Showing 249001 words to 252000 words out of 395027 words

Chapter 84 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

,,,,,,,

Kirjin ya dafe da sauri naji wani iri ina mashi sannu tankar ina inya cire ciwon ajikinshi dana cireshi na rabashi dashi a lokacin.

Sannu nake ta faman fada a cikin turanci ya dan amsawa da kyat a lokacin kan kome zai faru saidai ya faru nake ji don tabbas dole in taimaka mashi inzamo mashi yar uwa a wanan halin.

Zaka iya shan maganin hmgargaji a gwada a gani ya dan lumshe ido yana fadin idan na samu zansha in kika ban ?

Na zaro maganin a cikin jakata ina fadin yanzu naje gidan maman Toyi na amso su saidai tace bayan kasha zaka iya yin amai ko dan gudawa kadan .

Idan kayi hakan zaka samu ya sauka insha Allahu in an dace ma ya rabu dakai kenan har abada insha Allahu .

Ya dan kallone a sanyayye yana fadin idan ba zaiyi yawa ba ai zansha tunda nasan ba zaki karbo min abinda zai min illa ba ai.

Na lumshe ido kadan ina fadin insha Allahu baya illa saidai maganin gargajiya wuyan shane dashi amma kaci abinci ?

Cikin daurewa ya girgiza min kai alaman a,a ya kara da fadin sun kawo dazun nace su bari sai anjima don ina tsoron ci saboda mai.

Almost to time din sallah tashi kayi wanka ka daure sai kayi sallah barin shiga kitchen din in gani na mike da niyar barin dakin a lokacin.

Ya lumshe ido yana miko min hannu alaman in kamashi ya daga lokacin hannun nasa na dan kalla kanshi na kasa bai dago ba haka na runtse ido na kamashi ya mike tsaye a hankali .

Kamar zai fadi nace inane ban dakin ina zuwa bai saki hannun nawa ba ya nuna min ban dakin na dan juyo na dubeshi naga bata kaina yake bama.

Haka muka shiga bayin komai a gyare na hada dan ruwan bayan nayi kokarin zare hannuna daga nashi don tsikan jikina da nake jin yana wani yamm a lokaci guda.

Ya bini da dan kallo saida na hada ruwan na sanya mai har maclean brush dinshi dana gani sannan na fito daga bayin ina ja mashi kofa.

Fita nayi daga dakin na inda na samu wanan Abdul din kamar me jiran fitowana yai zubur ya mike tsaye nace don Allah inane kitchen din ku gidan nan ?

Wani abu yake so hjy in hada mashi No ka nuna min sai kaje idan yana son taimako a dakin ka taimaka mashi don ya shiga wanka yanzu.

Ok ok ga kitchen din a nan ya nuna min da hannu na nufi wajen da sauri shi kuma ya nufi dakin nashi kai tsaye

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[9/22, 9:32 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊7️⃣6️⃣🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Tsaye nayi ina bi kitchen din da kallo tare da fadin ko waye matar gidan nan ta more rayuwa ita kam kichen haka kamar a gidan shugaban kasa ?

Gaskiya matar bawan Allah nan nada sakaci wanan wani urn sakacine zata bar mijinta a nan ta koma wani wajen ta zauna ?

Naja tsuki tare da takawa zuwa gaban carbinet din da naga an rubutawa food items budewa nayi kamar munafuka ina leken cikinsa.

Daga sama har kasa abincine a cikinsa irin na kasan waje din nan a cikin ledansu siled kamar ba a amfani dasu na duba a ciki meye wanda baya illa a jikin dan adam musanman mai ulcer.

Na dauko macroni guda haka don shine zaifi saurin dahuwa dan dan coslow banyi amfani da mai ba sosai haka nayi ta duba kayan hadin ina dan zuba wanda bai illa ina gamawa na dafa ruwan zafi na juye na hada wani tea mai kauri dan ruwa kadan na nera a ture zuwa dakin.

Na dan tsaya daga kofa ina sallama da sauri Abdul din dake kwashe kayan daya cire ya karba min sallamata yana fadin shigo hjy aiya fito tun dazun abincin na dire shi ya jawo dan wani table dake dakin na dora a kai.

Naja gefe ina fadin bissimillah ka fara shan tea din sai kasha maganin mu gani ya dan

kalloni bai amsa ba yana dan gyara zama da sauri nakai gurinshi na dauki cup din na mika mashi ya karba.

Ina tsaye cikin damuwa na matsa mashi ya sha mana kada yai sanyi ya dago yana fadin a kwai zafi a hankali na juya da nufin incewa mai kula dashi ya dauko kofi na samu ya fice daga dakin ashe dagani sai shine ciki a lokacin.

Na mika hannu na karbi cup din ina dan juyawa hankali na akan abinda nakeyi saida na dago in tambayeshi ko yayi na samu yana kallona .

A ransa tankar bani bace mai tsiwan tsiya din nan amma yanzu na kideme na nuna concern a gareshi haka niko .

Kasa nayi da kaina da sauri ina fadin na miko mai ne yasha yaji ko sanyisa yayi daidai ?

Ya mika hannu na bashi ya kafa kai ya zuka sosai ya dan daga cup din zuka uku yayi mai ya shaye lokaci guda don dama kadan na hado mai shayin don ya buda mai cikin na karbi cup din ina mashi sannu da kai kawai ya amsa min na juya koya zata zan fita da cup dinne naji yana fadin

No ki aje cup din kada ki fita haka su ganki akwai maza gidan nan fa kin sani cikin mamaki na kalloshi kafin in dubu jikina dagani sai wasu siket da riga na less dan yalalon gyale iya wuya na dora a wuya na kuma ajeshi da zan shiga kitchen din gidan yanzu haka nake sambal dina.

Jikina yayi sanyi a raina nake fadin shidai komai nasa na religious ne ina ruwana da mazan dake nan tunda ba wajensu nazo ba ?

Zanso naga matar mutumin nan wajen ka,ida irin nasa kodai shi din dan malamai ne wai ko a gidan malunta ya fito a kano ne ?

Jakata na nufa na dauko wanan maganin ina kadawa marfin goran biyu tace asha a lokacin na dan tsaya kusa dashi ina fadin ga maganin a zubane ?

Yayi alama da eeh da kai na zuba na mika mashi makin ya karba daga hannu na din sai yaki yana bude bakinsa ya min alaman in bashi da kaina a lokacin.

Kamar dai yaro sir na fada dariya yana son kufce min a lokacin yayi alaman oho yana kara bude bakin nashi na bude maganin na zuba marfi biyu na bashi kamar yadda ya bukata yana hadewa.

Na mika mai goran ruwa ya bude ya kwankwada ya miko min na karba ina fadin barin zubama abinci ko kadan kaci sir sai inzo in tafi gida kada makwabtanka su gani su dauka wata macen banzace tazo wajenka su fadawa matarka wata rana.

Baiyi magana ba illa dan murmushin daya sake a fuskanshi kawai na zuba abincin kadan na mika mashi yako karba yaci sosai ina gefe zaune ina duban wayana a lokacin.

Naji yana rufe plate din alaman ya gama na karba da sauri na kwashe kayan na hada komai na fito dasu daga dakin .

Wanan guy din na tare dashine zaune a falo yana ganina ya mike da sauri yazo ya karbi kayan daga hannuna yana fadin sannu da kokar ya danci ko kadan ne ?

Yaci sosai na bashi amsa har da dan fara,anshi yana fadin wallahi na damu sosai rashin cin abincin nan tun shekaran jiya baici komai a cikin shi ba dan dama jiya lemun da kankanan da kika kawo sune ya dansha ya kwanta.

Naso inyi mai ko dan ferfesuf ne ka zaisha da dare amma ina gudun kada makwabta su ganni su fadawa matarshi sunga wata mace tazo gidan nan ya zama masu fitina kuma ?

Wace mata kuma son Allah tunda yana ci ki taimaka ki dafa muna koma meye da dare sai inbashi ko zaici ?

Balle unguwar ba ruwan kowa da shiga gidan wani ki kwantar da hankalinki ba matsala muje kitchen din ingani na fada muka jera tare zuwa kitchen din dashi.

Na danyi nazari ferfesu na hada masu tare da tuwon semo sai miyan yauki ban karasa ba sai zuwa karfe biyar na yamma nagama duk tsawon lokacin nan tun shan maganin shi yana kwance yana barci.

Nagama ina shirin fitane likita yazo gidan dubashi shigowan likitan yasa shi tashi a lokacin allura da magani ya kara mai ya fita duk ina kitchen ina aiki na fito nace zan tafi gida.

Na fadawa Abdul din yadda kan maganin yake nayi mai sallama don yace min yana bayi a lokacin nace idan ya fito ya fada mashi yamma yayi na tafi gida.

Banyi nisa ba sosai da fita daga gidan naji Abdul a bayana yana fadin hjy maryam oga yace ki dawo a kaiki gida niko gabanane ya fadi don tunda yace ya kewaya na tsure kada dai maganin iya toyine ya sakar mai gudawa ?

Amma da naji yana fadin yace in tsaya akaini gida nace No kada ka damu don Allah kace mai har na samu mota kadai tsaya ka kula dashi don maganin gargajiyan daya sha.

Ok naji yace ya guda yanzu kuma yaji dadin barcin da yayi din nan yana jin jikinshi da dama yanzu shine yace inkiraki a falo nace kin tafi ai yace na tsayar dake don Allah.

Ba zan koma ba dama dubashi nazoyi kuma Alhamdullahi tunda ya samu lafiya sai anjima nasa kai na tafi yake fadin idan ba damuwa hjy gobe ki dawo don Allah ki kara mai abinci ko zaici ?

Shiru na danyi kafin can nace dashi Allah ya kaimu goben lafiya insha Allahu zan shigo ka dai kula ka bashi maganin na kara mai bayani a daidai lokacin mai jan motan nashi ya fito da mota daga cikin gidan dole nashiga ya tafi dani.

Ina jin yana fada mai gobe don Allah kaje da safe ka daukota zata dawo ta dafa mai abinci ko zai samu yakara ci din.

Har kofan gidan mu ya saukeni nayi mai godiya ya tafi nasa kai zuwa cikin gida tare da addu,a don gidanmu a yanzu ya koma saida hakan gareni don kaucewa fitina.

Sa,a na guda shine kamar duk suna tsorona a yanzu gidan wanda ba komai bane sai dorani a kansu da Allah yayi min a yanzu .

Bandai neman komai a wajen kowansu banda uncle da kwana bibiyu zai bada dan kudi yace anty tabani ko kuma ya ban a hannuna don kudin taxi zuwa school.

Baya dashi sukan ba zance a yanzu zasu iya nuna min wani abu ba bawai alfahari ba don sai dai inbasu gaskiya.

Hajje Yabice dana samu sakat da ita yanzu komai nawa bataci daga gareni na aske hakan tun bayan cin mutuncin da tayi min ba gaira ba dalili na kiyayi kaina da ita gidan.

Sai tayi kamar ta sauko sai kuma ta kare haye da dan abu ya hadata da wani zata hade kowa ta sauke haushi a gareshi kinsan haka wasu mutanen halinsu yake.

Babu kowa a falon gidan don dama anty dai ta fada min zasu unguwa da yarta tunda basu samu fita ba jiya sai wanan ranan.

Dakina na bude nashiga na fara cire kayan jikina lokacin wayana ya dauki kara Saudat ce a layin na dakatar da abinda nakeyi na dauki wayan.

Yayan mu kwana biyu yanzuma innace tace nakiraki aji ko lafiya kike ta fada batayi karya ba idan na lissafa ankai kwana biyar ban kira ba su basu kirani ba .

Saudat lafiya kalau kinsan idan muna school bamu faye samun lokacin kan mu ba ga kuma wanan ogan namu daya turawa ina kudi lokacin baida lafiya sosai wallahi.

Dama ina son kiran inna in fada mata kuje gidansu kuyi barka don Allah ance mahaifiyarshi ta haihu a nan kano ?

Yayan mu mahaifiyarshi fa kikace ke nan ogan naku karamine ma nina zata wani tsohone wallahi idan naji kina fasin ogan ku sai in dauka irin Oga habune ai tsoho na gidan bread ?

Dariya taso ban na dan murmusa ina fadin wanan kan ba tsoho bane fa yama ce ajinsu daya da Bello a secondry don yasan bello.

Ke uwalema aita sanshi ina wata rana da nazo kano muka dawo muna fadin bello ya tare mu yana bi da mota har kikace da dakece da kin zageshi ?

Wanda ya dauke mu shi din ne fa ni saida ya tuna min nagane shine a lokacin gashi nan mun hadu kofan gidan malam in,nuwa na unguwan mu dake motarshi ta watsa muna ruwan kwata ranan ?

Kai yayan wanan mai kama da balarabe din ko wanda bai magana wallahi shi kuwa shine muka hadu ashe nan Lagos yake da zama dama .

Inane unguwarsu ta tambaya nace niko ko ina ma oga sulaiman ya fada na dan fara tunane naji tana fadin ashe ogan suna da yawama ?

Ke unguwar kabo yake nayi mata kwantace sosai yadda akai min tace tagane zata fadawa inna din kuma idan ta koma gida zata ba inna waya mu gaisa.

Wanka nashiga na fito ina fashin sallah a lokacin don haka gado na haye abina duk da cikina yana da yunwa don abincin dana dafa gidan can ko lasawa banyi ba balle nakai ga ci.

Nidai na hada masu nafito abina abinci haka a yanzu bai dameni ba sai dai in dan samu snack inci ko drink irin neutrons milk dana sha cikina ya koshi.

Don na zama hustle banda lokacin kaina taka maimai in ba karatu ba da hanyan da kudi zasu shigo min sune a gabana kawai yanzu.

Banji motsin kowa a gidan ba haka kuma ban damu da neman kowa din ba tunda dai nasan ba,a rasa mutum a gidan lokacin sai har kokin gabana nakeyi har na gama na dan jika golden more na kwanta dana sha.

Barcina nayi sosai don ki ranan na dan gaji don saboda yawan jigilan da nasha dole tunda na kwana biyu da hakan indan samu gajiya a jikinna .

Don haka ban san lokacin da masu gidan suka dawo ba haka washegari dana tashi gyaran dakina nayi tunda na idar da sallah asuba na gyara dakin tsab kafin na shirya fita zuwa school.

Bai koma barcin ba don magariba daya kawo jiki duk musulmin kwarai haka wanda yasan ciwon kanshi baya kwanciya wajajen magariba don lokacine na shedanu da ciwurwuta dake yawo a lokacin.

Horn din mota sukaji suka tare da bude get din maigadi hakan na nufin wanine ya shigo gidan a lokacin ba a jima ba kuwa su sulaiman suka ishi shi da Adebayo.

Sunji dadin ganinshi falo zaune yana kallon tv a lokacin don suma yadda suka barshi da safe hankalinsu ya tashi sosai in anyi magana yace makwabcinshi yana dubashi a gida.

Nan suka zauna suna mashi sannu kafin su dan mai bayanin abinda office ke ciki a ranan yace ba damuwa idan ya samu sauki ya shigo zai duba ansan yadda akayi.

Nan Adibayo ya wuce ya bar sulaiman din don lokacin sallah da yayi tare sukai jam,i a wajen gidan aka sallame Abdul ya shiga ciki abinci ya fito dashi falo ya jera a dinning don yasan yana shigowa kwanciya zaiyi tunda an samu ya dan jima a zaune ranan.

Alaman sauki yana shiganshi a lokacin saida sukai sallah isha,ine suka shigo ciki shida sulaiman din sun


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login