Showing 201001 words to 204000 words out of 395027 words
Chapter 68 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
da koka fito hayaniyar wanan matsiyacin injin din ya hanaka sukuni a gida.
Wai an tayar da nikan ke nan kuma gidanku ashe kedai bari hjy Tani yanzu nagane yar nan dani take gasa ashe ?
Tunda nayi injin a baya yanzu banda shi shine ta sayowa uwarta saukin abin su sukaci baya don sai yanzu sukai injin su hjy ta kwashe da dariya tana fadin Rakiya ke nan ?
Ni wani lokaci kina ban dariya wallahi dama dake zatayi gasa mana a yanzu duk abinda kike masu takama a da a yanzu takawo karfin da zatayi takara dake .
Kece yaranki basu da zuciya Rakiya ace duk abinda suka wawaro saidai su ba bakinsu ko jiki su har yanzu ba wani na kwarai dayazo ya taya.
A,a hjy ba zaki fadi haka ba tunda kinsan komai ba samari suka rasa ba kema kin sani wanan dagar ce dai data yaba masu bakin jini ko samaein sunzo kwana biyu su gudu.
Tunda nasan tasan irin bakin jinin dana sakawa yar ta a baya shine taje mayar min da raddi akan nawa yayan nayi mamakin irin uban kudin dana kashe lokacin kan hakan ba zance aiki baiyi tasiri a lokacin ba don nagani kowa ta raba saiya tsaneta.
Amma mamakina yadda takai har wanan lokacin tare da mutanen nan basu korota ba har suna mararin ta koma danaso hanawa abinda na hango maki ke nan a lokacin da kika kawo min shawara Rakiya.
Yanzu gashi tana nema ta zamo maki gadangariyan bakin tulu ta hana ruwa shiga ta hanashi fita ke da yaranki ku koma yan kallo an ma koma din aiko yanzu.
Wanan uban kudin da kikai min lissafi kwanaki ta aiko dashi koni nan ina na gansu balleke Rakiya ?
Shawara daya zan baki shine ki mike tsaye kan yarinyar nan wallahi don tun yanzu alama ya nuna yarinyar nan zatazo ta zamo maku matsala nan gaba ita da uwarta da yan uwanta ku koma bin bayansu don hanyar data dauko na ginasu nan gaba.
Aini hjy abine kanayi yanzu kamar bakayi malam sun zama macuta a yanzu kafin ka samu na kwarai sai kaje kauye ko kauyen ma akwai macuta a ciki.
Ni Rakiya yanzu in abu yakai saina bar gari ina tsoronshi wallahi tun kan wanan sarakuwar mahadi din nan hjy Naito da tayowa dan mijinta dauke a hanyar dawowanta mota ya tuntsurar dasu har yanzu tana kwance tana wahala.
Shiko ance arziki kamar an kifar da kwaryantane akanshi jikan nan gidan malamai mana na unguwar nan kwanaki da yazo su Alh na wajen bakiga irin kudin da ya raba masu bane Rakiya.
Ai kuwa naga anyi gyara kofan gidan malam nake tambaya akace wani jikansu mai kudi dake kasan waje ya aiko akai masi gyaran tundai da dare kikaje wajen kamar rana zawiyan nan nasu malam yanzu an kara kawatashi sosai an kara mai girma har kunnun sadaka akace duk marance ana fitowa dashi wajen.
Dan wajen kaunansu malam dinne ai da suke kisantaka da hjy Naito matar Alh yakubu mai glass ba shima da a unguwar nan can hayi yake ba.
Shine malam din suka bashi kanwarsu to danta yanzu ance yaron ya taso sosai ke inkinji yadda Alh ke fadan bunkansan yaron sai kinji tsoro wallahi.
Ance kasan waje yaje ya dawo da wa yan nan mahaukatan kudin masu ban tsoro ke bari Rakiya masu kudi na inda suke kinji mu dai Allah inbaka bamu ba kaba yayan mu .
Ni aikin sa jikina yayi sanyi ke nan ita hjyn taje don yaron dauko asiri shine abin ya bare da ita ko ?
Aiba ance bane don da wanan sambatun ta farfado a bakinta tanata tonawa kanta asirin abinda taje aikatawa kamar an matsi bakinta ?
Hjy Naito gata nan wata farar mace gajera haka mai kiba da isa da izza da takama mijinsu ko yayi kudi sosai lokacin amma kuma karayan arziki yazo ya sameshi daga bayan nan.
Samun kudin dan akace yanzu ya bunkasawa mahaifin nashi shagonshi a kasuwa hakama yan uwan haihuwanshi suma yaba ko waninsu jari yana juyawa yanzu.
Kinji kuma nikan ta gidan mu ko duniya ta kwaso aike kinsan uwarta bata taba bari ta dubemu balle yan uwa ke kibar Ai nan inda kikaga makitan matar nan .
Ana cewa yar kauye yar kauye a lokacin da aka auro maki ita saiga yar kauye tazo tana iya shege a gida ji yadda ta kwata maki a baya kamar yar ga aikinki yanzu naga ta kyankyashe idonta ai kwanaki naga tashigo nan wajen ta nuna part din anty fati da baki.
Nan suka kara rage murya suna gulmansu dayake cin rayuwansu har yamma yayi suka kama gabansu.
Zakice nayi wani aikine a ranan don har makara sallah nayi kodana tashi bakwai da rabi ya shuda tsuki nayi na wullo saman gado bandaki na shiga da sauri na watso ruwa tare da alwala.
Allah ya gani an takura min irin lokacin nan nake samun hutu a rayuwana lokaci hutu da bamu zuwa school nakanyi ramuwan barci na sai rana sosai zan tashi indanyi wasu aiyukan gida ban fita ko ina a wanan lokacin ina gida ko yaushe .
Amma yanzu wanan aikin da Paapa ya dauko min kamar an shiga hakkinane nake gani waima wani irin aikine haka ba takardu ba komai ba wani details ace wai kai ma,aikacine ?
Da irin wanan tunanen har nayi sallah na shirya na fito na samu hajja yabi a kitchen tana hada masu ruwan shayin da zasu karya dashi na safe.
Muka gaisa danta yana faman miko min hannu na danyi mai wasa nace in antyna ta fito na tafi duk da nasan ba zata fada mata ba din.
Nakai kofa take cewa dani don Allah maryam idab zaki dawo ki rikowa kaninki Permppers nayiwa babanshi magana sai yace min ya manta.
Na ansa da Allah sa nima kada in manta kinsan uncle dinane na gadoshi da mantuwa ta danyi murmushin yake kawai a fuskanta iri na ciki na ciki din nan.
Abin hawa ya kara min tsaiko saida kyat na samu na dauki drop zuwa Apapa din har ma,aikatan aka kaini na biya na shiga ciki yanzu ba saina tsaya tambayan kowa ba.
Abinda na kula wajen akwai uniform na ma,aikata da ake sakawa ban tsaya bin wanan ba na shige ciki kai tsaye wana mutumin na sama a saman table dinshi yana aikinshi.
Gaidashi nayi da kwana ya dago yana fadin yau naso makara don oga yace ya kirani dazun yace ban shigo ba kai na daga na dubi office din nashi ni tun ranan farkoma ban sake ganin shi ba ko jin duriyanshi zuwa nakeyi inyi ta zama ba wani aikin da akace din zanyi dan dama sulaiman din nan ya kawo min wasu bayanai yace na adana su a computer na.
Office din na bude nashiga na samu mai shara ta gyara waje tsab yana kamshi an sake ac yana aiki don zafi akeyi a lokacin.
Zama nayi a kasalance ina kallon offince din duk daba wani bakon abu a cikinsa da ban sani ba amma sai nake ganin kamar akwai canji a ranan ashe fridge ne aka saka dan karami a cikin office din.
Sabone dal dinshi na kara kai idona kan water sytem shima bayan fridge din ajiyan zuciyana sauke ina tuna maganan sir sulaiman.
Da yake cewa dani in kwantar da hankalina inyi duk aikin da aka sakani ba wani manufa a tare dasu kaina sai dama suna neman mace yar arewa a nan da zata taimaka masu da irin wanan bayanan da bakowane zasuso ya sanda shi ba don yan kabilan nan ba son hausawa sukeyi ba.
Wanan bayanin da yai min yasa na dan gamsu da bayanan wajen wanda kusan abinda ya fadine yake faruwa banda wanan bayanan da nakan tura na kayan da aka shiga da aka firar kuma banda wani aiki na azo a gani da nakeyi a wajen.
Abinda ban sani ba shine ba yabon kai ba zamana talent yasa ban dauki aikin da wani muhinmanci ba sosai aikine mai kyau da muhinmanci ban sani ba sai karshen wata da akace in fito da abinda na tara din ya turawa ogan nasu.
Ba kowa yasan da aikin da nakeyi ba a wajen suna dai ganina ina shiga sai kuma antashi zan fito donshine banyi irin sabon nan na mu,amula da kowa ba a wajen.
Tun ranan farko da wanan ogan yai min shagube akan sallah ban yarda matukar ina da tsarki sallah ya wuceni na zauna ke nan aka turo kofan office din aka shigo.
A hankali na dago kaina daga inda nake zaunen dan zabura nayi kamar zan mike sai kuma nakoma na zauna don kada yaga gazawana.
Ina kwana na fada a cikin hausa murya a sanyayye zuwa gareshi lafiya ya fada tare da dukowa ya rankofo a table din yana fadin.
Yanzu ne lokacin zuwa aiki ko kin dauka nan jami,ane da zaki dinga shiga duk lokacin da kikaga dama ?
Mamaki maganan ya bani nace makara nayi daga barci ban tashi da wuri ba haka nake dama ban iya karya ba balle in soma akanshi din.
Ke nan baki dauki aikin naki da muhinmaci ba tunda har zaki iya makara aikin mu yana son kula da lokaci don wasu lokutan masu kaya a nan suke kwana suna dakon fitowan mu.
Zan kiyayye hakan na fada ina kawar da kaina gefe daya ya daga da kamshin turarenshi daya cika min hanci har ina jin kamar ciwon kai a lokacin.
Ya fice na sauke ajiyan zuciya ina gyara zama dan tunane yazo min na fara ganin gaskiyan maganan oga sulaiman din ashe yana da saukin kai idan aka bishi sannu.
Meye na zafi acikin haduwan mu illa duk abinda ya fada min gaskiyane a kaina ya sanni din ne ba karya a cikin duk abinda ya fada game dani da sanin dayayi min a kano a baya.
Nina san haka na taso da bin motocin mutane ina kallace kaina kuma inbi motar da rubutun banza ina zana sunana dan murmushi na sake a fuskana tuno da wanan haukan kurciyan nawa na baya.
Har inma ya sanni din to me zanwa gudu a yanzu tunda dole har gidan mu da iyayyena ya sani ke nan amma kuma bai fada min dalilinshi na shigowa rayuwata ba a yanzu.
Kila zancen oga Sulaiman din daine gaskiya don addana masu sirinsu din yasa suka nemu inyi aiki dasu zanyi din ba tare da kowa yaji bayanin komai daga bakina ba kuwa akan hakan.
Don ban tsamanin ko wanan sakataren nashi dake ta wajen mu yasan ainihin aikin da nakeyi a cikin office din nan don da zaran an kawo takardan zan turo a computer na in nade bayanin in saka a jakata tunda ace sirin wajen nake adanawa.
Da wuri na fito don zuwa gida saboda ban tsaya sallah ba ina son in biya in sayowa hajja yabi sakonta kada tace ko naki sayane .
Zafin garin yayi yawa a lokacin ko wani lokaci za a iya jin fadowan ruwa dama haka yanayin garin yake da zaran an fara irin zafin nan ruwa baida nisa da sauka ke nan.
Mutanen wajen keta hada hadasu wasu na haraman zuwa gida wasu kuma suna karasa aiyukansu na sauko daga saman a cikin shigata ta wando da rigan jeans mai dan dogon hannu.
Dako mazaunaina bai gama rufe min ba haka kuma nake saka abina illa dan dogon rigan da nakan saka daga cikin wanda zai sauka ya dan rufo min baya kawai.
Ina tsaye ina duban time a jikin wayana naji horn a bayana hakan yasa na zata kona hau saman hanya ne ban sani ba.
Shine a zaune gaban mota yana gefen mai zaman banza wanan sulaiman din yana tuka motar kaina na kawar da sauri daga kallonsu.
Miss maryam ba gida zaki bane shigo mana mu rage maki hanya sulaiman din ya fada da sauri na girgiza kaina alaman a,a nagode na dora.
Kamar me ban umurni yace ke ki shigo mu saukeku idan kin tsaya wajen nan da wuya ki samu mota by dis time haka sai sa,a.
Jim hakan yasa na matsa zuwa motan da sulaiman din ke budewa ta baya nashiga na zauna ina fadin nagode ba matsala ya fada sulaiman din.
Muka dauku hanya nidai bance komai ba daga hakan sai kokarin saita zamana da nakeyi ta hanyar dora jakkan laptop dina saman kafata don gudun samun matsala.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[9/7, 9:56 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
6️⃣3️⃣🐊
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15_ HAWAYEN KADA🐊
*Account* No
*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*
2254380105 *ZENETH* *BANK*
*PHONE* *NO*
08036959257
Na dawo daga aiki ranan na samu mommy tazo gidan abinda tayi shekaru batayi ba tun wancan zaman da tayi da zamu kano wancan lokacin bata dawo gidan ba sai wanan karon kuma.
Nima baifi zuwa biyu ba duk dadewan nan da nayi gidanta don konaje ba fuskan arziki nake gani a wajenta yasa ko antyna tana son ta aikeni sai in bata rai alaman ban zuwa dole zata kyaleni tunda tasan abindake tsakanin mu .
Wanan zuwan ma wai ashe bata da lafiyane tana fama da laluran hawan jini shine yar nata ta daukota sukazo asibiti akace wani sati su dawo to sukaga gara ta zauna a nan din don yafi kusa.
Abinda nayi ta tunane a raina shine a ina zata zauna kuma tunda duk dakunan are occupy muna amfani dashi indai akace ma mutum yarene ya baro abu da dama a baya a cikin addinin shi da kunya .
Yanzun dai inba dakina zata zauna ba dakin yarta dai anan Paapa ke kwana don sabodani a yanzu baida dakin kanshi a gidan dole yawon bin dakunan matanshi yakeyi yana kwana.
A falo na samesu zaune da yarta anyi ciye ciye an bata wajen sun baje suna hira duk da ita mommy din a kwance na sameta a lokacin .
Sai bayan mun gaisane nakai zaune tana magana a cikin yarensu da intaso gulma dashi take zance a lokacin tana fasin nice nakoma haka wai ?
Nice mama bana fada maki cewa yanzu karatunta yayi nisa ba tana gab da gamawa yanzu hakama aiki takeyi temporary a wani ma,aikata Paapa ya samo mata.
Ki daibi a sannu mutanen nan mugaine basu da hankali jifa wai kallon da sukewa hausawa ke nan a wajensu don koyi da addini shine rashin hankali wajensu su.
A,a mommy na fada maki karkizo ki saka yarinyar nan a gaba don Allah yanzu ba dabane tsab zata tsaya tayi maki rashin kunya nadai fada maki banda matsala da ita ko kadan.
Ledan hannuna take tambaya meye na dauko nace Permppers ne a ciki hajja yabi dazu tace in sayowa danta aikin kyauta zamu huta da fitsari ina jin koda Paapa zai fita tana kara tuna mashi dazun sai yace ya manta.
Ita yar kauye har tasan amfani da wanan abin sallon ta kwashe mai kudi ita da danta yafiku wayau kuna ganin shi nan haka.
Kofan dakin hajja yabi din na tsaya nayi sallama ta amsa na mika mata na fito tana magana ban tsaya ba na nufi dakina na kewa tare da daro alwala don har lokaci ya kure min.
Bayan na fitone nayi sallah na jawo ledan abincin da nasayo wanda yake wrap a cikin wani dan takarda mai walkiya amira nasawa kira tazo na mika mata na mamanta nace idan takai