayuwa ?

Idan kakai wanan matakin ka zamo mai godiya ga ubangiji subbahanahu wata,allah daya tsarkakema zuciyarka daga aiwatar da mugun nufi ga dan uwanka gobe kiyama ku tashi kuna shari,a dashi a gaban ubangiji.

Allah ubangiji yasa mu dace da rahamominsa Allahuma Amin ya Allah yau a duniya duk wanda sunansa yakai ba abanza yakai ba idan mun kula zafin nema bai kawo samu sai idan Ubangiji ya tsaga da rabon bawansa.

Tawakkali da imani ko kaucewa ubangiji bashi ke kai mutum matsaya ba, yardan ubangiji da soyyerwa bawansa shike kai mutum matsaya har ya taka matakin da kowani mahaluki yake fatan cin mawa a rayuwa.

Hausawa sunce inkaga wani ba banza ba haka na sheda wanan domin na dandana karamin kudana kafin na san abin yi a rayuwa .

Don tun lokacib da muka dawo daga arewa ba wani jimawa abubuwa suka fara sauyawa a rayuwan zaman mu da uwar dakina,.

Abin ya somane wata rana muna da kusan wata biyu da dawowa daga arewa na fara zuwa school a lokacin duk da dan sauyin da nake ganin wajen uwardakina sai ban dauki hakan a komai ba lokacin.

Amma tun ranan dana dawo a gajiye na shigo gida inata sallama ba a amsa min ba ina sakai na ganta zaune da makwabciyarta maman baby .

Ni kaina na tsani wanan matar don halinta baida kyau ita kanta uwar dakin nawa da farko takan fadi bata son shigowan matar gidan inba dole ba wani lokacima idan ta shigo takance nace tana barci kota fita.

Gaidasu nayi ina mamaki kasan raina yadda basu damu da shigowan nawa ba a lokacin dan in yan arzikin na nan takance dani kun dawo na amsa da eeh anty sannu da gida sai ban samu hakan ba ranan a wajenta.

Ban damu ba saidai nasha jinin jikina ga yadda suka watsa min kallo a lokacin mai kama da harara ko tsana dakina naje na kwabe kayan jikina na fito zuwa kitchen inda na shiga ko zan samu abinda na saka a cikina babu komai da alama ranan ba a girka koda nudles ba a gidan saidai alaman sydine din gwangwani da akaci da bread an rage guntu bread a plate din ga maikon kifin a saman plate.

Haka na daure na dora girkin abinda zamuci wanda nake ganin ya dace basu da zabin abinci idan na dafa doshine ma na daina tambayanta a yanzu saidai in girka abinda ya dace dasu kuma aci cikin yabawa don kona tambayeta zatace naje nayi abinda ya dace.

Amma ranan sai aka samu akasin hakan saida na kusa kammala dahuwa don a kitchen din ma nayi sallah magariba a ranan don nakanyi haka don rage sintiri a kitchen din.

Sai gata ta tsaya daga kofa tana fadin me kika girkane na dauko a hankali ina fadin cuscus ne anty da koda na hada sai ganye.

Da izinin wa kikai hakan kona fada maki ki taba min kodan ne ko haka kawai za a dinga taba min kaya babu sanarwa don samu waje ko nuna min isa da izza za a fara kawo min a gidana yanzu ?

Tunda ta soma maganan na dago ina mata kallo mamaki don ganin abinda bai taba faruwa a tsakanin mu ba yau yana faruwa kamar a mafalki.

Ta gane hakan itama naji tace dani kin wani tsureni da ido kina kallona ko harda raini akace kiyi min tunda an turoki kiyi lacca a kaina daga baya ki aure min miji.

Innalillahi na ambata n

tare da dafe kirji nace ni kuma anty nice zan aure maki miji kada Allah ya nufe da tunenen hakan a rayuwata wallahi.

Rufamin baki ai duk abinda kuke shiryawa Allah ya baiyana ku duk daba laifinku bane hakan amma har da munafuncin ku ai tunda daga ke har kanwarki ba wanda ya fada min abinda ake shiryawa.

Ni kuma anty wallahi ban san komai akan zancen da kikeyi ba bayan haka ai Paapa ubanane taya haka zai faru ai zakice hakan sau nawa akayi a wajen ku tunda ku baku dauki hakan abin kunya a wajen ku ba.

Wayanta dake ta ringing Amira ta dauko mata shine ya hanata cigaba da maganan ta juya ta fita daga kitchen din binta nayi da kallo kafin in koma da baya na jingina jikina da dan abin girkin ina hawaye.

A lokacin wanan maman baby din dana samesu tare ita na dorawa alhakin hakan don na santa munafukace ta gaske a cikin unguwar gata da kishin mijinta su kansu matan auren unguwar tana kishin suga mijin nata balle yan mata gashi mijin wani figage dashi sai yan kunnuwa.

Ranan a dadafe ba karasa girkin abincin na zata ba maici kowa na cikin bacin rai irin yadda nake ciki saida safe na kula da ashe sunci abincin su da daren nice na kwana cikin wahala.

Tsoron dora abin karyawan safe nayi don bayanin da taimin cewa na dora girki bada izininta ba hakan yasa banyi gangancin dora wani abin karyawa yadda na saba,ba idan natashi din kafin in fita.

Wani lokaci har abinda zasuci da rana nakan dora in kwashe inbar masushi a cooler na zauna a cikin fargaba ina jiran fitowansu can naji motsin bude part dinsu.

Itace ta fito jin gidan tsit ba alaman motsina yasa ta nufi kitchen nan ma wayau ta samu wajen da alaman ba a shigo ba tun jiya.

Dakina ta nufo inda ta sameni kwance rigingine ta budo dakin tana fadin meya faru yau baki girka abin karyawa ba kuma kinsan Paapa zai tafi office da safen nan .

Nayi shiru sai kokarin mikewa daga kwancen da nayi ina gaida ita da kwana ta sake maimaita tambayanta nan nayi kasa da kai ina kokarin soma magana naji tace dani.

Ooh gaskiya ashe kina kokarin nuna min true colour dunki ke nan a yanzu amma anty ke kikace dani jiya waya ban izinin in dora girki ba tare da kince nayi ba ?

Ohh nida gidana dama me kike nufi aiba wanan yanzu ayi min yadda akaga dama din nan har a wuce min gona da iri don anga nayi sakaci ko to ban yarda da hakan ba .

Wai me ke faruwane muryan mijinta yake tambayan abinda take dagawa harshen daga kofa don fitowanshi ke nan a cikin shirinsa na fita office.

Ta juya tana fadin ka duba mi yarinyar nam fa Paapa wai bata girka komai ba ta koma ta kwanta abinta kuma tana jiran a fito a bata na mota ko a sauketa su waye bayinki halan da zai maki wahala ?

Wai meye haka Sariya meya kawo wanan magana haka tsakaninku kuma kika sani ko bata jin dadin jikintane yasa bata fito ta girka ba ?

Kajika da wani magana kuma lafiyanta kalau kawai dai ta fara nuna muna true colour dintane dama boye mugun halinta tayi kasan dan adam da iya wuce gona da iri idan ya samu waje.

Please ya isa haka tunda bata girka ba har lokaci ya kure saiki dafa mana yanzu kuci nikan zan wuce kada in makara .

Ba inda zata saita dafa muna ai karatun ba dole bane ta zauna gida dama aiki ya kawota wajen mu don haka karatu bai zama dole gareta ba.

Wai meye haka pleaae ya kike magana kamar wace wani abu ya hau kantane haka wai ke fito in saukeki a hanya da sauri ta juyo tana fadin Allah ba inda zaka da ita yau.

Allah fa kikace Sariya tace kwarai kuwa inma zata badai da kaiba Paapa saidai tabi taxi ta tafi ita kadai iam tiyed with dis mess .

Nayi sakaci a baya yanzu kuma ba zan kara yarda da hakan ba wallahi yadan kura mata ido na dan lokaci har juya sai kuma ya tsaya ya juyo yana fadin taso ki karbi kudin taxi din ki tafi zata mika hannu ta karba ya jaye hannun yace tazo ta karba.

Saidai ki tuna mune muka dauko yarinyar nan amma duk abinda tayi maki ki tsaya kiyi mata hukunci daidai da abinda ya dace bayan ya mika min kudin ya nufi hanyar falo na zata ya wucene lokacin ashe yana falo zaune naga dai da zan fita batace dani komai ba har sallaman da nayi mata kin karbawa tayi a lokacin.

Na fita ina sharan kwalla sai lokacin naga Paapa din a zaune falo yana latsan wayan hannun shi ni kaina nasan na makara amma haka na daure naje nayi arziki an malamin farko shima ya makara ranan na samu nashige ajin ba matsala.

Ashe a bayana sunyi fitana sosai da anty din gidan inda ya nuna mata ba zai yarda da hakan data dauko min ba kada kuma taja mashi raini akan zancen da bai san dashi ba.

Sun daiyi ba dadi ya fito ya fice daga gidan ta zauna tana nazarin fadan nasu da kuma abinda aka fada mata nashirin faruwa tsakanin mu.

Amma kuma inta auna zancen aminanta sai taga komai me iya faruwane koda saninsa ko ba saninsa ko kuma da yardana koba yardana idan iyayye sun yarda angama.

Wanan zance na Paapa yasa ta dan lafa kan abinda ta shirya zatayi min a gidan zuwa lokacin na rasa inda zansa kaina don damuwa haka yasa da aka fito break na kasa zama cikin aji na fito waje na zauna inda ba hayaniya sosai.

Nakai mintuna sha biyar bansan inda nake ba na lula duniyan tunane inshiga nan in fita nan a cikin tunanen nawa na kasa kamo kan zancen antyna ga fahintana dai nema ake a shiga tsakanina da ita.

Have you done ?

Saurayin dake tsaye gefena zaune ya tambayeni cikin kura min idonshi yana son hango yanayin dana dawo daga duniyan tunanen danaje a ciki.

Hey ya furta yana daga min hannu na dan sauke ajiyan zuciya ina dan sakin murnushin gefen fuska na amsa mai da abinda ya ambata gareni din hey!

Meya faru kika zauna nan ke kadai kina tunanw kyakyawa tunane bai dace da mace mai kyau irinki ba ai beauty ?

Ko kema anyi maki halin da kukewa mazane yau saurayinki ya samu wata ya juya maki baya cikin mamaki nake bin guy din da kallo wanda yazo ya isheni da surutun banza lokaci guda.

Hannu ya miko min tare da fadin nerve mind my name us Okennah but you can called me with Oke that's my name nazo nan wajen zan wuce naganki a cikin yanayin damu sai na kasa tafiya na zauna nan ina kallon ki .

Amma ke bakuwace a school din nan ko ya tambaya yana kare min kallo na dan girgiza kai alaman a,a gareshi anyway naga kamar bakiji dadin haduwa dani ba kada ki damu ya mike yana fadan hakan.

Har lokacin hannunshi yana mike da nufin in bashi hannu mu gaisa naki ya dubi hannun nasa da nake kallo ya furta sorry .

Alamu sun nuna ke musulmace ko yaba kanshi amsa da fadan hakan har lokacin kamar in zura da gudu nakeji yadda ya matso gab dani ya tsaya kamar jikin mu zai hadu da nashi.

Kaina na kawar gefe daya ina fadin nagode da kulawa nayi saurin mikewa tsaye na bar wajen don ganin wasu saurayi da budurwa da suka nufo wajen.

Suna karasowa tun banyi nisa ba naji macen na fadin me kakeyi tsaye da girl in hijjab baka tsoron su kota boye wani makani a cikin jikinta ?

Dan dariya yayi ya gyara tsayi yana fadin she is my friend ai ba zata cuceni ba kadaiyi a hankali kansan an fada muna ausa girl basu da sauki fa.

Mamana tana fada min cewa duk inda na gansu in gujesu kada su cutar damu yasa ban zuwa kusa dasu a duk inda nagansu da rufaffen jiki din nan .

Har na koma aji na zauna yunwa ya fara tuna min yana nan don cikina daya soma kugi a lokacin rasa me zanci nayi don banga inda zan samu abinda nake so ba a fadin school din.

Ko lemun kwalba kona gora bai dameni ba tun farko da muke daukanshi da giya ko yanzu da nasan ba giya bane bai wani dameni ba din nan sosai.

Amma ba yadda na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login