Showing 6001 words to 9000 words out of 395027 words

Chapter 3 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

hannun ki yanzun nan kuwa bai min wuya kin sani.

Da sauri maryam din ta juya ta fita daga gidan tana sauke numfashi sai lokacin ta tuna da aiken mama dataja mata kunne kan tayi sauri hakan yasa ta karasa taje ta sayo gishirin kwana ta samu ta nade kudin yadda wani ba zai taba ganinsu a jikinta ta nufi gida.

Tun daga nisa ta hango mama na leke a kofan gida hakan yasa ta kara sauri aiko tana zuwa mama din ta figi gishirinta tana fada takai mata rankwasa a kai tare da ja mata kunne tana zaginta da gantalala kin san gidan ubanda kika tsaya.

Kinci arziki yau kudin nan basu fadi ba don wallahi da an biyani kudina don bansan babu ni a wajena don Allah bace min da gani shasha kawai.

Haka suka karaso ciki mama sin nata zabga mata zagi dake alakantata da tsiya wanda ba a son anawa dan musulmi shi a bakin mutum.

Wuri ta samu ta zauna don har lokacin tana sababi da ita tana fadin abinci harya bushe ace yarinya daga karbo min gishiri kina can kina ta zubar dinki na gado ?

Uwar dai bata daga kai ta kallesu ba sai aikin gabanta takeyi ba wankau da yan matan unguwan suke kawo mata harma da wasu matan aure dashi take samun na dan laluran daki wani lokaci.

Kyalewan da inna din tayi shine kuma ya batawa mama din rai ta koma fadin ba doke a kyaleni ba tunda an mashemi mara hankali a gidan kamar mairo za a aika ace ta tsaya shirirta in ba sakarci ba ?

Nazo ina magana kowa ya zuba min ido ana kallona gobe in aiketa in halinane yar iskan yarinya kawai mara mutunci in ina da rana kowa sai yaji a gidan nan.

To me kike son ince kuma yanzu bayam wanan fadan da kike mata inyi magana kuma kice naji haushi kina mata fada shiyasa ni yanzu in kuna abinku ban saka maku baki wallahi.

Ke mairo ina kikaje tun dazun ke meyasa bakijim maganane wai baki gudun baki kullum a cikin laifi kike kika kara hakan saina karyaki a gidan nan muryam mahaifinne yake fadin haka ga yar tashi .

Mama data gama yarfa mai race daga baya ke nan ai mu zuba da kowa a gidan nan ni za a nunawa mairo yar soce in yar soce mugani a kasa don Allah ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[6/18, 9:59 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

3️⃣

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

Sai bsyan shigan mama din daki na banye habar zani nafito da kudin wurin baban mu naje na mika mai ina fada mai babansu salma ne ya ban kudin.

Na kwashe yadda mukayi na fada mai hakan yasa innan mu tabar abinda takeyi tazo tana saurare ko basuyi abinda sukeyi ba lokacin watau magana da inkiya irinta kurame na dade da sanin kamar suna tsoron mamane itace basu son su daga murya taji.

Naga babana yace a bari yaje ya mike ya fita inna ta jani zuwa daki tana min tambayan daya ban tsoro donni a lokacin dana karbo kudin sam banji komai a raina ba sai yanzu danaga action dinsu tsoro ya shigeni.

Nasan inna ta hango fitowan mamane yasa naga ta barni ta fita muryan mama din naji tana fadin ina kuma shiya tafi yanzu na barshi zaune ai ko wani makircin aka samu kowanku yabar tsakar gidan mafarin akiyoyin mutane su shigi suyi min barna.

Nagama baku abinci kuyi min sakaiyan tsiya abincin na duba ba wani abinci bane fa namu rabon kanzone na kasan tukuya ake kwaso muna nida innan mu da kannena biyu.

Shine kuma ko yaushe akai magana mama tace tana ciyar damu daga mu har ubanmu bamu da daman dogon motsi a gidan gorine zai biyo baya yasa innan mu bata wani motsi tana kuma yini a wahalce ga aikin gida ga nata sana,an.

Shiko baba yana zuwa kofan gidan ya tura yaro a sallamo Alh ya dan jima bai fito sai gashi ya fito tun kafin ya karaso ya soma fadin a,a mlm Abdullahi kaine ashe ?

Nine Alh suka gaisa ya soma fadin yarinya ce yar wajena ta koma gida muna da wa yan nan kudin wai cewa kaika bata ?

Murmushi Alh ya sauke kafin yace kwarai don nabawa yarana kamar yadda na saba idan dan wani abu ya shiga hannuna tana wajen yasa itama na mika mata don rabonta ya ratsa tunda tana wajen lokacin.

Amma Alh kamar kudin sunyi yawa ai mlm Abdullahi yarkafa yatace nima kuma bayan hakan muma muna more mata a gidan don yanzu haka idan kaga tulin kayan data wake a gidan na abinci sai kayi mamaki don haka don mun mata alheri ai bai zama wani abu ba.

To Alh kasan yaran yanzu duk da bata da irin rayuwan nan amma dan yau baka shedanshi hankalinmu ya tashi sosai wallahi da ganin kudin nan .

Wallahi ita da yan uwanta na rabawa kada kaji komai baba ya dubi kudin a hannunsa ya juya ya sauke ajiyan zuciya yace to Alh mun gode Allah ya karawa arziki albarka.

Amin nima nagode naji kuma dadin tasowan da kayi kazo ka bincika hakan daga gareni ga wanan kaima ka kara ayiwa iyali hidima dashi wancan kuma kudin cin tarane na basu ai ba wani abuba don yanzu idan na koma saina dauki lokaci ban dawo garin nan ba yasa nake masu hakan.

Ya mikawa baba kudin yayi godiya sosai ya bada baya ya koma fadin da yamma bayan magariba azo a amshi dan wani abu don iyali.

Haka baba ya dawo gida kafin ya dawo na kula da tashin hankalin da mahaifiyana take ciki don gudun jin mugun labari akan kudin bayan sakani daki da tayi ta tsure nayi mata rantsuwan cewa wallahi bani yayi kuma dadewan da nayi wanke wanke hjy tasa nayi mata .

A lokacin maman su hafsa din bata koje makka ba kudi daine ya fara tasowa mahaifinsu suke jin kansu a cikin unguwar.

A lokacin abu biyu sukafi tsayawa inna a rai na farko kardai ace dauko kudin nayi bada sanin su ba don kudin a ganinsu yafi gaban kyauta ga yaro.

Sai nabiyu kuma rokon Allah take Allah yasa ba wanan bawan Allah ya kasance irin masu batawa mutane diyansuba yazo ya lalata mata yarinya ga banza ta shiga wani ukkun kusa da tara.

Saiga baba ya dawo ya zauna ya bude abincinsa yaci gaba daci mama ko ta kara shiga firgici ina kallon sanda ya saci ganin mama yayi mata inkiya da hannu alaman babu komai ai.

Lokacin na sake labule ina ajiyan zuciya na jawo matattacen roban abincin da mama kan dan watsa muna kazo na dan kyafata ina kaiwa cikina abincin cikon wani yanayi na tausayin mu.

Baba na gamawa ya fita daga gidan har mama na zolayanshi da yau kuma me aka samune za a fita yace kinsan abin Allah bari dai in fita in ga garin.

Ba,ako jima ba sai gashi ya dawo da cefane irin ta maza mama dake duke saida ta mike tana kallonshi cikin mamaki a kofan mama din ya aje yana fadin aina fada maki abin Allah yawa gareshi gashi ko kin gani na fita a cikin sa,a yau.

Malam wanan ba karamin cefane bane fa kayo muna ya kai zaune ya soma fadin meye ranan samu ga mutum Rakiya idan Allah ya kawo alheri iyali su sheda hakan.

Duk zancen da baba keyi idon mama yana a kan ledojin daya shigo dasu din kafin ta bar aikin da takeyi ta karaso wajen kayan ta duka ta soma budewa tana jagula.

Dan shimkafane da ba zaifi sa,i ukku ba sai alaihu da kayan miya budan bakin mama sai cewa tayi Ai kawo roba a raba da sauri baba ya dago yace me za a raba kuma a nan Rakiya ?

Ohh to kai kaga hakan ai gara a raba don idan ya kare kuma kowa yaci barnanshi kuma ni yanzu na gane ai kowa ya samu kansa ya sani ashe ?

Wai meya kawo zancen nan kuma Rakiya tace meye ma bai kawo ba Allah ya kyauta ina ta fada ta dago kai tana fadin inna Isa dauko roban ki kawo mata da dan gora.

Isan banza isan baka isa ba watau ke har kinga abincin yau mijin ki ya kawo zakiyi min maganan bamza ko dadina da gobe saurin zuwa.

Yanzu kuma yaya mena fada don Allah kince a kawo roba nace ta dauko nasan tunda kika fadi hakan sai an raba shine kuma laifi yanzu.

Ai da kin sani kada ki bata bakinki indai wanan dan abinda kike gani har yasa zakiyi min rashin kunya yau a gidan kece kika taso a hakan a tsiyace ni ban saba da wanan rayuwan ba sai da aka dauko muna alkakai a gida yanzu.

Baba na kurum baice komai ba tana fada tana rabawa da suna sunan daki kinga ke nan mu za a kwara a dakin mu don gwangwani gwangani tayiwa kowa da sunanshi har wa yanda basa nan saida ta cire masu.

Ina tsaye na rakube ina dana sanin bawa baba wanan kudin gashi yanzu gaba daya ya koma hannun mama ke nan da dan abincin daya sawo muna.

Nasan ya gaji da gorin mamane ba ranan da gari zai waye a gidan nan bata gorantawa maman mu dashi ba kan tana ciyar damu kuma ana mata bura,uba da jiji da kai.

Ki duba fa mutanen da basu data cewa sai yadda tayi damu amma hakan bai isheta ba sai tayi gorin nan da habaicin data sabawa innace damu tsiyar gidan mu.

Wanda ba komai takewa hakan sai baba dayaki sakin inna din kamar yadda tasha hada baki da yan uwarsa da abokai kan cewa innace mai farar kafa dayasa baba ya talauce ai.

Shi kuma yaki sakin inna din wanda shiyasan dalilin hakan yabarwa cikinsa kuma saidai mama tayi bal,inta tagaji bai aki din .

Wanda nasan in har haka ya faru zamuga tasku a wajen mama inna na nan ma yaya aka kare balle ance babu ita a gidan hakan yasa duk da shekaru bai kai ba nake gani mutunci baba a idona.

Na dauka zuwa dakin mu ina dan juya dan abinda aka bamu din a cikin roba kamar ina bakace naji muryan mama na fadin to askaran na sidi ko kina da maganane ki fadi don nasan ki aika wata rana ke din nan da nake gani da badon Allah ya dorani a kanku ba dana takus a gidan nan wajenki da uwarki.

To Allah ya tarfa min banda gado tsiya balle a ga bayana kuma har abada munyi gaba ke nan saidai kare ya mutu da haushin kura ehh,he ?

Ban jiyo ba don nasaba jin hakan a bakinta dakin mu na shige na aje kayan gefen daya na koma na zauna a kofan daki inci gaba da kallon draman gidan mu.

Ina ko kallon yadda baba baiji dasin hakan a ransa ba ya dai ja takalmansa zuwa waje ya zauna yana tunane wanda maza da yawa a yanzu yakesa su fadi da hawan jini lokaci guda.

Muna zaune muna kallonsu har yamma lis innan mu bata dora tukunya ba nima banyi magana ba muryan mama naji tana jefo min zagi ba zan tashi in share gidan bane ko gulman ban gama bane na tashi cikin sanyi jiki zuwa aiyukan da nakeyi a kullum.

Ohh dai bansan mutum yayi fushi da hukuncina ba sai naga ya dawo min dashi haka naga daman ayi hakan kuma za ayi din.

Badai wanda ya tsaya tankawa a cikin mu waye zai tankata ma har yaranta dake talla suka fara dawowa gida a lokacin.

Ina jinsu sun shige lungunsu suna kwasan dariya ita da yaranta abin na miji daidai lokacin baba ya saci jiki ya shigo namu dakin yana fadin meyasa baki girkawa yaran nan abinci ba kinsan kuma ba zata bayarba tunda ta fadi.

Baban didi hankalinane bai kwanta ba banji yadda akayi yarinyar nan ta samu kudin nan ba ina zanje dafa abinci bayan an barni a cikin fargaba ko ita yaya taji daga inda kudin ya fito nasan ai da bata dafa don zarin da zata saka min yau gidan nan.

Nan ya kwashe komai a gurguje ya fada mata tare da fiddo da kudin ya mika mata yana fadin kin gansu nan wallahi kwandala ban taba a cikinsu ke na barwa ku samu na jan jari ko dan wani sana,a ku fara da mairo dan kudi na shigo maki saidai rike zan zo daga baya in labarta maki komai.

A sanyayye inna ta karbi kudin ya juya ya fita yana fadin kiyi masu dabara don Allah kada su kwana da yunwa yafice baiko jima da fita ba mukaji muryan mama tana fasin kamar naji muryan malam ko ?

Allah ya taimaka yarta ta bata amsa da fasin shine mana ruwa ya shigo ya diba ya fita aibai tsaya ba kai jama,a akwai mata a duniya da kishi kesa su manta da lahiransu.

To mama na cikin irin matan gaskiya don sam rayuwanta ina ganin bata tsoro ko tuna mutuwa gani take tana da daman zama a duniyan nan har abada ita.

Haka kuma bata taba muna fatan alheri ko mu kusa kaita balle mu fita ita abinda ta rike shine mu din dai jinin tsiyace kawai ba wani abu ba.

Ban dai san yaya akayi ba naga inna ta fara sana,an koko da kuma kasarin koko din danya tana saidawa da safe.

Bayan hakan ya faru munsha habaici da zargi iri iri a gun mama don tace baba yaba mama kudi a sace don ya dagata ya rantse mata baita kudi ba bai kuma san inda ta samu kudinta ba.

Haka yasa takoma cewa zuwa inna zuwa tayi ta ciwo bashi a cikin mutanen unguwa nan ma tasa ido ko zatagano bata gane komai ba bata kuma kyale zancen ba ita ala dole sai tasan komai akai.

Inna kuma cewa tayi yayantane ya bata don ta juya daga haka taja bakinta tayi shiru don an shammaceta saida taje unguwa aka shigo da gero da dawan gida.

Duk da muke wahalan nikan mu amma haka mama zata cikawa nikan kudi sai inna ta biyata bamu gane hakan ba sai bayan lalacewan injin din nata da muka fara kai nika wajene muka san ba karamin cutawa inna mamakeyi ba.

Wanan dai yana tafiya hakana sai wani kissa da aka dauko na lalatawa inna kasarinta idan an niko ko a zuba gishiri ko kuma wani abu dai haka da zai lalata mata nikan nata a kashe mata kasuwa .

Cikin ikon Allah kuma haka mutane zasu saye saidai suyi korafi a kai wanan yasa muna tacewa zamu dauka mukai daki saiya kwanta a fito dashi a tsiyayye karshenta kuma akuyoyin mama za aba ruwan yamin susha amma kuma duk hakan baiwa mama din dadi ba.

Ashe da gaskene da akecewa kishiya bata son taga kishiya tafita koda gashin giran ido wanan zance gaskiyane inna da take dan sana,anta da Allah ya rufa mata asiri take samu taci tasha a ciki ba burin aje komai daga hakan sai rufin asiri amma mama ta kwallafa rai ga wanan abin .

Ban tafiya makaranta saina fita da safe na sayarwa inna da kokon ta a kofar gidan mu don mazan dake sammakon zuwa nema suke saye saboda bai yami yasa suke son kokon baiko isa wani lokacin.

Haka kuma zata dama muna wanda zamusha daga ciki shine abincin ranan mu duk wanda ya dawo a cikin mu shi zan kamfata yasha sai da dare take muna abinci muci a lungun mu.

Don mama ta raba girkin gidan kowa tashi ta fisheshi Allah ne mai son bayinsa ya kawo muna mafita wanan sa,anan da inna keyi yanzu.

In bashi ba kafin ta soma sana,a mama ta dauko hanyar gasa mu da yunwa a gidan muna kallo ta tsiri girkin dadi don mu a ganin mu girkin dadine taliya da jajjage su fito suna ci ita da yaranta sai gashi ba afi sati biyu a hakan ba inna ta fara sanan,an kamu din wanda ya dagawa mama


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login