Showing 189001 words to 192000 words out of 395027 words
Chapter 64 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
da dan dumin sai lokacin da uwarshi ta karbeshi zuwa daurayeshi din na samu na mike nashiga daki na canza kayan jikina tare da wanka.
Bansan yaushe rabona da ko kofan dakin tabama don nakiyayyeta gaba daya saboda na fahinci ba mace bace dake son a zauna lafiya ba.
Sallama nayi nashiga dakin tayi mai wankan tana bashi nono nashigo ina sam a gasheka namiji na fada a kasan zuciyana sam ba za a hada wanan kazamar matar da antyna ba ko kusa anty tayi mata zara son wallahi hajja yabi kazamace ta gasken gaske.
Nayi mamaki sosai yadda Uncle Paaapa har yake iya shiga dakin harya kwana a cikinsa ya tashi don wani tsami da bashine zai tarbeka idan kasa kai a dakin.
Ya jikin nashi na fada na dan duka ina taba jikin yaron ta dago tana fadin da sauki maryam nagode haba na fada na dan kurawa yaron ido har lokacin yana jin jiki don sai kuka yake nonon ma bai iya kamawa a bakinshi lokacin .
Na nisa lokaci guda tare da fadin Allah ya sauwaka na juya zan tafi naji tace dani maryam nagode kinji kiyi hakkuri da abinda ya faru a baya don Allah bacin raine ya sa hakan .
Dan murmushin yake na dan saki ba tare da cewa komai ba najuya kawai nafice daga dakin ina mamakin karfim halin maza a lokacin.
A yanayin dana ganta taban tausayi sosai naga dai da tana jin dadin mijin data kirashi kodon halin da yaron nan yake ciki a lokacin saidai nasan hakan da suke ciki bai rasa nasaba da tsantsamin da akayi a gidan a dan kwanakin daya shude.
Wanda har lokacin nan ba wani shiru duk tsakaninsu a gidan in banda nida antyna da muke yadda muken kamar kullum.
Dakin antyna na nufa na sameta kwance tana waya Amira na gefenta tana rubutu nashigo na zauna inawa Amira din tambaya kan rubutun ta juyo tana fadin .
Kinga min yar iskan matar nan ashe tasan muna da rana mu zata daure mu rike dan ya mutu a hannun mu ace mu muka kasheshi kuma ?
Hakane fa anty zata iya fadin hakan don ina tsoron wanan matar ina ganinta kamar step mother dina idan tayi abu sai ta tuna min da mama a lokacin da nake gida.
Rayuwansu shigen dayane don rayuwa sukeyi na nuna kai baka isa garesu ba wanan ne ranan da har muka zauna mukai magana akan yabi din da halaiyanta.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[9/3, 9:51 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
🐊5️⃣9️⃣🐊
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15_ HAWAYEN KADA🐊
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Duk abinda yakeyi hankalinsa na kan zancen mahaifanshi ba abindake ranshi a yanzu sai zancen lafiyan mahaifiyarsu.
In ya fahinci zancen hjy tana nufun cikine na haihuwa Allah ya kawowa mahaifiyarsu a yanzu haka sai tausayin uwar ya dan kamashi lokaci guda yana tambayan kanshi dama haka ake cikin a wahala ?
Duba ga yadda yaga ummah din ta zube masa a ido raman da tayi yayi yawa ga ta ba alaman tana cikin walwala don koda ciwon abindake damunta akwai rashin sukuni a tare da ita kuma ?
Yusuf muje wajen malam ina ganin yau din nan zan koma da sauri yusuf din ya juyo yana fadin yau kuma mam Aley na zata ai zaka dan kwana biyune har na tura mutane su gyarama gidancan da kake sauka.
No zan koma dama nazo naga yanayin jikin na ummah ne kuma naga da sauki kaga tunda ba sai anje asibiti ba No need in tsaya kuma.
Beside nabar aiki a can din ya kamata in koma don kada aikin ya dakata muje kawai inga Abba kasuwa daga can in leka malam ka kaini airport ko jirgin Abuja na samu zan shiga don nayi sammakon shiga lagos a gobe din.
Hakan yusuf yayi ya fara kaishi wajen mahaifinshi da yasha mamakon zuwanshi tunda koda safe sunyi waya ai amma baice zai shigo kano ba.
Malam Ali sai gaka kuma ka taso bayan na maka bayanin jikin nata da sauki lalurace kawai irin na mata Allah ya kawo mata a wanan lokacin kasan kuma ai an dan wahala da hakan tunda tajima batayi ba.
Wallahi sai hjy mamace ma take sanar min ga abinda ke nan ai nina dauka wani ciwone na daban yake damunta ai so yanzu zan juya Abba in koma ko da Abujane sai gobe in shiga lagos din da safe.
Nasan ummah ba zatayi min bayanin me takeso ba Abba amma din Allah a dinga bata kulawan daya dace don ta dan samu ta samu sukuni.
To kasan halin uwar taku ai malam Ali ita hauwa har yanzu abu takeyi kamar yariya abin nan Allah ya nufa a wanan lokacin za a sameshi.
Amma ita sai zancen wai me za a fada kuma nasan ba komai takewa hakan ba sai don saboda hjy da irin haukanta.
Abba indai da damuwa ummah ta koma wancan gidan nawa na Nasarawa ita da yaran nan in haka zai yuyu ga yusuf nan a bude gidan a saka masu duk wani abinda zasu bukata acan din ma ko zata samu natsuwa da hakan ?
Aliyu karka manta gidanane hauwa kuma matatace nasan saboda zancen Naito kake wanan magana to ka barni da ita kawai nina san maganin abin idan ta matsa nasan yadda zanyi da matsalanta a yanzu.
Abba a daiyi hakkuri don Allah ba wai don haka bane dama ina da planning din hakan a raina don a zauna lafiya .
Aliyu ke nan wani abu kake tsoro yanzu zai samu mahaifiyarku wanda bai sameta a baya ba sai yanzu kaima fa a nan tare da kowa aka haifeka.
Don haka gidanane iyalinane nine zan juya kowa bisa ra,ayin kaina yadda naga dama kaida fatanka damu dakai duka shine Allah ya sauki ummah naku lafiya.
Amin Abba ni zan koma dama nazo na gaidakai muyi sallama daga nan in naje na gaidasu malam airport zan tafi ko jirgin Abuja na samu yau zan tafi.
Daga hakan ya sa kai suka bar wajen Abba din shida yusuf ko gidansu malam a gurguje yaje suka gaisa don jirgin da aka samu na yamma da zai tashi zuwa lagos din.
Sallama tayi dakin ta dago kai tana mamaki a kasan zuciyarta matar da har haihuwa tayi amma a kofa ta tsaya tayi mata barka ta juya ta tafi itace yau har dakin ta kado kafanta.
Lafiya dai ko ta fada don tasan ba alherine zai shigo da ita ba tunda yasha samunta ta dake kamar bataji ba taki shigowa part din .
Lafiya mama Imamu magana nazo dashi don Allah wajenki to ina jinki ai ta fada a nata bangaren takai zaune bakin kujera ta soma fadin .
Watau Fati zancen salma ne don Allah kinga dai aiba za a biyewa yarinyar nan ace ba zata koma koma ba amma Alh yaki saurena balle muyi maganan arziki dashi.
Humm ikon Allah ni kina ganin zai saurareni ke bai saurareki ba kinsan ance maza sun fimu hangen nisa wata kila akwai abinda ya hangone a komawan nata.
Bayan haka kuma naga dai mutanen nan banda uwarshi data kawo yaron nan akaki karba tun ranan ba wanda ya sake tako kafanshi gidan nan.
Hjy ya kamata ki duba wanan abin kema idan su suna dansu muma nan muna son tamu yar ai don haka ya kama tun yanzu a nemawa yarinyar nan girma da mutunci hjy.
Bada tafito a dauketa a mayar masu ba tun basu biyo ba kinga hakan dole zasuga ai bamu iya daukan matakine a kansu.
Fati baku fahintar abinda nake duba ni yarinyar nan da suka fara samu nake tausayawa gara takoma ta nema mashi abokin shawara yafi koba haka iyayyen mu ke fada ba a da ?
To gaskiyane kuma ta koma din don yar kada ta taso daban a cikin yan uwa tunda ba mutuncine ga dan iska ba ka kama yarinya da duka ga ciki kamar baka san inda ta fito ba ?
Kunyace ya hanashi zuwa ai yasan Alh yana hake dashi yasa bai zo ba Allah ya gyara idan ya dawo zan gwada yi mashi magana ko za a dace insha Allahu.
Allah yasa a dace zamanta haka a gida yana daga min hankali wallahi Fati auren nan kowa hakkuri yakeyi fa yanzu dashi .
Allah ya kyauta insha Allahu zata koma din haka dai yafi gaskiya nagode tasa kai ta fita saida ta tabbatar da fitanta taja tsuki tana fadin sakarai har yanzu bata aiki da hankalinta.
Yaro yayiwa yarinya dukan mutuwa sanan har kike sha,wan komawatan gidanshi don naci da kwadayin son ace yarta na gidan wadata.
Jimin mata watau ita tasan nata shine ta lababo zuwa wajena don tayi amfani dani idan gaskiyane ita taje mana tayiwa mijin nata magana ai tare suka haifi yarsu.
Ta mike ta dauko raggab zani tana goge inda hjy Tani din ta zauna don rashin yarda da imanin ta don ba Allah ne a zuciyarta ba yanzu haka kila taje wajen malamintane yace saita biyo ta gareni a samu saukin abin Alh ya yarda ?
Cikin ikon Allah shi da kanshi maigidan ya fitowa fatin da zancen yariyar taji dadin hakan don haka tayi amfani da daman data samu take fadin Alh naga ayi hakkuri kawai ta koma dakinta ta haife masa cikinshi gidanshi.
Dole dai idan ka nemeshi yazo kayi nai kashedin dukan da yake jibganta kamar dabba ya daina hakan a kanta saika mayar mai da matarshi.
Koda hjy tani taji cewa Alh ya bugawa Bello waya yana nemanshi sai ta dauka maganan da tayiwa anty Fatine yasa ya sauko take zage zage a dakinta tana fadin.
Dama ai nasan haka zai faru tunda rabin ransa ta kula da maganan ta saka baki a cikin zancen ai yanzu zaice yana neman bello din a sulhunta .
Barsu nasan hanyar da zan fito masu ai in samu dai salma din ta koma a yanzu shine kawai muradina a yanzu.
Mamace data dawo take fadawa inna wai ashe salma zata koma gidan mijintane ance an shirya da watace akaiwa haka cewa zatayi ai kwadayi zai sa a mayar da ita.q
Yaya idan Allah bai kare abu ba ba mahalukin daya isa yakai iyakarsa sai Allah aurene fa bakaiwa dan kowa fatan hakan ya sameshi sai dole.
Yanzu ni kika nufin ina murna da fitowan tane dama koko ni bansan zafin haihuwan diya mace ba kike nufi tunda nawa basu iya kutsawa suna yaki halal yaki haram suna kawo min ba ?
Ikon Allah wata sabuwa ke nan kuma yaya zancen nan kece kika zo dashi gidan nan na baki amsa daidai da abinda kika fada sai hakan kuma ya zamo fitina har kina batun yi min gori.
Yaki halak ko yaka haram ai kowa zai samu a yanzu karba zaiyi don garama wace ke aikowa dashi gida ana gani da wace kullum fitan akeyi ba wani cigaban rayuwa.
Mai kashi a duwawu ai baiwa mai zawo nunen hanya kin haifa na haifa banga abin gori ba a yanzu Allah kuma sheda kan abinda kowa keyi ai ?
Eeh lalai Ai kina jin kanki ke watace a yanzu badai dan wanan tsiyan da yarki ta turo maki waye bai san tsiyan da take can tana shukawa ba garin mutane ?
Kamar yadda aka san abinda yarki ke fita yi ba ranan dai inna ta rufe ido ta cusawa mama irin maganan da abaya bata iya fada mata saboda nauyi da kunya .
Duk abinda suke fada tas saudat tayi reconding ta turo min dashi a waya ido na lumshe daga inda nake kwance din na lumshe idona ina majin kuna da zafin irin kalamin da mama ke yawan jefa min tun ina yar kankanuwata har zuwa yanzu din.
A cikin bacin rai nayi weekend dina washegarin monday na nufi school inda na samu Ozil yana min bayanin sunji dadin mutanen don har anyi sa,a kayansu zai tashi a gobe zuwa arewa.
Nima din ai naji dadin hakan dubu dari biyar na samu a zama guda daga wajensu gana su Ozil din hakan yasa ido rufe nace muje kasuwa washe gari nayo abinda ban tashi yi ba a lokacin .
Gara inwa iyayyena alheri tunda ban tsira ga mama ba kona aika ko ban aika ba cewa zatayi dani abindata turoni kudu yi shinakeyi din ai gara in aika din ayi mai gaba daya wanan karon.
A wanan darenne kuma ina kwance daki Paapa yasa min kira don har na soma barci sai gashi ya kirani nafito ina gaidashi ya miko min takarda yana fadin .
Takardan aikinkine ya fito sun daukeki aiki a wajensu kamar yadda yai min alkawarin hakan na kuma kira malam can kano na fada mai komai yasa albarka.
Amma kuma ya rokeni da in fada maki don Allah ki kama mutuncinki dana addinin ki a duk inda kika tsunci kanki ?
Kasa nayi da kaina ina maijin wani iri a kasan zuciyana lokacin yace shine nima nan zan fada maki maryam bar ganin na barki kamar bansan me nakeyi ba ?
Na sani maryam duk wani motsi naki wallahi a idona da kunnuwata yake a garin nan ni dan sandane kin sani nasan mutane har wanda baki tsamanin na sani ba a cikin garin nan.
Aita sani dadina da maryam ko saurayi ban taba jin tayi a rayuwanta ba No ki kyaleni in fada mata wanan ba zancen ki bane zancen nida itane tsakanjn mune wanan ya kwabe antyna data saka muna baki a lokacin.
Fitowan hajja yabi daga dakinta ta nufo ta zauna cikin rashin fahintar maike faruwa don ganina da tayi a zaune kasa tasan idan nayi irin zaman nan akwai magana mai muhinmanci da nakeyi da Paapa a lokacin.
Ta dan dubeshi ta duboni a cikin rashin fahinta sai danta daya kyala ido ya ganni yake zillon zuwa wurina daga hannunta ko anty ya gani haka zai dinga mika hannu ta daukeshi itako ko duban yaron batayi.
Tun lokacin danaso lurar da ita hakan ba daidai bane shi yaro ba abinda ya shigar dashi cikin zancen kishinsu ta dakatar dani da yi min kakkausar worning akan hakan ban kara gigin zancen yaron da ita ba.
Wai ashe cewan da hajja yabi tayi tana bakin ciki da yaron da ita ko kashesu tana iya yi idan ta samu daman hakan shine ta rike a zuciyarta daga uwar har dan bata kula zancensu kuma ana zaune a waje daya.
Jeki ya fada bayan hajja yabi din tace kaga anty ko anty tana magana da daddy ne ka zauna nan na dan juya ina fadin Al,amin how far now ?
Shine Paapa din yace dani jeki shike nan don Allah ki kula maryam Allah yabada sa,a na amsa da amin ina mikewa tsaye daga gurin na dan lakaci kumatun yaron nan uban ke fadin yanzu haka tsirara ta barshi a daukeshi ya batawa mutum jiki da fitsari.
Hakan na nufin shima Paapa ashe yasan kazantar matar nashi ke nan maganace kawai bayayi yana da wuya ka daukivyaron ka sameshi da Permppers a jikinshi is hard gaskiya kome yasa take hakan oho ?
Dakina koma na barsu a falo din zaune don antyna ko kara kallon mu batayi ba a wajen nasan tayi fushine yadda Paapa din ya katseta a kaina lokacin.
Wayana na samu yana ringing na dauka ina dubawa number ce ba suna na dai daure na daga muryan