Showing 231001 words to 234000 words out of 395027 words
Chapter 78 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
yabice da girki a ranan hakan yasa na kwanta don in huta duk daba wani aiki bane mai wahala amma sai jikin mutum duk ya nike a waje daya.
Tunanen abinda zan bukata don shiga school nakeyi na tabbatar da dan kudin wajena zai isheni maneji har in samu in kwantalawa uwata da yan uwana tunda yanzu ba wani kashi kudi a kaina kamar baya da komai ni zan sayawa kaina na rayuwa.
Paapa yana min gaskiya don koda shiya haifeni ya tsaya haka nan irin abinda yakewa rayuwana ba tare da nuna gajiya da hakan a kaina ba.
Rai da kwadayi idan nace ban damu da rashin ban kudi ga wanan aikin ba nayi karya don kuwa da buga bugana nakeyi da zuwa yanzu na tabbatar da na dan tara kudin da suka fi haka a account dina.
Amma ba zancen kudi ba ko dan hasafi amma kuma sai Allah ya taimaka hakan bai wani damuwana ba sam don ko wana alherin dana samu a wajen bawan Allah nan dan zamana dasu da kudin zasu bani ba zan iya sayan wanan kayan ba haka.
Ko a hakan kawai nasha godiya wanan ya ban kwarin gwiwan dana nemi matsalaha dashi tunda na hango yarda a tare da bawan Allah nan.
A haka bayan nayi sallolina na kwanta can barci ya soma daukatane naji muryan Amira a kaina tana fada min wai uncle yana kirana a falo.
Ban fito ba saida na duba time goma da rabi saura na dare tare muka fito da Amira din zuwa falon na hangosu a zaune tun ban karaso ba a raina ina anyana me kuma ke faruwa haka da wanan daren ?
Ina gaidashi da dawowa yake fadin meke damunki ance tun dawowan ki kina daki kwance yau senior yace yayi neman layinki yaki shiga kuma ?
Wayarce na kashe tun a office na manta in kunna dana dawo gida ya kirani ai shine na dawo nake tambayanki akace kina daki kwance tun dazun ?
Lafiyata kalau nagajine na dan kwanta so ki nemishi zuwa safe don bansan neman da yake maki ba din na yunkura zan tashi antyna ke tambayana abinci fa ?
Na dan juyo gareta ina bata fuska nace banjin ci a yanzu anty koma zataci ai ban girka da ita ba tunda na fahinci sai ranan girkiki yanzu take shiga kitchen a gidan nan ?
Ni kuma hajja yabi na fada cikin mamaki ina kallonta haka kike min kada ki dauka ban sani bane nasan komai ni za a hadawa kai don kina taya ,,,,,,,,
Ke ke dagata don Allah ke meyasa kika faye tsegumine wai don Allah ina yanzu kinji abinda yarinyar nan ta fada a wajen nan ?
Ba zan lamunci cin fuska ga yarinyar nan ba akanshine kikaga na mayar da mummy gidanta don bai yiyuwa yarinya ta dinga kwana falo a cikin sauro haka ?
Idan tayi ko batayi ba banga abin magana ba a nan tunda kina da lafiyan yi ko zaki hada kanki da Sariyace ba tare kikazo gidan nan kika samesu a nan ba ?
Ai kuwa naga alaman a tare na samesu don shine kuma nima idan na dafa ba zan bata ba din matukar tace haka zatayi min a gidan nan kuwa.
Ganin yadda Paapa ya karbe zancen yasa na juya na nufi dakina cike da mamakin cin mutunci irin na hajja yabi din don da da ragowa naci hakan a wajen hajja yabi ko don girman da nake bata saboda Paapa din duk da antyna bata son hakan amma kuma bata hanani yin wasu abubuwan daya danganci hajja yabi din ba amma kuma wai wanan matar bata duba hakan ba gareni.
Ai ba a nuwa shege hanyan neman uba haka na kwana ina tunanen wanan matar a raina ina fadin wai mai mata suka dauki kishine a rayuwa da yakan manna masu hauka wani lokaci ?
Naci ragowa a zato gun hajja yabi amma tunda ta furta haka kuma ta makaro yanzu kan zan nuna mata lalai tare tazo ta sameni da anty nawa kuwa.
Izuwa wanan lokacin cikon hjy hauwa ya gama baiyana wanan yasa mata zaman gidan dole a cewanta nauyi da kunyan a ganeta da ciki a yanzu take ji.
Wanan yasa bata fita ko ina ko a gidan sai sa,a ko girshi zaka sameta a waje idan kayi sa,a koda yaushe tana dakinta a zaune.
Dadin abin yar aikin da Alh ya daukan mata a yanzu mata mai kirki mai mutunci ga tsabta da sanin ya kamata da zaran tazo aikinta zata sa a gaba idan ta gama kuma ta zauna su danyi hira kafin ta samu wani aikin yi tana gamawa magariba zata bar gidan sai kuma washegari.
Da farko hjy Naito da yaranta sunso su tsawalawa matar mai suna Asibi saida Alh ya kawo iyakan abin hakan ya farune ranan da hjy Naito din ta kirata wai tayi mata girki wanan da tayi na dukka gidan bai gamshe ta irin ikon nan nata da isa da take nunawa mutane dai .
Asibi tace ayi hakkuri ta dora girkin darene a lokacin idan ta kwashe saita dafa don ranan naman kan shanune take dafawa yana da wuyan nuna sai anta kulawa dashi yana daukan lokaci mai tsawo bai nuna ba a cewanta.
Zakije ki dafa min abinda nace ko sai kin jawo abinda ranki zai baci a gidan nan tsakanina dake.
Ai hjy baikai can ba nace kiyi hakkuri na sauke sai in dora maki shine kadai abinda nace ai daga gefe daya Asmau ke fadin yakai mana aikin hjy hauwa yafi na mamane ?
Baku fahinceni ba yar nan me zamu fahinta idan ma wani ya fada maki kiyiwa mama haka yayi maki karya don haka kada ki kawo muna wanan munafuncin a nan kinji.
Ni yar nan tun ina Ashibi bana munafunci balle yanzu danake a wanan shekarun ince zan tsaya munafunci a tsakanin ku kuma ai abin baiyi ba ke nan ?
Ita hjy ta fada Asmau dake nan gun hjy a lokacin itama ta fada sai hakan ya bakantawa Asibi rai ta mike ta fita.
Wai kuma tayi laifi ga hakan wanan yasa da Alh ya dawo mama ta aika a kirashi saida ya gama ko mai yaje ya shigo da sallamanshi yana fadin gani ance kina nemana ?
Wani malolon bakin ciki ta hade kafin tace dashi ai lalai dole yar aikin gida ta nemi ta rainani har in sakata aiki ta tsaya min akan ba zatayi ba saboda tana wani aikin hauwa can
Gani nace Asmau tace kina nema na gsshi ko ina fadama wanan yar aikin kaja mata kunne don ni ba sa,ar yinta bace .
Don yar aikin dama kika aika kirana yar aiki ai ba taki bace tunda ba ke na daukowa ita ba don laluran hauwa dake fama da kanta a yanzu na dauko mata yar aiki kuma bani na dauka ba danta ya saka a nemota kinga sai yayanki su daukar maki yar aikin kema fada ya kare.
Ai bansam har wani iko kuke nuna mata ba a nan su wa yan nan meye amfanin zuwan da sukeyi gidan nan kullum da har basu iya yi maki abinda kike so ?
Daga yau zan mata iyaka ta tsaya iya inda aka dauketa aiki ba a kawota gidan nan don yiwa kowa abinda yaga dama ba .
Danta ya daukar mata mai aiki yana biyo so kike ki turani kamar yadda kika saba turani a baya inje inciwa tsohuwar nan mutunci ko hauwa ko ?
Don haka nayi maki kashedi akan kayansu kinji na fada maki kamar an dasa dusa hjy tayi tana kallon Alh saida ta tabbatar dayagama magana zai fita ta soma fadin.
Dama na jima da sanin hakan a tsakanin mu anci miriyan ganga za a yada kwarenta ko yanzu ban gabanka balle yayana duk hakkuri mukeyi a gidan nan mun zama yan kallo a wajenku.
Ashe kin gane hakan masu kallon mu a da can da kika hana su Allah ya mayar yanzu abin kallo wajenki ke ma ke Naito ki barni inji da istigifar din da nakeyi ko Allah zai yafe min lefukan da kikaini dauka a baya don Allah ?
Idan ke baki dauki darasi akan rayuwa ba nina dauka tuba nake nema a yanzu wajen ubangijina Allah don naga ke baki da niyar hakan a zuciyar ki ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA[9/17, 9:28 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
🐊7️⃣1️⃣🐊
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15_ HAWAYEN KADA🐊
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Tsab na shirya a daya daga cikin kayan da Sir Aliyu ya sai min haka kawai naji in saka mana ya gani yasan nagodewa kyautanshi gareni.
Wani dark blue atamfa da akaiwa dinkin kamar zubin abaya dinkin ni kaina nayi mamakin yadda aka zauna aka hadashi haka da atamfa da yadin abaya original sai duwatsun da aka daza mai tako ina kinsan mu mata haka komai namu take da kyalkyali kamar matan indiya ko fulani No bad dinkin an tsarashi irin sai kin isa ki saka din nan dai.
Takalma da jakkan na saka sai humra na da nabi jikina dashi har zuwa hammatan riga na dangoga tare da oud mukhal asiwad har zuwa gyalen kayan da shima akayishi tankar gyalen abaya namu na mata.
Dana dubi kaina a dan mirro na saida gabana ya fadi gado na koma na zauna ina nazarin abubuwa da dama a cikin raina ganin lokaci na shigewa yasa na mike na kara gyara dakin na fito nayiwa dakin key na kada jakkata.
Sautin takalman kafana yasa yau zaki gane fitowana don yadda yake bada sauti kwas kwas irin ga mace nan zuwa din nan sabanin irin su low pass din dana saba sakawa a kafana.
Hakan yasa hjy yabi dake kitchen lekowa daga kitchen nice ta hango na nufi dakin antyna don in sallameta kodana shiga basuma tashi daga barci ba a lokacin jin motsina yasa ta bude idonta tana saukewa gareni.
Maryam har kin fito niko tashi banyi bafa a raina nace shine babban raunin ki anty sakaci da ibada amma Allah ya shirya zuciyarki a fili kuma cewa nayi ni zan fita anty .
Ina ganin daga satin nan zan dakata da zuwa wanan wajen don monday zamu koma school insha Allah amira ta dan bude ido tana min magana injin shiya hanata ban amsa na juya nace zan tafi take fadin ba kudi a hannuna maryam naso tun jiya na tambayeki ko zan samu dubu goma wajenki da akwai abinda nake sonyi dashi dama.
Ba cash a hannuna anty idan na isa office zanyi maki transfer dinsu mukayi sallama tana hamma nace nina tafi na bar dakin na fito.
Ina ganin hajja yabi hakana shareta na fice abina ban ko san Allah yayi ruwanta a lokacin ba matar nan ta takalowa kanta tsuliyar dodo gidan nan na ayyana a raina.
Ina zuwa titi na samu drop har zuwa company A A Y limeted dake Apapa mota na ajeni ina ciro kudi inba mai taxi din motocinsu suna shigowa cikin company.
Kai na kawar gefe daya tankar ban gansu ba though akwai kunya a hakan amma ni dan kunyan ai kadan naji tunda niba diyar wani done bane dama meye na abin kunya a ciki don anga ina bawa mai taxi kudi ?
Ance ubana yayi mota abaya a da niko tunda na taso ko keke bansan mahaifin mu dashi ba don haka ban fankama ko alfaharin ubana wanine ko ni yar wanine tunda nasan niba yar kowa bace sai bawan Allah Ali senior .
Na taka a hankali zuwa ciki har lokacin suna tsaye waje yana magana da ma,aikatansu kamar fada yakeyi na karaso a nan na samu wani shugaban cleaner yana mashi bayani nasan akan tsabtan wajen ne yake fada dasu lokacin.
Kai tsaye na dage kaina zuwa cikin company nayi sa,a ba wanda yace dani kala a cikinsu duk dasu oga sulaiman hankalinsu yana kan abinda sukeyi din don naga ana nune nune da hannaye a wajen.
Nashiga office na zauna ina hada na,urana aka turo kofan office din hakan yasa na dago kai oga sulaiman ne a tsaye daga kofan muka gaisa dashi yake tambayana dama a motan haya kike zuwa ne maryam ?
Mamaki tambayashi ya ban kafin in bashi amsa shi dan murde fuskan ya shigo office din shima fuska a daure yake fadin.
Ina wanan takardun na jiya kon hadasu kinyi aiki a kai na dago kai na dan dubeshi kafin nace na dai hada a waje daya aiki akansu baida wuya sir ?
Don tun jiya na duba sa nake adanawa bayanan su daidai yake da yadda sukai bayani din wanan karon kamar zai juya ya tafi sai kuma ya kara dan kallona kafin ya juya kan Sulaiman din dake tsaye yana fadin what else me kake jira a nan kuma ?
Kawai nazo mu gaisane kasan hjy ba fita takeyi ba ita ya juya da sauri ya bar office din nan ya dan kalloni yana fadin take care ban son irin hakan a nan wajen aiki ya fice ?
Ji min wanan mutumin me yake nufi da zancen nan ina ruwana dashi balle ysce hakan oga sulaiman ya kaishi kusancine dani ?
Inma hakane shiya kamata a fadawa wanan maganan ai shida na kulla yana dan zure min a yanzu abu ba abu ba zai aika a kirani a office dinsu.
Guntun tsuki naja ina kawar dakai gefe daya a fili na furta a rayuwa naki jinin zargi da sa ido ga mutum har kayiwa wanda kake zargin mumunan fahintan daba shi ba.
Aikin da naji yana magana na jawo nacigaba dayi har mai abinci ta shigo kamar kullum ta kawo min take away dina ban taba ciba don tarbiyan da nake dashi a kan kabila.
Iyakar rashin yarda ya kare ga kabilane wanda bai taba yarda koda da dan uwanshi balle bare a irin haka a take zasu salwantar da rayuwan mutum a banza.
Ko a kashe ko hauka ko ciwo da za a nemi maganin duniyam nan a wahala sunyi yakini da hakan sosai yasa na saba da zama ciki da yunwa ban damu da inci wani abin ba har na saba da hakan.
Ina tsaka da aikine ya shigo misalin karfe shadayan rana yana shigowa yake fadin taso muje ki dauko wanan system din naki ya juya na mike da sauri na hada abinda zan dauka nabi bayanshi.
A mota na samesu zaune sulaiman yana gaba zaune da driver shi kuma yana bayan motan a zaune na kararo da dan saurina sai kuma naja na tsaya don ban san inda zan shiga lokaci .
Saboda fahintar bada mota daya za a fita ba kada inzo injawa kaina jin kunya don nasan baya dama wajen zaman ogane nan oga kwata kwata ke nan Sir Aliyu Abdallah yaquba.
Karki bata muna lokaci man ya fada ta window motar da aka dan zuke mashi da sauri na zagaya dayan gefen inda yake zaune na zauna aka tayar da motan.
Kinsan yarbawa da gulman tsiya tun a nan gaban mu wajen suka soma kuskus din hakan a cikin harshensu na yarbawa suna tambayan wai waye ni din ?
Wanda suka san an kirani da nieces din shi a ranan suka basu amsa dani ai tobashiyar shi ce nazo daga arewa ina aiki a nan tare dashi .
Sea side mukaje inda jirgen ruwa ke sauka sai a wanan ranan na yarda cewa karyane mutum yace yasan ko ina a garin lagos don wani waje idan kajeshi saika zama bakauye.
Ai