Showing 357001 words to 360000 words out of 395027 words
Chapter 120 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
hakan tun a nan duniya aje lahira kuma ta iske abinta idan bata tuba ba.
Nasan wani abin yana saka mace zuwa wajen bokaye ko malamai amma kada a raja,a da hakan ya zama kamar ibada ga mutum.
Munyi lafitayyen girki a ranan don abincin dare saboda Paapa kawai don ni dai bance wani ba abincin da naci dana dawo ya kosar dani har dare koda zanci wani abu a lokacin saidai in samu abu mai ruwa insa a cikina lokacin.
Ina daki muna waya da Aliyu don ban kira gida ba har lokacin ba son komai ba kuwa don gujewa magana kada ace munji dadin hakan daya samu mama din har na matsa da kira don inji halinda take ciki din.
Paapa ya dawo shiya turo Amira takirani na tashi naje yake fada min sunyi waya da senior ashe abinda ya faru ke nan kuma bayan tafiyan mu din nace nima dazun da safe saudat takirani take fada min.
Amma nakirasu jikin da sauki akace yake fadin Allah ya sauwaka bayan haka kuma Aliyu ya fada mai cewa zamu umurah karshen wata yace nabashi list ko amma ina son a tafi da sariya ko ?
Na amsa da eeh uncle yace to banki ba kinsan laluranta yanzu ai na shigan ciki din nan ayi hakkuri dai har wani lokacin ai yanzu aka soma insha Allahu.
Zuwa saudiya a wajen irin su Aliyu kamar shan ruwane duk wanda rabonsa ya koka sai yaje tunda ana tare.
Nace to uncle uncle baida matsala da wanine zai nuna ai nayi bugun gaban kaina ba tare dana fada mashi ba amma sai bai nuna komai ga hakan ba a lokacin.
Ni kaina naji nauyi da kunya amma ya na iya da mutumina dan ujila yadda ya matsa min a bashi sunaye din a lokacin ?
Idan banda ba kuma yace zaiyi zuciya yace nayi abu na kasa tsayawa inyishi akan lokaci wanan yasa na biye mashi nabada sunayen kamar yadda ya bukata.
Dan matsalan da aka samu shine ina duban yadda yaran mama zasu tafi su barta a aaibiti sai nayi zato ba zasu tafi ba ke nan su idan hakane kuma kujeran gidan mu zai ragu ke nan da mutum biyu.
Saidai da tafiyan ya kara karatowa nake jin ai basu fasa tafiyansu ba ashe wai zasu mayar da mama can family house da zama ko kuma tsohuwar ta tazo ta zauna da ita anan din ?
Shawaran iyayyen mu kenan a kasu kan tafiyan inda a lokacin naji cewa matar yaya ibrahim da yarantama sunzo a nan zasu zauna har mu dawo din .
Dole akarshe dai tafiyan ya sauya bansan ya akayi ba saiga tafiyan ya kama da anty da yarta ba karamin dadin hakan naji ba a raina.
Gashi dole a kano zamu tashi wanda hakan yasa na dauki excuse a school kuma wanda dakyat suka bani permission din tafiyan a lokacin .
Sosai naji dadin dawowan mu kano ko banza zanzo inga mama tare da Paapa mukazo har kano din bayan muyi sallama da makwabta a can lagos din.
Ba karamin fitina paapa sukayi da hajja yabi ba akan tafiyan inda ta rantse da Allah dashi ya biyawa anty kila har dani don kawai a munzatata a gidan.
Magana har gun mahaifiyarshi aka zaunar dasu yakoro masu bayani da cewa wanda na aurane zai kaimu umurah ya dauki bangarena da nashi inda su anty din suka samu shiga a bangarena.
Kuma shi baima so tafiyan sariya ba tunda juna biyu gareta a yanzu don da akwai shirine tsakanin mu da itace zata tafi makwafin sariya din amma da yake bashiri a tsakaninta da maryam dole ya yarda Sariya din taje tare dani hakana.
Aiko bakiyi ba yabi da kowa kika zauna ba zaman girma da arziki a tsakaninku sai anyi fitina dama nasan abinda ya koroki ke nan daga can har wanan yar dake zama daku itama baki barta ba ashe ?
Abinda mutum yakewa gudu ke nan bakasan me Allah zai mai da mutumba watarana in Allah bai ba bawa ba saiya ba danshi idan bai bayar duka ba ajikama sai a samu mai tallafawa watarana.
Shi zaman duniya iyawane yabi ba komai akai maka zaka tsaya magana a kanshi ba don kada a kwareka akan bar wani abune don gaba.
Ki gyara halinki mijinki yasha kawo min karan zai sakeki yau idan ya sakeki yabi ki dafa ina don Allah ?
Ni kaina saida nakai zuciyana nisa a kwanaki dake gidan nan haka kikazo nan da yan uwa kikai cin mutunci tun wanan lokacin kika zube a idona wallahi.
Ayi hakkuri hjy zan gyara nima wani lokaci abin yana damuna wallahi kinga ita abokiyar zamanki ai yanzu mun fahinci gaskiya akanta wallahi yarinyar bata da matsalan komai da muke zato akanta ?
Ke meyasa ba zakiyi koyi da irin halinta ba a zauna lafiya da kowa yanzu kan kinyiwa kanki a nan saidai kuma gaba idan kin gyara.
Wanan zuwan da zamuyi tafiya anty gidan mijinta ta sauka ni kuma na sauka a gidan mu wajen iyayyena munje asibiti munga mama na dan jima a wajenta.
Ba laifi jikinta tunda tana sheda mutane tana gane kowa na samu duka yaranta a wajen tare da ita har yaya murja.
Wace data ganni ta kawar da kanta gefe daya bayan na gaida kowa na juyo kanta ina gaida ita ta soma fadin a,a ni kan rufamin asiri keda, ai gatace a garin nan tunda har anyi min iyaka daku.
Ayi hakkuri yaya murja sherin shedane don Allah tace nima kuyi hakkuri dani ku tayani addu,a sai nayi abu ya dawo ya dameni daga baya .
Gasu zasu kasa mai tsarki sai suyi maki adduan Allah ya taroki kakansu ta fada akayi dariya koba komai dai na sauke nauyi zumunta tunda mun shirya aida yar uwata.
Da zamu tafi harda ita zuwa rakiyan mu har take fadin ai da sahura tabimu taje tayi kitson da tace tana sonyi din kada ta makara sai taban tausayi sosai wallahi.
Ina dai zaune a motan amma ina tunane wani hanya zan fara taimakawa yayan murjan mu dashi yanzu abune da jahilci yana da wuya tagane taimako nake son mata saita dauka fariyace yadda suke fada amma zan gwada in gani ko zatayi saukin kai ta fahinceni.
Munje gidan paapa na dubo antyna daga nan muka shiga family house dinsu sai namu gidan gadon inda kakanin mu suke rayuwa a ciki.
Muka dawo gida yamma lis a ranan ban taka gidan kowa ba duk da inna nata korafin wai muje mu sallami abokan hurdanta kada suji zancen daga sama.
Nikan koda zasu ina kwance ina waya ban binsu ba sukaje gidan malama da gidan ummah Hafsat suka dawo suna nuna mata abinda suka basu wai na shan ruwa.
Ina jin ita inna na fadin jallabiya ke nan zaman kudin nan suna hada baki cewa ,a,a inna akan wanan kudin zamu riki jallabiya ?
Dama fa ai duk wanda ya baka asha ruwa hanya saika bashi tsaraba suka shiga musawa ina jin su murmushi kawai nayi daga inda nake din.
Saudat ta shigo tana fadin kin huta yaya da bakiji karbo wanan kudin wahalan ba uwale tace wallahi da nasan hakane ma bazani ba sai lokacin nayi dariya mai dan sauti nace aibaku gama zuwa ba saura gidan malam habu ko da gidan,,,,,,
Don Allah yayan mu kyale inna ba inda zamu koma wallahi idan mun dawo kada su gaidamu din haka kawai ba inda zan koma kuma inji uwale.
Inna dake fada daga tsakar gida naji muryan yaya murja ashe ta dawo itace take diban ruwa ta watsa ta fita tana fadin ke innan mairo bata zuwan kan tunda kince idan sun dawo sai sun bisu da tsaraba ?
Tsaraban namu zasu kwashe su mikawa yan waje bafa makka zasu ba balle umura zasu tafi yi har nawane kudun da za a basu surike ?
Duk da abin yayi min zafi amma na daure na fito ina fadin yaya kin dawo ashe tace nadawo ke dai ina nan da innan ku wai aje sallaman mutane haka kawai ?
Nayi dariya ina fadin ya kika baro mama din tace mama yanzu ai kwadayi takeji na barta drinks din da kika kawo mata da nama ana yaga mata tanaci da kyar tabari na dauko katara da gaba guda naci.
Wai kince taci taci saita koshi ai kada mu cinye mata nace kwarai kuwa idan irin haka ya samu mutum ana son ya samu abu na taunawa ya dinga ci kamar nama din ko chewingun haka dadai makamantansu haka nasa bakin ya dawo daidai da sauri.
Allah dai ya sauwaka kinji tadai samu cingam din nace har naman ma zata samu da yardan ubangiji ba gaki a kusa ba yaya dan nama dai da za a sayo mata aibai gagara tace umm,humm mairo ke nan Allah dai ya duba muna na amsa da amin.
Ta dauki ruwan ta nufi daki nima na koma daki don na kula ruwa zata watsa yasa na barta a lokacin idan nayi kure ra fice din nan sai kila mu hadu kuma.
Ina jin muryanta don ita bata magana a hankali idan tana gidan kowa na sani irin abinsu na yan shaye shaye din nan takeyi cikin daga murya.
Nayi sallama na isa dakin nako samu ta shirya zata fice din nace yaya har zaki fita tace wallahi mairo zama baiyi ga tallaka kinsan zan fita induba inda zan lalubane kuma ?
Dako naso muyi magana dake yaya tayi wani iri tana fadin ni din nan dai murja to ai gani ina jinki mairo ?
Ki zauna yaya na fada na samu wuri nakai zaune na fara fadin fadin da farko abinda ya faru tsakanin mu yaya don Allah kiyi hakkuri mu daukeshi a kaddara Allah ya nufa sai munyi hakan nida ke naji kunyar abin matuka daga baya yaya kiyi hakkuri don Allah ?
Saida tayi wani irin nisawa mai nauyi kafin tace to shike nan tunda kince hakan komai ya wuce mairo nace kiyi hakkuri da kanwarki yaya kinsan zuciya bata da kashi.
Allah ba komai mairo ya wuce har ga Allah tunda kin gane hakan nace nagode tace ba komai ai nima ya wuce a wajena ai.
Sai kuma na biyu don Allah yaya har wayau ina baki hakkurin rashin daukanki daga cikin masu tafiya din nan kada ki zata don abinda ya faru yasa ban sakaki ba a,a dama mutum biyu akace a dakin mu nan kuma dakin mama mutum biyu.
Au nina zata ai kun debenine a cikin dangi ai kukayi min yan ubanci haka ina kallo da sai ince to muje zuwa daku ai mugani a,a yaya ba hakan tsakaninmu ai tace naga alama sosai a idonki yanzu haka zancen nan da mukeyi ai ?
To don shine yaya nayi shawara yanzu me zai hana ki fara sana,a kinga za a barki ke kadai yaya lalura zai maki yawa ke daya ga mama a kwance komai kuma ke za a sakawa ido karshe.
Nima abindake cikin raina ke nan wallahi na rasa me zanyi kinsan shi baba baida case da lamarin mama yanzu sai yaga dama yake lekata ya dan bada wani abu ya wuce.
Haba dai shiko baba tace ance mijinki ya dauki duk nauyin asibitin ai komai da za ayi ko za a bukata daga wurinshi yake zuwa wallahi shiyasa kikaga jikina ya soma sanyi ai.
To ai dole yayi tunda uwatace akwance tayi dariya nace yanzu yaya wani sana,a kike ganin zaki soma wanda zai kawo kudi haka dai ?
Sana,an da nake so mairo yafi karfinki gaskiya wajen abinci nake son in bude haka irin wajen da zan buda ga yan aiki ko mutum biyu na samu indinga saida abinci kinga kuwa aiba karamin kudi bane wanan ?
Eh to yaya duk da bakaramjn kudi bane sai ayi tunane ta ina zakiyi wanan din a gani wajen idon jamace akwai kasuwa a wajen tace sosai ma waje baida wuya mairo kudin dai shike da wuya ai yanzu ?
Na samu waje koba shago inga kayan aiki ai ni wallahi duk wanan tabaran zan daina in kama neman kudinane yanzu ?
Nagaji da yawon nan na banza nima dai haka mairo har wanda bai usa ba yace zai kawo maka iskanci don bariki .
Kinga kuwa yaya sana,an abinci kuma akwai alfanu sosai a cikinshi don gaskiya idan ya karbeka sai hamdallah na kara bata karfin yin abin .
Tace ashe kin gane dai amma wai nace zanyi shine sahura ke kushewa miji yanzu mairo Allah na tuba wa zai soni a haka don Allah dama ace ina da kudine ko don kudina aisai a soni ko ?
To ban aje ba mairo kuma ba natsuwa ina zancen aure don Allah gareni nace babu gaskiya to yaya indai hakane zan baki dubu dari biyar ki rike saiki fara mugani kafin mu dawo idan akwai ci sai acigaba ko a karawa wajen jari kuma.
Ni dai saiji nayi mace ta kamkameni sosai tana fadin waida gaske kikeyi ko wasa mairo dubu dari biyar fa kikace mairo ?
Yaya to meye don nabaki dubu dari biyar yar uwatafa naba ba wani ba meye amfanin samu a gida yaya ?
Sai kawai naga ta fashe da kuka wanda bansan ko kukan meye bani dai nima kukan nakeyi don hawayen da nagani yana fita mata lokacin.
Cikin kukan ta soma fadin mairo baba ko innan ki sunda zaki bani kudin nan kuwa akan me sai sun sani yaya tsakaninmu nefa wanan zumunci fa yaya ba wasa bane mune dai yan adam da bamu gane hakan muke sakaci da zumunci.
Meye ranan ina dashi ke kina wahala ban taimaka maki ba ni wallahi kaf duniyan nan ba wanda yasan da zancen nan bandake dani a yanzu ?
Nikan nasani garama innan ku mairo nasan itama ba zata hanaki ban ba idan kinyi niya amma baba yanaji wallahi nasan ko Allah ya isa yana iya ja maki mairo yace don me kika ban kudin ki ?
Ba zaice ba yaya baya koji saidai idan kece kika fada mai to amma ni nan inda mukayi nabar wanan zancen a nan ke nan hana rantsuwa Saudat zata sani ita don itace zata je ta ciro kudin gobe kuma kinga dole ta sani ai ko ?
Na saudat mai saukine idan mun kwabeta bata bari yaji amma matukar baba ya sani nasan zai hanaki bani kudin nan wallahi ?
Nafayi niya yaya ba wanda zai hana tunda ba sheri nabaki kiyi dasu ba ta kara kamo hannuna ta rike gam tana fadin na yarda mai dan uwa rabin jikine hakane.
Mairo wanan idan bake ba duniya kaf babu mai tsayaqa ya dubi lamarina ina cikin wani hali mairo amma ba wansa zan iya fadawa hakan bandama su karamin zafi akaina .
Mun jima da ita don tace ta fasa fita fitan me zatayi kuma ita data taka alheri da kafafunta ita wanan kudin ai yafi mata zuwa umura a yanzu idan ta samu ta tafi tunda aikin Allah ne za a?
Har yaya sahura ta dawo ta samemu a dakin tana mamaki banjima ba na tashi zuwa dakin mu har lokacin ina mamaki da ogana bai kira ba a daren.
Sai wajajen sha biyune ya kira yana ban hakkuri yace yana gidane suna wani case sai yanzu ya dawo daga can .
Haka kawai naji baki ya ambata mai abinda zuciyana taba shine akaina kuke case da iyayyenka ko daddy ?
Yaya akayi kika gane hakan ya tambaya ba tare da boyewa ba nace zuciyanane dai ta ban hakan wallahi yace kwarai kuwa amma nayi mamaki da kika gane haka da sauri ?
Zan gane mana daddy ko wata mace idan zata shiga gidan mijinta tana fatan soyayyab mijinta da yan uwanshi a kanta amma ni sai naga ba hakan a gareni.
Why nace kwarai kuwa yau da sunyi na,am da shigowana cikinsu daddy at least ko sisters din ka zasu kirani ko a waya mu gaisai insan sunsan dani amma kamar na auri bako haka shiru ba nuna wani sign na soyyan akaina kasancewan mu tare ai dole in gane hakan.
Nifa macece daddy dole in fahinci wasu abubuwa koda ban tashi gaba daya arewa ba ai dai nasan wasu al,adu na arewa yadda akeyinsu.
Watace can wata sister din ummah take son caza min kai ni kuma nafita zama jan wuya wallahi nasan nufinta a kaina maryam so take ta hada min tarko da ummah in fada ita kuma ummah bata gane plan dinta ba.
Katseshi nayi da fadib Allah ya sauwaka ni zan kwanta saida safe na kashe