Showing 342001 words to 345000 words out of 395027 words
Chapter 115 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
kada kai yace tun yaushe muka koma yan kallon arzikin gidan nan tunda baki,muna shimfidan da zamuci yace ayi ba ?
Gashi har yanzu yaron nan yana iya kokarinshi a kan mu amma kullum kina nuna muna kamar shi din macucin mune ba dan uwan mu ba.
Yau da muka dawo mai da labarin an daura aurenshi kinsan me yace mama don a gaskiya koshi baisan a yau za a daura har aure ba ?
Yacewa yayi a,a sam bai aureka su yaya habib basuyi ba saida su fito idan za ayi buki a hada gabadaya rana daya ai muna tare wallahi sadiya ya fadi hakane bausan muna ta wajen kofan dakin ba suke magana da yusuf dinsu.
Kawai ka bari yaya ni nadade da gano gaskiya wallahi yanzu har kunyar hjy hauwa nakeyi don tuno da abubuwan da suka faru a baya yadda mukasa matan nan agaba gidan nan ko fita mommy bata bari tayi tsakar gidan nan tana daki a kumshe don tsoron mu.
Eeh lalai kun nuna min hauwa taci galaban ku a kaina yau keda bakinki kike fadan haka sadiya to kita kunyan ta din ba,a dai canzawa tuwo suna kishiyar uwarki take har yanzu.
Tau nidai na dade da fita cikin irin zancen nan kuma wanan matar Larai take ko duk na kara ganin kafanta a gidan nan saina karyanta itama.
Yana fadin hakan ya juya yabar dakin rai bace sadiya din ta dubi uwar tana aje ledan dake hannunta tace tun dazun fa naso zuwa babansune bai dawo gida da wuri ba wai ashe yana can wurin daurin auren nan Abba ya gaiyaceshi.
Saida ya dawo yake fada min yadda abin ya faru a can yanzu shine na taso tunda nasan kina jiran miyan da kikace in girka maki na shuwaka.
Shima mijin naki ya fada tarkonsu ke nan ko yabi kudi sun rufe mai ido koda yake ba abin mamaki bane idan yayi hakan ga yan uwanki,ma sunyi ?
Mommy aiba sunyi bane mutum yana saka cikin rigar arziki kace baka so a wanan zamani gara subi din su lakaci arziki kada wasu su lasa masu.
A zubo maki miyan da tuwonne take tambayan mahaifiyar nasu da a lokacin da yar nata zata fice ta barta ita kadai a dakin hakan zaifi mata dadi a zuciyarta.
Saidai a yanzu din tana bukatan yar nata a kusa da ita take fadin bar abincin nan har zuwa anjima don yanzu banjin cin komai a bakina.
Da kicimana da zafinsa mommy sadiya don Allah ki barni inji da abinda ya dameni gidan nan na fahinci ku baku gane meya tunkaro mu bane yanzu.
Duban uwar tayi tace kwarai da alama baku gane ba abinda dai nake gudu din shine ya faru sak a gidan nan yaron nan a yanzu ya shige muna gaba da komai na rayuwa.
Duk kokarina akan haka amma saida yaron nan yayi muna zaara a cikin gidan nan a yanzu bansa rai za a iya kamoshi ba kuma ?
Mommy don Allah ki fita zancen Aliyu da uwarshi kiji da abindake damunki yanzu mu fatan mu muga kin mike dakyau kina tafiya ba tare da sandan nan ba .
Ina zaune haka kike ganin sauki zai cin min bayan kullum ana tsotsona kin dauka hakan banzane da nake zaune ?
Ai in kuna da hankali yaci ku gano ije akai min kafan nan yaki gyaruwa amma kona fadi baku yarda da hakan sai kuce shirmenane kawai nakeyi.
Mommy kiyi hakkuri don Allah wanan abufa haka Allah yaso kisa Allah ne ya jarabeki da wanan ciwon ba wani ba duk aka tashi magana kice aike akai maki kinsan wanda yayi maki hakan to idan kin sani ki fada mana ?
Haushin yar taji ta fita zancen ta don taki yarda da magananta a lokacin yasa taji haushi ta fita batunta gaba daya.
Ina zaune nayi shiru sai faman tunane nake ina zargin Paapa da yasan da wanan shirin dama yasa yazo dani garin nan ashe.
Idan ba haka ba kobani ai za a iya min baiko tunda ba fuskana za a tofawa addu,an baikon ba ai amma ace wai saina taso tunda lagos nazo kano akan baiko gaskiya da saninsa akai min hakan kuma wallahi nidai bai kyauta min ba ko kadan da yayi min wanan tabaibayin a yanzu.
Saboda kudin Aliyu har iyayyena suka yarda da wanan shawaran kome aure mena tanada a yanzu kan aure ni ban tanada ba iyayyena basu tanada ba ?
Na tabbatar da innan mu ko cibi bata aje ba yanzu da suna aurena ba balle can din wajen antyna burina idan nagama school in fara dan aiki in samu dan kudi inwa kaina dan tanadi kafin auren .
Sai gashi kamar a mafalki wai yau auren Aliyune a kaina mutumin daba aurema yaya muka kare dashi wajen fitina balle ance akwai igiyan aurenshi a kaina yau ?
Mugu yasan abinda suka shuka yasa bai kira wayana ba da yasan yana da gaskiya dole nasan zai kirani yaji lafiyata abinda zuciyana ta fada ke na a lokacin.
Muryan hajja yabi ya katseni tana fadin toni maryam zan koma kinga dai antyn ki bata zo komu gaisa da ita ba nikan zan tafi dama don Paapa ya matsa min saina zone nazo ?
Ba halin bata amsa a lokacin son zancen ta a yanzu bai gabana duk daga ranan mayar da martanin bakin da tayi min Allah bai karba mata ba ya fitar dani kunyan duniya amma ba lokacin tsayawa wani magana a yanzu.
Saudat naji tace ayya bata samu kanta bane ai itace taban abinci tace na kawo maki amma barin kira maki ita ai tana kokarin dagawa daga gefen kafana data zauna takasa ta tsare kamar zan gudu a lokacin.
Yabi din tace ki barta aini na tashi ko na kalli yarin nata ina cewa Al,amin sai anjima kaji ina nan zuwa in duba ka insha Allahu kafin mu koma tasa kai ta fita.
Haka mutane suka fara watsewa inda duk wanda zai tafi nake jin suna fadin yanzu tarewan sai yaushe za ayi ?
Wanan bakin tambayan da yawansu sukeyi yana cimun rai sosai wallahi har nake ganin bakinsu a kasan raina gwaggona naji tana fadin wanan kuma aisai maza sun zauna kuma tunda girshi aka daura auren bada sanin kowa ba.
Don ko yaya nagidan nan dazun mukai magana dashi wallahi shima bai sani ba yace daga bada sadakine sai akaga a daura auren mana kawai a huta zaifi.
Ke nan ko baban mu bai sani ba towaye ya bada umurnin haka a kaina naja tsuki ina fadin kai nidai abina daban yake zuwa dana kowa wallahi ?
A bari aimin yadda akewa kowa sai kawai a daura min aure haka kamar wata bazawaran da aka gaji da ita wai kuma ace gata akai mun ga hakan.
Gata haka ba shawaran komai aure fa ba wasa bane haka iyayyena suna da hakkin sanin za a aurar dani a yau din amma an ari bakinsu aci masu albasa dashi a kaina.
Allah kadai yasan halin da innan mu tashiga a ranan duk ina jin dangin baba na mata barka da arziki da gamawa lafiya da budurci lafiya sunawa yan baya fatan hakan ta hanyar cewa Allah ya nuna muna na yan baya lafiya.
Sai wanan ranan na fahinci abinda wanan kalman ke nufi idan irin haka ya faru anyi aure akwai sauran yaya mata sai kiji ance Allah ya nuna muna na yan baya a amsa da amin.
Nikan ai bayana ban fatan ai masu wanan bazata din an watse an barmu dagamu sai yan uwan baba mata a gidan su hudu.
Kosu suna dakon dawowan su babane da sukai waya yace su jirasu suna tafe sai wajajen karfe shidda da rabi na yamma su baba suka iso gidan.
Akwatuna aka fara shigowa dasu da goro dasu kayan sha da sweet da chewingun kwalaye kwalaye ana jibgewa a kofan inna.
Muryan baba balane naji yana fadin yaya Hadiza kinga kayan baiko kamar za a bude shago ko naga kinyi tsaye kina kallo ?
Ta dan nisa tana fadin wallahi kadai ashe ka ganni tunane nakeyi dama dai da shirunsu sukazo ko wanan abu haka ?
Hardasu akwatuna saiti kamar na daurin aure baba bala yace duk kayan baikonne fa ai kinsan da niyar baiko akazo saiga babanta shi umaru mai rikonta yace a daura tunda sun aje sadakinsu gaba daya me za a tsaya jira kuma ?
Gwaggo Laraba ta saki wani irin guda a wajen tana fadin yarinya tayi goshi ta shigo duniya a kafan dama ba,a san maci tuwo ba akace sai miya ya kare.
Yau duk wani kace nace akan yar nan yazo karshe inji Allah tunda tagama da waje lafiya Allah yasa a shiga gidan miji kuma a sa,a tayi zunde da kofan mama da suke cikin daki da kannenta.
Baba bala yakai zaune yana fadin toga kayan nan da can gida zamu kai shine yaya Lawal yace a,a ayo nan dashi don haka akewa kowa a kawo iyayyenta mata sugani susa albarka sai a raba a aika muna da can gida dana sauran yan uwa shine nace ku tsaya ku jiramu muzo ?
Yayi daidai yaya sai a kira su Rakiya ina Ai tana daki ai suzo su gani su sawa alheri albarka yace ai office umaru yabawa kowa shawa wajen tundai wanan malam din kawun yaron daya bada sadaki nan ya soma basu labarin abinda ya faru a wajen taron.
Mama dun da inna ain fito sun duba kayan sunsa albarka suka koma dakunansu su kuma sukace a bar kayan har washegari don yamma tayi sosai lokacin.
Sai bayan an watsene muka saura mu kadai don antyma sun fita zuwa gidan anty Fati a lokacin an fito sallah isha,i baba ya shigo gida ina jin yan gidan mu na zuwa gaidashi daya bayan daya yadda aka saba nima na tofa na fito don gaidashi din da dawowa .
Yana zaune zaici abinci ya amsa da maryamuce na amsa murya a sanyaye da nice baba yake fadin sai kuma kikaji zancen yadda ya koma ko ?
Bance komai ba ya kora ruwa yana fadin lamarin Allah ke nan maryamu shi Allah kana naka shirin shima yana maka wanda yaga ya dace dakai wani lokacin sai muyi addu,an Allah yasa hakan shine alheri garemu baki daya mu dake duka Amin ?
Don da naji naso sa damuwa a zuciyana dazun din amma kuma dana duba na auna irin mugun nufin abinda ake binki dashi ko a gidan nan maryamu sai naga gara da hakan ya faru kowa ya gani din.
Don haka ina sonki rugumi wanan abinda hannu biyu yadda muma muka runguma din don wallahi ba wanda yaje wurin da niyar daurin aure a kanku yau din nan amma sai gashi Allah yayi ikonsa ba a watse ba saida aka daura har auren ga baki daya a yau kinga ai ubangiji ya nuna maki gata ga hakan .
Ance mairo nacan ta kama daki tana bariki ance mairo bata dawowa gidan nan sai tayo muna tsaraban shege tunda kina aiko da kudi munaci bamu damu ba yau mairo kece ubangiji yayiwa wanan gatan ai Alhamdullahi .
Kowa ya watse a cikin farin ciki da raha ana annashuwa da sam barka ai alhamdullahi ga hakan yau akwai abinda yafi muna dadi nida uwarki a rayuwa irin haka.
Yau ko bariki kikeyi kin biyani a rayuwa maryamu tunda kinbi maganan magabatanki balle ba hakan ba ko aceb kin samu shedu na alheri bana tsiya ?
Shima yaron naji ance zancen yazo mashi da mamaki ai kamar yadda yazo muna nan don haka kada ki tuhumi kowa idan kinyi hakan kin butulcewa Allah nake gani ki dauka haka taki kaddaran auren yazo maki yasha daban dana kowa.
Yaushene tafiyan naku dashi office yace zaizo da yamman nan donshima na dawo cikin unguwan nan da wuri yau amma bai samu zuwan ba nasan wani uzuri ya tsayar dashi dai.
Inaga ranan sunday zamu koma don ina da school ranan monday ko yanzu zuwa da nayi saidana dauki execuse kafin nazo.
A,a lalai dole ki koma kuwa kada hakan ya zamo laifi amma nasan zancen tarewanki bai nisa ai tunda kin kusa hada karatun ki ga baki daya ai yanzu.
Nakusa baba insha Allahu nanda sabon wata mai fitowa karshenshi zamu kare in Allah ya yarda to alhamdullahi abu yayi kyau sosai wallahi Allah ya sakawa umaru da alheri banda abinda zan bashi a yanzu sai addu,a mairo ?
Zancen kayan daki dai nasan kuyi magana da ita Ai muji idan zamu iya daidai karfin mu dama ina tanadi don gudun girshi irin haka kinga kuwa gashi.
Sai a bari ko idan kun komane sai muyi magana donshi officer bansan shirinsa ba akan hakan amma zan tuntubeshi idan Allah ya mayar daku lafiya.
Wai ance maryam tazo inji Oga Aliyu daga inda nake ina jin kannena na rige rigen hada baki wajen tambayan waye baba ke fadin ku bakuji wanda ya turo kiranta bane ?
Ko wani ya taba zuwa tunda tazo badaga bangaren shi ba saiga yaron ya dawo yana fadin wai Saudat tazo akace baba ya sake fadin shine don shike dabi,an idan yazo yace ana sallama da saudat.
Kafinma nakai dakin naga saudat din ta fito tana saka hijjab tafice da sauri nashiga dakin namu rasa me zanyi a lokacin nayi ?
Donshi na jawo hijjab din sallah na na zurawa jikina sai turare dana dan feshe jikina dashi na dauki rabin rayuwan zamani wayata ke nan wanda yafi kusanci ga kowa a yanzu na rike nafita.
A waje na hangosu tsaye jikin mota Saudat tana kwasan dariya a hankali cikin rausaya tare da rashin kuzari nake takawa harna iso wajensu ina masu sallama naji saudat din tace dani toga yayan ta fito.
Yayan mu ashe mijinki matsoracine wai tsoro yake ji yadda zaku hadu yau dashi don ko rantsuwa cikin kwando yayi maki ba zaki yarda dashi ba a yau ?
Ke saudat muna haka dakene kuma kazafi zakiyi min a gabana matar tawa zanji tsoro kina nufin na zama mijin tace ke nan ko to barin nuna maki ba haka nake ba a gabanki kigani.
Ta juya da sauri tana fadin ai kunfi kusa don tare naganku nikan ba a hakan a gabana ta juya tana dariya nake fadin Saudat ki hado mai ruwa da abinsha don Allah idan kin shiga idan kuna da kunun Ayya ki kawo mai sanyi ba drinks din lemu ba.
Ta amsa min da to yaya ta shige ciki na juyo ina fadin ina wuce daddy cikin dakewa zakice ba wani damuwa a tare dani a fuskana lokacin.
Yaji dadin hakan ya amsa da sauri da lafiya kalau daughter yaya gajin taro ance min nan ma ancika sosai dazun yan uwa duk sun hadu a nan din.
Eeh gaskiya nima banzata ba sunzo amma duk sun koma gida babu kowa yanzu sai mu kadai a gidan naji suna cewa gobe zasu dawo in Allah ya kaimu.
Ya dan shafo fuskanshi yana fadin sai kikaji zance ya juya kuma a yau manya sunyi halinsu garemu sun daura auren a yau kuma ?
Haka akace Allah yasa hakanne alheri garemu baki daya na fada a takaice ina gyara tsayina ta hanyar jingina jikina a motan inda saudat ta daga din.
Aikin malamne da uncle su suka nuna isarsu a kan mu a yau Allah ya saka masu da alheri yasa kowa yace gara da akai hakan garemu Allahuma Amin.
Na zata zaki daga hankalinki da jin hakan tunda nasan baki son hakan ya faru a yanzu tsakanin mu sai kuma naga kin ma fini kwantar da hankalinki ashe kan zancen ?
Dan murmushi nayi ina fadin kenan inja da ikon Allah in nuna ban mashi godiya ba idan nayi hakan abinda iyayyenka ke so kaima kafisu kaunan hakan a lokacin.
Wani abune idan iyayye keso kake shiru maryam ya kirani da sunan yankana na rago a ranan da maryam sunan da bai faye ambata hakan ba a gabana.
Naji ya katse min mamaki da fadin wani lokaci wani zance yakan fi karfin ansa ga da zuwa ga iyayyenshi don illan abin kusan hakane ya tashi faruwa a kan mu jiya nasan wanan dama malam ya canza shirinsa a kan mu ya mayar da baikon mu aure a yau din nan .
Kafin na tambayeshi meye wanan din daya tashi faruwa akan mu saiga Saudat ta iso da abinda nace a ture ta hado tana fadin to gidan namu ba falo balle nakai maku a can saidai a aje mashi a mota