Showing 384001 words to 387000 words out of 395027 words

Chapter 129 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

ta fashe dashi lokaci guda a gefe ya dakatar dasu ga maganan da sukeyi din ta soma fadin don Allah Aliyu ka yafewa mum ka yafe muna don Allah ?

Munsan mun aikata ba daidai ba a rayuwanku kaida ummah ka amma baku dubemu da wanan ba a yanzu sai kokari kakeyi kaga ta samu lafiya haka cikin kulawa.

Duk baka dubi irin abinda ta aikata maka a baya ba ka taushe zuciyar ka kana aikata muna alheri tsakani da Allah.

Murmushi yayi kafin ya soma fadin haba sadiya idan na gujeku yau in kamawa a duniya kunefa yan uwan mu najini ko ana so ko ba a so dole a kiramu da yan uwan juna.

Nidai bukatana shine ku zauna lafiya a dakunansu ku rike juna a cikin amana idan kunyi hakan komai da baifi karfina ba nayi maku alkawarin zan maku a duniyan nan.

Sun daiga hjy ta mike zaune daga kwance ido kawai ta zuba masu sai maman dake tare dasune take ta faman tambayanta abinda take so ta kuma koma ta kwanta batace komai ba.

Ku barta batama san da tanayi ba maganin kila ke aiki ya fada sun dan kara magana kafin ya mike ya bar wajen zuwa part din ummah don suyi sallama da juna.

A nan kuma ya dan mata bayanin abinda yake so na kada tabiyewa Abba ta dinga dan kula hjy din tana gewayawa tana dubata tace dama tana da niyar hakan Allah bai maka yaki kuma kace kai zakayi da kanka ai.

Ya basu duk wani abinda zasu bukata nagida dana laluran kanneshi ya sallamesu ya tafi da niyar da safe airport zai nufa kai tsaye basai ya biyo ta gida ba kuma.

Karfe shadaya yana cikin lagos ina pepper a lokacin yasani yasa bai kirani ba sai yamma dana dawo gida ina zaune ina cin abinci ya kira yana fadin in fito gashi kofan mu.

Na zata wasa yake min nasa yar dariya ina fadin kano tayima dadi ai don baka da ranan dawowa yace toki fito din ki gani kona kira Amira ta karbe abinda nazo maki dashi.

Na dai fitane badon na yarda ba a lokacin yana zaune a cikin mota ya fitar da kafa daya a waje daya a cikin mota murmushi na sake na karas ina fadin shine ba sanarwa ?

To ai gani kin ganni yanzu nasan kina exam kodana kira yasa ban fada maki ba nayi mai yaya hanya tare da tambayan mutanen gida ?

Muna tsaye muna magana ina ganin yadda neighbours din mu ke lekowa sai maman sunny ke fadin meram na you new oga bi dis ?

Nayi murmushi ina fadin shine tayi sowa tana kiran sauran suzo suga mijin nawa nan suka taru akan mu suna min sheri wai munyi aure mun boye masu nida antyna ba a fada masu ba ?

Hakkuri ya basu yace aure aka daura ba ayi buki ba zasuji idan zan tare ai gidanshi yaban dubu hamsin in basu haba yasha godiya sosai a wajensu.

Bayan sun tafine yake fada min sako malam ya bashi ya kawo min wai baisan na tafi ba tunda yaga bai tafi ba nasa shi dauko kaya tun daga kano har nan an bashi wahala kaina.

Yasan in ban kira nayi godiya ba malam zai gane bai kawo min sakon ba wani saurayi yasa na kira dan makwantan mu shiya dauki wani kwali zuwa cikin gidan mu dashi nace ya aje a falo.

Mun dan taba hira yace zai tafi wani wajene mukai sallama ya tafi na koma ciki na samu anty Falo zaune yasa na zauna take min andawo nace eeh ya exam din nace Alhamdullahi.

Oga Aliyu ya dawo ashe yanzu na leka naganshi a waje ya dawo anty bai fada min zai dawo ba yau yanzuma yazone ya kawo min sakon kakanshi na nuna mata kwalin tare da mikewa na jawo ta duba muga abinda ke ciki.

Takarda na soma cin karo dashi irin takardan masu nama din nan ina zaro daya muka ashe kilishine mai yawa aka cika kwalin dashi haka.

Munyi mamaki nan anty ke fadin na yarda maryam da akace iyayye suna son dansu ya auri wanda suka sani a arewa .

Ku kuma kice kikai dacen sarakan kwarai ban sani ba ni har yau ga nawa sun kasa sakin jiki dani maryam sun kasa daukana a matsayin sarakuwa matar dansu.

Na zata ko zasu so yabi sama dani sai naga itama ba wani shiri sukeyi da itaba har garamani bamu irin cin mutuncin da sukeyi da ita din.

Wai yanzu wata macece sukace ya aura a cikin dangi kuma gidan yayiwa yabi girma ita kadai tana batawa da kazanta da sauransu .

Kuma again wani aure zasu karawa uncle tace su suka sani nace haba dai anty abin ai yayi yawa me suke nema dashi hakane ?

Kokarin budan kofan da akeyine yasa mu dakatawa mommyce tazo wai tace zatazo ance ta bari yar nata tazo taga har yamma basu zo ba shine ta taso.

Yadda na ganta a yamutsene sai taban tausayi sosai na tashi ina mata sannu da zuwa itako anty fada ta soma tana fadin ba tace kada tazo ba idan ta huta zatazo su ganta.

Maryamu jimin fa yaya ba zanzo inga diyata ba ina da rai taje kasa mai tsarki ta dawo banzo na ganta ba idan mijinki baison nazo gidan ku sai ya mayar min dake gida mana ?

Haba mommy da zuwanki zaki hau min antyna da fada haka da ita da mijinta basu son zuwana nan yanzu bansan abinda yasa suke min haka ba duk nace zanzo sai su hanani .

Yanzu dai zauna na fada na nuna mata wajen zama bayanta zauna nashiga na kawo mata abinsha tare da sauran abincin dana soyo din ban taba ba na kawo mata duk na tara a gabanta.

Kin gani ba ina can ina zan samu wanan inci haka mummy haba mummy yar ta fada uwar tace ki bari in fadi gaskiya mana ungo maryam zan samu irin wanan din ?

Dariya taban nakai zaine ina fadin yanzu kice ki huta sai a gaisa da haka naci karfinsu suka daina fadan.

Mummy din bata da dadi fada da sababi yayi mata yawa hat yar da take ji da ita basu shan innuwa daya da ita wani lokaci.

Dakin hajja yabi na gyara gudun tace a dakina zata sauka don Allah ya gani nayi alkawarin ba zan kara yarda in hada daki da itaba kuma again.

Ina magariba tunda na shige ban fito ba don ban iya sauraren rigimansu a lokacin don naji ra soma fadin dama ciki kike dashi ban sani ba sariya ko kun fara zargina da maitane dake da mijinki ?

Dariya ya kumeni na shige daki na barsu ban sake fitowa ba Amira a dakin ta sameni don anty ta dora mata kwalin kilishin ta kawo min daki.

Yaron daya kawo min na dibarwa shida maman teema muka fita nida Amira muka kai masu tunda muka dawo kuma muna dakina tana kallo ni kuma ina waya.

Saudatce ta kirani tana fada min malama tazo wai bata san na wuce ba tazo min godiya muka gaisa a waya da ita tana min irin nasihan datake min din koda yaushe.

Exam yayi dadi sosai mun kusa kammalawa yayin da yake ta shirin tarewa a asirce ba tare dana sani ba don yace ba wani shirin da zanyi a bangarena.

Shi mata ya nema ita kadai za a kawo mashi donshine ma bai fada min shirin da yakeyi a bangarenshi din ban kuma jin komai a wurin kowa tunda bawani na kusa dashi da nake tare dashi balle inji.

Lefene daya hada za a kai gidan mu mahaifiyarshi ta gaiyato yan uwansa da suzo su gani kafin akai din saida ta shawarci matar malam yaya zatayi da yaya hanne ?

Matar malam tace ta sanar da ita kawai zancen lefen tazo ta gani yadda yan uwa sukazo don rashin fadin kuma laifine a wajenta.

Donshine ta daga waya ta kira yan uwan nata a gaban matan yan uwan nata tana fada mata yaya ya gama hada lefenshi da za akai don tarewan nasu ya kusa.

Hauwa ni zaki kira kice inzo gidanki ganin lefen Aliyu banci mutuncin da za a dauko kefen a kawo min nan gidana ba ingani lefen me can lefen banza da wofi har me kika dauki kanki da dan nakine wai ?

Yaya kiyi hakkuri malam ne yabada umurnin hakan a je a nan kowa yazo ya gani ya saka albarka to ba zanzo malam ubane ne ko me ?

Allah baki hakkuri yaya bansan raki zai baci ba haka kan zancen har me kika dauki kankine yanzu ke hauwa kibar ganin nace a hada yaran nan aure a tsakaninki har ki dauka kimata da darajana ya ragune a yanzu fa ?

Ina nan hannena da kika sani kedake bin malam da cewarshi kije can kita binsu suna kara dulmiyar dake cikin duhu jin fadan yasa ta kashe wayan don matansu dake zaune a falon nata.

Nan suka soma fadin albarkacin bakinsu sukayi shirin komawa gida tare da saka ranan da za azo akai kayan gidan mu inda akace za a aikawa gidan mu su sanda zuwansu din a ranan jumma,a kinsan malam bahaushe yasan daraja da albarkan da ranan jumma,a ya kumsa duk da a yanzu boko yasa ana amfani da ranan asabar asabar kuma ba sa a ko alheri a cikinsa.

Da zasu tafi sun biya suka gaida hjy Naito wace a yanzu ta koma ba eeh ba a,a saidai ta zauna kurum tana bin mutane da ido ba zai wuce magana daya zuwa ukku ba abinda zata iya furtawa mutum.

Ya Allah yasa muyi kyakyawan karshe a rayuwan mu yasa mufi karfin zuciyarmu mu mutu muna masu imani da ubangiji.

Ita bata mutu ba ita bata cikin masu morewa numfashinsu hakana Allah ubangiji ya barta a yanzu ita dai gata nan kawai ba a magana don bata cikin lissafi.

Malamace washegari ta samu innan mu take fada mata zancen zuwan nasu a asirce don a fara shiri don ance sai ana gobe za azo zasu sanarwa gidan namu don shine tazo ta sanarwa innan namu.

Anty fati innan ta kira da sahura ta sanar dasu zuwan bakin inda su kuma suka shiga lissafin abinda zasuyi na taron bakin kamar yadda yake ga al,adan bahaushe a zamanance.

Anty fati dince ta kirani nida anty take sanar muna da abindake faruwa nace zan turo masu da kudi wajen saudat suyi abinda ya dace ayi wanda ba za aji kunya ba.

Sunyi din kuwa don sun shiryawa zuwan sosai sunyi nasu karyan da suke ganin burgewane suma a wajensu balle abu da anty fati uwayen rigima.

Gulman da yai yawane yasa hjy hanne yanke shawaran zuwa ko banza zata taga gidan banzan da dan yar uwar nata ya kai kanshi da har ya iya barin yarta.

A bangarena nace a fadawa salma da yanzu nake kokarin mu koma kamar farko duk da a bangareta ta kasa sake jiki dani har yanzu din.

Nasan halin abina shiyasa banyi fushi ba nake biye da ita hakana abin duniya me wucewane ai balle nida Allah ya dubi kukana yayi min sakaya da mutum irin Aliyu.

Ga ilimin da sanadin hakan ya haifar min wanda a ko ina zan iya takawa insa kafana a cikin yan boko wanda yai karatu a unilag ai karshen ilimin dan Nageria ke nan dai a kasan nan.

Tunda taje kowa ke mamakin zuwan hjy hanne din don sunsan bata zuwa don alheri dole akwai wani abindata shirya akan hakan.

Tare aka fito da ita tana takama da isa a motar mijinta data dauko donta burge mutane dashi saidai tunda aka fara fito da kayan ta bata rai da kyar ta iya budan baki tana fadin.

Yanzu shi wanan uban kayan daya hada duk wacan diyan matsiyatan zai kaiwasu kamar wanda ya samu yar gidan minister ko wani basarake can ?

Ba yar gidan minister bane ba kuma gidan basarake ba gidan dai yan muntunci da kima za akai mai daki ai shiyasa inda ke masa yoyo.

Nan yaga sun dace dashi kuma yake son abinshi don yakai wanan ai ko cewa aikai ya karo karawa zaiyi rabu da namiji idan yana son abinsa.

Matar malam babban maman su yusuf itace ta fadi hakan ta bata amsa take fadin kune ai masu daurewa karya gindi dama ai ?

Ba karya a zancen nan hjy inda yaro ke so ai ka biye mashi yanzu a zauna lafiya ba zaku gane bane itama ai yarinyar ai tasan karan banine yakawota nan din din don ruwa ba sa an kwando bane ?

Yanzu waya saura auren jari a shigo a dameka da bani bani kowa inda zai huta yake kallo ai har yanzu akwai yan mutunci irin baya wa yanda suka san darajan kansu duk irin wanan abin sun daukeshi a matsayin riya su.

Lokacin data shigo daga motan hjy hauwa sai wani mota na maigidan don haka bayantane motocin da zasu shiga suka iso kofan gidan.

Saida aka fitone taga motocin da suka cunawa nata da komai ta hade rai bata samu yadda taso ba a nan din.

A kofan gidan namu ma da motocin suka tsaya saida ta rainawa kowa wayau a wajen tana kallon wanan dan gidan kaskanttacene za a kawo wanan uban kayan haka ?

Unguwa ya dauka akaita shiga da kayan zuwa ciki su anty fati suna karba da guda sai kallon hankada takewa mutane kujera ta zauna ta hakince a sama.

Ta soma fadin to ga kayanan mun kawo munsan me muka saka don kada a kwashe a rabawa dangi muzo bamuga amarya dasu ba a jikinta .

Allah sarki hjy bamu da wanan rayuwan a nan don ko wanda kuka kawo na mungani muna so har sunyi kura ba wanda ya taba har yau kinsan yar tamu bama irin kayan nan take sakawa ba ita don haihuwan gidan nance amma tashin lagos yar boko kuma wayayya ce ita.

Anty fati take fadin hakan a cikin raha aka dara tare da saka guda aka shiga budan kayan ba wanda ya kara bita kansu ta mike tana fadin su tafu tunda an aje kayan a bari ayita gani ana guda.

Ai dole muyi guda gida nawa kayan nan ya wuce yazo gidan mu duk gidajen nan da wanda suka fisu suna son komarsu ya kamo mutum irin danku ai ?

Manyan robobi da aka shirya masu na tukwaice anty fati suka soma fitowa dashi ana jida zuwa wajen motocinsu ana direwa roba har goma da abin sha na alfarama suka rakasu har waje akai sallama da juna kafin su dawo cikin gidan.

Inda a gabansu ba wanda ya bude kayan balle tace ana zumudi anga banza sai aka nuna mata wayewa inda yan unguwa da suka santa suka soma fadin halinta da akidarta a wajen.

Suna barin kofan mu taso wucewa gida amma kuma kada a fahinci hakan dole ta hakkura aka koma gidan yar uwar nata da kayan don akai masu sako.

Itako mahaifiyarshi sai cewa tayi suka wahal da kansu haka wanan abu ai yayi yawa mana kuko ba yawa yaba kyauta tukwici dama aini na ji dadin da suka nuna muna su yan girmane sunsan mutuncin baki da iya karramasu a mutunce ko gidan wani mai kudin ai yakar ke nan dai ba aure ba har roba haka manya tana budewa take fadin hakan daya daga cikin yar uwar mahaifiyan ummah din datazo take fadin hakan.

Saidata budene kuma sukasha mamaki yadda karamin gidan da ake fadi sukayi wanan abin ta kalla taja tsuki tana fadin an dai dafa kifi da ruwansa kawai a nan a ina kudin wanan karyan ya fito wanan gidan ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[11/8, 8:59 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊1️⃣0️⃣0️⃣🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login