Showing 141001 words to 144000 words out of 395027 words

Chapter 48 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

har hakan yajawo Paapa daya yadawo ya samu banje school ba ranan yayi min cin mutunci sosai ya shige dakin wanan matar.

Bai jima ba kuma ya fito kome matan nashi ta fada yana kwala min kira nafito yake fadi tun kan in karaso wajenshi ya soma fadin.

Ashe baki da wayau Maryam ina ganin ki kamar me wayau wai in tambayeki zaman wa kike a gidan nan ne ?

Shiru nayi ina kallonshi cikin mamaki don tambayan da yayi min din a lokacin ya kara daka min tsawa gami da maimaita tambayan nace zaman wa kikeyi a gidan nan ?

A hankali nace kai sai naji yace a,a zaman Sariya dai da zamana kikeyi aiba zakiki zuwa school ba yau ki koma ku hade wa matana kai keda wanan mara hankalin.

In zamana kikeyi don me ita wanan dana kawo baki bata kulawa yadda kike ba sariya kike nuna mata kega bangaren da kike ko abunci kin sani tuke take so amma kika dafa shimkafa don uwar dakinki tace shi take so ko ?

Da sauri na dago kai ina mashi kallon mamaki yace to bari kiji dukkansu matane abinda kowa ke so shi zaki mashi a gidan nan ba ra,ayin mutum daya ba kinji na fada maki.

Ke har wani dadi kikaji a wajen Sariyan matar da ta tasaki a gaba gidan nan Allah dai ya gyara baki halaka ba itace don sakarci kike wani rawan kafa akanta yanzu kuma ?

Amma ni anty batace min ga abinda zan girka mata ba idan nace zan tsaya girki haka ba zan tafita zuwa school ba don makara zanyi .

Ni kike fadawa haka maryam ashe baki da kunya nake ganin ki kamar me hankali kin daiji abinda na fada maki ya juya zuwa dakin matarshi.

Shiru nayi ina binshi da kallo tare da tunanen lalai namiji a barshi yanzu shi Paapa akan wanan guzumar matar nasa yake wanan haukan haka ?

Nikan gaskiya zan daukarwa kaina matakin da zan basu mamaki a gidan don a yanzu da nake gabar karshe banda lokacin batawa ga wasu wai in tsaya yin girki.

Muryan antyna naji a bayana tana fadin kyaleshi Maryam neman jidali yakeyi dani ni ban taba tsayawa ce maki ga abinda zaki dafa muna ba a gidan nan ai.

Balle yace nice na kitsa maki hakan a dole anshiga daki dashi an hura mai kunne yazo yayi tujara banda lokacin dan iska yanzu.

Wayana sako ya shigo min hakan yasa na duba sakone daga ma,aikatan mu na zamu hadu da costumers din dana jawo masu don haka suna bukatana a wajen tunda nice na kawo su ranan laraba misalin karfe hudu.

Nake fadawa anty don tana zaune nan muka zauna ina mata bayanin yadda muke abin sai bina da kallon mamaki takeyi na yadda idona ya bude da bussiness haka.

Katseni tayi da ambatan sunana tana fadin maryam kiyi hakkuri ki gafarceni nayi maki fahintar da bashi ba ban tsaya nayi bincike ko tunane zaki iya koba zaki iya ba nabi zugan mutane na dinga munana maki kan laifin da bakiji ba baki gani ba.

Dan murmushi na sake a fuskana ina fadin kai haba anty nasan zugane ai yasa ban biye makiba a lokacin don nasan mutane basu kaunan suga kana cigaba a rayuwanka .

Anyi min haka da Salma lokacin tun ina karama mun taso tare da salma muke komai amma rana daya aka hadani da ita da har yanzu ba shiri tsakanin mu.

Shiyasa da kika fara hakan na natsu na fahinci hadamu akeson yi don anga yadda kika rikeni da zuciya daya don haka za aso aga an rabamu tsakanin mu wanan yasa na daure ban biyewa duk abinda kike min ba tunda na fahinci hakan.

Saiga kuma Allah ya turo min Ozil a rayuwana da farko naji tsoron hurda dasu amma damu da kadaici yasa har na fara kulasu sai gashi na fahinci Allah ne ya turo min su a rayuwana.

Kwarai kuwa maryam wanan wani hikimar ubangijine daya hadaki dasu a lokacin dana tashi cutawa rayuwanki ni kuma naga zancen daga fati ya fito don haka gaskiyane tunda tana tare da iyayyen ki.

A duk lokacin data ambaci sunan Fati wani iri nakeji a raina don ban taba zaton hakan daga gareta ba amma abinda take fada a karshe yasa na kura mata ido inda tace.

Ai in kin kulla maryam tun bayan fadan mu da Paapa lokacin na canza maki don dana fadawa Fati sai cewa tayi da banyi hakan ba ai don tana tuhumar Rakiya ta fada mata hakane don tasan hankalin mu zai tashi a lokacin.

Kuma zan iya turoki ki dawo gida don da farko gaskiya munso haka din amma Paapa ya hana yace ba inda zaki tunda kin soma karatu.

Idanuna na lumshe a hankali ina jin wani iri a raina yanzu dai duniya bata da tabbas ke nan idan har gaskiyane ni yakamata ace anty Fati ta soma kira kafin ta kira antyna taji ko ina da masaniya akan zancen tunda nita fara sani kafin antyna.

Amma yanzu kudi sai ya rufewa mutane ido har su manta da mafari da sanaiya saboda dan abinda zasu samu ga wani a gaskiya anty fati bata kyauta min ba don ban taba tsamanin hakan gareta ba.

Daman da nake nema ya samu a lokacin don haka na dubeta nace a watauna sai nake ganin keda anty Fati zaku iya tsaya min ga komai a duniyan nan ashe ba haka bane a wajen ku anty ?

A tsamina Yau ko wani yace dake zan iya maki hakan ba anty fati ba sai inda karfin ki ya kare don ban sa zaki dauki wanan maganan da nuhinmanci haka ba.

Dan sassauta murya tayi tana fadin wallahi nagane maryam bakuma zuwan Paapa da wanan matar ba tun kan haka ya faru na gane gaskiya duba ga yadda kike da Amira.

Ita mommy nasani tun farko bata kaunan ta ganinni da wani mutum ya rabeni tun azal haka na taso ko kawayen kirki banda su maryam.

Shiyasa zakiga yanzu idan nayi abu keda kike bayana saiki fini tunane da sanin ya kamata shiyasa yanzu nake kokatin kaucewa irin halaiyan nan nata akaina.

Ko zancen nan da badon ke ba da Allah yasa kina nan da mommy taji da yanzu tana gidan nan tana baza min abin kunya don itace zasuyi ta karawa da Paapa da matar nan tashi.

Amma yanzu kinga shawaranki yai min rana sosai ya kuma koma jin haushin yadda nake sharesu din nan shine yanzu yake kokarin dora maki laifi kuma.

Yana zaune yana duba takardun dake gabanshi wayanshi yayi alaman sako da badon wayan da yan uwa da abokan arzikinsa kadai ya adanata ba da ba zai daina abinda yakeyi a lokacin ba ya tsaya duban wayan.

Sakone daga Yisuf can kano yana sheda mai ya kira Alh yakubu mahaifinsu don yaji yana fadin ba zai yarda ya dankawasu Habib dukiyansa ba su salwantar mashi dasu tunda basu koyi komai wajen uwarsu ba sai ha,inci.

Dan murmushi yayi ya gyara zama yana mayar da sako ga yusuf din daya rubuta mai ka barshi da su malam su zasuji da wanan maganan.

Kai dai idan an gama ka fada masu yana turawa ya cigaba da aikin da yakeyi a lokacin saidai tunanen baudewan mahaifin nasu a yanzu kan hjy Naito da iyalinta ya hanashi cigaba da aikin nashi.

Alh yana ganin ya manta da komai da akai masu shida mahaifiyar su da yan uwanshi mata wanda hakan yasashi fushin zuciya yabar gida inda ita hjy din take ganin asirin data jefa mashine yasa ya bar gidan a lokacin tare da hunkunci nai tsauri datasa mahaifinsu yai mashi a lokacin.

Wanda hakan ya kara sashi zuciya dayaje can bai zauna ba ya soma ya buga buga har Allah ya hadashi da uban gida na gari daya tallafa mashi shima ya soma nashi harkokin a boye.

Wanda cikin yan shekaru ya fara hurda da manyan mutane ma,aikatan gwaunati da sarakuna da yan siyasa don ya samu gogewa sosai a waje ubangidan nashi a lokacin.

Da sannu yayi kutse da rigiman fara shigo da yan masuka da tallaka zaiji dadin da saukin saye a kasan yana sakawa a cikin kayan ubangidansa ana shigo mai dasu.

Daga nan ya soma fitowa fili ya nunawa ubangidansa irin abinda ya fara wanda ba kyashi yaji dadin hakan yabada goyon baya wanan karon masuka hauwa irin na yayi da samari ke so da suke kira da wayo kudina a lokacin son sai ka isa zaka sayeshi.

Rufe ido yayi yayo odansu aka zube su a lagos ba karamin riba da daukaka hakan yaja mashi ba a rayuwanshi.

Aiko nan kasuwa ya balle daya gano kaya masu saukin kudi suna karbuwa gun matasa sai ya koma kuma harkan motoci yana hadawa dasu ana shigowa dasu ta ruwa.

Sannu a hankali ya samu hanyar hadawa da gwaunoni yana masu safaran abin hawa daga waje a cikin saukin farashi sai hakan kuma ya karbu a gareshi.

A wanan lokacin banda su malam innuwa ba wanda yasan ya soma shigowa Nageria don bai zuwa gida kano sai daya soma gina nasa ma,aikatan kanshine suka sami ganishi.

Don haka shi wanan abin a yanzu alheri ya zamo mashi ga part part na motoci da yakeyo oda daga chaina ana shigowa dashi nan da manyan motocin noma na zamani wanda hakan ke kawo mai alheri sosai .

Duk da wanan abin bai bar ubangidanshi dake zaune a turai ba har yanzu yana cikin babban yaran mutumin da suke gudanar da sana,an ma,adaine tare dashi.

Ga kuma wanan harkan man da yake son somawa don hadama irin na dan adam duk da dai yana tunane ko sana,an zata samu karbuwa yadda yake tsanmani da fatan samu hakan .

Yasan rigamace amma da gwaji jirgin sama ya soma tashi ai don haka shima zai gwada harkan mai din ya gani koda sa,a a cikin harkan.

PÅ din shine ya shigo dan office din nashi a lokacin ya dago yana amsa mashi sallama nan yake fada mai anturo daga wajen su Ozil zasu zauna dasu ya fada mai ranan da time yace yaji.

Aikin da bai samu yi a ranan ba ke nan dole ya aje ya tashi fita yayi a yar motarshi dake burge samari da yan mata a lokacin wanda ba kowane ke hawanshi ba sai wanda ya isa.

Bakin ruwa yakai kanshi a lokacin don yammace nan keda dadin zuwa ka huta kaga abubuwan da zasu dauke ma hankali a wajen .

Sai kusan nagariba ya dawo ya tsaya nan wani masallaci yayi sallah ana idarwa ya fito ya nufo gidanshi inda ya samu Abdul ya kara gyara gidan tas sai kyali yakeyi yayi mai sannu da zuwa ya amsa dakinsa dake sama ya nufa don bai fitowa sai ya idar da sallah isha,i haka ka,idanshi yake.

Ranan laraba tunda safe da zancen PA shi ya tareshi yana tuna mashi zaman da zasuyi da iyamuran da zasu fara hurdan mai din .

Dan iska ya furzo ga bakinshi alaman abin ya dan tsaya mai a rai kafin ya kallin PA din yace kana ganin wanan harkallan zai yuyu a tsakanin mu dasu kuwa ?

PA din ya dan kwantar da kai cikkn girmamawa yace rankai dade ni sai nake ganin kawai tunda an soma a gwadasu kawai agani in harkan mai yuyuwace idan kuma munga ba fita a business din sai mu barsu.

Amma sam ni hankalina bai kwanta dasu ba duba ga yadda sune suka nemomu ba wai mu mukaje don ra,ayin kan mu ba .

Sai nake tunanen kamar yan damfarane ko dai wani abu somethings like that amma zamu gwada din mu gani ai don su Alh Buba naga hankalinsu bai wani kwanta da zancen ba.

Yanzu mun riga da mun amsa tayinsu sabbeni saidai a gwadasu din a gani koda riba a har kan a gani da haka suka bar zancen zuwa yamma.

Nikan a bangarena tunda zan fita gida nafita da shirina tsab tare da addu,a don nasan ranan insha Allahu har in an shirya to zanfi kowa farin cikin kasancewan hakan a rayuwana.

Wani sabon dinki nasaka a jikina atamface akaiwa staley mai kyau dingin kamar zubin jallabiya akayi shi sai aka bi adon da stone daya kara fito da atamfan dinkin lagos akwai kudi amma akwai kyau sosai.

Don har da gyaleshi an sakamai kyale yadin kayan shi nayi roling a kaina nabi jikina da turare mai kamshi sosai wanan ka,idace na bude ido da kamshi don zama da uwar dakina.

Ban tsaya girkawa kowan su abinci ba a gidan don tun ranan da Paapa yayi min fada na girka abincin dare irin da yace sai ga kuma matar na fadin wai bata son tuwon semo a lokacin .

Hakan yasa na yankewa kaina shawara bandai fadawa kowa komai ba tunda bagane magana takeso don taga mijin yana daukan iya shegen da take tsulawa a gidan tun zuwanta.

Biyu da rabi Ozil yazo ya daukeni shi da Oke muka fita don zuwa inda zasu hadu din a tsara komai wanan haka ka,idan yake damu.

To my surprise banyi tsamanin wanan haduwar harda mahaifin Ozil bane sai gashi naga ana tsara wajen harda mazaunin shi wanda zance baifi gani daya nayi mai ba duk zama da danshi.

Yan kabila suna son diyansu sosai haka suma diyan tun zuwan mutumin danshine yaje ya taroshi har suka shigo wajen ya fara ganawa damu lokacin.

Yake tambaya waye ya nemo masayan da sauri Ozil ya nunawa mahaifin nasani dake can gefe daya zaune ina kallon ikon Allah don a gaskiya na zata mahaifin nasa wani tsohone sosai ashe ba haka ba za a kirashi dattijo dai kawai amma bai kai can sosai ba.

Gabana sai faduwa yakeyi kada su badamu sozo suki zuwa don ansha muna hakan wanan ko gashi harda mai company a wajen.

Hudu da minti ashirin suka kira waya gasu a haraban hotel din dole a ka,ida nice zanje nayo masu iso zuwa wajen donshi Ozil ya tashi ya bini muka fita tare dasu da oke.

Shiga irin ta hausawane a jikin matashin da kallo daya zakai mai kasan yana cin lokacinshi wata kila shima yazone bisa jagoran wani nashi ko mahaifinshi ko family dinshi .

Sai dayan Alh da shima yazo a mota na dabam don yadda naga sun tsaya suna gaisawa a wajen tsakaninsu na karasa tare da sallama a bakina ina fadin.

Muna maraba da zuwanku wanan wajen mungode da amsa tayin mu da mukai maku da fatan zakuji dadin hurda damu.

Bissimillah ga hanya ku shiga na fada ina nuna masu hanya na fara yin gaba suka biyoni a baya gaba dayansu .

Sunji dadin yadda mr Victor ya karbesu da kanshi bai turo wani nasa ba nan aka dan soma bayani da dalilinshi na son hada bussines da yan erewa .

Wasa wasa saida abin yajasu zuwa har karfe shidda da rabi na yamma suka samu kaiga matsaya dasu inda ko wani bangare sukaji dadin abin sosai tare da fatan samun kulluwa mai albarka.

Muna waje Okeh na min shirin nayi babban kamun da ba wanda ya taba zaton hakan sai gashi Allah na ya ban sa,a lokaci guda a daidai lokacin suka fito.

A ka,ida zamu samesu da zancen tukwaicin da zasu bamu sai gashi na tsunci kaina da kasa zuwa koda kusa dasu sai okeh ne ya tafi a madadina ya soma magana.

Kamar ba zai amsa mai ba saida ya bude mota yake fadin kace maryam tazo da kanta ta karba don itace muke gari daya da ita.

Mamaki ya somayi yana fadin dama kasan meiram No wander kukai accept din mu ashe hannu okeh yayi min dole na tako zuwa inda suke ina zuwa na wayance da fadin mungode da zuwan ku .

Wanan yace sai anbada tukwaicin hakan no ku barshi babu komai na fada ina kokarin juyawa don barinsu ki bamu account a tura maki PA din ya fada.

Shiko ya riga daya shiga mota a lokacin don haka da PA dinshi muka karasa maganan zance wanan harkallah tafi ko wani dagani don saida gabana ya fadi ganin irin kudin da suka turo min a lokacin .

Ina hanya ina tunanen waye shi waye kuma a ina yasanni haka yake kokarin nuna min sani duk da fuskanshi a daure yake ko wani lokaci ?

https://chat.whatsapp.com

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[8/20, 9:42 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

4️⃣6️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login