Showing 288001 words to 291000 words out of 395027 words

Chapter 97 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

cikin abinda ya soma daga mai hankali da ita ai .

Cigaba tayi da cewa kinsan Allah maryam da tazo da zaman lafiya gidan nan ba zan bari haka ya faru ba amma ita sam babu zaman lafiya a tare da ita burinta kawai taga na bar gidan nan har ke ta zauna dashi ita kadai.

Ni datazo ta sama ban daga hankalina donta ba sai ita datazo ta sameni zata shigan min hanci da kudundune ta lalata muna tarbiyan ya.

Koda suka tafi dazun ai ba abinda bata fada ba saina bar gidan nan har abada sai ta nuna min ita wacece bata fito kabilan bamza ba dagani har ke ta bamu wata daya lafiya cikin gidan nan kiji mun mata sai kace itace Allah.

Zubur nayi na mike daga yadda nake kishingide ta kwashe da dariya tace kinga ko niko banji komai ba wallahi nasan dai duk tsiyarta tace zataje tayi muna sheri a can ta hada kai dasu Rukkaiya tunda dama basu kaunata a zuga Paapa shine kawai dai ina ?

Zata iya makircin hajja yabi yawa gareshi anty ni yanzu dana fita harkanta gidan nan sai naji dadin hakan sosai amma da a tsarge nake wallahi sai ta biyoni idan zan fita tana marairaice min in sayowa danta abu paapa yaki ya saya masu.

To ai tsuntsun da yaja ruwa shi yaka duka ko a jikina wallahi mu taso ta hada Allah ya karemu daga sherinta taje kano din ta gani idan zasu daukar mata hakan ai.

Lokacin sallah da naga yayi yasa na mike zuwa sallah itama ta fita zuwa dakinta muka bar Amira tana kallon cartoon a waya.

Koda na idar da sallah na jima a zaune ina rokon Allah ya kareni daga ko wanine irin sheri na jima a hakan kafin in mike ina kwashe sallayan a wajen.

Fita nayi naja Amira muje muci abinci jeloup rice ne da kifi nayi amfani dashi na hada dama na debowa anty damu itama ta fito don da alama sallah tayi tun bayan fadan da sukayi da hajja yabi ta goranta mata hakan yanzu tana sallah sosai gaskiya saidai wani lokacin ba a kan lokaci ba za ayi.

Har mun soma cin abincin wayana daga daki ya dauki kara a guje Amira taje ta dauko min wayan ta kawo min na karba ina duba wake kira lokacin.

Shine a layin na daga da sallama irin ta addinin musulunci muka soma gaisawa dashi muryan Amira da uwarta da yaji yake tambayata kamar a gida naji muryanki ko ?

Kina nufin gida kikene yau baki shiga school din ba ko yau baki da exam ne yasa baki fita amma aiko kun fara naga kuna fita ?

Naje na dawone na bashi amsa a takaice tare da mai bayanin abinda yasa na dawo gida a lokacin .

Okey ya fada na tareshi da fadin ya kano yasu ummah da sauran yan uwan suna lafiya gani tare da ita barin baki ita ku gaisa ko kafin ince wani abu naji yana fadin ummah ga waya ku gaisa.

Muryan mahaifiyar nasa naji rakwai a waya tana tambayan waye a layin ya bata amsa da fadin maryam ce take tambayana ke nace gani a wajen ku ai .

Ban damu da barin wajen ba don Antyna dake zaune a lokacin don tsaban kwantar da muryan da nayi saida na tabbatar abawa mahaifiyarshi wayane na dan daga murya ina fadin ummah ina wuni ?

Lafiya kalau yar nan yaya kuke can ya aiki ya iyayyen ki kuma suna lafiya kalau ummah tona gode Allah yayi albarka na amsa a kunyace da amin ummah nagode sai anjima.

Tace Allah bamu alheri ga babana din bance komai ba ya karbi wayan yana fadin har kungama gaisawa ke nan naji tace so kake in zauna inta zuba da yar mutane inkai baka da kunya na fahinci ita tana da kunya ba irinka bace ita.

Naji yace hello maryam saida na sauke ajiyan zuciya nace na,am daddy kinji ummah wai kin fini hankali don taji muryanki a natse ?

Murmushi nayi kawai ban iya cewa komai ba ban ma san me zan fada ba a lokacin don kunyar daya barni a cikinshi.

Abin mamaki sai kawai naji ya dan kwashe da dariya tabkar ba a gaban mahaifiyarshi yake ba yana fadin nasan meke damunki kika kasa magana da zaran munyi aure kin shiga gidana zaki saba da ita .

Uhummm kawai nace na kashe wayan ina murmushi yayin da antyna ta duboni muka hada ido da ita take fadin Oga Aliyune ko ?

Shine anty daureni yayi ashe yana tare da mahaifiyarshi yanzu shine ya bata waya muka gaisa son baida ta idon maza.

A shi ina ruwansa bai dauki hakan wani abu bane meyema a cikin gaisuwa kawai kun gaisa da mutum kunji lafiyan juna ai bawani abu bane hakan amma sai a fassaraka da baka da kunya tunkan ka shigo kana nuna kanka.

Nidai mamaki kawai nakeyi kasan zuciya meyasa yayi min hakan na dan jima a zaune kafin in mike inbar falon zuwa daki har anty na fadin badai kwanciya zakiyi ba yanzu ana zancen magariba ?

A can kuma yana aje wayan ya lumshe ido kafin ya bude yanawa Na,ima magana dake ya zancen karatun nakine wai har yanzu mark din jamb dinki baikai yadda ake so bane ?

Ni da baba zai yarda england zan kaiki karatu gaba dayan ku banson karatun shirmen nan na bata lokaci da akeyi kasan nan karatu aitaba yaro wahala kamar karatun zuwa lahira abinda iyakansa nan duniya.

Ba inda zasu kokai a kasan nan aika fara karatunka ba saida ka soma hankali bane ka fita waje Allahma ya nufa ai zaka fita din badon Allah ya kaddara ba malam ya saka baki aida baka fita wajen bama har yanzu.

Wanan yasa nake son malam kamar yadda yake sona daku ai bakai kadai ba malam na matukar mutunta zancena sosai baba .

Duk akace abu ya dangamceni bai wasa da lamarin a baya yakance dani tausayinki nakeji hauwa ke kadai Allah yayi a cikin mu kuma kike hakkuri da kowa hakana.

Ummah ya kamata ace kinje katsinah kin dubo mutanen nan tunda sunyi fushin zuciya bai kamata yanzu mu kyalesu ba tunda kinsan dalilin hakan da sukayi.

Zan tafi baba ina da niyar hakan a raina ina son sai abubuwa sun lafa min ne ai inje in dubasu a can din yanzu ga wanan zancen da hjy hanne ta dauko dana je ana wanan gabar zatace sune suka zugamu ai.

Wani zance kuma ummah kai yanzu tsakanin karya da gaskiya ba zaka yarda ka amince da abinda take so ba a zauna lafiya baba wani fitinane kuma fa zaka jawo min a cikin dangi kan rashin yarda da hakan ?

Ummah aikin sheda yanzu ko ina da wace nake so zan aura yarinya ce karama iyakarta Na,ima don zasu zo sa,an juna da ita.

Iyayyenta yan garin nan ne kowa nata yana garin nan zama ya kaita can wajen dan uwan mahaifinta dake aiki a can take karatu yanzu haka baifi yan watani ta karasa ba ai.

Ni banda zabi akan hakan mahaifinkane dai kasan sai yayi korafi yace bata tashi a arewa ba don haka bata da tarbiyanmu na nan arewa.

Maryam kan ko wanda ke rayuwa a kauye nan arewa bai gwada mata tarbiyan malam bahaushe ai balle ina tsaye da abina ina bata kula yadda ya dace kamar yadda zan ba wa yan nan gasu ya nuna kannesa da wuya.

Haushin yadda yake wani yabo yana tarewa tasan yana hakane don taji haushi akan yar uwarta yasa ta kyaleshi ta juya wurin Na,ima tana mata magana.

Ya dan jima a zaune dasu kafin ya fito don kirashin da akayi ana nemashiba kofan gida yasa ya fito din har ya daga yake fadin.

Yana da wuya in shigo gidan nan kuma sai dai in Allah ya dawo dani lafiya kuma ke Na,ima in akwai wani abinda kuke so kiyi min text ki turo min a yau din nan ta amsa da to yaya saidai zancen makarantar nawa donni ban ganewa yaya Yusuf din ba idan nayi magana yace min ana kan kokari.

Murmushi yayi kawai ya fita don yasan me yusuf din ke nufi akan yar uwar nashi yasan abinda zai mashi zaisa a nemowa yarinyar karatu saidai yaji kawai ta shiga jami,an in yaso yayi abinda zaiyi.

Yana fita ya gama magana da bakin nashi bai koma ciki ba ya shiga mota ya nufi inda yake son zuwa din kamar wancan karon na baya haka ya shako mota da sayayya ya nufi gidan mu da kaya niki niki ya tura yaro a kira mai saudat again.

Suna zaune sun dawo daga islamiya yaro ya shigo yana fadin wai ance saudat tazo ana mata sallama sam bata kawo cewa shine ba haka dai ta yafa ta fita tana lekawa.

Motar data ganine ta fara kwankwanton koshi dinne dai ta karasa fita ya sauke glass yana waya yake fadin amma ke matsoraciyace ko ?

Ba tsoro bane bandai san waye bane kin zata ko wani dan yankar kaine kike wani leko kai daga zaure ko ?

Sannu da zuwa yaya ashe kana gari yaya baya ko fada muna ba ko dazun munyi waya da ita suka gaisa take fadin kanata mata wayau kana zuwa gida kai ?

Dan dariya maganan ta bashi yasa yace da ita kinsan mu mazane ba a san mu da kulle ba dama sai ku mata tana tafe ai insha Allahu tunda ta kusa gamawa.

Itama haka take ce muna idan mun tambayeta ta fada a cikin sautin dake nuna damuwa sosai a tare da ita yake tambaya koda matsalane tace a,a dama zancen karatunane dai idan nayi magana sai baba yace itama da takeyi bata karasa ba balle ya kaini.

Ya danyi shiru kafin yace kin fada mata tasan da zancen inna tace kada na fada amma tasan da zancen ai tunda tasan nagama karatuna shekaran nan.

Yanzu hado takardun ki na wuce dashi kada kicewa kowa komai sai ita barin duba zansan abinyi ya murja data sauka a mashin a lokacin.

Tana mikawa mai mashin kudi amma hankalinta na kan wake da motar nan su waye tsaye a wajen lokacin shi kuma yace ta kira yaran da yagani su kwashi kaya zuwa ciki.

Har yabar kofan gidan mu yana cike da mamakin halaiyan yan uwana din daya gani muna da kama sosai da juna saidai ya kance na fisu komai.

An shiga da kayan ya rabawa har yaran da suka taru a kofan gida dari biyar biyar yara nata tururuwan zuwa karba a cewansu ana sadaka a kofan gidan su mairo don har yanzu sunan nan hakana duk da mama tayi fadan haka harta gaji.

Takance kafin mairo tazo duniya yannenta sun rigata don kwakwa za a dinga kiran gida da sunana ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[10/6, 9:38 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊8️⃣7️⃣🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Wanan karon kamar wancan haka ya cika muna gida da abin arziki wanda har yakai mama fitowa don jin yadda yaran dake taya kannena kwasan kayan hayaniya a cikin gidan murnan dan kudin daya raba masu a lokacin.

Kokarin mikewa takeyi tsaye daga inda take zaune har ta samu ta mike din ta dafa bango ta gyara zata fita yaya murja ta juyo tana fadin to ina kuma zaki don Allah ?

Zan dan fitane inga abinda akeyi wajen mana ina ta jin hayaniya a tsakar gidana don Allah dai ki zauna me zaki fitayi banda ganin takaici kayane fa wanan mutumin ranan daya kawo ya sake dawowa yauma ya kawo masu.

Bari naje na gani ai ta fada tana kokarin fita daga dakin nata cikin tsawa murjan tacewa mahaifiyar tasu kiga me kiga takaici ko me ?

Kayanne baki taba gani ba kayan abincine dana shafa tunda sun maida kansu mayunwata har ansan da hakan zakazo hira saika wani shako mota da kaya kamar kaga gidan mayuwanta din nan ashe su ?

Niko kina ban mamaki wallahi ki barta ta fita mana tunda ansamu har tana iya fitan koma meye dai damu za acishi gidan nan meye na takaici a cikin hakan sahura ta fada.

Dake dai dake binsu don kwadai nikan banga abinda zan gani a nan ba ya tsone min ido wanda ban taba gani ba idan ina so aisai inje in sayowa raina inci.

Uwar bata tsaya saurarenta ba ta karasa ficewa daga dakin zuwa waje inna na tsaye suna magana da Saudat data dauko takardu takai mashi ya cire wanda zai dauka ya bata sauran.

Abin arzikine muka samu haka mama ta fada wanda jin muryanta a bayansu yasa inna juyowa tana fadin gashi nan dai abin Allah bai karewa ga bawa .

Dazun nake fadawa malam shikafa ya kare ya hau fada yanzu ga Allah ya kawo muna na Allah waya kawo ta tare inna da tambaya tana bin kayan da kallo.

Kafin inna ta bada amsa uwale dake gefe take fadin saurayin yaya mairone ya kawo ta bude baki cikin mamaki tana fadin duk wanan din?

Wallahi ita mairo tana da mai nema a nan ke nan ita tana can dan garin nan ne amma kila ba a garin nan yake zama ba zuwa yakeyi shima.

Shiru tayi tana bin kayan da kallo Abdul ya dauko roban cock daya fashe wajen daukowa zuwa cikon gida ta mika hannu tana fadin ban wanan din in dan tsotsa da sauri uwale ke fadin ai sai baba yazo ua gani.

Idan yazo ya gani din ba sha za ayi ba kai Abdul mika mata ka karo mata biyu yaran nan ma da suka dauko kayan kiramin su in basu kafinsu tafi.

Yaron ya mikawa mama inna na fadin kara mata mana tunda tana son sha ya dauko biyu ya mikawa mama din ta karba a sanyayye yake fadin nagode.

Ta juya ta koma dakinta don tasha tana shiga tana murmushi murja ke fadin yanzu mama kwadayin wanan abin kikaje don Allah ?

To meye ba tana so bane kuma don asha aka kawo ba gashi ta dauko ba kinji wani yayi maganane yaya sahura ta fada.

Haba ki bari in mata magana mana wanan ai jawa mutane rainine don Allah daga kawo abu taje tana roka saboda Allah ?

Gubane halan idan ta roka aiba waje taje ta roka ba itama mairo yartace ai ko don tana auren baba ta zamo ba yarta ba ?

Wani aure ko cuta da cin amana saida ta gama halakewa ya juya mata baya ya barta tana wahala don ,,,,,

Wai murja kanki daya kuwa babane ya barta tana wahala ko Allah ya jarabeta da ciwo don Allah ki san abin fadi mana murja iyayye bafa wasa ba.

Maganganu marasa da a ta somayi a dakin sukai shiru suka kyaleta ba wanda ya sake kulata tagama kuma tasa kai ta fice daga gidan.

A yadda tayi tsamani zata zo kano ta sama a wajen yan uwan miji da suke waya lokaci lokaci dasu sai gashi tazo kano din taga ba hakana bane.

Don kwanansu biyu a kanon ba wanda yazo gidan da sunan yazo masu sannu da zuwa ko azo ganin danta take zaton akanshi zata iya samun kafansu ta juya kowa yadda take so.

Ga Paapa idan ya fita sai dare zai dawo gidan wani lokacin kuma daya dawo fita zai sakeyi sai dare zata ganshi koda zai dawo har tagaji tayi barci ita da danta.

Duk da ranta ya baci da abinda ta kula dangin mijin sunyi hakan bai sa tace zata gidan wajen


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login