Showing 345001 words to 348000 words out of 395027 words

Chapter 116 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

ko ?

Idan ba falo ai akwai natsuwa cikin ta falo ba natsuwa ba mutunci agara hakan sau dubu ga bawa yasan Allah ne bai kaddara a samu falon ba a lokacin .

Magana yake muna a baibai da bamu gane manufar hakan donshi dai mukai shiru gaba dayan mu muka bar zancen ga amsa yaba saudat din itace ma ta danyi dariya tana fadin wallahi hakane yaya.

Ta bude mota gefen zaman banza ta aje kayan yake fadin ki juye a nan ki tafi da tire din sai naje gida zan sha ba jimawa zanyi ba nazo naga rakishidade dinane inyi mata bangajiyan taro .

A,a aimune da gajiya ita tana kwance abinta muya kamata ka gaida da gajiyan Saudat na kula kin baci yanzu da surutu don Allah shige ciki kada ki cikamuna kunne da surutunki don Allah ?

Meyasa kika kore min ita bayan kinsan tana rage min damuwa a yanzu din don na kula ke baki cikin son magana a yanzu daki barta ta rage muna abinda ke zukatan mu.

Ba komai a zuciyana surutune banso na kula tun zuwana ta baci yanzu da surutu don ba haka take ba a da nice ma nafisu kaudi amma yanzu duk sun fini iyayi da kaudi.

Lokacine a baya ai basuyi wayau haka ba da kika barsu ke kuma yanzu kin mallaki hankalin kanka kinsa abinda yakw daidai da wanda ba daidai ba anyway ni zan koma Yusuf yana jirana kofan gidansu nan bayan ku.

Ka gaji ke nan No bamgaji ba zamu shiga gidane in gaidasu can ma din yan uwa sun taru dazun zanje in gaidasu da gajiyan taro kafin na karasa gida na kwanta a gaidasu idan kaje.

Na zata zaki shiga ku gaisa zuwa gobe ko jibi kafin ki wuce ai No gaskiya ba zan iya hakan ba saidai zuwa gaba insha Allahu.

Why ba yanzu ba ni bagani nazo gidanku ba gobe nake son yusuf ya rakoni inzo in gaida inna already shi baba ko dazun mun hadu dashi da uncle muje har shago mun gaidashi.

Bai fada ba kuwa don yanzu haka koda ka aiko muna tare dashine manya basu fadin magana ai bai jima ba kamar yadda yace mukai sallama ya tafi na koma gida daki nashiga nayi ahirin kwanciya ban tsaya dakon dawowan antyna ba don nasan a wajen anty fati zata kwana.

Barci ya soma daukana nake jin murya sama sama a tsakar gidan namu hakan yasa na dan buda idona don hayaniyar da yai yawa a lokacin.

Muryan yaya murjane yake tashi a lokacin sai na baba dake biyowa bayan nata ga kuma kuka muryan daba zan tantance konawaye ba a lokacin.

Abinda naji yaya na fadin shike nan don ana kama masu sai ko magana kada muyi a gidan ace bamu isa ba nace irin auren nan ai auren barikine mun saba ganinsa in yayi wuta karkonsa wata ukku.

Karya na fada ba haka bane shine baba zaka kama tsinana don na fadi wanan magana ka nuna min yaran innan mairo sun fimu daraja a wajenka ke nan yau ?

Wai ashe mamace ke kuka daga dakinta don baba yana zagin yaya murja din ashe abinda ya faru data dawo gantalinta take fadin wai ance an daura aure yau a gidan nan ashe dama aure sukazo daurawa ke nan.

Indai irin auren nan ne na bariki akazo ai muna burgan aiki mun dade da sanin irinsa ai duk inyayi wuta karkonsa wata ukku ko biyu a watse.

Ke saudat sai kikace mukan bamuji bakinki ba yaya murja insha Allahu sai mutuwa takalmin kaza mutuwa zai raba auren nan insha Allahu.

Kam uban kaza ke saudat har kin isa ina magana kice zaki saka min baki a zancena to wallahi in baki hankali ba yau ina kwaye maki gidan nan in nuna maki ke karamar yar iskace .

Shine baba yaji suna sa,insa a cikin dare ya taso yana tambayan ba,asi saudat din ke mayar maida abinda ya hadasu ya juyo yace murja fatanki ke nan akan yar uwarki dama ?

To bata gaji hakan ba ga uwarta don ba karya saudat ta fada ba kedai kije ki karata a hakan da kika zaba tunda kina ganin hakace mafita a wajen ki don tsiya yanzu har masu nama a tire kike nema da kudinki suna gudunki.

Ai ba yau ka saba min kazafi ba baba nine ke maki kazafi murja lalai tambadan naki ya wuce musali yanzu jeki ga duniya nan ta isheki riga da wando ki yafa.

Aiko ta soma zagin baba tana mayar da amsan daya bata daidai da abinda ya fada mata din.

Son kawai na fito nace haba baba ba girmanka bane hakan ka kyale tunda ita taki tayi shiru mana sai cewa tayi dani ke karamar karuwace mairo ?

Tunda duk barikinki kike tsoron nuna mashi ke yar iskace ta kwarai na juyo rai bace nace murja niba karuwa bace inda karuwanci ko iskanci yabi bamu hada hanya dashima balle in sanshi .

Amma dabancin nan da kike takama kan zan nuna maki yau karyan daba kikeyi a gidan nan inkin isa kuma ki kara zagin wani daga cikin iyayyen mu yanzu kiga aiki da cikawa.

Gadan gadan na harota ba tsoro koja da baya na haukace mata lokaci guda in zaga da turanci inyi yarbanci a take nashiga daki na dauko wani kwalban danagani na abinsha a gabanta nafasa nayi kukan kura kamar zanyi kanta ta arta da gudu waje .

Fadan daba ai saidai muba da labarinshi nace ashe keba yar iskan gaskiya bace murja da baki tsaya na nuna maki nashiga bariki ba gida ya barke da koke koken iyayyen mu.

Hakan da nayiwa yar iska shine zaman lafiyan mu a ranan donko bata dawo gidan ba takoma inda tafito a tsorace tana fadin wai ina zan tsaya wanan tafini hauka da iskanci ashe irin fadansu na rashin imani na can ta taso yi dani take fadawa mutane a waje.

Sai washegari danaje gaida babane yake min fada yana fadin asha maryama kika biyewa hauka murja a zageki ?

Haka muke da ita idan tayo shaye shayenta tazo tana muna hauka da tijara a gida jiya duk da naji dadi kinyi min maganin yar iska tabar gidan amma banso ki biye mata ba ai haka.

Baba ya kamata a dauki mataki akan ta son gaskiya ina tsoron kada wata rana tazo ta jin ma wani agidan nan musanman yan dakin inna da take takura masu da fitina.

Zanso ita da abokan shashancin nata a dan tsorasu don Allah ka bari kafin mu tafi in dan dauki matak akansu ?

Murmnshi irin na kunan zuciya yayi ya soma fadin kaiya murja ta wuce yadda kike tsamani mairo ina dana sanin haihuwan yarinyar nan da nayi a yanzu iyakar zubar da mutunci murja taga zubar muna dashi a unguwar nan.

Abinsune uwarsu ke girba a yanzu muma muna dandana hakan kowa yace a duniyan nan baida fatan alheri akan dan wani to a kan nasa zai kare kuwa abinsune ya koma masu a dakinsu suke girba.

Bamu bar kano ba saida aka zuba kudi aka kamo yan uwan shaye shayen yaya murja akai masu kwakwaran kashedi tsakaninsu da yan dakin mu sannan aka sallamota ta daku akace an bata wa,adi ta fito da miji tayi aure.

Zakice ba ita bace tazo da iyashegenta gidan dom ta tayar masu da hankali kawai yanzu ta sheda hukuma don ta dandana kudanta a can.

Yaso naje gidansu din ingaida iyayyenshi amma na nuna hakan ba yanzu don Allah yayi hakkuri yace ba matsala.

A bangaren hjy hanne kuwa sai washegari ta samu labari a wajen danta dayagani a waya wani dan uwansu yayi posting yana taya Aliyun murna gasu a wajen daurin auren nashi.

Ya fito ya samu mahaifiyarsu yana fadin mum wanan ba Aliyu bane wani Aliyu ta tambaya yake fadin Aliyu gentle ?

Aliyun ummah hauwa mana gashi anyi posting dinsu a waya jiya nan an daura mashi aure kuwa bash din kawu hamzane yayi posting.

Aliyu fa yayi aure kace wallahi mum gashi kuwa ya kara nuna mata photon wajen daurin auren ta soma fadin aure fa aure kai wanan wasane fadine kawai suna zaloya.

Anya kuwa mum amma barin bincika ya dannawa bash din kira ya dauka yana tambaya Bash Aliyu yayi aurene da gaske ?

Wallahi jiyan nan aka daura mai aure bayan mosque da wata yarinya based in lagos don can take zaune lagos din yarinyar dai yar garin nan ce.

An daura wallahi bashin din ya kara fada ya kashe wayan nashi kafin yace wani abu ya juyo ga uwar yana fadin kinji ko an daura a yadda naga posting da gaskene ba karya ba.

Ni hauwa zatayiwa cin fuska kome dama akwai yarinyar da Ali din zai aure boye min bata fada min ba ta bari ina wanan hauka ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[10/25, 8:14 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊1️⃣0️⃣0️⃣🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Da gudu Amira ta karaso ta dauki wayan daketa faman tsuwa misalin karfe tara da rabi na safe a lokacin mahaifiyar nasu nadaki tana sallah wahal data soma.

Waye ta juyo tana tambayan Amira din ummah hannece taba uwar amsa tana mika mata waya a lokacin gabanta ya fadi rasss.

Izuwa yanzu zaman darrr ya kare gareta don tasan labarin abinda ya faru ta samu yasa ta kirata tahi mata tass a waya.

Tasan halin yayan nasu hannen da izglanci da tijara idan idonta ya rufe komai tana iya fadawa mutum a lokacin game da cin mutunci haka rayuwanta yake ita.

Amma ba yadda ta iya dolene ta daga wayan yar uwar nata a lokacin don taji shakuwanta na dalilin kiranta a wanan lokacin don haka ta karbi wayan tana karawa a kunnenta don yarta ta rigada tayi receive din call din ko a lokacin.

Assalamu Alaikum yaya hanne an tashi lafiya abinda ta fada ke nan a lokacin ga yar uwan nata bayan ta karbi wayan .

Wai hauwa zancen nan da nake ji gaakiyane ko wasan yan zamaninan da sukeyi a waya yanzun nan nake ji wai Aliyu yayi aure kome nace hakan ba gaskiya bane meye gaskiyan maganan nan ne ?

Wallahi yaya hakane yadda kikaji din nan haka naji nima yaya dasu Alh sun daura me aure a jiyan nan ashe da wata yarinya yar unguwar mu.

Dakata hauwa gaskiyane ko karya shi nake son in sani in kuma ji daga bakinki a yanzu a sanyayye ta sake fadin gaskiyane yaya an daura me aure jiya.

Lalai sai yanzu nagane zancen da hausawa ke fadin dan gado baya kama da dan nagadane yanzu shi Aliyu har yayi matsayin da zai gujewa tsarin mu ya kai iyayyensa maza su daura mai aure da wata ?

Waima tsaya yar gidan uban waye a kanon nan aka daura auren da ita haka don da gani ba wata tsiya bace irin jama,an dana gani a wajen taron.

Yar gidan ubantane don nima bansan ainihin ko yar gidan waye ba abinda na sani dai shine itama yarinyar a can lagos suke zaune ba a garin nan ba ?

Sai yanzu nagane ai kice min abokiyar shashancinsa ce yarinyar daya aura saboda sakaci da rashin wayau irin naki hauwa har kika bari haka ya faru da yaron nan bayan kinsan irun shirin da mukeyi a kanshi .

Har kika yarda ya dauko muna bare ya hada a cikin mu ga yar uwarshi itama mace ce ta yarda da tsarin mu balleshi namiji don wauta kin kasa shiga gaban daki zaki bari wasu su shige maki gaba a yanzu.

Wallahi yaya ba yadda banyi ba amma Alh yaki ban hadin kan hakan wai sai inda yaron nan keso shima ra,ayinsa ke nan har yana kokarin hadani dasu yaya akan na nace ga abinda nake son ayi.

Su yayan me can su yaya ubankine ko haihuwanki sukayi su tsaya mana ga yayansu suyi iko dasu kece duk kika bata tsarin nan keda danki.

Nace ki turo min Aliyun tun farko in zaunar dashi in fada mai abinda nake so kinki hakan saidai inji ya shigo garin nan ya fita ni zai nunawa ujila kafin ya shigo system ai mijina ya fara shiga nasan yadda abin yake kafin shi.

Zanje in samu yaya akan zancen don me zasu dinga shiga mukna harkan mu mubamu shiga tasu ba suna hana muna ruwa gudu a cikin lamarin mu.

Dolene su sakashi ya auri Fadila kafin tarewan yarinyar nan don bai fi karfin mu ba ai shi yaya irin jahilcin nan nasu yake son ya kawo muna kome ?

Ta yaya gida bai koshi ba za akaiwa waje basu tsayawa suyi tunane akan abu sai su affakawa mutane cikin lamarinsu su bata abu sun dauko wata diyar matsiyata sun aura mashi aure haka lami ba wanda ya sheda cewa Aliyu yayi aure a garin nan kamar auren kurama kamar Aliyune zaiyi irin wanan auren a dunkule ?

Ki fada mashi yazo ina neman shi ya tabbatar da yazo garin nan kafin ya koma in jaddada mashi akan zancen auren Fadila yaji daga bakina ?

Ta amsa da to yaya yanzun nan zan kira Yusuf in fada mashi suje gidanki kina nemansu wani yusuf kuma ai kinji matsalan ki hauka da rashin wayau don me zaki kikira wani Yusuf can keda da danki kada ki saka min wanan dan banzan yaron a cikin zance na.

Yusuf fa namu dan wajen,,,,, nace dake kada ki saka minshi a zance yaron da ya iya munafuncin ina da labarinshi sarai ai nasan Aliyu bai iya bai iya numfashi idan ba yusuf a kusa to duk wanan abin zan maganace shi ni ba a kawo min irin iskacin nan a lamarina ni zai nunawa zumunta kome ?

Kinji na fada maki ki turo min Aliyu din nan yau din nan ina son ganinshi a yau zanyi magana dashi ta amsa da to suka kashe wayan tasu.

Ajiyan zuciya ta sauke tana fadin dama nasan yaya laifina zata gani a zancen nan gashi kuwa tana kokarin dora min laifin bayan anfi karfina a cikin zancen ?

Tsayama ta kara dauko wayan daga gefenta ta dannawa dan nata kira akai sa,a yusuf ne yadaga wayan yana gaisheta yace gwaggo mai wayan ya shiga wanka yanzu.

Idan ya fito kace nace dashi duk abinda yakeyi kuje gidan yaya hanne yanzun nan tana neman ku ya amsa da zamu insha Allahu yau din gwaggo.

Sai bayan yafito ne yake fada mashi sakon mahaifiyar nashi ya dago da mamaki yana kallon dan uwan yace gidan hjy hanne muyi me kuma akan me zan tafi can din kuma ?

Umurni aita bamu bai kuma zama dole in kaje ka dauki zancen da zata fada ma din ba ai kawai muje tunda ita gwaggo tace aje din ka nuna kai mai biyayyane ga mahaifiyarka.

Kada kayi mamakin itama ta takura mata dinne a hakan kasan halinta daba da umurni don dole a binta kuma hakan da yusuf ya fada yaji yana son zuwa gidan lokacin yace idan mun fita mu fara biyawa can din tukun .

Sai kuma ga wayana nakirashi ina labarta mai abindaya faru tsakanin mu da yaya murja a daren jiya duk da yayi min fada kamar yadda baba yai min shima amma kuma yayi ra,ayin aiwa abin iyaka damu wanan yasa suka nufi police station a lokacin suka bada kudi aka kamo yan group din nasu wanda yaya sahurace ta bada sunayensu a asirce.

Bai samu zuwa gidan ba sai bayan magariba ya tafi inda suka tura ace suna waje suna sallama nan tahau


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login