Showing 252001 words to 255000 words out of 395027 words

Chapter 85 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

dan zauna sun taba dan magana daya shafi office din kafin yayi mai sallama ya tafi.

Shima ya mike da niyar shiga daki nan Abdul din ke fadin abinci fa yallabai ga abinci nan data girka maka kafinta tafi tace na tabatar da kaci abincin don Allah ?

You means maryam ta tsaya ta girka wani abincin kuma again yace hakane yallabai da zata tafi kuma tace in tabbata kaci kasha maganin data kawo maka kafin ka kwanta.

Ya danyi shiru kamar zai juya ya wuce sai kuma ya hari dining din ya zauna da sauri Abdul din ya nufi wajen ya soma bude kayan abincin yana fadin.

Wanan ferfesune wanan kuma tuwone na semo da miyar yauki ta girka wani zan zuba a ciki yallabai ?

Zuba min tuwon kadan yace don yana marmarin tuwon a lokacin saidai shi ba ko wani tuwo kuma yake ciba haka zai dai gwada ya gani ko bakinsa zaiyi dan galmi a lokacin.

Bai zuba mashi da yawa ba don yasan koya zubama bayaci tunda bako wani abinci yake ciba shi haka halinsa yake bai wani damu da abinci ba a rayuwanshi.

Abdul din yana zuba mai har ruwan wankin hannu ya aje ya bar wajen daki ya koma ya dauko magani ya fito ya samu waje saman kujerun falon gefe daya ya zauna yana satan kallon ubangidan nasa dake cin abinci.

Yazata loma daya ko biyu zaiga ya mike amma sai yaga sabanin hakan saida ya kusa tashi da abincin da aka zuba mashi din ya dago yana fadin.

Abdul zoga zuba min wanan in hada dashi ya taso da sauri zuwa gareshi ya zuba mai inda yaga yasha ruwan miyar sosai fiye da naman ya mike zuwa daki bayanshi yabi yana fadin.

Yallabai maganin gashi ance da yamma kafin ka kwanta asha tace in tuna maka hakan yace kawo min daki nasha kafin na kwanta.

Saida yasha ya kwanta sau daya ya kewaya a cikin dare bai kara ba ranan ya samu barci sosai sai asubahi ya tashi daga barcin.

Washegari da safe ban samu zuwa ba school na tafi haka kuma ban kira waya ba don bansan ko zan samu ya daga wayan ba a lokacin tunda safiyane sosai ina shiga school wayan innan mu yana shigo min na dauka muka gaisa da ita.

San nan ta soma fadin jiya Saudat take fada min ko waye ta haihu kince muje muyi barka nan na soma mata bayani a gurguje yadda zata gane .

Saida nagama take fadin to amma yarinya baki ganin basu san mu ba kar muje sai mun tsaya masu dogon bayanin da baida asali ko tushe fa.

To inna ku barshi dama dai nace kujene don shima yana min kokari a nan shiya amma a barshi ba sai anje din ba.

Zan dai duba mu gani idan zuwan ya dace to in zaku tafi inna bari na turo maku da kudin mota sai ku dauki drop zuwa da dawowa don Allah kada ku wahala tunda akwai nisa.

Bari dai mugani din idan zamu tafi sai a kiraki a fada maki ki kara muna kwatanceb gidan kada muje ayi shirme kinsan halin saudat ai mukayi sallama na kashe wayan .

Class nashiga ban sanu fitowa ba sai wajajen sallah azahar gashi in zamu shiga muna rufe wayan mune don kada kira ya shigo ya dame mu.

Ina kunna wayana sako suna shigo min na fara duba sakone daga saudat sai kuma sakon MTN da sukan shigowa mutun su cika mai waya.

Mun kiraki yaya wayanki a rufe dama inna ce take son magana dake sakon da saudat ta turo min ke nan a lokacin.

A gurguje na nemi abinda na dan sakawa cikina na koma class ban kira ba a lokacin sai bayan na firone na koma gida wayana ya dauki ringing ina bayi nafito na samu miscall din shi.

Sai lokacin zancen alkawarin da nayiwa Abdul din ya fado min a rai haka kuma duk wunin ranan ban kira na tambayi jikinshi ba ?

Nayi hakanne kuma da ganga zance duk da na dan shagala kada suga zakewa na a kanshi don zancen ina ya sare min gwiwa har nake Allah Allah kada su tafi din ma gidan.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[9/25, 9:06 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊 7️⃣7️⃣ 🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Naji nauyi da kunya da yakira ban kaiga kiranshi na tambayi lafiyanshi ba a wunin ranan ance tabarman kunya da hauka ake nadeta don ko daurewa nayi ina sallama tare da fadin ya katfin jiki ?

Don ko ai nayi mai abinda zan iya in nuna kulawata a gareshi lokacin nayi iya kokarin da zan iya in nuna caring din na akanshi tunda ba kudi zan bashi ko wani abin kudin ba da zai yaba bayan wanan abinda nayi din na nuna kula a kanshi.

Dr maryam sai kibar percent dinki kuma haka ba kula bayan kece likitan nawa a yanzu tun safe bansha magani ba kuma banci abinci ba fa.

Dan dariya abinda ya fada ya bani har nake sake murmushi a bayane ta yadda yake ji na furta wanan kan ba aikina bane aikin likitocine hakan ni dai na taimakane kada mu rasa mai jinyan namu ai.

Thanks kinyi kokari kwarai da gaske na kuma gode sosai don jiya naci abinci kuma na samu barci the only things shine ban samu wanan gatan ba a yau kuma ina tsoron kada ciwon ya dawo min kuma don rashin kulan da ban samu ba din.

Haba dai bayan duk kulan da mutanen gidanka ke baka ai baka bukatan wani kula kuma bayan wanan din da suke maka a kullum matsala kawai matarka da bata a kusa dakai a yanzu shine matsalan sai naji yace Allah ko ?

Wanan kike gani matsalata a yanzu ko tana nan aiba zata iya min irin wanan jinyar dana samu ba a wurin ku jiya din ga ciwo kamar an zare min shi kaf a jikina nake ji yanzu ?

Allah ke nan shi yayi wanan ikon nasa a hakan yayi ciwo da magani a lokaci guda Allah maganin matan nan yana da matukar kyau sosai naji mutane suna yaba maganinta shiyasa nayi shawaran zuwa na karbo ma a gwada a gani amma a cikin tsoro na baka shi jiya din.

Tsoron me kuma ya fada cikin mamaki nace kasan mutane da yawa suna tsoron maganin gargajiya irin haka ba kowane kuma zai yarda haka kawai a dauko magani ace yasha ba ya yarda yasha din irin da kayi.

Narasa way out ne da naji yadda kake magana a lokacin shine nace bari kawai naje na karbo in gwada kai maka ko Allah zaisa a dace sai gashi kasha banyi hasaran kudina dana bayar ba.

Au maganin ma ashe sai an biya ake karba tona gode ya fada a bangareshi sai banji dadin furta hakan da nayi ba a lokacin nace.

Aiba sai kayi min godiya ba sir don kai min abinda yafi hakan nima a rayuwana har yanzu kuma ina cin moriya daga gareka nice da godiya ai yace me nayi maki hakan ?

Kafin nayi magana naji muryan sectery din nan biodu yana fadin sir ga takardun an akawo an gama hada komai yanzu turawa ya rage.

Lokacin na fahinci a inda yake haka na nufin yana office ke nan alokacin ranan inko hakane karfin hali kawai yayi ya fito office din a lokacin.

Sir kana office ke nan don naji muryan Biodun a kusa dakai ina office madam ta yaya zan zauna gida tunda naji sauki.

Hakane Allah ya sauwaka kasha maganin don Allah naji ya dan furzo da iska a bakinsa kafin yace ai baki bani ba yau ko don ni bansan yadda zansha ba ai ?

Kafin nayi magana naji ya saki zancen yana fadin kece kika tura yan gidan ku barka gidan mu wajen hjyn mu ?

Sai lokacin na tuna da ai bai fada min zancen haihuwan ba yanzu me zance saidai in nade kunyata in fadi gaskiya na dake ina fadin .

Barka kuma ko dai gaida ummah da jiki shine barka ashe sun gane gidan su tafi nice na fada masu suje su gaida ummah din don kace min bata da lafiya ranan kana kano.

Waya fada maki gidan mu maryam ?

Kanoce fa ta yaya ba zan sani ba nida garina sai naji yace ashe ke nan kina bibiyata har kina bincke a kaina daga nan ban sani ba ?

Na dan ja iska a bakina ina ina fadin in ma har hakan bincikene ai kai ka fara hakan a kaina na bashi amsa da hakan.

Ba gaskiya bane don ko rantsuwa zanyi ban taba sanin gidan ku ba maryam balle insan wani abu a kanki ba wallahi maryam ?

Amma nayi mamakin yadda kika san zancen daya shafi rayuwana a kano ?

Allah ne ya nufa inji daka fada min bata da lafiya kana kano dubota na tambaya don yan gidan mu suje su duba ta su gaida ita.

Ok indai hakane kin kyauta nagode da hakan su waye sukaje don ummah tace min kamar har da mahaifiyar ku a ciki ko ?

Su dai biyar ne inshort da yara biyu yan kanana sai su ukku manya tace so kika basu wahala tun daga unguwarku zuwa gidan mu ko ?

Ba wahala bane alherinka garemune na mayar maka ta hanyar hakan donshi kadai zan ma in saka abinda kai min na alheri tunda banda abinda zan baka a rayuwana.

Murmushi naji yayi yana fadin alherin me kuma maryam don mutum yayima alheri sai kace saika rama da wani abin a gareshi ?

Shine tukwicin godiya a isalama kada ka matsawa kanka da abinda baka dashi amma ka bada koyi da addinin ka sai naji tace

Hakane tabbas amma haka kike gani a wajenki kece kike da abin bani kuwa maryam gashi kuma kin bani din ko a yanzu .

All this while baki san me hakan ke nufi ba ke nan a tsakanin mu ai mutunci yafi komai daraja a wajen dan adam an gode da kuwala sosai ?

Pardon sir ban fahinceka ba da wanan zancen go through it zaki gane me nake nufi nima sai jiya na yarda da abinda zuciyana yake zargi a kanki maryam.

Dif ya kashe wayan ina mayar da numfashi don abinda kunnuwa suka dauko lokacin daga wayan ta yaya zan fasara kalaminshi a yanzu ?

Ni kadaice a dakin don haka ban san iya lokacin dana dauka ina auna zancen ba dan yadda zan fassara wanan kalamin nashi a kasan zuciyana abune da ba zan iya cewa ga manufarshi na fadan hakan gareni ba yanzu.

A daidai lokacin da wayana yashiga kara alaman kira ya shigo min kuma again hakan ya katse min zancen zucin da nakeyi a kanshi lokacin.

Saudat ce takirani a lokacin na dauka take fadin yayan mu mun dawo yanzu daga gidan ogan naku.

Kafin mu tafi munyi neman layinki ance wayanki tana kashe tun jiya muke nemanki kuyi magana da inna ba a sameki ba.

Inna dai tasa mun hada turare masu yawa masu kamshi mun tafi mata dashi kuma ta nuna taji dadin hakan sosai a lokacin katseta nayi ina fadin.

Eeh na manta in kunna ne kinsan ba a shiga aji da waya bude wanan yasa idan na kashe sai inmata dashi.

Amma yayan mu ashe gidan manya kika turamu dubiya saida mukaje muka ga babban gidane ashe ?

Gidan manya kamar ya kuma gidan yawane gidan ko kuwa ?

Tace wallahi gidan manyan mutanene muka je Allah ya taimaka muka samu matar malam In,nuwa a gidan itace ta shedamu saboda malama tana turamu kai masu turaren da muke saidawa ni saida naji kunya ai.

Don badon itaba bamu san ya zamuyi ba a gidan nan ta soma ban labari komai na zuwansu gidan tace da farko cewa inna tayi su koma don ko sun shiga ba saninsu akayi ba .

Zamu koma din dama bamu sallami me keke ba shine wani ya hangomu yace mu shiga kawai ba komai ai.

Muna shiga suka hadu da wata yar gidan Amira na santa sosai tana zuwa gidansu malama itace mukace munzo gaida maman yayansu dake Abuja tace muzo ta kaimu part dinsu .

Wanda yanzu yasha gyara sosai ankara fadin falon ga manyan kujeru na alfarma har set biyu an zuba da filawowin kawata falon sai kamshi ke tashi acikinsa.

Ba zakace matan itace mai haihuwa ba don tasha kwaliyanta tayi kyau sosai ta zauna muka gaisa kafin ta soma fadin batako shedamu ba ?

Inna tace Eeh hjy ba zaki samun muba don yarinya ce ta turo mu muzo mu gaidake yarinyar wajena dake can lagos zaune tace muzo mu gaidake da jiki.

Ikon Allah ni din nan kuwa gashi ko ban sheda wace kuke magana a kanta ba a lagos take ke nan ?

Inna tace eeh dama wajen aikinsu dayane a can da yaron gidan nan shine ya taba taimakonta ita kuma yanzu tace muzo mu duba mai jiki wanan yasa muka zo gaidaku .

Allah sarki ai nice kukazo gaiyarwan dama jikin kuma Alhamdullahi karuwa na samu dama ai yazo dubana na a nan.

Don haihuwane nayi yau kwana hudu ke nan da haihuwan kinsan yaran yanzu nasan yace dasune kawai banda lafiya a can .

Duk suka dubeta Allah sarki ashe ciwon alherine namu na mata ubangiji Allah ya raya munashi akan sunna maddala da samun wanan alherin.

Saudat ta mike da kwalaben da suka sako tsaraba ta durkusa a gabata ta aje tana fadin gashi ummah a shafa.

Daga inda matar malam ke zaune tana saurarensu ta soma magana tace lalai kuwa anyi haka yarinyar wajenki dake can ikko din ko ?

Aina zata ta dawo garin nan ne don lalai nasan ace yarki tana ikko wajen kanin maigidan ku tana karatu can.

Wani lokaci na ganta nan wajen malama ai take fada min ikko take da zama sun zone ganin gida yarinya mai hankali wallahi ashe sunsan juna da baba a can din ko a nan dama suka san juna ?

Sai lokacin suka sheda matar malam din dake zaune can gefe daya saman kujera suke gaisawa da ita.

Saudat tayi amfani da labarin dana dan bata tana fadin a,a tun a nan dai suka san juna dashi shine acan dai suke dan zumucin fitowa waje daya ta daukeshi tankar dan uwa a gareta.

Hakan nada kyau sosai gashi yanzu ya zamo alheri har ta turo ku zuwa nan an gode hjyn ta fada tana dauko ledan ta bude kamshi ya kara tashi falon.

Take fasin har da dawainiya haka kuko matar malam ta amsa da ai sana,arsune kamshi don wanan turaren ma ai a wajensu na saye wanda kike magana.

Shigowan hjy yasasu mikewa suna fadin zasu tafi Allah ya raya hjy din ta mike tana fadin tana zuwa ta dauko kudi ta basu sukace ba zasu karba ba duk yadda taso a karbi kudin sukaki dole ta kyalesu tana masu godiya.

Su wa yanan din su waye hjy Maria take tambaya a gitsire matar malam ta bata amsa da makwabtan mune daga unguwar mu suke hakan yasa aka kashe maganan.

Don ta fara tambaya wacece wace nake jin kuna fadan ta turosu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login