Showing 9001 words to 12000 words out of 395027 words

Chapter 4 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

hankali.

Tafiya dai ya tabbata ga Aliyu don yanzu duk wanda ya kamata ace ya sani yasan da zancen tafiyanshi karo ilimi a kasan turai tun ana fadi ana ji har yakai ance washegarine tafiyan.

Suna daki da mahaifiyarshi yana shirya kaya suka soma jin muryan Alh yakubu yana rantsuwa yana fadin ai gasu nan idan na bashi ko kwandala ki tambayesu kiji .

Suyi fitina daya kai hae hauwa ke fadin dan ya fasa don irin kalaman da hjy take fada mara dadi akan dan nata uwa bata jure jin kalamin ga danta komai hakkurinta.

Daki suka shiga abin da da mahaifi yaci karfinta da kalamai masu tasiri yasa taji kwarin gwiwa akan tafiyan ta fahinci gaskiya dan da yan uwanta suka fada akan tafiyan yasa hjy take wanan haukan haka.

Ba kunya da safe dayaje sallamanta tayi mai Allah ya tsare bayan ta tabbatar da gaskiya mijin ya fada bai taimakawa dan dako sisinshi ba yasa ta dan sake ranta .

Tunda tasan ga banza zai tafi ya dawo ba wani tsiyan da tsinano ga tafiyan kafin nan kuma yayanta sun gama ginuwa sun zama abinda zasu zama cikin dukiyan uban nasu ai.

Wanan shawaran aminiyarta dake zugata take fadan hakan tare da kawo mata musalai da illan dakega tafiyan yasa hjy jin kamar har abin ya tabbata ma ga dan .

Ta taushi zuciyarta tana nuna nadama harda cewa ya yafe masu don Allah idan anje ayi karatu daya dace banda wasa ya amsa da insha Allahu mama shine sanadin tafiyan na gadanga turai a lokacin.

Ya rage sai yaranta mata biyu da suke tasowa a gidan yanzu a gabanta haka kuma bai hanata cigaba da yiwa nagabata biyayya ba tana gani za a kawo abu daga kasuwa a dan debo masu a kawo masu wai shine kason su .

Ta karba har taje godiya da murnanta bata nuna komai a fuskanta na bacin rai inda take dan samun dama shine wajen sutura da gaba daya ake kawowa don haka bata da kishin ruwa ko yunwa ko rashin sutura yasa ta dauki komai da sauki a zuciyarta a gidan.

Wanan yasa zaman ya koma daidai kamar ba abindake faruwa na hassada a tsakaninsu a yanzu zamansu ram ram saboda biyayyan hauwa din garesu ita da yaranta.

Saidai wanda ya tuna dashi zaice dada shi gadanga boko ya zaba a rayuwansa sai tace haka ya zaba ai zamuga yan boko yaro da fadin rai wai ace duk karatun da akeyi a cikin kasarnan bai mai ba saiya ketara yaje waje cikin turawa yayi karatu kamar shiyafi kowa ilimi a garin nan.

Ranan danta dake zaune ana zancen yace waike mama idan anyi magana kice ilimi ilimi baga masu ilimin nan muna gogaiya dasu a cikin kasuwa ba anyi ilimin ya tafi ga banza yanzu ?

Shifa Aliyu raggone dan karyane banda karya ba abinda ya saka a zuciyarshi waishi don ana cewa yana da kokari yake son yaga kurewan biro.

Itama maman tace yoo Allah na tuba ni ko yayi ilimin akwai abinda zai taba tsoratani da iliminsa habibi yadda kuka kai hakan nan a yanzu aini ko gaba da turai in ana zuwa aita zuwa hakan bai taba damuna.

Niko nace kishi hoo watau ko wani gida dai da tasu kalan kishin dake kawo masu hassada har ya hada da yaransu shi kishin ma hawa hawane kamar yadda yan adam suke daban daban a ciki duniya.

Duk wanan maganganun bai taba damun hauwa ba illa abinda takeyi shine tana raba dare tana rokon Allah ya shirya mata zuria,anta .

Donshine yawan maganan tafiyan nasa a yanzu ko anayi bai damunta iya jan kunne tajawa danta kunne yanzu kuma tana addu,an Allah ya tareshi ya kare a duk inda yake shine nata a yanzu sai neman albarka ga zuri,a wanan tasa a gabanta

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[6/19, 10:07 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

4️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

Sauri nake in saka uniform dina don ni kaina nasan nayi mugun makara a yau nasan sai sha bulala dolenema sai an dukeni .

Gashi kuma ban iya fashin zuwa school din don na kwallafawa raina son karatun kamar yadda naji sister din salma suna hira ranan a gabana.

Kowa tana bayanin illan rashin boko a yanzu da zamani ya zama na boko in baka dashi tankar dan kallo kake kawai a diniyan nan don ganin wata mata da sukai zamani da mahaifiyarsu yadda a yanzu ta tsofe kamar ta haifi mahaifiyarsu.

Yadda wahalan rashin wayewan kai ke saurin durkusar da mutum a yanzu da komai ya juye ya zama a zamunance.

Ire iren maganganun da nike ji na labarin dagewa akan ilimi gidan nasu salma da burakansu nagaba yasa na kwallafawa raina karatun dole har yakai ban iya fashi don babban yarsu salma takance kada in biyo mutanen gidanmu da rashin son karatun indage ko secondary in samu ingama wata rana hakan zai min amfani.

Don sam a yanzu mama ta saka karatu baida tasiri cikin gidanmu tsarinsu a yanzu shine tallah da suka sa a gabansu.

A dawo ana lissafi a gaban mu sana,an shinkafa da miya da naman kaza ko na shanu sukeyi ruwa da iska bai hana fita don a cewansu suna da masaya wanan yasa mama ta watsar da zancen nika a ranta ta daukeshi wahala a wajenta.

Yayin da mu kuma dakin mu nan ma ba hutu don likkafa yacigaba a yanzu muna da gwargwadon rufin asirinmu bamu kallon takaicin da mama ke kokari izzo muna a kullum don taga bayan mu.

Yanzu banda kunun safe da fanke da mama keyi sun bukaci a dinga masu na rana suna saye don gidanmu idon kasuwane hakan yasa inna fara dora tukunya yin shinkafa da mai da yaji da ganyen salad ana fita dashi kofan gidanmu anan za a saye har bai isa.

Don yanzu maza sun lalace da cin abinci waje abar iyali can suna fama da dabaran abinda zasuba yaya a cikin gida ba kunya zakiga kato ko samari a waje suna wagan baki da abincin sayarwa sunaci haka wanan rashin kunyar zamani ya kawoshi yanzu a kasan hausa.

Yana da wuya da can baya kiga namiji balle mace na sayen abincin sayarwa a waje balle har a zauna anaci yanzu hakan ba a daukeshi komai ba a gurin bahaushe ba mazan ba har malalatan mata zasu aiko da kwanukansu a zuba masu.

Wanan sana,an da inna ta dauko yi a yanzu ba karamin fitina akayi ba tsakaninta da mama sai lokacin naji bakin innan mu ta mayarwa mama da martani kan zagin da take jifanta dashi na talauci.

Don cewan da mama tayi tunda safe a tsakar gida ta soma fadin komai gasan mutum dai ba zai taba abinda tayi ba saidai hassada ya kashe mutum da haushinta.

Meye abin hassada yaya sa,acefa ba sata ba ina zaune ban komai gori da zagi nida yayana ba wanda bakiyi min a gidan nan ?

Yanzu kuma Allah ya rufa min asiri ya bani abinda zan duba kan mu shine hassada a gureki ai bansan kinfi bukatan ganin mu a talaucen da kike fada ba kina muna dariya da zagi.

Amsam da mama ta bayar shine kuma ya zamu fitina a wajenta fada sosai akayi a ranan har tana ikirarin cewa zata linkidawa innan mu dukan tsiya idan ta kara mata rashin kunya.

Yaya murja yartace data tashi da barci ta fito take fadin haba mama meye haka don Allah ina ruwanki da abinda sukeyi ai gaskiyan innan mairo ke daga kin hutuma da ciyar dasu da kike magana a kullum yanzu ?

Komai abinda sukeyi dai bai taba kai namu don Allah kisa masu ido ga sana,ansu tunda bada kudinki kona wanin ki suke sana,an nan ba gasa kuma dama shi zama haka yake ai kowa ya iya allonsa ya wake daidai ruwan gabansa.

Maganan yaya murja yasa mama sassauta fadan duk da bata bari duka ba amma yaran sunci karfinta a wajen fadan haka yasa dole ta saka ido tabar inna.

Nayi saurin shiryawa a cikin kodaddadun uniform dina na mike hanyar school tundaga nisa na hango malamai sunkai mutum biyar a wajen class din mu suna magana.

Nazo sudu sudu zan shige wata malama tayi min dakuwa gami da zagi na daga gidan ubanwa nake a wanan lokacin har an kusa tashi tara ?

Nan suka far min da zagi da cin mutunci irin na wasu malamai da basu da tunane har wata na fadin wai a dubi yadda nazo masu makaranta nidin kazamace don Allah a korani gida kawai zaifi tunda iyayyena basu damu da bokona ba .

A,a malama ku barta din Allah yanzu zai iya yuyuwa kuma mu korata muzo mu zama sanadin barin bokon ta ai kinga hakan ba zai muna dadi ba muma ?

Irin yaran nan dakike gani wullakance wata rana sune suke zama abin kwarai a duniyan nan balle gata da kokari kanta yana jawo wuta don yarinyar gaskiya ba laifi.

Ke mekesa kina makarane haka kuma aka kasa dinka maki sabbin tufafi irin na yan uwanki ke baki ganin yadda yan uwanki suke tsaba kowa na zuwa makaranta a mutunce ?

Shiru nayi na kasa dukar da kaina ta daga min tsawa tana fadin bakiji bane ana tbayan ki kinyi shiru ko kinfi son a koreki din ?

Jin hakan yasa na dago kai ina fadin malama ina taya innata aikin gidane na sana,anta sai nayi tallan koko mun samu kudin da zamuci abinci dashi nake zuwa makaranta a kullum.

Ta juye harshe da turanci tana fadinwa yan uwanta malamai you see nasan wanan makaran ba banza ba wata tace ita uwar naki bata da hankaline bata san kina karatu bane halan ?

Ke inane gidanku nace gidanku daya ta sake jefo min tambaya ta bayana hakan yasa na juya gareta ina fadin gidan Abdullahi smugal don haka suke kiran gidan mu dashi.

A,a,a wanan kan aiba zata taba samun kulawa ba yaran da sukafi ba talla muhinmanci ashe yaranshi sun saura karatu har yanzu wani malami daga cikinsu ya fada ya juya wajena yana fadin tashi kije class din ku.

Yaya zakace taje class bayan yanzu tazo makaranta malam farko data fara magana tun isana wajen ta fada bari taje don Allah aji bata fadi karya ba malama su din abin a duba masune yanzu don uban baida komai a hannunshi kamar abin yaso taba mashi kwakwalwansa ma yanzu haka.

Ni dai iya nan naji na fada ajin mu ba zan iya karas da abinda malamin yake nufi ba amma na fahinci dai duk wanda zai kwatance akan mu haka yake kwatantamu dashi na hasaran da ake cewa mahaifinmu yayi.

Haka mukai karatu har tashi ka,idane idan an tashi da gudu zan fito zuwa gida don fitar da shinkafan rana da mukeyi wanda kafin nazo inna ta hada min komai da zan fita dashi da kuma na isa gidan tsintsiya zan dauka in share wajen da zan zauna din ba awo nakeyi ba don a kwanuka take kasawa da kanta iyakana idan ka dauka inzuba maka mai da yaji da ganye idan kana so.

Dana fito jira sukeyi nake saidawa yasa na hada saro ruwa muna ajewa a gefe daya ance mai karami shike da babba wata rana hakane wanan maganan ba karya bace kaidai kabi karamin naka da addu,an alheri da fata nagari har girma Allah ubangiji ya tsaya maka akai.

Dana sayar zan kwashe kaya in koma gida na hada in zauna inci abinci sai na wanke kayan sana,an tamu in kuma taya inna aikin kamu da muke sayarwa da safe aikin kenan idan gari ya waye ba hutu a garemu muna neman nakai da rufin asiri a cikin mutunci.

Duk da namu aikin dake da yawa yanzu hakan bai hana mama tsiro da nata da take sakani yi ban kuma damuwa da hakan irin wanke wanke gyaran nama don su har sana,an dare sukeyi da yaranta .

Da baba yai magana tace ina ya fito bai bata bai hanata bida su rufawa kansu asiri don haka ya sa mata ido dole ko ya kawo idon ya zuba a kai ba dama yace yayiwa yaranta fada tayi cikinsa da masifa da cin mutunci.

Zakiji labarin kamar kake haka dinne kuma yake faruwa a gidan namu wanda ba komai ya kawo hakan ba sai jerabawan rayuwa da mahaifin mu ya shiga an rasa wanda zai taimaka mashi ya farfado.

Mahaifinmu ance yayi boko a baya anan ya hadu da wani ubangida daya koya mashi harkan smogal na shigo da kayan waje cikin kasan nan arziki ya taso mashi sosai ga kuma yan uba masu hassada a lokacin ya auri innan mu dan ita mama kamar auren gidane a tsakanin su yan uwa suke dashi.

Wani wanda suka sani kuma dan uwa shiya hada baki da jami ai aka kama masu kaya da har yanzu babu labarinsu wanan ne dalilin talaucewa baban namu.

A yanzu kuma taimako yayi karanci koma mutum na son yi babu halin hakan a gareshi idan ba karfi gareshi ba sosai baya iya taimakawa wani saboda halin rayuwa a yau.

Haka dai muke rayuwan da dadi ba dadi a gidanmu tare da yan uwana da komai bai hadani dasu sai aike ko aikin gida da zasu saka in masu koda kuwa ina kan yiwa inna nata aikin ne.

Ban isa ince banyi ba ko ina aikin innan mu yanzu zasuyi kaina da zagi suda uwarsu suna tsina har a hada da inna a zagemu tass ba kuma mai magana.

Wani hakkuri idan yai yawa cuta yake zama na yarda da hakan gun inna don saidai ruwan ciki yasa inna ta koma daki cikin dare tayi ta kuka akan abinda ke faruwa damu gidan.

Bsn manta wani ciwo da inna tayi duk da ba a zuwa asibiti gidanmu wanan karin an tafi likita cewa tayi damuwane yayiwa ina yawa tana gab da kamuwa da ciwon zuciya.

Wai kuma sai hakan ya zamawa inna abin gori a wajen mama tace ba ciwon zuciya ba ko zuciyarce zata fashe kadan ta gani ai.

Wanan yasa nakai inna kara gidansu don takan jima bataje gida ba haka muma gidan nasu yana muna wuyan zuwa saboda mahaifiyarsu watau kakanmu bata raye.

Hakan yasa ko munje gidan bama jin wani dadi saboda sai ayi kamar ba a san inda muka fito ba har ita inna din bata damu da zuwa gidan nasu ba don wanan abin.

Ninaje da kuka ina labartawa matar kakana duk irin abinda mama ke muna da abinda akace zai iya faruwa da innan mu har mama ke goranta mata akan ciwo.

Nayi mamakin yadda ranta ya baci da abinda na fada mata din ta hau fada tana fadin ni nasan zurfin ciki irin na Ai zai kaita ga haka.

Baka taba jin Ai ta fadama damuwata saidai kaji wai a shanun talla kullum zakaga Ai abin tausayine amma bata taba bude baki tacewa mutane ga halinda take ciki a gidan mijinta.

Shi kishi aiba hauka bane tsamaninta zamuki ta don an hanata auren Abdullahi a baya tace sai shi yanzu ai komai ya wuce tunda ga zuria a tsakani.

Koshi malam da baiso auren ba ai da aka haifeki ya saki komai a ransa ya koma daya sani da bai furta komai ba akan auren a baya ga rabo a tsakaninsu.

Shine fa ta fadawa mijinta daya dawo shi kuma ya tako har gidan ya sallamawa baban mu yace yazo daukan yarshi ce kada a kashe mashi ita don yana son abinsa.

Hakkuri baba ya fara bayarwa nan malam din ya hau fada yana fadin da tsiya da arziki aina Allah ne shike bayarwa kuma ya karbe a lokacin dayaga daman hakan ga mutum don me za a lakawa yarsa tsiya har diyanta dama shi baba ai yasan gidan daya dauko Inna basuyi mashi karyan arziki ba tun farko.

Ba sai hakkuri yake bayarwa yana fadin za a gyara har ya samu malam din ya tafi na kuma ga baba ya dauki mataki kan hakan .

Don ranan da mama ta tayar da masifanta saiga baba ya fito yana fadin shifa wanan abin ya isheshi ya gaji da masifan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login