Showing 306001 words to 309000 words out of 395027 words

Chapter 103 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

wani ba.

So ni banga abinda zai rudeni dashi ba gaskiya da zaisa har inyiwa kaina sakiyar daba ruwa in dakatar da karatuna daga baya kuma abin yazo yana min ciwo .

Mazan mu na hausawa daban suke da sauran maza anty a lokacin da sukace sunayinka lokacin nan zasu nunama har duniya ta nade ba zasu dubi wata mace ba a rayuwansu saike kadai amma daga kin shiga gida tafiya ya fara nisa mace ke gane tayiwa kanta sakiyar daba ruwa.

Yanzu na fahince ki sosai maryam na kuma gane me kike nufi idan kinyi hakan wallahi ba laifi bane .

Kadama kikai zanceki nisa yanzu ba gani ba ina poly ne fa muka hadu da paapa karshe na tattara karatun na tare a wajenshi lokacin ba unguwar nam yake ba can kusa da campus din poly yake zaune.

Daga karshe dai mukai aure infada maki maryam wanan zaman da mukayine dashi hjynsu take kyamar auren mu dashi har zuwa yanzu.

Da ace na tsaya nayi karatuna aida ba haka ba da yanzu ina nan ina dan wani abin ban damu da duk abinda zaiyi ba balle dangin miji.

Shi ilimi yana son dagewa sosai kamar yadda kika dage din nan don ko yayane zai maka amfani a duniyan nan koba aiki kuwa ?

Don haka kinyi dabara maryam gara dai ya bari har ki karasa karatun naki idan Allah ya nufa mijinkine kwana nawa ya rage maki ki karasa ina daga wanan time din shike nan kun karasa karatun ke nam ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA[10/19, 9:00 AM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA[10/12, 10:00 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊9️⃣1️⃣🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Kwanan motan biyu a kofan gidan mu kafe a rufe anyi gulma har angaji a cikin shiya muna gidanmu bamu sani ba don suna son ganin motar ko ya take amma tana rufe yadda ya turo aka rufeta a wajen.

Sai ranan monday da zan fita na shirya tsab bayan nagama rokon Allah a duk kwanakin ina neman kariyan ubangijina Allah daga ko wani irin kaidi na abin ki da dan adam ke tsoron ya cinmasa.

Na fito don a ranan zan koma school bayan sati dayan dana kara sama da abinda aka bamu a school din lokacin .

Abayace baka jikina sai takalma half cover namu na mata mai kyau mai dan tsini tare da jakarshi kamshi dake tashi a jikina ya kara min ma,ana sosai na fito na nufi dakin anty tana kwance tana barcinta Amira keta faman buruntu a dakin nasu saboda sun shiga hutu suma a lokacin.

Kudi na bata ta shiga gidan mama Ayyo ta samu abinda zata karya dashi don ban tsaya girki ba a ranan kada in makara tare muka fito da ita bayan nayiwa dakina key saida naga ta shiga gidan na juya zuwa wurin motan bakina dauke da addua na dafa na karanto Tawakhaltu har karshe da sauran addu,an daya dace in karanta na kware motan tare da budeta na dan zauna da bissimillah na bude bayan motan na jefa rigan nata a ciki.

Wanan duk na iya duk da ko taya ban mallaka ba amma saboda ganin hakan yasa na iya komai shi ake kira da iyawa kafin samu ke nan.

A hankali nake tuki ba tare da garaje ba har na shiga school din ina neman wajen parking a daidai kofan deparment din mu ta inda nake ganin yawamcin masu motoci a school din suna parking nan na samu waje nayi parking.

Saidai ban fito ba haka da dama dana sama wajen idonsu na kan motan suna son ganin waye a cikin motan ko kuma dai kawai hakan daya zama dabi,an mutane ko ina idan anga mota mai kyau sai an kalla anga mai tukinta.

A lokacin dana fito mamakine karara a fuskokon yawancin wajen inda saka key na rufe motar na gyara jakata da riga na doshi cikin wajen don shiga wajen mu.

Inda a dayan bangaren su Okenah da sauran mutanen mu suke zaune sun zubo min ido cikin mamaki da al,ajabi suna kallon ikon Allah.

A hankali nake takawa don ban kula dasuwaye a wajen ba idan mutum ya hangoni saiya rantse yanga nakeyi don yadda nake takawa kamar mai tsoron kasa

Chineke god wooo is maryam be this okenah ke wanan sabarin yana dafe kai da hannnu daya yayin da dayan hannun ke dafa mota yana budan baki.

How comes she become like this in a short period ?

She totaly change in my see Ozil yake fadan hakan daga gefe wata yar bayeraba take fadin hey maryam na amsa cikin daga mata hannu ba tare dana tsaya ba irin na mata masu da jinkai.

Abin ba koya bane yau da kullum kana gani dole ya zaunama a rai damace da samun wuri yake saka mutum harbin iska ba tare dayasan yanayi ba wanan irin damance na samu a lokacin.

Haka zalika bansan wai ina wani jan aji da tako bama a lokacin tunda already idanuwan a bude suke dole inyi hakan kafin akawo min rainin wayau irin na dan adam.

Naji dadin ganin har nakai aji ba wanda ya tsayar dani a hanya na samu waje na zauna ina fito da takardana don insan daga ina zan fara.

A kalla a yanzu babu wani zancen tsayawa wasa ko shashancin banza a gareni tunda nasan irin tarin abinda ke gabana kan karatun nan.

Balle wani ko wata yace zai mayar min da hannun agogo baya a yanzun ma kokari nake na manta da kowa in fuskaci karatuna duk da nasan hakan abune mai wuyan faruwa da sauri.

Fuskana ba yabo ba fallasa na dago ina amsa sallama irinta gayu da Ozil yake min a lokaci inda okenah ke daga gefenshi tsaye yana kare min kallo cikin mamaki.

Yace zan iya zama don a lokacin ba malami a ajin saimu dalibai dake ta shigowa ana shawagine kadai a cikin ajin.

Dan takaitaccen murmushi na sakar mai tare da danja numfashi ina gyara zama nake fadi hello ozil how are you ?

Gaba daya jikinsu yagama saki da lamarina inda fuskokinsu ya nuna alamun muzanta a tsayin da sukayi gabana din.

Don yadda nake kallonsu din wani shekeke ba wani kafa da zasu kawo min iyashegen nan na okenah akaina kuma yanzu.

Wata kila kuma ganin yadda nake tsare gida a fuskana ga kuma shigata har kamahina ya nuna canjin dana samu a lokacin bata wasa bace tare dani.

Kallona Ozil ya koma yi kafin yace zan iya zama muyi magana dake don Allah na dan sake dagowa ina fadin zaka iya kafin malami ya shigo .

A ransa kuma sai mamakin wanan sauyin na dan lokaci guda yakeyi wanda kesa har yake jin dan shakuna a lokacin don hata maganata ya koma na classic lady din nan masu ji da kansu kuma da gangan na kara da hakan donsu.

Naji yaja dogon numfashi yana kaiwa zaune idanuwansa akaina yanayi min wani kallon tambaya dake baiyane a fuskanshi.

Bai fahinci muryansa ba shima lokacin da yasa fadin maryam nasan abubuwa da dama sun faru a tsakanin mu wanda ni kaina banso hakan ya faru ba a lokacin to amma saidai.....

Ko kallon dana sake dagowa nayi mai a lokacin mai cike da ma,ana ya dakatar dashi daga fadin abinda ya soma fada oho ?

Haba abokina ka zama namiji mana ban dauki wanan a komai ba haka kuma ba zan taba mantawa da alherinka gareni ba.

Kafin nakai wanan matsayin kaine mutum na farko daya fara fito dani wanan rayuwan da nake cikinta yanzu na danja numashi tare da kiran sunan shi cikin wani yanayi nace.

Ozil you know what mu a yaren mu bamu manta alheri haka bamu mantawa da duk wanda ya taimakemu koda da rana dayane kayi min taimako da dama cikin rayuwana wanda har yanzu da taimakonka nake tafiya.

Amma ina son ka dauka kamar yadda ka sani tun baya ina yawan fadama akwai bambamci a tsakanin mu irin addini al,ada da sauran abubuwa kaga ashe akwai iyaka a tsakanin mu ke nan ?

Da sauri yace i know maryam na sani tun farko kin fada min hakan so tari da yawa amma saina dauka kamar kawai kin fadane sai yanzu da naga hakan gaskiyane ashe kike fadi.

So har yanzu wanan abinda ya faru ban rike shi a raina ba don akwai mutunci kamar yadda addnin mu ya fada saidai ba zamu zauna kamar baya daku ba don a yanzu ni din nan na kusa aure a gaakiya.

Lokaci guda suka dubi junansu sai Okenah ne ke fadin da wasa kodame maryam ba wasa a cikin zance na idan da yau din nan zan bada dama wanda zan aura ya fito a shirye yake da yazo a daura muna aure dashi.

So ina son sai na kammala karatuna hakan yasa ya zaba min security a duk inda nake ana duban dawa nake mu,amula da suwa nake tare a kullum ?

Guys mubar wajen nan please na fada maku tun bamu zoba akwai abinda yarinyar nan ta taka na fadama a inda take aiki nina ganta da idona don haka ba a banza take ba kungata nan .

Yana magana yana dan waige waige yana duba ko zai gano suwaye security din dake tare dani a lokacin Ozil din ya watsa mai wani harara.

Da sauri ya mike yana fadin sai kazo nikan nabar wajen nan ban iya kasadan jefa kaina a cikin kaddara ya mike yana gyara wandonsa da yayi saging yayi hanyar fita daga ajin.

Ya danyi shiru yana jin kamar an watsa mashi ruwan zafi a jiki don gaba daya hope dinshi akan yarinyar nan ya kare ke nan daga jin maganan ta gaskiyan okenah tana tare da wani babba mutum kenan mai fada aji .

Su kuma suna bala,in tsoron rikici da yan arewa don a kullum iyayyensu na horonsu da hakan akan bahaushe sukance da yayansu suyi hattara da hurda da aboki miyagun mutane shu,umai ba a taba gane masu gashi ko ya gani.

Shi a zatonahi ba zan taba rabuwa dashi ba ga irin abubuwan da yake min na rayuwa kamar ya gama sayenine a lokacin.

Sai gashi lokaci guda na shanmaceshi ina nuna mashi a yanzu gaisuwace kawai ya rage a tsakanin mu kamar irin hakan da muke zaune a yanzu.

Ya dan jima a zaune yayi shiru ina zaune na harde hannayena a kirji ina sauraren ko zai karasa maganansa amma naji shiru har zuwa shigowan malamin kafin ya mike ya fita daga ajin.

Ajiyan zuciyana sauke dama nasan abindake sarewa dan lagos gwiwa shine soja ko dan sanda suba irin hausawa bane da basu tsoron zuwa wajen hukuma barkatai.

Dan kabila yana matukar tsoron zuwa gaban hukuma akan abu biyu na farko basu kaunan hukuma suci kudinsu na biyu kuma hakan barnan sunane ga zuri,an mutum ace ya taba case aida hukuma.

Wanan yasa na zauna na tsara yadda zan fito masu a rabu lafiya ba tare da wani hayaniya ba tsakaninmu sai mutunci na kuwayi nasaran yin hakan a yanzu.

Tunda baba ya shiga gidansu sukai arba da mahaifiyarshi gwaggo a yadda yaga fuskanta a ranan sam batayi farin ciki da ganinsa ba lokacin.

Duk da yaji hankalinsa ya tashi amma bai nuna yagane hakan a fuskanta ba balle halinda ya shiga din a lokacin balle ko banza ba wanan a tsakaninsu yanzu da ita su baba balane yan gaban goshi kasancewa shi babbane dama a dakin.

Haka ya daure ya gaisheta tare da aje mata tsaraban daya shigo dashi don wanda dama a yanzu da abubuwa ke budewa baba din duk zai shigo baya shigowa gaida iyayyen nasa hannu sake saiya riko masu wani tsaraba yazo dashi gidan.

Da kyar gwaggo din dake zaune bakin gadonta irin nada ta iya bude baki tana fadin meye wanan kuma gadanga ?

Ina cikin kudin haramun din da yarka ke turo makane da baka son a fadi ka kawo min wanan din to ka dauka nagaji da cin kayan haram a dai ban yarda bane kaga ina amsa amma a yanzu kan muntabbatar da zancen Rakiya ashe gaakiyane yarinyar nan watsewa take acan da baka son a fadi.

Tunda tana aiko mada kudi tana rufe maka baki ka kasa magana aifa nan gwaggo tace ina wuta in sakaka dashi inda take shiga banan take fita ba har dasu Allah ya isanta akan yar uwarta da danta da suka cuceta ta yarda dan zumunci ta bayar dani da zuciya daya garesu.

Yanzu ga abunan ya koma mata ciki sai rade radi akeyi a gari ana bacinsu kan yarinya na can tana holewanta tana aiko mashi da kudi yana yadda yaga dama dashi da iyalinshi tunda ita mama bata san ciwon kanta ba.

Wallahi kai din nan baka isa ka wullakantamu a garin nan ba kaida zuri,anka gadanga duk abinda kuke boye muna mun ganoku kai da uwar yariyar nan.

Ashema ba gidan Faruq take zaune ba yanzu zaman kanta takeyi a can din dama na dagatane inga iya gudunku yanzu kuma na tabbatar da hakan .

Baba dai yana kurum ya kasa cewa komai wanan zance koshi kanshi yana damunshi wani lokacin amma abinda ubangiji ya zayanowa bawa ba magani gareshi sai gareshi.

Gwaggo din ta katseshi da fadin ai yanzu dai ayita ta kare idan kaika kasa don kwadayin duniya shi bala bai kasa ba don hannunsa bai rubewa ya yar da yayaka sun shirya shida Lami zasu tafi can iko din wani sati su zoda yarinyar nan gida har idan tana daukuwa a garesu.

Allah yakai mu jibi lafiyan gwaggo iya abinda ya iya fada ke nan a lokaci cikin mutuwan jiki ya dora da fadin nima hakan zaifi min gwaggo don a aje a tabbatar da gaskiyan zancen nan dai ba kuma iya suba zan bada kudin motan yaya lawal dana yaya hadiza kinga ko wani bangare a dauka daga nan suje ko da sunan ganintane sugano muna gaskiya da idonsu.

Wani kallo ta watsa mai na baka da hankaline ya gane me take nufi yace gwaggo ina sane shin ba gaskiya ake son sani ba akan maryam mu ?

Yau idan iya bala da lami kadai sukai tafiyan nan ba wani dayan bamgaren ai in sun dawo cewa za ayi sun sameta a cikin wani mugun hali don tana nasu sun rufe zancen ko to a bari din a diba ko ina kowa yaje ya ganewa idonsa.

Tunda haka kaga yafi ai shike nan nikan wallahi wanan abin ya koma min ciki gaskiya da muguwar rawa gwanma kin tashi don da nasan haka tafiyan yarinyar nan zai ja muna magana da ba,ayishi ba tun farko wallahi.

A,a gwaggo Allah yasa dai muji alheri din ba zamuyi saurin fadan hakan ba mu daiyi fatan hakan ya zamowa kowan mu alheri nan gaba.

Kai dakata don Allah kaji kana min magana kamar kana da yakinin alheri yar naka ke aikatawa a can din kai yanzu har wanan abin bai dagama hankali ba don Allah ?

Baba yai shiru tunda ya tabbatar da komai ya fada a yadda gwaggo ta hau din nan ba yarda zatayi ba bata kuma ganewa da abinda yake nufi yasa yaja bakinshi yayi shiru.

Ya daiyi mata sallama ya tafi akan yadda suka tsayar da maganan koda baba bala yashigo gwaggo ta fada mai abinda baba yace ya kai zaune ya soma fadin.

Anya gwaggo bamuyiwa zancen nan mumunan fahinta ba kuwa nafa san halin yaya akan gaskiya matukar yana da gaskiya ga abu irin yadda yakan dage.

Amma bari dai din anje tunda anyi niya amma tunda kikaji ya bada wanan shawaran zancen nan ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login