Showing 303001 words to 306000 words out of 395027 words
Chapter 102 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
ina fadin amma daddy shine baka fada min ba a lokacin in dakatar da hakan ?
Wallahi idan anji anji ance ina da mota kowa zai dauka wani sharholiya nakeyi a nan har nakai ga mallakan mota a yanzu.
Shout up my friend suyi ta fada mana ni nasan ainina sayawa abina mota don saukin kaina duk wanda zai fadi wani abu yaje ya fada wanan shida Allah kuma.
Ga key dinki kibi a sannu please banda tukin ganganci nasan irin koyon motar da kikayi a baya na ganganci irin na masu hauka a kai so kibi wanan a sannu don Allah ?
Ki kuma san irn takon da zakiyi don nasani gaskiya kika fada ido zai dawo a kanki na zargi amma rashin sanin dawa kike tare zaisa har su tofa hakan ai a kanki ?
Ya mike min key din motar har lokacin ban mika hannu na karba ba ina tsaye kamar an dasa gunki a wajen na kasa ko motsi balle in daga hannuna in karbi key din da yake miko min din.
Ganin hakan yasa ya mika hannunshi tare da kamo hannuna ya dasa min key din motar a tsakiyar hannuna yana fadin take care ni zanyi tafiya gobe ban sani ba ko na samu zuwa ko sai idan Allah ya dawo dani lafiya zan samu shigowa nan din .
Duk bayan sati na fadawa hamza gashi can yazo ya dinga daukan motan ana duba maki lafiyanta don gudun samun matsala ya juya ya tafi ina tsaye har lokacin ba wani motsi a tare dani.
Saida naga da gaskiya ya nufi dayan motan da malam hamza yake zaune yana jiranshi hakan yasa na danyi far da ido ina fadin wai da gaskiya a nan zaka bar motar don Allah ?
Murmushi mai sauti yayi ba tare daya tsaya koya juyo ba yace mota aiba tawa bace takice kuma na kawo maki abinki ya bude motan ya shiga suka tafi.
Nikan mamaki ya hanani ko motsawa balle na iya furta wani abin kuma idona na mayar akan motar a hankali farace sol sai shekin sabontaka takeyi na daukan ido.
Ban taba tsamanin da gaske bane akwai masu mayar da alheri a duniya sai gashi nagani a gabana yau ashe duhun kanki har yakai alheri ya sameki haka a bagas ki kasa farin ciki maryam ?
Ban taba ganin inda akaiwa mutum alheri irin wanan ya kasa godiya ya tsaya yana shashancin banza kina ganin yau dabaranki ko wayonki ko wani abinki ya kwanto maki motan nan haka a hannunshi.
Allah ne ya baki lokacin da kema zaki dama kici gashin kanki shine yazo maryam ya tsaga rabonki a hannun mutumin nan .
Maimalon ki buge da godiya ki manta da komai kin tsaya kina wani fadin rai irin na wanda baisan komai ba so ki matsa garin jan aji irin naki harki tsunka zaren ai maki dariya .
Motace gata nan ya kawo maki kuma tsakani da Allah ya kawo motan nan ya fadi dalilinshi wanda ke nuna cewa bai kaunan ganinki a wani motan kowa daga yau din nan tunda kinji ya fada yanzu kina da naki motan dai.
Da yawa maza suna da mugun kishi kan abinda suke So musanman mace don idan namiji yana son mace bai iya boye kishinta a kan kowa .
Mata mu Allah ya ba wanan hakkurin na taushe zafi da radadin abu mu daure mu hakkure dashi koda kuwa hakan na muna illa a zuciyanmu.
Ajiyan zuciya na sauke na dan kallota ina fadin yanzu anty me zancewa Paapa da iyayyena zan fada masu namijine ya saya min mota saboda yana so na ?
Zaki fada mana wanda keda magana ya nemoshi yaji ba,asin hakan daga bakinshi ba komai yasa ya furta wai da albashin kine ya sayo motan nan don kaucewa irin tunanen nan na mutane ne kawai yasa ya fadi haka nasan ?
Amma ina albashinki ya isa ko sayen tayan motan nan, bawan Allah nan yana matukar sonki maryam ki godewa Allah daya hadaki rayuwa da irinsa yau ko baki aureshi ba kina da riban zama dashi maryam don ba zai taba amsan motan nan daga hannunki ba.
A hankali na taka zuwa wajen motar na leka ina duba cikin motar komai sabone fil kamar yadda jikin motan yake sabo na nisa ina fadin.
Gaskiya anty motar nan tayi min girma na fara tsoro da shakkun oga Aliyu matashi kamarshi har zai iya kyautan wanan mota mai tsada haka ?
Me kike nufi this is Lagos fa not kano nan bariki ce sai yayi kyauta da abinda yafi hakan gareki ba tare da wani yasan da yayi hakan ba.
Nan ba arewa bace maryam Lagos garine na yanci ga kowa ba takura ba sa ido ba gulma da arewane nima na tabbatar da ba zai iya baki koda tayan mota a yanzu ba .
Sai ya tabbatar da kin zamo matarshi saboda abubuwa da dama yan uwanshi ma kadai sun isheki su kawo maki matsala game dashi balle yan gari kai ko a cikin gidan ku sai ansamu wanda zaiyi hassadan haka din balle yan waje.
Sai kiji an fara sukanki ana fadin munanan kalamai da mutum baison shi a soki dan uwansa da hakan amma yana iya rufe ido ya jefawa dan wani wanan kalman ba tare da tunane ba wanan rayuwan sai arewa kinji.
Jin zancen ta nakeyi awa zuga take min a lokacin ta karbi key din motar daga hannuna ta bude ta tayar ta gwada injin din da komai ta fito.
Maman sunny data zo wucewane ta tsaya take fadin mm Amira abi na your car be this ?
Ta fito tana dariya tare da fadin No be my own wooo who go dash monkey banana ?
Na maryam car be this her boy friend buy am for her wani ihun murna tayi tana sowa wanda hakan ya jawo hankalin sauran makwabta dake waje suka so sa albarka a wajen.
A raina nace kaji arnancin ba nan aka shiga yin addu,an Allah ya tsareni ya kareni daga sherin duk wani abinki na fili dana boye a cikin irin addu,ansu na kiristanci saura na fadin Amin.
Ni maryam naga ta kaina a wanan ranan ba zancen damuwa bane don har chief security saida anty ta kira tafada mai saboda tsaro dama duk wanda ya sai mota a wajen idan yana son tsaro na kwarai zai kira ya sheda masu tare da dan ihisani.
Ba zancen barci a gareni ranan tun bayan da nayi sallah nake zaune ina tuna ina duban yadda wanan labarin zaikai ga iyayyena wai yau nice da motan kaina haka a kofan gida ?
Tunane bai bari na samu kirashi ba a lokacin duk da harda nauyi da kunyar hakan idan ma sayen bakine ko zuciya zance ya gama saye a yanzu a gun ko waye.
A sanyayye na jawo waya zuwa gabana na jima ina kallon number kafin in danna mashi kira kamar ba za a dauka ba can naji ya dauka yana sallama na amsa a sanyayye cike da girmawa na soma gaishe da fadin.
Ya ka isa gida daddy sai naji yace kalau ya na barku dazun din na amsa ina ajiyan zuciya da lafiya kalau sai kuma nayi shiru.
Shima dai a bangaeahin shirun yayi yana saurarena kafin yace meya faru naga kin kira kuma kinyi shiru ko kawai don kiji yana iso gidane dama ?
Umm,humm ni me zance a yanzu tunda ka barni da imaninka daddy kamar ni ace wai an saya min mota motar ma irin ta yayan manya masu fada aji a kasa.
Okey keba yayan manya bane ke nan ke diyar Aliyuce kuma bari dai nayi shiru kada katobarana ya kaini ga sakin maganan da za a kashe wayan kuma a yanzu ?
Murmushi na danyi ina son fadin abu ya rigani da cewa to ya motar tayi maki ko a canza maki da babbanta wanance ta mata ai kinga komai nata nakune na mata ta maza din daban take ita.
Daddy don't kill me before my time wani irin a canza min kuma ni ina batun a dauki motar har zuwa gaba kana zancen wai a canza min ita kuma ?
Allah daddy bansan ya zan fara shiga mota a yanzu ba bawai wani abu bane kawai ina gudun abinda zaje ya dawo nan gaba akan hakan.
Kada a dauka zancen da mama ke fadi a kaina ko gaskiyane tunda ansan cewa karatu nakeyi ba wani sana,a ko aiki ba a nan din.
Baki taba jin ance Hawayen kada kwanto bane halan maryam nima ba yin kaina bane dana saya maki mota a yanzu .
Allah ubangijine ya tsaga da rabonki a gareni maryam ki kauda zancen abinda ake fada akanki gida ko kuma wasu zasuce a yanzu kanki lokacin mikewan kine Allah ya kawo.
Nikaina nima ban tsaya tunanen komai ba a zuciyana lokacin da zan sai motan nan sam ban kawo wanan tunanen a raina ba a lokacin.
Wanan yasa nace maki Allah ne ya tsaga da rabonki din a wajena kinsan shi kada idan yayi kwanto sai yaba duk wanda ya ganshi cikin irin wanan halin tausayi da har mutum zai jiya manta da illan da idan yatashi zaiyi gaba.
Don haka manya ke cewa HAWAYEN KADA KWANTONE GA MAHARBAN SHI DON DAKAYI SAKE YA CINMA KAFAN KA SAIDAI WANI BAKAI BA A DUNIYAN NAN,,,,,,,
Murmushi nayi don jin meya fada yace iam telling you maryam lokacine na haskekin ba wani mahaluki a duniyan nan daya isa ya hana hakan sai ubangiji da kansa ya isa da hakan
Daddy kana kashe mi jiki kana hura min kai kana sa in dauka ni watace fa da iein maganan nan da kake fada a yanzu kaina ?
You are kidding kar kice min baki san ko dawa kike bane har yanzu maryam kina tare da Aliyune fa Aliyu kainuwa dashen Allah,,,,,,,
Dariya sosai na kwashe dashi lokaci yace wallahi sunan da wai mutane suka saka mi ke nan ashe kinsan nima nasha iri wanan faman da kike cikinsa da matar babaki zance nawa ya cunawa naki sau dubu iri rayuwan da mukayi a hannunta nida mahaifiyata maryam.
Haba dai har akwai wata mace da tafi mama sheri a duniya gaskiya ko akwai kila saidai suzo daya yace Okey ban taba zama na baki labarina bane amma barin dan baki wanda zan iya.
Na dubi lokaci nace dare yayi sosai fa daddy gaka da tafiya gobe a gabanka yace tafiyan da zanyi raina bace tunda banga engel dina a motar taba wani aiki zan iyayi kona tafi.
Kinsan ance farin cikin iyalinka shine namaigida don matukar ran iyalinka na a bace kaima ba zaka taba samun farin ciki ko sukuni ba a tare dakai.
Dan murmushi nayi daga bangarena da har yaji a lokacin yace Allah bansan zancen nan gaskiya bace sai haduwana dake maryam.
Don a yanzu ina jinki a wani bangare na rayuwana ta yadda har nake jin idan banjiki ba kamar na rasa wani sashe na rayuwanane a lokacin.
Ni din nan daddy na tambaya a dan shagwabe yace kin dauka da wasa na fada iya gaskiyar nake fada maki maryam .
Wanan yasa nake son daga na dawo daga tafiyan nan zan tura aje gidan ku nema min aurenki kowa yasan da cewa ke din kina zamanane a huta da wani tsegumi kuma .
So soon daddy ni da,,,,,,,,
What me kike nufi da fadan hakan da kikayi kin dai san ba zan tsaya shirme ba a yanzu ina bin mace a waje ko wani lokaci na dauki wanan shiriritane a wajena.
Na dan dara irin mai nuna mamaki din nan yace yes kice min banda tabbas ke nan ki hutar dani daga shiga kaidinku na mata karki tsaya kina ban wani kwanaye kwanaye please.
Daddy meya kawo kwanaye kwanaye a zancen nan tun farko idan ban amince ba da bamu kai hakan ba da kai ai ?
Wani lokaci kafaye saurin fusata ka fahinceni please abinda ya hadamu ke nan ranan ga magana mai muhinmanci da nake neman shawara a kai amma kaki ka tsaye ka fahinci komai ?
Ni wallahi idan kana fadan nan wani lokacin tsoro kake ban inga ka zama wani iri har na fara tunanen anya kuwa ,,,,,,,
Ya isa haka mu bar wanan maganan tunda baki son hakan meye damuwanki a ranan da nakasa tsaya in saurareki ?
Na danja numfashi ina fadin ai ranan ta wuceko bayan haka kuma na nemawa kaina mafita akan zancen ya tareni da fadin bankai ki fada min damuwanki ba ke nan koda ya wuce ko ?
Ba haka bane dama dai zancen wanan friend din nawa Ozil ne ozil okey nagane sai akai yaya wai baida lafiyane nan dai na kwashe komai daya faru na fada mai naji yace what me suke nufi da hakan ?
Wallahi nima ban sani ba daddy shine ai baka bari nayima bayanin abindake nan ba kazo ka hauni da fada ka kasa fahintana niko taba motan okenah banyi ba balle in shiga.
Na fahince ki yanzu haka suke fada ko anan cewa ina da saurin daukan zafi da mutum wani lokaci kin gane banson rainin wayaune wani lokaci.
A yadda naji maganan ne saina dauka cewa wani yazo ya daukeki kuka fita amma daga baya cikin maganan ki saina fahinci ba haka zancen yake bama ashe ?
Yanzu meye abin yi kin tafi din kenan kome na amsa mai da bantafi ba naji yace good ki share dan iska kawai kafiran banza idan sun matsu da hakan suzo inda kike mana idan gaskiya.
Sai karfe kusan biyu saura na dare a ranan mukai sallama da juna koshi hamman da yaji na somane ya barni mukai sallama dashi.
Washegari ban fito da wuri daga daki ba duk da hakan ba a dafa komai ba a gidan badon babu ba kuma don muna da komai na amfani matar gidance dai ke jin ikonta a zuciyarta.
Gyara kitchen din nayi na dora muna abinci kafin in soma gyaran gidan tundaga kitchen har falo na gyaro ko ina tsab turarena na dauko na feshe ko ina dashi gidan ya dauki kamshi.
Wai sai lokacin da kamshin ya isa hancintane tasan dana fito haka ta fito da rigan barcinta tana fadin wanan kamshin haka ke kan maryam mijinki aiya huta don ba sai ya nema maki yar aiki ba ai.
Murmushi nayi ina gaida ita da kwana tace wallahi a cikin barci kamshin nan naki ya tayar dani barci ashe rana yayi hakane sosai ana neman sha biyu yanzu ?
Eeh nima barcine ya daukeni ban fito da wuri ba don jiya banyi barci da wuri ba nima kusan hakane na kwana ina mamakin wanan bawan Allah naki maryam.
Don Allah maryam ki dinga lalabashi a sannu kinsan yanzu irinsu tsada sukeyi a gari wallahi haka kuma yanzu idan kin bibiya bai rasa wace ake son hadasu aure a gida.
Anty nima ina tunanen hakan shiyasa banson in zure mashi don ban manta da yadda akayi min a baya ba akan bello duk da shima a lokacin fin karfinsa akayi har aka samu kanshi ya yarda sai daga baya nake jin komai da mukaje wancan lokacin.
Ido na lumshe ina ajiyan zuciya anty ke fadin irin wanan ogan naki Maryam dolene sai anyi fama dashi don wallahi yan uwa ba zasu bari ya dauko bare ba a cikinsu .
Don yanzu zakiga cikin dangi suna bashi mata har sai ya ture tunda ya tara abubuwan da mata da mutanen zamani sukewa yayansu kwadayi.
Akwai kudi shine gaba da komai a yanzu kana akwai ilimi akwai kuma kyau ga wayewa ke shi dai sai ince komai Allah ya bashi a rayuwanshi gaskiya ni bansan haka yake bama sai jiya na kara mashi kallon tsab.
Humm nace kafin in soma fadin jiyan nan yake fada min ai wai da ya dawo daga tafiyan nan da zaiyi yana son ya tura aje gidan mu na dakatar dashi ga hakan.
Da sauri naji tace dani sabodame zaki dakatar dashi maryam na dago ina fadin anty banfa gama karatuna ba a yanzu.
Idan yakai zancen gida akace aure fa a yanzu zancen karatuna kuma fa gara dai yayi hakkuri har in karasa din don karatun nan yafi min komai a rayuwana.
Shifa so tsuntsune anty idan ya sauka a kanka wataran yana iya tashi ya tuma ya fada kan wata karatu kuma nike da abina a cikin kwakwalwata ba