Showing 378001 words to 381000 words out of 395027 words

Chapter 127 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

Hakan data saka a rai shine ya dawo yake damunta har ya haifar mata da hakan irin yadda tayi da zamu wuce umura nasan wanan damuwanne ya haifar mata da hakan a karshe.

Duniyan nan meye a cikinta bada ta shagal da bawa lokacin fa dan kankanine ga bawa idan ya gane ya gyara tun irin haka baikai ga faruwa dashi ba.

Abindana fada ke nan ina kallonshi haba aishiyasa nake son da mun koma lagos ayi zancen tarewan ki din nan don yanzu gaskiya ban iya yarda kina nisa haka dani kuma ?

Sabodame daddy kema kin sani ai tunda kece kika koya min hakan a yanzu kaina kawar gefe daya ina murmushi don nagane me yake nufi amma na dake bangane ba ina fadin.

Nikan ban koyama komai ba wallahi bayan nice ake kokarin lalatawa inna ni bayan dadewan da tayi tana min nasiha akan kada in yarda ko in soma wani namiji ya taba min ko hannu balle sai kuma nayi shiru ?

Balle me ya fada yana kallona ya juyo da kyau yana fadin yanzu me nayi maki fisabillah baki tausayina ke baki fahincima wani abu daga gareni ba ke nan ko ?

Me zan fahinta nikan na fada ina kara kawar da kai don maganan tana da nauyi ga mai kunya donshi nake son ma yabar zancen gaba daya.

Banda lafiya nake jin kaina ko kuma ban kosa bane har yanzu ban sani ba ina son zuwa wajen malam donshi kadai nake iya fadawa wanan maganan a yanzu .

Sam ban fahinci me yake nufi a zancen shi ba ban ma kawo wai rashin lafiyan wani abu bane tunda naga yadda yakeyi a can zaman mu saida nake tambaya baka da lafiya me maka ciwo kuma yanzun ?

Murmushi yayi yana fadin ba inda ke min ciwo matsalan dai ina jina kamar ba namiji nake bane a yanzu shi nake so inje inwa malam bayani.

Kafin nace zanyi magana naga ya dauki kwanan lungun gidan malam din ga namu titin ya sake ya shiga nasu malam din da aka gyara yanzu.

Da sauri na kalloshi ina fadin ba gida zamu bane yace zan kaiki ki gaidasu malam ko baki zuwane nasan yanzu duk suna nan gida wajen karatu gaba dayansu a yanzu.

Kamar yadda ya fada haka dinne don kofan gidan yana cike ga motoci da masusuka a jiye gasu can sunyi da,ira suna wazifa gaba dayansu.

Ajiyan zuciya na sauke don tuno da zancen mama kan wanan akidan da take fadin sun cika waje ko kano son fita ba dama mama ke nan ibada ga baki zuciya babu imani.

Can gaban gidan ya tsayar da mota ni dai bansan ta ina yusuf ya fito ba sai ganinshi nayi yana bude min motan tare da fadin ashe tare kuke da amarya.

Tazo gaidasu malam ne kasan malam zai iya cewa zasuje gaida ita da dawowa shiyasa na kawota kafin ta wuce nayi mamakin jin wai malam zai iya zuwa gaidani ni,awa da mutum kamar malam zaizo dubana.

Ka kaita ciki wurinsu umma bari naje na gaidasu can ya fada Yusuf din ya dan dubeni sai lokacin nake cewa dashi ina wuni ya gajiyan hanya ?

Lafiya hjy maryam gajiya kan sai ku mu ai mun watsake da tafiya ko mun fara hada hada nayi murmushi yace muje ciki din yayi gaba nabishi a baya zuwa cikin gidan nasu.

Tun ina karama rabona da shiga gidan lokacin mama na aikena karbo nika ko inkai masu banda haka banda wani halakan shiga gidan don banda kawa ko wata da ake hurda gidan mu dasu.

Yaran gidan nasan ance iyakarsu primary a da da sun gama aji shida ake aurar dasu ga mazajen da iyayyensu suka zaba masu don basu fitar da maza aure da kansu donshi basu girma a waje balle su famfare ido irin mu.

Don gaskiya nasan da suna barinsu su girma a waje sosai zuwa yanzu da ansamu wace tayi masu gardama da irin wanan akidar tasu na hadin aure din.

Gaban gida yana yadda nasanshi a baya amma daga cikin gidan naga sauyi sosai a cikinshi don an canza fasalin ginan gidan an kuma kara wasu sabi daga wani bangare.

A inda nasan matan malam suna zaune yanzun ba nan suke ba don angusa dasu can gaban gidan suna ta baya sarakaine zaune a nasu ginan da aka gyara yanzu din sai aka bude kofa can ta baya da wani babban falo a bangaren nasan inda yake ganawa da bakin sirinshine.

Dakin ummah hassana maman su yusuf muka shiga nan suke ta shigowa muna gaisawa dasu saidai tace ita bata shedani ba waima bata taba ganina ba a cewanta.

Nayi murmushi kafin nace umma mairoce fa mai kawo maku nika mama tace idan baku ban kudi ba kada in dawo lokacin ace in zauna in jira malam har shigo.

Salati ta saka tana dafani tace ke anyi haka yar kece dama kece wai ban ganeki ba duk mamaki sukeyi yace hassana baka da hasana fara ko ?

Don haka nakance idan an aikoni don ko malam ya tambaya waya bada nika sai ince nikan hassana bakace ko na hassana fara .

Na dan dukar da kai ina murmushi cikin jikina don tunawa da abubuwa da dama tace ai hassana fara ta rasu da jimawa itace abokiyar fadan nata ai.

Innalillahi na ambata ina fadin ta kare ashe suka amsa a yanayi na bacon rai suna fadin ta rasu wajen haihuwa da ita da dan ba a tsira da kowa ba.

Allah ya jikanta yai mata rahama yasa aljanna makomace a gareta da al,umman musulmi baki daya aka amsa da amin muryan mijin ke fadin ashe sarakuwarce tazo gaida mu.

Dogone mai karfi zance daga Yusuf danshi harshi Aliyun shi suka kwaso ga jiki duk da dai mahaifin suma ba baya ba haka mahaifiyarshima tana da tsayi da jiki itama amma bata kaisu ba dai.

Ina zaune a kasa ya shigo har dakin umma hassana din shida Aliyun muka gaisa yayi min addu,an Allah ya karba umuran mu na amsa da amin.

Malam baka shedata bako ummah hassana ta tambayeshi yace a,a matar gadangane mana bakiji nayi mata gaisuwan tafiyansu ba ?

A,a mai nikan muce fa dake fadin hassana baka da hassana fara idan an turota karban kudi ko tace ba zata tafi ba sai ka shigo kada mama ta bugeta.

Yayi shiru kamar yana tunane kafin ya dan kalloni yana fadin a,a,a anyi haka kuwa itace nan dama ashe itama din yar gidace ?

Ikon Allah dama itace ta koma ikko da zama ashe lalai ko anyi haka ta kara fadin ai yanzu muke fada mata hassana fara ta rasu ashe bata sani ba tun kan ta rasu ta tafiyan.

Hassana kan ta rigamu nayi mai ta,aziyan ta tare da fatan gafaran ubangiji a kanta ya amsa da amin yana fadin ya gode.

Kafin ya dora da fadin yace gobe zaku wuce zuwa ikko ko kina da jerabawa da zaki zana?

A kunyace na amsa da eeh malam to ubangiji Allah ya bada sa,a da rabo na alheri nace amin yana soma magana naga su umma din sun mike suna fita daga dakin guda guda.

Mazan jiya ke nan iyayyen mu da kakanin mu dako tari sukayi ko tafiya ya isa yasa iyali natsuwa lokaci guda.

Ba kamar yanzu da sai anga uba za a soma shakiyanci ba shiko uban ya kawar da kai kamar bai damu ba baima san wainar da ake toyawaba a gidan nashi.

Sai bayan sun gama fitane ya soma fadin to nasihana gareku gudane dukkanku yayanane kai dan kanwata ke kuma diyar makwancina kinga ba inda baku zamo yaya a garemu ba a cikinku garemu ba bare ke nan ?

Abu na farko shine rike amana don in ba amana tafiya bai tabayi a tare sai anta samu tangarda a cikin zama .

Don haka dukkan ku amanan junana a gareku zomo zauna zo mu saba akace to a saka hakkuri banda rike juna sirin mijinki ke mace ki barwa cikinki a cikin gidanki kuma dakinki ku kashe ku bizzine ba tare da wani yaji tsakaninku ba koda iyayyenkune kuwa.

Kaine babba Aliyu ka rike yarinyar nan cikin amana da gaskiya kada inji ko kadan wani hali ya fito a gareka wanda ban sanka dashi ba akan yarinyar nan kai kaji ka gani Allah kuma yasa ita din daice abokiyar rayuwan naka don haka kayi hakkuri da abinka in an tafi a hakan da alama zaman zai dore don akwai alaman tarbiya a gareta sosai gata kamar renon mutanen da bana yanzu ba ni dai na yaba don Allah kada ki canza halinki daga baya.

Na amsa da insha Allahu baba don ban kirashi da wai malam ba a lokacin tunda gashi zaune a gabana kuma yana yabonane ai ?

Aliyu kadai ji don Allah banson jin matsalan komai a zaman ku ka rike yarinyar har abada amana ya amsa da insha Allahu malam.

Kace akwai bayani ko sai wani lokaci ya amsa da a,a malam domshine ma na daukota zuwa nan don tasan halin da ake ciki don wallahi malam jina nakeyi kamar mara lafiya dai don ba zan iya sauke mata hakkin taba a kaina.

Dan shiru dakin yayi kafin malam din yana kada kai ya soma fadin dolene dama hakan aikai jinin malam babbane ba zaka taba aikata wani abu da wata mace ba sai ranan data shiga gidan ka Aliyu .

A ranan da matarka ta tare ranan zakaji kafi ko wani namijin duniyan nan lafiya don shine bamu da tashin hankali ko fargaba a duk inda zaku tafi a duniyan nan don addu,an dake tare daku din.

Ba zai bari ku taba aikata wani abin asha,aba a rayuwan ku ku kwantar da hankalinku lafiyanka kalau insha Allahu.

Kaina na kasa sade tun lokacin dana fahinci bayanin da yakewa kawunshi din na kasa dago kaina don kunya ga kuma amsan daya bashi na cewa aiko mahaifiyarka da nayi mata wanan bayanin naga ta kwatar da hankalinta kan zargin da hanne ke maka da wanan yarinyar na zaman banza .

Donni nasan da dai idan numune tun haihuwanshi ake tofa mai wanan addu,an na kariya daga alfasha nako san da yardan Allah addu,an yana karbuwa.

Ga yaran almajiranmu ma dake tare damu muna masu kuma yana karbuwa idan kaka baiyi amfani ba an karya dokanshine.

Tafiyan ku zaiti kyau matuka don dukkanku taurarun ku suna haskawa wanan yasa nayi gagawan daura auren ku a lokacin kafin hanne ta kawo muna akasin hakan don zata iya abinda na sanine.

Don kuwa kafin ku tafi saudiya din nan saida muka hau sama da ita sosai don ta kafe da lalai sai an daura aurenka da yar wajenta.

Ya dago kai ya dubi malam din cikin mamaki yace kana mamakine hannece fa wanan kasan karamin aikintane ai .

Tazo nan tana muna hauka suka hadu da hamza yayi mata tas tun ranan ban kara jin duriyanta ba kuma nako san ba wai ta hakkura bane.

Wancan zancen kuma shi hamza din dai har walau yau shine ya sameta yayi mata kashedi akan ita mai dakin naka ta nuna ta isane tayi.

Ni lamarin hanne yana daure min kai ko ta manta da cewa itama a irin gidan nan aka aurota ne meke garemu lokacin da malam mahaufinmu yaba da sadakanta ga mijinta ?

Shima baida komai a lokacin wanan mai kudin makwabcinsu shine dalilin fita dashi waje data dawo tanawa mutane iya shegen nan ita da mijin nata halinsu daya wajen rainawa tallaka wayau ai.

Don kwanaki makwabcinsu ya kawo min karanshi nan kan kwatan unguwa da yasa aka like masu inda ruwa ke bi nakirashi don yazo amma ya nuna min rashin mutunci.

Wayana da yayi karane na daga ina duba nakashe saudace ta kirani ta sheda min ga salma tazo gaisheni sai na kashe ban daga ba ta sake kirana yace daga mana ba saudat bace ?

Na daga ina fadin ke gani tafe muna cikin unguwar nan gidan baba malam take fadin ga anty salma nan sunzo gaidake kice su jirani ina zuwa.

Malam din ya duboshi yace da alaman ana dakonta a gida ko kuje goben zaku tafi ke nan da yamman yace eeh indai an samu yadda ake so din zamu tafi din ga goben insha Allahu.

Saida muka shiga motane yake tambayana waye yazo nace Salmace kawata da muka taso tare na aika mata da tsarabane nasan shine tazo godiya.

Matar Bello nake nufi kila ka ganeta wace ko yaushe muke tare da ita shiru yayi yana tuki saida yasha kwana yace kice min wace tayi maki snatching dai ni kuma ta taimakeni da yanzu kila ragowan dan iskan nan zan samu ai tunda akwai aure a tsakanin mu.

Dip na dauke tare da kallonshi cikin mamaki ba tare da nace komai ba har ya tsaya da mota a kofar gidan mu ban iya cewa dashi komai ba a lokacin .

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[11/6, 9:33 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊1️⃣0️⃣0️⃣🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Kamar yadda yace zaiwa Abba magana ya samu Abba din akan zancen dawo da hjy gida don a nema mata magani irin na gargajiya.

Ko Allah zaisa hannu a lamarin Abba din yaso yaja zancen da tsauri don bayan ya gama sauraren dan nashi.

Murmushi ys sake yana fadin Allah sarki yaro man kaza kai Aliyu karka fara ka tsoma kanka a cikin zancen nan don bai shafeka ba.

Nasan yaran nan marasa tunane suka turoka kazo kayi min magana ko tunda sunyi min nace ban amince ba.

Zancen banza sukeyi a dawo da ita gida su tsinana mata me idan ta dawo din sai mu barta cikin masu lafiya tazo tayiwa mutane illa wata rana komai ?

A,a Abba don Allah kayi hakkuri bisa wanan hukuncin ba dadi yau ace hjy tana dawanau an tsareta a can kowa yaji haka yasan abinda yakaita dawanau din.

Wayaja hakan ya faru ba ita bace taje wajen bakin shige shigenta ta daukowa kanta bala,i da take son addaban mutane a yanzu ?

A,a Abba wanan dama yana cikin kaddaran ta yau Allah ya tsare ya kare har haka ya samu umman mu ba zan yarda kowaye yakai min ita dawanau ya aje ba tunda ba tuburan tayi tana duka ba ?

Do Allah Abba kayi hakkuri su dawo gida azo a dinga na malamai akumayi mata wanan alluran natsuwa da likita yace zai mata a samu sassauci ga matsalan.

Kai Aliyu baka fa nan tare damu ranan data kubce tazo tayiwa iyalina wani abu fa tunda ba kaunarsu takeyi ba komai zata iya aikatawa da sunan hauka.

Zata iya tunda lamari ya hada da rashin hankali amma zan san yadda nayi na ko a canza tsarin ginan wajenta ko kuma a dauketa daga unguwar nan a sauya waje da zata zauna ita da diyanta in ba damuwa naga abar masu nan gidansu zauna harsu habib din Abba sai ku koma wacan gidan da nake sauka yanzu ciki tunda ba a nan zamu zauna ba mu.

Shiru Alh din yayi kafin yace sai nayi shawara da mahaifiyar ka akan hakan mun duba idan hakan mai yuyuwace a garemu sai a yi din .

Su dawo din da ita amma duk ranan da suka sake ta fito daga wajenta zuwa cikin gidana a ranan zan mayar da ita can garinsu.

Godiya ya somawa Abban tare da tunanen ashe soyayya na iya zama kiyayya haka ya tuna a baya yadda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login