Showing 390001 words to 393000 words out of 395027 words
Chapter 131 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
da dilka muna wajen ranan har dare a cikin gajiya.
Washegari duk da mama na asibiti akai kamu wanda yayi kyau sosai fiye da yadda na zata ina cewa banda mutane sai gashi naga wuri ya cika makil da jama,an arzikin mu.
Mum wai ashe da gaske bukin nan kinga photon kamunsu an saka a median yau akai kamu ashe fadila ke fadin hakan wa mahaifiyarsu daga inda take zaune.
Bar yan iska dazun matar sani ta bugo min wai basu ganni ba a wajen kamu naci mata mutuncin karta kawo min rainin wayau ?
Ki barsu kawai mum tunda ya zabi wacan yarinyar sama dani don gaskiya ba zan zauna da yar tallaka irin ta muna kishi ba ?
Zan barsu amma zamu saka kafan wando daya dasu a garin nan dagashi har uwarshi sai auren nan ya koma masu ciki dani suke wasa ke nan basu san hanne bane jin sunan sukeyi.
Sun dauka na bar zancenne kawai ba zan dauki mataki a kansu bane ai ita hauwa ta sani ta kuma san hali tasan da shirin da nakeyiwa zancen.
Ko yanzu din kuwa idan naso tarwatsa auren nan zan iya don gidansu yarinyar zanje in lalata komai muga ta tsiya kuma dan iskan yaro mai kama da aljanni kawai.
A,a mum basai kinyi haka ba ki barshi kawai don Allah tunda kowa yasan yace ba zai aureni ba nima yanzu zancen ya fita min rai .
Kallon yar tayi tana jan tsuki ta mayar da hankalinta kan tv dake aiki kamar tana bin shirin da akeyi a cikin tv a lokacin amma zuciyarta ba a nan yake ba gaskiya.
Tabar zancen akan da safe zatayiwa gidan mu diran mikiya ta lalata duk wani tsari da shirin da akayiwa bukin sai kuma Allah ya aiko mata da nashi tsarin.
Don da asuba din nan suka kwashi mijinta zuwa asibiti ciwon sugar shi ya tashi wanan ya dakatar da ita daga shirin da tayi niyar yi din a lokacin Allah ke nan.
Anyi komai da aka tsara din dinner dai ya kyau sosai ya samu halartan mutane sosai anci ansha a wajen washegari da zan tarene akai walima na mata zallah a kofan gidan mu inda gwargwado matan unguwa sunyiwa inna kara.
Anyi dace an sallamo mama daga asibitin kwanata daya da wuni suka dawo gida bayan haukan da yaya murja tasoyiwa mutane yaya ibrahim ya taka mata burki akan hakan dole taja baki tayi shiru don bai raga mata ko kadan yadda taga yayi fada da yan iska yaci tauri basu dibi komai a jikinshi ba tashiga tsoronshi tun lokacin dawowanshi sabo gida.
Karfe hudu motoci na kofan gidan mu aka kwasa zuwa gidan iyayyenshi kafin namu gidan da zamu zauna.
Gidan cike yake da jama,ansu haka muka ratsa zuwa dakin mahaifiyar nashi akai addu,a da nasihohi itace tace a kaini dakin hjy ban zata uwargidanta take nufi ba sai da muka shiga tana zaune saman kujera an mata kwaliya ba zaki gane laluranta ba farat daya ?
Matar malam ke fadin hjy ga sarakuwarki hauwa tace mu kawo maki sai lokacin na fahinci inda muka zo tana jin hakan ta mike tsaye duk idonsu na kanta ta nufoni ta na sa hannu ta bude fuskana dake rufe.
Sai kuma ta sake mayafin da sauri ta juya ta koma ta zauna a inda ta tashi kowa na kallon ikon Allah dai dakin yayi tsit baki masu addu,a ba hjy matar malam ta fada ?
Hannu biyu ta hade a waje daya da kyat ta iya budan baki ta furta a zauna lafiya muryan yarta sadiya naji tana fadin ai nasu yazo daya da ita don ko ranan dataje gaisheta asibiti haka ta riketa tana cewa diyantane.
Banyi aune ba ina tunane naji sun kwashe da dariya wai ashe cewa tayi Aliyu wayau ya samu mata mai kyau mai hankali ya faye wayau shi.
Shine ake dariya aka mike muka koma dakin mahaifiyar nashi kafin wanda zamu tafi dasu suyi muna rakiya zuwan gidan su fito muka shiga mota aka tafi.
Gidane na zamani mai hawa biyu ina dai jin yadda ake yabon gidan da yake idona yana rufe ba zance ga kan gidan ba lokacin.
Muka fita ina rike a hannun gwaggo Fati takamani zuwa ciki aka tsaya nan falo akai addu,a tare da fatan alheri kafin suka mikeni kuma zuwa inda dakuna suke a bene.
Ina ji ina gani haka aka watse aka barni dagani sai halina da zan nuna sabon rayuwan dana tsunta a yanzu saida ya rage daga mu sai kawayen dana samu sabbi ta dalilin auren nan suka gama shirmensu suka tafi don ango yaki shigowa kudin sallama ya aiko masu da cewa su fito a mayar dasu gidajensu yana son ya shigo ya huta.
Aliyu kam da ace ya fito gidan mulki da natarw dashi sunsha iko da doka iri iri don tun wajen dinner yake cewa shi basuyi mashi ba sun faye rawan kai.
Bai shigo ba sai da ya rurufe ko ina shiko irin rakiyan nan na abokai bai bari anyi mashi ba sai gashi ya shigo min da sallamanshi.
Ina kwance don na gaji da zama a lokacin na dan kwanta na dunkule saida ya shigone na dan dago ina amsa mashi sallaman.
Yake fadin sorry don Allah na barki ke kadai a gidan ko ina can gida yau ciwon mama ya tashi kuma shine muke can wajenta.
Yana magana yana kokarin rage babban rigan dake jikinshi nasan din bai saba bane ya matsu dashi a jikin gefe ya aje yana zama tare da bissimillah a gefen gadon .
Nagaji wallahi har wani irin kasala da barci nake jin yana dibana kona dan watsa ruwa naji dadin barcinne amma dai ina zuwa ya fada ya mike yana cire aninin rigan daya saura jikinshi din lokacin.
Ya dan jima aciki kafin ya fito yana fadin tashi kiyi alwala muyi sallah godiya ga ubangiji daya nuna muna wanan ranan a garemu.
Sai lokacin nayi magana ina fadin da alwalana yanzu haka ban dade da nayisa ba kallon da yayi min yasa na dora da fadin ban kwanciya ba tare da alwala ba tunda naji fa,idan hakan .
Kiyi dabara sunnace mai kyau ga musulmi kwanciya da alwala don kamar riga kafice a wurin dan adam ya fada yana gyara kafet din sallah da kawayen nawa sukai sallah dashi kafinsu tafi.
Mikewa nayi na biyoshi muka tayar da sallah ina bayanshi ya gama ya jima yana addu,a da sai su suka iya irinsa a bakinsu don tasowa a cikin ta kafin ya dan juyo gareni yana ambatan sunana da maryam ?
Hakan yasa na dago inda nake zaune a takure ina kallonshi ya soma fadin kin gaji ko gaki har kin rame na gani meke damunki haka kin sauya kwana biyu ?
A hankali na dago kai na dan dubeshi inda yake zaune nayi dan murmushi ina fadim gajiyace kawai ba abindake damuna .
Akwai gajiya amma kuma akwai wani abinda kike tunane nasan bai wuce yadda abin nan yazo muna ba ni sai na dauka kowa da irin yadda kaddaransa kezo mashi a rayuwa.
Mu dauka hakan shine alherinmu ga baki dayan mu daga haduwan mu har zuwa auren mu yau gaki gidana wanan wani mukadarne na ubangiji subbanahu wata,ala ga bayinsa da yake so.
Maryam haduwanmu kaddararllahuce daga ubangijin mu daya tsamemu a nan gaban iyayyenmu ya hadamu a can wata nahiyar ta daban ya kaddara aure bayan hakan kuma.
Zanso ki kasance min mai amana da taimakona bisa harkokin rayuwa ni mutum ne mai jama,a da kuma sanin darajansu don ni dan dangine gaba da bayana haka kema hakan to murike yan uwa da amana musosu irin son da suke muna saikin kula sosai a gidan nan yana cikin abinda ya kara kwantar min da hankali dake.
Na zaboki a matsayin abokiyar rayuwata mai kula da duk wasu al,amuran rayuwana a bangeren gida da waje Allah ya baki ilimin sani na addani dana boko da zaki iya saurin fahintar abu lokaci daya ina fada maki hakanne badon baki sani ba nasan kin sani amma ina son ki kara kula yadda kika gani a office din mu nake fama hakama a gida nake fama da yan uwa don sai ka natsu kasa ido hikima da basira zaka gano mai bibiyan sawunka.
Taso muje mu danci abu falo kafin mu kwanta da sannu zaki fahinci mijinki KADANE SHI WANDA HAWAYENSHI KWANTONE.
Mun samu an shirya dinning din ba wani abinci bane mai nauyi da zakaci yayima illa a lolacin namane irin nako wace amarya a daren farkonta sai Fresh Milk da gani bana kasan nan bane ?
Shi muka danci muka kora kafin ya mike yana waya ya zagoyo inda nake yana kamo hannuna muka koma cikin daki banda fargaban komai akanshi don nasan iya inda zai tsaya a zanceshi.
Saidai abin yasha banban a ranan da wasan da muka saba a tsakanin mu don kuwa saidai labarin yakai a ranan na zama mace na tashi a sahun yan mata masu budurci duk tsawon shekarun da nayi ina boyon wanan abin tare da tanadi cikin dan lokaci Aliyu ya daukeshi lokaci guda gareni .
Sai faman addu,a yake zubawa a bakinshi lokacin daya fahinci ina nan a macena da Allah ya halicceni tausayi da kaunata suka shigeshi lokaci daya.
Ba don komai ba sai kallon dashi kanshi a baya yasha min na nadade da wuce wanan wajen amma da muke so closed dashi ya fara fahintar ko aboki namiji kwakwara bandashi tsayayye na nunawa ya soma zargin ba haka nake ba wayence kadai a idanu min.
Bayan ya fitone ya matsa min da natashi muje bandaki kafin jikina yayi min tsami naso ki a lokacin amma ya dan lalasheni daba tare ai zamu shiga ba hakan yasa na mike naje na samu ya hada min ruwa masu zafi na shiga na zauna a ciki.
Bayan dan lokaci nayi wankan tsarki nafito na sameshi yana sallah kuma nikan kwanciya nayi a lokacin ina mai rufe idanuwana tare da tuno yadda abubuwa suka faru cikin dan kankanin lokaci.
Idan ka duba kayi nazari zaka fahinci wanan rayuwan gaba daya na dan lokacine ga bawa ba komai a cikinta sai rudani da shagala idan ka biyewa hakan ?
Yau da ace irin fata da hasashen da nataso acikinsa wanda mama ke min a kullum kan karatun dana nace nida iyayyena sai nayi na shagala da shedanun duniya na biye masu da a wanan ranan naji kunyar .
Kunya daban taba jin irinsa ba ga abokin rayuna da mazaman amana zama na mutu ka raba dake dashi zaman da za dubi dan uwa a cikin mutunci har abada koda mai sunanshi aka gani.
Tun bayan sallah asuba da muka koma muka kwanta bansada rana yayi haka ba har sha biyun rana saura kadan lokacin koshi fitsari ya falko dani na bude ido na samu baya saman gadon a lokacin .
Tashi nayi a hankali ina bin dakin da kallo don a jiya gaskiya ba zance ga yadda dakin yake ba don mutane da akai yawa gefen daya kwanta na duba dukka wayoyinshi suna a wajen aje.
Hakan yasa nagane ba nisa yaje ba ashe yayi wanka yana dakinshi yana shiryawa wanan dakin da muka kwana ciki shine a matsayin nawa dakin a gidan.
Tashi nayi na lalaba zuwa bandaki inda na kara gasa jikina gani sa wanka na fito na zauna ina shiryawa sai gashi ya shigo ya sanya riga da yar t,shirt da wandon jeans duka da gani sabbine kuma masu tsadan gaske.
Kin falka ashe yanzu nake zancen in tayar dake mu karya tun dazun aka aiko da abinci daga gidan ummah.
Amira tazo ta samu kina barci nima ban fito ba suka tafi banso hakan ba nace haba dai da ummah basu wahal da kansu ba zan iya daurewa nayi abin karyawa ai.
Yinin ranan bai fita ba haka nayi mamaki daba wanda yazo gidab ga al,ada nasan duk aka kai amarya waahegari yan uwa da abokan arziki suna tururuwan zuwa gidan amarya koda kuwa bazawarace ?
Abinda ban sani ba suna zuwa din amma gidanne a rufe anbawa maigadi umurni kada ya bari kowa ya shigo.
Don maigida naciki yana hutawa da iyalinshi nayi mamakin hakan ganin har dare banji duriyan su maman teema da zasu koma a ranan ba.
Gashi wayata da nashi agabana ya kashe ya fita dasu ban kuma iya tambayanshi dalilin hakan dole na zura ido har dare muna cin abincin darene lokacin nake fadin matan nan ko zasu kara kwanane wai ?
Sun ce idan zasu tafi zasu biyo tanan munyi sallama gashi najisu shiru nake fada cikin damuwa a gefenshi.
Wasu mutane ke nan ya juyo yana tambayana nace matan da suka zo daga lagos mana yau ya kamata su koma ai ?
Tun karfe biyu suka bar garin nan ai cikon mamaki na dubeshi yace koda sunzo aiba zasu ganki ba don ba wanda zai shigo gidan nan yanzu sai mun huta.
Wani kallo nake mashi cikin mamaki yace haka kawai a zo a hana mutane hutawa nace duk wanda yazo a fada mai bamu garin mun yi tafiya.
Wanan yasa ba kiga kowa ba gidan nan yau saida dare nake son shiga in duba jikin hjy hakan daya fadi yasa na fahinci abinda yasa su Saudat basu zo ba ashe ?
Ko kuma din sunzo suma an fada masu cewa bani gari sun koma ga kuma wayana a kashe saisu zata gaskiyane din bamu nan.
Duk daba tare nake dasu ba a ranan naji kewan yan uwa da gida sosai mu saman ma Amira dako yaushe muke tare da ita tunda yarinyar ta bude ido dani tayi wayau a gidansu gashi yau aure ya rabamu.
Yana da wuya iyayyenta su barmin ita mu zauna tare tunda zasuga capacity dina bai kai na rika masu yarsu ba ai ga yaya ibrahim din mu yaban yarshi ta fari tun zuwana da aka daura aure amma yan dakinsu sun nuna basu yarda hakan ba.
Nima ba zanso in dauka badin sai naga yadda zamana a gidan zai tafi wanan yasa ban kara yin zancen da kowa ba kuma.
Matukar mama na raye ba zata taba bari muyi zumunci mai tsabata ba tsakanin mu da yan uwanmu tunda har gobe halinta na sheri da hassada akan mu yana nan tanayi kuma.
Don kuwa ta koma irin datayi min a baya kan Saudatu inda taje gidan yaron dake neman Saudat din takai suka yaron yazo ya fadawa Saudat din.
Hali ba daya ba don saudat ta zauna a cikin gida saida tafito tsakar gida take fadin ancewa Nasir ya rabu dani mu yan asirce mazane duk namijin dayazo wajen mu saiya koma ko zancen uwarshi baya ji a kan mu.
Ni me zanyi da Nasir da za aje akushe mu wajn mamasa anyiwa banza donni ina da mijina da zan aura ba Nasir dake ci a kwanon uwarsa ba har yanzu.
Shike nan mutum baida aiki sai yawon sheri duk unguwa ansani da angamu a dinga muna sheri ana fadin ga uwarku can me yawon munafunci duk da bata da lafiya kabari kusa bata fasa yawin gulma ba .
Saudi dani kikeyi dama ashe mama ta fito ta tsaya a kofa tana tambaya tace mama na ambaci sunan ki wanda yaje gidansu Nasir yakai suka dashi nakeyi in kuma kece to dake nayi.
Nasir shike sona bani ke sonshi ba nace ya rabu dani don gudun haka yaki to yanzu ai ya rabu dani don dole ni koda naje aiba cewa nayi ya rabu dake ba tambaya nayi inda gaske yakeyi iyayyensa sun sani ?
Inna ta leko a lokacin tayiwa saudat din tsaya tasa ta daga daga wajen suka bar mama tana borin kunya akan zancen daya fito don bata zaci haka zai koma ba.
Da yaya sahura ta dawo matar yaya ibrahim ta fada mata shine ta samesu a daki tana basu hakkuri anyi haka da kwana biyu sukazo lagos wajen bukin yayyemu na gama karatu na.
Fuskana ya dan hura na sauke ajiyan zuciya yake fadin tunanen me kikeyi hakane na danyi murmushi ina fadin draman gidan mu nake tunane.
Fadan saudat da mama data taje gidan saurayin saudat takai suka yace kuma again bayan naki ta kara wani ke nan zata fasane na bashi amsa.
Na fada maki saudat nayi mata miji Abdul zan hadasu aure tana kammala karatu shikuma yayi nisa da aiki a lokacin .
Abdul dai naka yace kwarai kuwa ko bai maki bane nace a,a