Showing 240001 words to 243000 words out of 395027 words
Chapter 81 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
ko mujjala zasu gane hakan a gareni karshe dai fadane kawai idan anyi min kuma shike nan amma nauyi da kunyar da zan bar iyayyena da yan uwa fa a ciki ?
Sunyi min tayi sosai akan in yarda in shiga wanan gasan amma sam na nuna masu addinina da yarena basu amince da hakan ba sukace sun ban lokaci inyi tunane don ba karamin riba dani dasu zamu samu ba idan naci nasara a haka suka kyaleni sai an kwana biyu zasu kirani suji ra,ayina.
Sunyi tain barazana iri iri amma naki yarda in amsa masu sai hakan ya dan fara jefani tunane har nakai ga son in nemi shawaran mai sunan baba inji kada inyi abu ni kadai matukar hakan bai sabawa addinina ba.
Na fito daga class ranan na kirashi a waya don in sanar dashi abindake faruwa shika daine a yanzu nake dashi da zai tsaya ya fada min gaskiya koda banso hakan ba kuwa.
Kira ukku na jera mashi lokaci guda bai daga ba hakan ya ban haushi sosai naja tsuki ina tura wayata a jakata dake gefe daya aje.
Ban jira tashi daga school din ba na nufi gida saidai sanin wace keda girki yasa na tsaya nayi take away a hanya kafin na karasa gida.
Bani kadai ba har antyna na hadowa shi komai saida na shago leda biyu da cimaka da zai kaini har dare munaci nashigo gida dalilin dawowana a lokacin kuma shine in samu antyna da zancen dake cina a rai na tsayawa gasan kyau da ake son inyi din.
Saidai na dawo na samu ta fita ranan bata gida haka bai wuce gida ta tafi wajen mommy ta dubota don sam ita bata damu da fita zuwa unguwa ba sosai don kullum tana gida kwance.
Ruwa na watsa a jikina na fito nayi sallah la,asar na zauna naci abincin da nasayo muna saida na koshi don tuwon gargajiya na sayo na alabo da miyar yauke da manyan nama .
Hakan yasani jin kasala da kyar na mike na saka dan dogon riga a jikina na koma na dan kwanta ina karatu a haka barci ya soma daukana a wajen.
Karan da wayana keyi yasa na dan falka a dan firgice ina daukan wayan na duba a zatona saudat ce da mukai kwana biyu bamu gaisa ba dasu take nemana a lokacin.
Sai naga number kamar yadda nayi serving a wayana da daddy Aliyu A A Y tambayan kaina nayi da dama bai kusane yasa bai dauki wayan ba ke nan lokacin.
Ina dauka yanayin muryanshi ba dadi yake fadin sorry maryam kin kira ban daga waya ba ina nan nazo kano duba mum dinace tana jin jiki kwana biyu ?
Subbahanallahi umma najin jikin da sauki yace Alhamdullahi ta samu sauki sosai har an sallamota ai yau.
Ya fada tare da tambayan ya kwana biyu na amsa da lafiya Allah yasa kafarane a gareta ya amsa da amin ina jin yana sauke ajiyan zuciya ta cikin wayan.
A gaida umma din Allah ya bata lafiya ya amsa da amin tare da fadin lafiya naga kira dazun jere da juna har kira ukku ?
Lafiya na fada ina kokarin son kashe wayan yace nafa san halinki maryam baki kiran mutum sai da dalili fada min meke faruwa ?
No ka barshi kawai yace No nace ki fada meya faru nace dama dama kawai dai a bar zancen shike nan naji yace look maryam .
Ki fada min ko meye ko kuma wani aikin ne kika kara samu kuma yanzu kike neman shawarana ?
Ba aiki bane wanan karon daga school ne na soma labarta mashi yadda abin yake da irin tayi da barazanan da sukai min kan abin ki jirani gobe zan shigo school din naku .
Iya abinda ya fada ke nan ya kashe wayan a lokacin wayan tawa nabi da kallo cikin mamaki ina fadi a fili wanan dan zafin raine daga magana baka tsaya kaji ba zaka kashe waya kace wai zaka shigo gobe towa ya gaiyaceshi da zai shigo din ?
Barcin da ban koma ba ke nan don yamma da yayi naji muryan antyna tana fadin wai maryam ce ta dawo yanzu ?
Na amsa da ba yanzu na dawoba anty ina gida tun dazun na mike na fito falo na sameta ruwa na dauko mata tare da abincin ta dinga godiya tunda ta bude taga abinda ke cikin roban abincin.
Tare sukaci da yarta suna hira na fada mata damuwana da yasa na dawo take fadin akwai alheri sosai ga wanan gasan maryam ai nan Lagos ne koda kinyi ba kowane ya sanki ba balle ace wani abu a kai.
Idan kinji kina da sha,awan yi ki shiga kawai kiyi abinki tunda ba wanda zai tsaya kallon ke wacece balle ya zama abin magana.
Sallah ya tayar dani daga izani da antyna ke faman zugani yi tana fada min fa,idodin dake cikin gasan idan har anyi nasara har mota ina iya samu ai nace mota a yanzu aiko da naci ubanta garin nan ta dora da fadin zakiga mutane suna girmamaki kamar wata hjy can ke abin akwai sha,awa fa sosai idan ka iya.
The only things shine saka wanan kayan mai kama da mutum yana tsirara kuma in zaki iya ai hakan ba komai bane nake gani.
Da wa yan nan maganganu nata namike naje nayi sallah ban fito ba na zauna azzakhar din yamma a wajen har aka kira sallah na mike nayi na idar ina addu,a wayana ta soma ringing hakan yasa na mike na dauko ina dubawa.
Maryam sorry to say ba zan samu shigowa school dinku gobe ba sai zuwa jibi ko bayan hakan so please kada ki soma ki yarda kiyi wanan abin .
Su nemi wata can tayi why zasuce saike kece ke nan baki san ciwon kanki ba komai kamar ya zakace min bansan ciwon kai na ba kuma don kawai suna son inyi contesting zaka fada min haka ?
Ohh Load ki fahinceni mana don Allah kin gane ko kada ki soma kiyi yarda da duk abinda zasu taya maki kinfi karfin wanan abin da zasu baki koma meye shi.
Da sun kara zancen nan nuna masu iyayyenki sun hanaki muji abinda zasu ce na amsa dana gode don magananshi yafi na antyna tsaya min a rai.
Dama na sani sam ba zai yarda ba saima dai ya kara min kwarin gwiwan cewa kada na yarda nayi abinda kimana da mutuncina zai zube gashi kuwa din ya fada min kamar yadda nayi tunane.
Saidai da yake cewa kome zan samu nafi karfin hakan shi yana daukana diyan wani mai kudine kome na fada mashi ai babana saida abokina ya taimaka mashi yanzu yake samu .
Zan dai bi shawaran nashi don shikan gaskiya ko malam Alin da naji wasu na kiranshi yaci wanan sunan wajen kula da addininshi is hard ka samu matashi kamarshi wanda kudi ya zaunawa har yana iya nuna kanshi a yanayinshi amma yana rikon addini haka kamar dan gidan sharifai ko wani shekk na musulunci.
Koda zan fita da safe saida antyna ta tuna min da zancen na duba idan zan iya in karbi form din in cika ita tasan yadda zatayiwa Paapa magana.
A raina nace kice haka mana tunda ke ba sanin daraja da kima kikayi ba balle kisan kunya saima naji hauahinta a raina har ina zargin ko so dai take dama in lalacene wai ?
Kamar yadda ya fada min haka na fadawa mrs Laurence nace mata iyayyena idan sunji zasu tsine min kuma zasuyi kotu dasu kan hakan .
Take tambayana dama iyayyena suna raye nace both dinsu da mamana da babana are alive suna kano zaune wanan yasa tace zan iya tafiya .
Ji nayi kamar an cire min kaya da wanan zancen hakan yasa naga inkirashi in fada mashi yadda nayi dasu ranan don haka bayan nagama komai na daga waya na kirashi muka gaisa dashi na soma tambayanshi jikin ummah din yace taji sauki gasu tare ma.
Naji ya mika mata waya ina jin kukan jariri a wajen take tambayan waye naji yana fadin ku gaisa tana tambayan jikinkene kawai daga can lagos ?
Aka karbi wayan ana fadi ina wuni na amsa da lafiya kalau ummah ya karfin jiki tace da sauki angode Allah yayi albarka na amsa da amin tare da saurin kashe wayan nawa koba komai naji muryan yan gida yau sai naji tankar in bude ido in ganni a garin kano don jin muryotin mutanen nan da nayi lokacin.
Barci ya daukeni ashe yayi ta kiran wayan ban sani ba don a silent take tunda zan shiga class na sakata silent din har wanan lokacin.
Barcina nayi hankali kwance har bansan inda nake ba sai asuba na falka na kewaya bandaki hakan yasa nagane cewa asuba ya kusa a lokacin.
Wacece wanan muka gaisa da ita uwar take tambayanshi ganin tun bayan data mika mai wayar yanata neman layin shiru.
Ya dago kai yana fadin watace a can take zaune tare da iyayyenta amma su din yan garin nan ne tana aikine a wajen mu can lagos .
Shiru tayi tana gyara hijjan din dake wuyanta tare da kallo hjy Asmau matar malam babba da tazo zama da ita zakice wani sabon haihuwane a gareta kamar yanzune ta fara haihuwan da saboda gatan da wanan dan ya samu dan da mutane ke masa lakani da yawa kamar haka.
Rabo , tunau, auta dan kalan hanji kamar yadda su hjy asamau keyi masa sheri tun haihuwanshi.
Ganin hjy Asmau ta mike da yaron tabar wajen yasa hjy hauwa din dagowa ta dan dubi dan nata da akai komai a tare dashi har tsakanin shi da mahaifisu an rasa wanda yafi wani damuwa a cikinsu lokacin labour dinta.
Wanda har yanzu duk da yadda ya nuna farin ciki da murna a fili na samun kanin da sukayi har yake kiransa da sunan mahaifinta baban watau Ahmad .
Baba sai yaushe zakaje ku shirya da Azima tun wancan zuwan da kayi na fadama abinda hjy ta fasa akanku amma kaki ka maida hankali ga zancen ?
Na turo maka lamba ka kirasu tace har yau baka kira layin nasu ba sai taga kamar nice ban son wanan hadin da takeson ayi tsakaninka da yar uwar taka ?
Ummah idan na tashi zuwa gidansu ai nasan hanya wanan kuma maganan ni tasan ba zata fara tayi minshi ba a yanzu ?
Ko ta manta da lokacin da kika kirata akan tafiyana ta hauki da fada don me zamuyi karyan abinda bamu isa yinsa ba muce sai munyi ?
Ummah ban manta da komai bafa komai yana nan min zaune a kwkwalwana kamar yanzu akayishi.
Ina bin kowa da halinsane inawa mutane abu daidai da abinda suka aikata min a baya ba zance zan sakawa kowa da sheri ba a,a ni alheri kika koyar dani na taso dashi kuma .
Amma kasan ko Alh yace ba za ai maka dole ba kaje din yadda tace in turoka zuwan naka zaisa tasan cewa na turoka din kuma kazo inyaso idan ta fito maka da zancen saika fada mata gaskiya a kai.
Shiru yayi yacigaba da dakilan wayanshi alama ya nuna ba zai tafi gun yayan nata ba ke nan a yadda ya nuna tasan abinda mahaifinshi ya fada yasa taja baki tayi shiru.
Ta sani yayan nata bata kyauta masu ba a baya sun bukaci taimakonta a lokacin da mijinta yake tashen naira amma ta nuna kamar suna son gasa da itane lokacin.
Don sunga yayanta na karatu kasan waje zaisa tace sai ta tura dan nata Aliyu itama zuwa kasan wajen ya karo ilimi wanda fafir take taimaka masu dako kwandala alhalin tasan tana dashi lokacin kowa kuma yasan hakan.
Mikewan shi a lokacin yayi daidai da fitowan hjy Asmau matar malam dake uwar daka tana jin abinda suke fada a falon.
A,a Aliyu har zaka tafi ke nan abinci fa yace mama abarshi zan samu a can gidan idan na koma zasu girka tunda sunsan kwana zanyi garin nam yau.
Yayi masu saida safe ya fice daga part din yana fita yana jin muryan mama dake faman zage zage daga inda tale zaune bai tsaya kula zancen da takeyi ba yasa kai ya fice daga gidan.
Su yusuf ya sama a waje da sauran mutanenshi bai tsaya ganin kowa ba a lokacin don yadda ya fito gidan ransa bace yau mahaifiyarsa ta tabo mashi zamcen mutanen da yafi tsana a rayuwanshi sune hjy Safiya din da yaranta da yanzu babu wani nagari bakin da tayi mai a lokacin.
Har tana fadin hauwa an fada maki shiga turai abu mai saukine ko yayan masu kudin yaya suka kare ballesu dako a cikin nageria bai gama sani ba ?
Izigili iri iri hjy safiya din ta dinga yiwa yar uwar nata da danta a lokacin har takai ga fitowa fili tana fasin hauwa nagane a dangi kaf dani kike kokarin gasa don kina ganin mijinki na rike dan canji ko to kije mijin naki mana ya tura danshi din karatu waje.
Yanzune da Allah yasawa tafiyan nashi albarka kuma take neman hada zuria da hjy hauwa din tunda su ba sa,an yinta bane a baya sai yanzu suka kai sa,anta ko ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[9/20, 9:32 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
🐊7️⃣4️⃣🐊
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15_ HAWAYEN KADA🐊
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Ke nan haka na nufin daddy Aliyu yana da mata ke nan da yake fadin family yaje kana ya duba family ashe ke nan family dinshi yake magana a kai ?
Kamar ko wace mace dake da hope ga da namijin da suke tare duk da bai taba furta min ko nuna min wani abu na soyayya kamar yadda mukan tsaya da bello lokacin idan Salis ya rakoshi wurina ayi ta shirme wai ana soyayya wanan shi yasan ciwon kanshi.
Ko a idonshi ban taba ganin wani abu daya danganci soyayya a tsakanin mu ba sai zalla kulawa da kyautatawa ne kadai a tsakanin mu.
Kawai yana ban kulawane a matsayin mu na wa yanda suka fito waje daya yana kishin addini da yaren mu shine kaunar da oga sulaiman yake nufin yana min a baya ke nan ba kauna irin ta soyayya ba ashe.
Nikan indai yadda nake gani gun kishiya irin kishin mama da inna ko irin kishin antyna da hajja yabi ko kishin anty fati da hjy tani da sauran matan dake kusa dani ina gani ana cin juna gaskiya mata mun shiga ukku.
Idan kije a ta farko matsalan ba zai barki ba saidai ya kwanta na dan lokaci sai lokacin da kika fara jin ke watace a lokacin kishiya zata sallamo maki a rayuwanki .
Hakama idan ata biyu kota ukku kika shiga gidan miji a yanzu tun a kofan gidan zakici karo da matsalan kishiya a dinga gwabzawa a tsakanin ku ke da zaman lafiya a raba hanya ke nan ?
Duk laifin hakan a ina ya samo tushe wai a ina lafin yakene wajen matan ne ko a wajem mazan ne da za ace kishin gidan mai kudi da gidan tallaka duk haukan gudane duk dai akan mijine kishin ?
Da zaisa yar uwa a kullun fata take wani abin sheri kona fade ya samu abokiyar zamanta ta samu abin darawa tana yaddawa a cikin al,umma game da kishiya.
Meyasa ba zamu gane cewa maza suna hakan bane wani