Showing 174001 words to 177000 words out of 395027 words
Chapter 59 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
bashi amsa ina fadin ban jin zan kara harkan nan don a yanzu na daina saboda elders dina basu sha,awan hakan gareni.
Why zasuce haka Allah ya kawo maki abinyi tun baki kare school ba hakan ba karami opportunity bane a wajen ki koda school kika kare yana da wuya ki samu aikjn daya kai wanan din a kasan nan.
Nayi amfani da hakan don in taimakawa rayuwanku don zama taren da mukayi da juna ta yadda ba zaku taba mantani a rayuwanku ba.
Ko hakan ai mun gode wayanshi yayi kara naji yana fadin wait my Dad is calling me ya mike tsaye numfashi na sauke tare da dan jan guntu tsuki ina fadi kasan zuciyana ai sai kuyi da wata kuma yanzu.
Ni dai wanan aikin tunda da kasada a cikinshi banjin zan kara jefa kaina cikin irin hakan gashi an fara min kallon mara tarbiya a idon mutane.
Dan raman da jigilan da nayi a dan kwanakin yasa kurciyana ya kara fitowa fili da kyau na koma ban son yawan magana dama ba gwanan hakan bace ni saidai ina da kaudi da rawan kai idan ya kama.
Zaune take tayi shiru tana saurareb inna cikin tashin hankali da abinda inna din take fada mata a lokacin .
Don ta kasa furta komai kozata furta bata san kalman da zatayiwa inna bayani dashi ba a lokacin sai faman tunane takeyi gaskiya sariya bata kyauta mata ba da tayi mata hakan.
Saida inna tagama fadan abinda ke bakinta ta dago tana fadin inna kiyi hakkuri don Allah amma zanso ki fahinceni don Allah ?
Don wallahi ban fadawa Sariya wanan zancen don tayiwa maryam haka ba ina son ki fahinceni inna don Allah .
Shiyasa nazo ai don ko ita matar gidan mu ai ban mata maganan komai ba tukun wallahi lokacin da mama murja tazo gidan nan tana fadin zancen nan ban daukeshi komai ba illa sheri irin nata kawai.
Shine bayan fitanta na kira sariya din ina labarta mata abindata fada don kawai ta tayarwa mutane da hankali.
Amma sai Sariya din bata tsaya ta fahinceni ba ta soma fadin dama an fada mata cewa haka Akeyi a arewa don sai mutum ya gama rike yarinya tsakani da Allah a karshe idan ta girma ta waye sai a aurawa mijinka ita.
Tun daga lokacin ta kasa tsayawa ta fahinceni balle in mata bayanin yadda abin yake har suka samu wanan matsalan amma ni gaskiya bata fada min har abin yakai haka ba gaskiya.
Don nima har mu samu matsala a baya da ita saboda zancen sai daga baya mukazo muka shirya tsakanin mu.
Amma kinsan hakan da kikayi wallahi da bake bace wanan abjn gaskiya sai inda karfina ya kare akan zancen nan koda na yarda ta tafi wajensu bawai na gaza da ita bane ai.
Fin karfina akayi lokacin da kuma Allah ya kaddara sai tayi rayuwa dasu a tarihinta wanan ne kawai yasa har ta zauna a can din .
Kiyi hakkuri inna anty Fati ta fada karo na barkatai a bakinta a cikin kunya tana fadin kuma nagode da yadda kikazo din nan kika sameni har nan gida ba tare da wani ya san hakan ba tsakanin mu don sai a dauka da niya nayi hakan ga maryam din don in raba tsakaninsu.
Inna ta mike tana fadin zata tafi don ta gamsu da bayanin da fati din tayi mata a lokacin har inna ta mike anty Fati ke fadib ashe shine dalilin dauke kafan yaran nan dani ?
Dolene duk wanda yaji haka fati ace kece kikawai yarinyar nan haka dole ransa ya baci ko abin ya bashi mamaki don Allah inna a basu hakkuri nima zan shigo da kaina in fada masu ba haka zancen yake ba .
Itako Saudat da inna ta koma tana fada masu yadda sukayi da antyna din sai cewa tayi wallahi inna da baki je ba ni wallahi matar nan tafice min a rai.
Ranan da aka kai turaren nan halima ta shiga tana neman innan mu da mama taci karo a tsakar gida tace maman maryam take nema don Allah ance nane gidansu.
Eh nan ne daga ina kike take tambayan halima din daga unguwar ,,,,,,, kizo ga innan mu ko kece zaki kawo sakon daga lagos ehh nice ga driver nan a waje don Allah muje ku sauke kayan yanzu muka shigo garin ko gida banje ba.
To yar bana bakwai ai bance nice innan taku ba tambaya kawai nakeyi in gidan nan ne dama kinzo kin wani tsare kina son muna fitsara.
A,a mama dama nasan da zuwanta don yayan mu ta bugo min cewa zasu shigo ni shiyasa ai nayi magana ta fada tana turo baki suka fita da sauran yan uwa zuwa wajen.
Sun dauka kawai dan sakone saiga sayayya sunga ana saukewa koda suka fita don irin manyan buhun nan na dauko kayan lagos ko kano sune aka ciko guda biyu sunsha dauri tama ake saukewa a kofan gidan.
Saida maza suka tallabawa driver ya dan shiga masu dashi ta cikin gidan don kayan sunfi karfin daukan mata saboda nauyin su.
Nan mama ta fara sintiri tana kai da komo a tsakar gidan a karshe taja tayi tsaye tana bin su da kallo halima data shigo da sauri tana fadin to mu zamu tafi dama alkawari na dauka kuma nacika ga wanan muje daki in maki bayani inna tabita zuwa dakin nata.
Kudine cash dinsu ta zaro ta mikawa innan din tace idan kunyi waya zatayi maku bayani su saudat suka foto su rakata nan mama ke fadin mairo din zata dawo gidane ko ?
A,a haba dai ai koku ba zaku so maryam ta dawo gida a yanzu ba kawai dai aikene tayo gida da mukaje suna matar yayan mu data haihu shine ta ban sakon inzo mata dashi.
Bango inna ta dafa saboda jiri daya dibeta a lokacin ta kurawa kayan da suke kokarin dauka zuwa dakin su ido na dan lokaci kafin ta sauke ajiyan zuciya tana fadin cikin biyu dai dole akwai daya a nan .
Allah ya kyauta ta juya zuwa dakinta nan ta samu sahura da take ta sharan barci tun safe ta dinga fadin keki tashi don Allah wanan barcin aisai a zo har a gama dake haka.
Ga kallo can cikin gidan mu yau wai Mairoce tayo sako tun daga ikko a kawowa uwarta wata mace ta shigo dashi yanzu.
Ita mairo din tayo sako gida sakon me kuma nikan ina na sani manyan buhune na zuba kaya saida aka takesu tab da kaya a cikinsu da wani katon kwali bansan meye a cikinshi ba.
Ihun da yaran inna suka saka shiya dan firgita wanda su ihhun murnan ganin tv sabo gal da sukayine cikin kwali yasa su sake ihun farin ciki.
Wajen ta nufa ta soma fadin lalai bariki ya soma rana wace ba aiki takeyi ba zata aiko kaya haka kamar mai zaman kanta ?
Zaman kai yanzu ai yaya ko a gidan iyayyeb ka kake in Allah ya saka maka hakan sai kayi don bai zama abin kunya ba kuma wasu insun fita aisai ranan da aka gansu kuma hakan bai zama magana ba ai.
Mama irin matan nan ne da in ransu ya baci tun a lokacin sai sun amaye zuciyarsu sun fadawa abokin zama abindake ransu da suke son fada mai dama yana ransu aje.
Wanan yasa ta furta hakan ta manta da cewa tana da avin fadi a dakinta ba wanda ya taba fada mata hakan amma sai gashi yau inna na mayar mata da amsa daidai da ita ta kuma san me inna take nufi da hakan data fada.
Ko kafin baba ya dawo gida sunyi kaca kaca da juna a ranan kowa ba bacin dan wani a cikinsu yaya sahura ce ta fito tana fadin.
Mama kin kai ga abinda kike so ina ruwanki da sakon kayan mairo tunda ba yarki bace saidana fada maki karki fito kika ki yanzu ai gashi an fada maki abinda ake so .
Koda ta koma dakinta bata daina magana ba sai fadi takeyi nayi nadama kwarai wallahi na cuci kaina da nasan haka abin nan zai zama da cikin ku na tura daya tun farko da duk wanan iskancin ai ba ayishi ba.
Mama bashi yasa akecewa in zaka gina ramin mugunta ginashi ya zam gajere koda kaka fada ya tsayama iya wuya.
Nifa nakance irin abinda kikaitawa mutanen nan yasa Allah ya tsame mairo a cikin mu ya kaita can gashi kuma har yanzu mama baki daina hakan ba don Allah.
Nifa banga abinda innan su mairo keyi maki ba gidan nan amma ke mama kullum neman sheri wa matar nan kikeyi har gobe don Allah dai mama ki daina.
Matar nan ko mu tana iya kokarinta damu wallahi amma ke ace in kin tashi abu saiki nuna dukka diyanta baki kaunasu ita kuma murja tana zugaki kin kasa ganewa ?
Nifa irin zancen nan nakine bani so in abu ya taso saiki nuna nice banda gaskiya ki nemi cewa zaki min nasiha Ai ne zan tsaya tausayawa matar da tun ranan data shigo gidan nan ban kara farin ciki a rayuwana ba ?
Duk da hadarin daya hadu a garin hakan bai hanani tsaya shagon in saiwa kaina abinda nake so ba a lokacin bakin hadari bai rudin dan lagos don cikin ruwa tsamo tsamo suke harkokinsu na yau da kullum.
Nashiga na tsinto yan kayan amfanina na daki da nake so sai antyna da Amira da suma na dan riko masu nasu har Aminullah da uwarshi hakan nakanyi duk lokacin da zan sai abu da kudina nakan dan hado dasu in masu sayayya.
Na biya ina fitowa da sauri don yadda garin ya kara rikedewa ina gudun ruwan sama ya sauko ya taba min jikina don nikan bai ban lafiya ko don ina farar macece oho ?
A bakin kofan shagon mukai kicibis da juna dashi wanda nasan ya kula da dan razanan da nayi a lokacin kai na kawar gefe daya ina gyara rikon ledan hannuna.
Ke baki ganin yadda hadarin nan ya hadune kike kokarin fita daga nan ina wuni na fada a cikin hausa sabanin shi da ya zuba min turanci a lokacin.
Ganin banda niyar tsayawa don cewa da nayi yanzun nan zan tare taxi na isa gida sai naga ya tako a nutse ya juya yana fadin muje na saukeki.
Daka barshi ka shiga yanzu zan samu abin hawa a nan din motarshi ya nufa ba tare da yayi min magana ba ya bude ya shiga ya tayar inda nake ya tsaya dole na bude motar nashiga.
Ya juya muka bar wajen baice dani kala ba nima hakan mota yayi shiru sai goge glass da yakeyi don yaga gabashi a lokacin.
Ke baki tsoron ruwane kika fito wanan lokacin muryan shi naji a kunnena yana fadan hakan wanda hakan yasani sauke ajiyan zuciya na soma fadin.
Daga school nake na tsaya nayi dan sayayya don gobe ba school ina son in huta gida ba sai na fita ba.
Idan ba school baki da aiki gobe ne ko kun daina aikin company nakune yanzu mai hatsari wanan aikin bama mata bane gaskiya.
Ko mace zatayishi sai macen kabila don dasu yayi dai ba irin ku yayan hausawa ba son bai dace da al,adan bahaushe ba sam .
Abin ya ban dariya don shi neman kudi a lagos ina ruwanshi da yaren mutum idan dai bana kaucewa bane saidai na dake banyi dariya ba amma sai nayi dan murmushin yake kawai nace na daina ai tunda baki yayi min yawa kada bakin mutane ya kamani.
Tunda wani bakin ba kyau gareshi ba wasu kuma tsaban sa idone kawai da rashin fahinta yasa sukewa mutum wani kallo na daban.
Shima murmushin naji yayi a lokacin yana dan jingina da kujeran mota can yace idan kin daina wani aiki zakiyi yanzu tunda kin sawa kanki neman kudi ?
Abinda na samu a wancan aiki ya wadatar dani a yanzu Alhamdullahi tunda na kusa gama karatuna a yanzu dama don karatuna nake aikin ai ba wani abu ba.
Ranan kan ba zancen kwatance don yasan gidan a lokacin don haka muna daukan round din juction din unguwar mu aka fara zubo da ruwan sama mai karfi gaske haka yaci gaba da tuki har zuwa side din namu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[8/30, 9:50 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
5️⃣5️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15_ HAWAYEN KADA🐊
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Muna kawo kofan gidan mu ruwa ya sauko da karfi sosai fiye da wanda muka baro a hanya i zuwa yanzu dai wayena yakai in san kan mota don haka naji karan rufe kofan motan nashi a wanan lokacin.
Dan satan kallonshi nayi bai kalloni ba zakice baima ganni ba saiji nayi yana fadin nasan zaki iya kasadan shiga ruwan nan yasa na kulle kofan ai so be cool beb ba satan mata nakeyi ba.
Ban daiyi magana ba sai tsiwan da nakeyi na dan zakuda ina rausaya kaina ina gyara zama tare da sauke ajiyan zuciya lokaci guda.
Sai cam nace ba,a san dan kano da aikata wanan ba ai saidai in haure yaiwa sunan dan kano murmushi naji yayi yana fadin so yanzu kin yarda ni dan kano ne ke nan tunda kin ganni gidan uncle dinki a cikin kanawa ko ?
Amma da farko dana fada maki dan kano nake ai boye min kikayi kika nuna bake bace nake nufi bayan kin gama rubuce min mota da sunan maryam ina kai wanki ko in goge .
Abinda ya fadane ya ban dariya har kumatuna suna dan lutsawa dan wishiryan bakina ya dan baiyana ido na lumshe ina tuna wanan shirnen na kurciya da nayi a baya wanda idan naga motar mutum zan tsaya saina rubuce motar kaf da jagwalgwale irin ta yara waini ina yadda malaman mu keyi a aji.
Zaki iya aiki da mu though badai wani aiki bane irin wancan amma sai nake ganin zai maki wancan sauki gaskiya amma kiyi shawara a natse idan zaki iya tura abubuwa a email shine abinda nake son daukaki abubuwan sirin ma,aikatana wanda ba kowa zanso ya sanda shi ba don naga kina da natsuwa zaki iya hakan understood ?
Ya dago kai yana kallona nima kallon nasa nakeyi a lokacin cikin mamaki da al,ajabin jin zancenshi a kaina inda a kasan zuciyana nake fadin dama maganan da yace yana sonyi dani ke nan nake ta kaucewa ashe ?
Kinji ai me nace kiyi shawara da kyau kika dacewan aikin idan hakan bai maki ba sai a duba wanda ya dace dake din a baki.
Karatu fa nakeyi har yanzu ban gama ba kuma So banda takardun da za a daukeni aiki dasu a yanzu inba na secondary ba ?
Na sani amma kinji na fada maki ai a karkshina zakiyi aikin ba a wajeb wani da zai bukaci takardun ki ko wani abu ba indai zaki iya tura sako zuwa emai ko gmail fine ba matsalan haka ai.
A raina nace a wanan zamanin aiko dan primary yana iya tura sakon email balleni da nake batun hada kwalin degree a yanzu don haka nace tun a lokacin wanan mai saukine ai saidai ta yaya zan iya zuwa tura sako ga kuma school da nake zuwa ina ganin hakan ba mai yuyuwa bane yanzu a gareni gaskiya.
Zaki iya zan tsara yadda