Showing 69001 words to 72000 words out of 395027 words
Chapter 24 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
iyayyenta itama ?
To Paapa naga aiga jirgi zamu tafi ina zamu dauketa zuwa kuma saita zauna nan da mummy har mu dawo watarana ta tafi ta duba gida din.
No tare zamu tafi yarinuyar nan fa amananta aka bamu sai iyayyenta suga munzo kawai bada ita ba kina ganin ransu zaiyi dadi ga hakan da zamuyi tare na saya muna ticket da ita don haka har da ita zamu tafi.
Ita mummy ta koma gida ta zauna ga kudi ki saya mata abin bukata da zata koma sai ki mayar da ita gida amma zataga kamar ai min koreta ko ?
Au dama ta dawo nan da zama ke nan kome don bangane zatayi fushi ba to naga dai bata tashi komawa bane can ai ta koma gida hakana ya fada a gadarance ba sasauci a zancensa.
Lokacin da take fadawa uwar tayi fada sosai da hakan nina zata idan ya dawo zatayi tashin hankalinnan nara amma sai naji shiru batace komai ba.
Shine washegari yar ta kaita gida saidai kafin ta tafi nasha zagi sosai inda take fadin ai zan dawo in sameta indai itace duk sherin danaje na hadawa yarta ko ita wajen iyayyena idan na dawo zamu hadu da ita.
Na daina yawan tsoronta yanzu haka yasa nace me akai min da zanje in kullawa anty sheri a gida in ba yabo aiba zagi kuma ga anty don ni tayi min komai a rayuwanā .
na haka na barsu ina jin yar ná mata yare a lokacin hankalin ya daina tashi yanzu ga duk abinda zatayi min don gaba daya nagama fahintar halin matar.
Tsorona daya shine irin rayuwanta na bin babalawon su na yarbawa don gaba daya ita al,adunta na yan kudune don acan ta taso tayi rayuwanta idan tana hira zaka fahinci yar duniyar matace ta gaske.
Saida ta mayar da mahaifiyarta gidane ta dawo min da sayayyan tafiyana niki niki nima nayi murnan hakan tundai dan jakkar saka tufafin data sayo min tare da kit dinshi da hand bag su takalma har kaya make,up sai dogayen riguna irin na shan iska din nan dana fashion.
Tare muka shirya kayan da ita washe gari muka kama hanyar kano duk da naji tace zamu tsaya a Abuja mu kwana biyu amma haka bai hanani murnan ganin zan taka arewa ba lokacin.
Mun sauka Abuja din a zatona wani gida zamu sauka amma sai naga an sauka a hotel wai ashe zai tsaya nan ne ya danyi wasu aiyuka dasuka shafi aikinsa.
Daki biyu aka kama nida yarsu a daki daya saboda yarinyar mun shaku sosai wani lokaci bata ko yarda da uwar ko kakan idan ina gida tana lake dani ko yaushe.
Hakan yasa anan ma din zama dani bai zama muna matsala ba kwana mu biyu a abujan har zaman ya fara gundurana a lokacin don matsuwa da nayi da mu isa gida inga kowa nawa a lokacin.
Muna da kwana biyu a garin ta sameni daki wai in shiryamu zamu shiga gari wajen wani dan uwansu dake nan garin da zama.
Muka shirya tsab koda muka fito naga da mota yazo ashe muka shiga wani gida mukaje gidan mata biyune kamar gidajen mu na hausawa.
Ana fadin ga matan daddyn lagos tazo suna fitowa yara da manya ana gaisawa ina lake da Amirah dataki yarda da kowa a lokacin .
Uwargidan tafi amaryan fara,a don itace ta zauna muna hira da ita saidai duk a cikin harshen turanci ake hiran don a zatonsu bamu da hausane a bakin mu yarda suka ganmu .
Gashi kuma ance yar lagos ya aura sai su dauka aiba hausa a bakinta anan kuma na fahinci ashe bama saninta sukayi ba yan uwansa ashe ?
Nice na mike don yin sallah suna mamaki matar da yaranta yadda nayi magana nace ina son inyi sallah lokacin sallah yayi.
Wai ashe dama kina jin hausa ai mun dauka kozo mu kasheki bakiji nayi dariya wata yarta ta mike tace in biyota Amirah ma ta lake min muka bar wajen tare.
Kodana idar da sallah nan dakin muka zauna dasu muna hira take tambayana amma dai nayi zama arewa ko nace ni yar kanoce ai daga baya Paapa ya daukeni zuwa lagos.
Allah nasha ke wata kabilace murmushi kawai nayi ina gyara zama na jawo Amira zuwa jikina take tambayana ina nake karatu ?
Na fada mata komai dangane da karatuna munkai wani lokaci a gidan kafin anty ta aiko infito muka fita tare da wanan matar gidan sayayya mukayi daga nan ta sauke mu a masaukin mu .
Kwanan mu hudu gana biyar muka bar Abuja din zuwa kano ta dabo tumbingiwa karfe tara na dare muka sauka kano din nidai sai na zama bakuwa a lokacin.
Don sai wajen ya canza min duk da ba laifina bane koda nake gida wayauna bai kawoni nan layin ba don iyakata daidai unguwarmu da muka taso a cikinsa koshi din zance a layinmu nafi wayau ai.
Anzo daukarmu airport din zuwa gidansu dake nan garin wanda ko matar gidan kamar zuwanta na farko ke nan a lokacin gidan tar da hasken fitilu dake aiki duk da darene zaki gane sabon wajene gidan don komai na gidan sabone.
A falo muka zube ga gajiya saidai ban yarda gajiya ya hanani ibadana ba abinda ba kula dashi da zama da antyna tana da rauni a wajen ibada wanan kuma nasan tasowa cikin kabilan da tayine haka kuma uwar itama dai gata nan ga kamarta neman kudi kawai akasa a gaba a kullum.
Tana zaune tana waya da mummy har mukai sallah muka dawo tana nan zaune ina jin mijin na mata magana cewa ta tashi tayi sallah mana tace waya takeyi da mummy.
Karshe kuma abinci muka hauci don tun fitarmu mota ya aika a sayo muna abinci aka kawo akwai gajiya a jikin mu din haka muna gamawa nake fadin anty zanyiwa Amira wanka kada tayi barci hakana.
Take fadin gaskiya fa barin tashi in duba wani daki zaku zauna a cikinsa mijin naji, naji yace ita ai gidansu zata tafi mana zuwa gobe taje taga gida suma su ganta .
Shiru tayi sai zuwa can ta samu fadin amma ai ta dan huta bada zuwan mu zata tafi ba kamar ana koranta gida ai dole taje taga yan uwanta ko ?
Ni ban damu da halinsu ba inda sabo na saba da ganin hakan a garesu so kawai nakeyi na samu inda zan dan kwanta don kaina dake min ciwo tun da muka iso din abincin daurewama nayi nacishi hakana don kada in kwanta da yunwa a cikina.
Bayan sun danyi dube dubensu naji ta kirani ta nuna min dakin da zan shiga da kayan mu ban kwanta ba saida na kwashe duka kayan nakai dakuna na samu naje nayiwa Amira wanka nima nayi muka kwanta.
Washegari mun samu barci sosai don bamu falka da wuri ba saida yarinyar take neman abinci lokacin cin abincinta yayi na tashi falin muka fito dabara nayi na zuwa kitchen din gidan inda na samu komai akwai a girki a cikin kitchen din har da kayan abinci.
Dabaran hada breakfast nayi muna kukan yarinyar ya tayar dasu daga barci har suka san rana yayi lokacin uwarce ta fara fitowa tana tambayan meya sameta ?
Wankane bata so na bata amsa uwar ke fadin kinsanfa lokacin karyawanta yayi dole tayi fitina ni bansan me zataci ba ?
Aita karya na hada brwakfast tun dazun na bata wankane bata so ayi mata wai yanzu kuma daidai lokacin mijin ya fito daga daki yana fadin baribya kira wani yazo ya kawo muna abin karyawa.
Matar tace dashi ai maryam ta hada breakfast akwai abinci a gidanne ko take tambayan mijin nata yace komai akwai ke baki duba bane jiya.
Nagaji ina zan tsaya dubawa tunda ba dafawa zanyi ba ta fada ta nufi wajen kujera ta zauna tana tambayana me kika dafa muna maryam ?
Dankali na soya sai kwai da ruwan shayi na bata amsa baki ta dan tabe tana fadin kin kyauta in don nice aida saidai ta jira.
Tsuki naji mijin yayi ya juya yana fadin wanan matsalarkice ki zauna da yunwa idan kinso yarinyar nan dai gidansu zataje taga iyayyenta.
Amma dai na fadama sai mun huta naga yanayin zamana a nan zata tafi kana ta magana ai kamata yayi taje din ta wuni ta dawo bata zauna can ba.
Baki da adalci Sariya yaushe rabo yarinyar nan da iyayyenta da zamu zo gari mu rike masu saboda son kai kome ?
Dauketa kije kiyi mata wanka ta fada hakan yasa na yunkura na dauki yarinyar tana kuka na bar wajen da ita don na fahinci zasuyi radhin mutuncine da juna kan zancen zuwana gidan mu din da mijin yace sai nayi.
Ta soma ya mike tsaye yana fadin ke baki da wayau wallahi idan mun rike yarinyar nan a nan baki ganin kano muka zo karshenta hakan yasa ita ta gudu zuwa gida din ?
Ki barta taje taga iyayyenta shine magana bana son abin rashin gaskiya don Allah shiru tayi tana nazarin magananshi a zuciyarta har na shirya yarinyar na fito da ita nakawowa uwar.
Amma yarinyar sai taki zuwa wajen uwar nan ta soma fadin you see nasan idan na barki kika tafi gida kika zauna can zansha wuya da yarinyar nan a gidan nan .
Tana cika tana batsewa har mijin ya fito cikin shirinsa yana fadin zanje kasuwa in samu baba ki shirya kafin in dawo muje wajen su hjy can cikin gida.
Ya fita ta jima a zaune tana waya dama ita aikinta ke nan ni har nakanyi mamakinta wani lokacin bata taba komai a rayuwanta idan ba taci ta kwanta ko ta zauna zaman waya na tsawon lokaci.
Gashi kuma ba zance ita din tashin wani gata bane can saidai ace tashin sakaci an taso irin ba aikin komai ba a taimakon iyayye da komai balle a saba da hakan .
Irin wanan halin kesa kikaga mace ta taso bata iya yiwa rayuwanta duk wani abinda zai taimaki rayuwanta saboda jiki da bai saba da wahala ba wanda hakan kuma ba wahala bane taimakin kaine a rayuwa .
Koda mijin nata ya daao tare muka shirya zuwa gidan koshi saida yayi da kyat ta fito ni abin yana daure min kai duk da nake yarinya na fahinci akwai matsala tsakaninta da dangin mijinta.
Ko kuma ince iyayyen mijinta din don yadda take nuna bata ra,ayinsu saidai ido don ba abubane daya shafeni don haka nidai da sun fara sai inbar wajen in kauce masu.
Gidane babban gida irin mai dauke da iyalan mutum guda amma zaka samu irin gidan ya tara mutane da yawa daga diya zuwa jikoki.
Sunyi murna sosai da ganin mu ba kamar yadda na zata zai faru ba idan munje yadda ita anty din ke nunawa idan an dauko maganansu.
A gadarance ba nuna ladabi a tare da ita take amsa gaisuwan da take masu din dama ta gargadeni dana rike mata ya kada inba kowa ita kada wani mugun abu tazo ya sameta kinsan yarbawa basu da yarda.
Ni kaina da farko ai haka akai min lokacin da aka haifi yarinyar kiri kiri ake hana min daukanta har da kashedi akai min akan in bar daukanta ta ina shiga dakina da ita a lokacin.
Don haka nan ma da akace min a yanzu kada in bari kowa ya dauketa banji mamakin hakan ba a wajensu duk da dai mijin nata bai sanda zancen haka ba.
Dakin mahaifiyarsu din babbane ciki daya ba kurya amma dakin yana da girma ga gado ga kujeru da sauran tarkace a dakin kuma har fili ya dan rage saboda girman dakin.
Hjy din tana zaune saman kujera tana muna barka da zuwa tare da lalle marhabin tana fadin yau ina da babban bakuwa a gidan nan ashe ?
Kun iso tun jiya baku kawo min takwara na ganta ba don sunanta aka sakawa yarinyar hannu ta miko ta karbi Amira din na mika mata ita yarinyar kuma bataki ba taje gun kakanta din.
Anty din ta zauna saman kujeran dake gefen hjy din ta hade rai tana bin dakin da kallo sai daga baya mijin nata ya shigo ya kai kasa daidai kafan mahaifiyar nasa ya zauna yana gaida ita.
Zakice antyna bata wajen sai ni dana gaida tsohuwar ta amsa da yauwa sannu yar albarka ke dai tare kuke ne tana tambayan dan nata cikin dubanshi.
Yace hjy yarinyar da maman gwammaja ta samo munane mana baki ganeta bane tace a,a,a ke zo nan kace min jikatace ai itace haka dama aiba saninta nayi ba har kuka wuce masha Allah ubu ko yayi kyau wallahi.
Zakice har lokacin anty bata dakin saida ta bushi iska ta soma fadin hjy ina wuni a wani yanayi a lalace ta fadi hakan kamar me magana dana bayanta.
Cikin mamaki mijin ya kallota sai naga tsohuwar ta girgiza kai tana fadin wa kike da suna ita duniya mutum a sannu yake binta duk yadda kika dauki rayuwa wallahi mutum a sannu yake binta.
Don duniya ta wuce nan nidaine mahaifiyar mijinki don haka kinga dole inci darajan girman hakan a wajenki koda ya gaya maki banda mutuncin hakan a gareshi
Ke mace ce zaki haihu ko ince kinma haifa ai don haka zaki san abinda nake nufi a nan laifine kaga abinda zai cutawa danka kayi magana don Allah ?
Duk kunya ya kama Paapa din a lokacin don shima ido yasa yaga yaya zatayi da mahaifiyar nasa a lokacin sai gashi tayi gaisuwan amma a banzace hjyn ta samu gaisuwan a wajenta din.
Inda hjy taci gaba da fadin idan akwai abinda nayi maki a baya yanzu ya kamata ki dauka ya wuce ko a wajen mu balle ke da kika haifo muna zuria amma ba kizo kowa na marmarunki kizo muna da rainin wayau ba ?
Da alama ran tsohuwar ya gama baci a lokaci don wullakancin da matar dan nata tazo mata dashi wanda nina san zugin mahaifiyartane yake aiki ga hakan gareta .
Daga haka tsohuwar tacigaba da wasa da jikan nata tana mata hausa yarinyar ta zuba mata idanu kawai don bata fahintarta .
Mijin ya yunkura zai bata hakkuri hannu ta daga mai tana fadi kada kace komai Umaru na dauka matarka tayi hankaline a yanzu ashe ba haka bane .
Kuje insha Allahu ka kuka samun macen kwarai da yardan ubangiji don ba zan yarda da wanan shanshanci ba cikin zuri,ata .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI KEBBI STATE
[7/16, 10:11 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
2️⃣4️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15- HAWAYEN KADA🐊 1000.
_Account No._
_*ZAINAB IDRIS MAKAWA*_
2254380105
ZENETH BANK
PHONE NO.
08036959257
Duk wani dan arziki hakan ya faru da uwarshi ba zaiji dadi a rayuwansa ba abinda ya faru tsakanin anty da maigidanta ke nan a ranan don kuwa.
Har muka fito gidan muka shiga mota fada sosai sukayi a tsakanin su inda take cika tana batsewa.
Yana fitowa tace to munafuki naji abinda ake kullawa an kitsama karin aure ko watau dama don aci min mutunci kazo dani shiyasa ka matsa min saina kawo Amira sun ganta ?
Har ana wani sanyani agaba wai inbi duniya a sannu dama da garaje nake bin duniya kome akarama auren mana saime idan ka kara aure ?
Daga inda yake zaune kake jin tas ya dauketa da wani wawan marita dangana da jikin mota nima dake baya saidana zabura na dan kadu.
Yatsa ya nunata dashi yana fadin wallahi ahir dinki uwata zaki zaga a gabana don tayi maki fadan gaskiya ?